MASU DUNIYA
Na
Waliyya MuhammadDis page is for u my panda, my tawan Nan Maryerm sa'id. Allah barmu tare!
10~15
"mutum ce ko kuma Aljanah" ya raya aransa. Taku biyu yyi ya k'araso inda take a durkushe fuskanta a tsakiyar cinyoyin ta idanun ta baza su iye jure hasken touch light din wayar sa ba.
Da ganin ya matso ta tayi wuf ta mik'e tana kokarin barin gurin. Bai ce da ita komi ba sai ido daya bita da shi ya Ciro wayar sa a aljihu ya shiga Neman Jo a waya, ko minti biyu ba'a yiba yazo ya bud'e kofar dake jikin gate din har zuwa wannan lokacin bata fice daga gun ba.
"Ina ka ajiye kunnen ka da baka ji ana knocking ba?"
"Kayi hakuri yallab'ai ruwan sama ya hana ni ji"
"Saboda akan ka ake ruwan ba"
"Sorry sir" Jo ya fad'a yana sosa kai
Ya juyo ya kalleta suka had'a ido tayi saurin kawar da kanta alokaci guda kuma ta juya da sauri zata bar gurin
"Ina kuma zaki je?"
ta tsaya cak ba tareda ta juyo ba bare tace uffan, ganin haka yasa shi shige wa ciki abunsa.
A falo ya tarar da mom da Daddy sai yar'auta dake rawar shoki.
"Kwaso ! Kwaso shokin mana da kyau mana" cewar mommy cikin yanayin wak'a"Wai Ashe haka yar'auta na ta iya rawa, nima toh zaki koya min" daddy ya k'arba.
Mom tayi dariya tana tafa wa yar'autan ta wai ahaka tayi abun burgewa, ji yyi kamar yyi ihu dan haushi wai ace iyaye da Kansu ke daurewa 'ya'yan su gindi gurin lalacewar tarbiyya su all in d name of waye wa da bawa yaro freedom. Yaja wani d'an guntun tsaki kana ya k'araso cikin falon with his usual looks.
Daga k'asa ya zauna ya gaishe da daddy ya amsa fuskarsa dauke da murmushi kana yace
"My son daga ina? Naji ka shiru tun shigowa ta"
"Uhm ina masallaci ne daddy""Shine ka jima haka my son sallahr da bai wuce ayi shi cikin minti uku ba ko kuma zaman masallaci ka fara ne smy son dan yanxu uztaz naga ka dawo kuma kuma social uztaz ne?" Ya fad'a yana yar' dariya.
Wani murmushin takaici ya sakar kana yace "Mun tsaya had'a sallahr maghrib ne da Isha'i saboda ruwan sama ""okay, ni kaga tunda na dawo ma anan na jibge I'm so tired Muna can nida dan'uwan ka Khalid Muna ta abubuwan zab'en nan Kasan nan da 2 weeks ne, sai na shiga zan had'a nayi Kawai sai na kwanta"
Ya d'aga kai yana kallon daddyn nashi a cikin zuciyar sa kuwa yana mamakin hali irin na mahaifin sa. Ba daddyn shi ba, ba mom dinsa ba, ba kuma kannen sa ba wurin watsi da ibada sunyi sake da addini wannan Abu yana matukar damun Hamdaan, anya ma kuwa shi jinin gidan ne dan kwata2 halin shi yayi daban da nasu.Murmushi kawai yyi ya mik'e Zai fice "My son a kawo ma abinci ne?" Mom ce ta jefo masa tambayar
"A'a ba yanxu ba"
Ya bata amsa murya can ciki ya wucewar sa yana watsa wa Nana harara amma ko ajikin ta ganin su mom da dad agurin. A stairs suka ci karo da Khalid kunnensa sanye da earpiece yana kad'a kai, hannu kawae ya iya d'aga wa wan nasa saboda santin music din da ya dage yana bi.Harara ya jefe shi ya wuce d'aki, har ya sa k'afar sa d'aya ciki ya juyo muryan ta kamar daga sama wannan yasa shi dawowa baya yyi k'uri daga sama yana kallon ta, ta durkusa a gaban mom tana kuka sosai.
"Hajia ummah na ne ba lafia dan Allah ki taimaka a kai ta asibiti wallhi ko motsi bata yi" tana maganan ne cikin muryan kuka
"I thought ma mutuwa tayi yanda naga kin fad'o mana falo haka" Khalid ya fad'a idon sa tsam akan ta.
"Yi hakuri bar kukan nan haka, Salamatu sallame ta dan Allah kukan nan nata na damuna Kinsan banason hayaniya" dad na kai wa nan ya tashi ya shige ciki abun sa."Ba abunda Zai samu umman ki, kinji ko Nabiha jira ni ina zuwa yanxu"
Mom ta fad'a kana ta mik'e ta wuce ciki kasancewar dakin su ita da dad a k'asa yake na yaran ne a sama hakan yasa bata ga Hamdaan da yyi tsaye agurin ba.
