Ɗaya

1.9K 138 39
                                    

👹 KURURUWAR SHAI'DAN👹
   ©Ummu Abdoul 

Sadiya Ahmad Ibrahim,matar aure ce wacce a k'iyasance zatayi shekaru uku da mijinta Sa'ad Bashir. 
  Auren soyayya sukayi,a yanzu haka su na da yaran biyu twins,Hanif da Hanifa. 
     Al'ardar Sadiya ce, matukar mijinta baya gida,yara suka tafi makaranta,tana kammala gyaran gida ba ta da wani aikin yi sai chatting. Itace Facebook can kuma ki tsinto ta a whatsapp. Karatun novels da shige shige kadai ta saka a gaba. Tana da son bincike akan dukkan abinda tasan zata k'aru dashi na fannin rayuwarta. Sau da dama idan ta danna wajen search ta soma rubuta harafin 'Sa' wato 'S' a turance,tun kafin ta kai ga kammala rubutun,shafukan da dama sun bayyana,don daman zab'in da ta bawa inda search dinta zai mik'ata fannin Pages ta zab'a maimakon groups da people da ma sauran zab'uka. 
     Sau da dama takan ga shafuka na b'atanci da hotuna marasa tsari ta wucesu. Duk da sau da yawa takan ji zuciyarta na raya mata ziyartarsu. Yau da gobe a cikin wani group da take na k'aruwa ta mata zallah,aka samu wata hatsabibiyar da ta tallata wani shafi na mata masu mad'igo bayan da ta aiko k'aramin labari marar tsari ko kad'an inda  ta nuna jinsi d'aya suna aikata masha'ar. Labari ne mai cike da shaid'anci wanda idan na Allah ne Ya tsare imaninka ba,babu abinda zai hana ka jin sha'awar abin. 
   Muskutawa tayi tana k'ara karantawa,inda a karshe aka yanke labarin aka ce mai son k'arashen ya bud'o shafin,tsaf ta rik'e sunan shafin,kafin kuma a kwashi mintuna ashirin,ta ga an goge post din. Anan ta ga wata wacce ta kasance d'aliba itama a gidan,tayi post tana faman yin addu'ar shiriya ga wannan hatsabibiya har tana ikrarin barin gidan matuk'ar shuwagabannin ba zasu takawa lamarin burki ba. Acewarta ba sau d'aya ba ba sau biyu ba,'yar iskar yarinyar mai suna Binta Zuma tana aiko da wadannan labaran banzan da tallar shafuka marar amfani. Ita kam in har baza'a cireta ba to zamanta a gidan ya k'are. 
     Kafin kace me,nan mutane suka hau (comment)suna goya mata baya ciki kuwa har da Sadiya inda tace "Gaskiya kam."
   A k'arshe admin ta fito ta bada hak'uri ta tabbatar an cireta. A karshe ta goge post din matar nan. 
   Sadiya ta numfasa,jikinta gaba d'aya a mace. Ta kasa mance labarin da ta karanta,har hangowa takeyi gashi a zahiri ana aikatawa. Ta nanata sunan shafin,da sauri ta bud'o b'angaren bincike ta rubutashi,nan take shafuka masu sunayen suka fito,wasu ana ganin abinda akeyi ciki wasu kuwa ba'a gani. Hankalinta yakai ga wani wanda hoton dake kan sunan shafin kansa ba abun arziki bane. Don kuwa,wannan jinsin dai d'aya ne na mata,suke alfasha aka d'auki hoton babu ko sutura jikinsu. Ta murza idanunta wad'anda taji suna yi mata wani iri,hannunta har rawa yakeyi ta danna ta shiga shafin don ganewa idanunta. 
    "Tab." Shine furucinta ganin irin ashararancin da akeyi,ganin yawanci duka posts din da sunan Binta Zuma yasa,anan ta ga ragowar labarin,nan tayi ta bibiya tana karantawa hankalinta yana k'ara barin ta. Batayi magana ba ba kuma tayi liking komai ba,ganin yanayin zai yawaita gareta tayi azamar sauka daga Facebook ta kashe data. 
   Sai lokacin ta tuno da gangancin da tayi,ta hau istigfari. Sadiya haka dao ta wuni amma labari da hotunan sun gaza ficewa a kwakwalwarta.

Kururuwan Sheɗan Where stories live. Discover now