Ta fi minti 15 tana durkushe agurin, mom shiru Bbu labarin ta Khalid kuwa sai wak'ar sa yake ko ya kula, abun duniya duk ya dameta ga dare yana yi ta d'aga kai ta kalli katon agogon dake mak'ale ajikin k'ayataccen bangon falon da aka yi masa wani design mai kyau da daukan hankali. Karfe 8:30 da rabi na dare, ta sauke wani numfashi zuciyar ta na k'ara tuna mata halin data bar umman ta aciki, ganin mom bata dawo ba ga dare yana k'ara nisa yasa ta mike jiki a sanyaye tayi hanyar barin falon...
Har ta kusa cimma ga bakin gate ya k'ira ta "Nabiha" ta tsaya cak kamar an daure mata k'afa, a hankali ta juya tana kallon shi, yana tsaye daga bakin motar sa. "Shiga muje" yyi mata nuni da kofar motan da tuni ya bud'e murfin. Ba tayi masa musu ba duk dama bata San inda maganar shi ta dosa ba, damuwa yasa bata fahimtar komi kamar ma she is not in her right senses.
A kofar gidan su yayi parking kasancewar gida biyu ne kawai a tsakanin su, yace taje ta fito da ummah su kai ta asibiti, da gudu ta fad'a cikin d'an madaidaicin gidan nasu ba'a jima ba suka fito da ita, ita da Maryam k'anwar ta mai bin ta. Ya fito ya bud'e musu kofar baya suka sa ta ya shiga ya ja sai Annur clinic.Mom ne ta dawo falon tana tambayar Nabiha, Khalid yace ai ta jima da tafiya ta tab'e baki Kawai tayi ciki abun ta.
A hankali ta tura kofar d'akin sa ta shiga hannun ta dauke da tire din abinci, abunda ya bata mamaki shine babu kowa a dakin, ta ajiye abincin ta murd'a handle din kofan toilet amma a bude alamar Bbu kowa aciki.
"I wonder inda yaya ya tafi kuma dis nyt, am sure naji muryan sa a falo d'axu shi da su mom" ta raya aranta.
Bata so haka ba, amma haka ta fito ta tura masa kofa zuciyar ta Sam Bbu ddi dan bata da wani routine kamar zuwa taga yayan ta every nyt before tayi bacci, duk da kuwa baya wani sake mata dan bata yin abunda yakeso but still sai ta kirkiro abunda Zai sa tazo ta ganshi kafin ta iya bacci.Falo ta sauk'o ta tarar da Khalid yana PS (game) "Ya Khalid plx kaga yaya Hamdaan?"
"Kin bani ajiyar sa ne, duba d'akin sa mana" ya bata amsa hnklin sa akan abunda yake yi."Na duba baya nan" ta fad'a cikin muryan shagwab'a
"Plx Safiyya don't disturb me, ban Sani ba naga dai kamar ya bi bayan yarinyar nan"
"Wace yarinya kuma?" ta tambaya da mmki a fuskanta
"Nabiha ce ko me sunan ta, 'yar mai aikin ku dai tazo wai uwar ta ba lafia"
"Toh yaya kuma me had'in sa da issuen su"
"Ya je taimaka musu mana Kinsan yayan naki da tausayi" Khalid ya fada yana shirin barin falon...
Ji tayi wani Abu ya tsaya mata a wuya, wani haushi da tsanar Nabiha ne ya sake dirar mata, taja wani dogon tsaki ta haura sama.
*****
Da taimakon Allah zarah ta isa gida dan kuwa a buge ta ke, wurin wuraren Karfe 1 na dare ta zube akan lumshasshiyar royal cusion din dake tsakiyan fakeken falon su. Har zuwa wannan lokacin daddyn ta na falo yana waya da mutanen sa akan zab'en su. Cikin muryan tace "Da-da-daddy har ka dawo ne"
"Haba my princess me hakan, banason kina yin dare sosai a waje fa mussamman yanxu da abubuwan zab'en nan suke k'ara matso wa kuma Kinsan inada 'yan adawa dayawa, u are not safe out there wannan yasa na had'a ki da body guards amma Sam bakya jin magana, plx my baby stop staying out this late u are all I have""Yesss da-daaddy, bazan sake ba" ta fad'a tana kkrin tashi amma sai d'im kake ji a k'asa.
Daddyn da kan shi ya tallafa mata zuwa d'aki kana ya tura mata kofa ya fita. Cikin Daren nan amma haka ya fito yayi ta can bayan garden dinsu hannun sa rik'e da wani damin kullin tsumma...
Wally.
Wattpad@waliyyaMoraq
I love u all a million times