MASU DUNIYA

35 2 0
                                    

                  MASU DUNIYA
                           Na
             Waliyya Muhammad

Bazan tab'a mantawa daku ba k'awayen rai da rai, dis page is for u MADUGU'S GIRLS in honour of d sweet funny moments we spent together in school...I miss u girls.
   #TeamAnatare

15~20.

Suna isa Annur clinic nurses suka k'arbi ummah nan aka shiga da ita dan bata taimakon gaggawa saboda numfashin ta da yake kkrin tsaya wa . maryam kam kuka sosai ta shiga rerawa ganin halin da umman su ke ciki. Daga can gyefe ya tsaya yana kallon su, inda Nabiha ke ta lalashin maryam wacce ta d'aura kanta bisa  cinyar ta. Tana d'aga kai suka had'a ido tayi saurin kawar da kanta tana kkrin goge kwallahr data buya a ramin idon ta, karfin hali Kawai takeyi amma sauran kad'an itama ta fashe da kuka toh amma idan tayi kuka waye Zai lallashe ta ita.
  
"Indeed, dis girl is strong" ya raya aransa, wani tausayin sune ya dirar masa alokaci guda, ji yyi kamar shima kwallahr Zai yi yasa hannu ya murza idanun sa kana yasa kai ya fice daga cikin clinic din zuwa motar sa nan yayi zamar sa. Maganar su da mom ya tuna, ya d'aura kansa bisa sitiyeri tunanin sa shine ta ina Zai fara, tunda ya rasa fatima Sam yaji Bbu so aransa. Itace macen data sace masa dukkan zuciyar sa da gangar jikin sa kuma a k'arshe ya rasa ta wannan yasa kwata2 baya jin sha'awar sake cusa soyayyar wata 'ya mace aransa yanxu ga mom kuma ta tsaya mai da yyi aure.
  
  Fitsararriyar yarinyar nan ta SAN HUSSEIN ne ta fad'o masa a rai, ya wani ja dogon tsaki Sam wasu 'yan matan basu da kunya da tarbiyya. "I have to take my time in choosing a wife, mace me tarbiyya da sanin addini wacce zata kasance uwa ta gari ga ya'ya na" wannan karon a fili ya fad'i maganar kamar shi da wani.
  Sake fitowa yyi daga motar ya koma cikin clinic d'in. Yana shiga nurse din tana fitowa daga d'akin da aka ajiye ummah, kai tsaye ya nufe ta nan ya shiga jero mata tambayoyi akan lafiyar ummah, yanayin fuskanta ne yasa jikin shi k'ara sanyi akaro na biyu ya sake tambayar lafiyar ta. Tayi d'an Jim kana tace "I'm sorry we lost her"  Wani Abu Mara misali yaji a zuciyar sa, duk shekarun da ummah ta d'auka tana aiki a gidan su baya wani shiga sabgogin ta mussamman daya kasance ba mai yawan magana ba amma ya bata wani matsayi na daban a zuciyar sa, lura da yanayin ta ya fahimci cewa mace ce mai rik'o da addini da yawan fara'a sau da dama yana ji tana Yiwa su Safiyya magana akan sallah, duk da kuwa suna yi mata rashin kunya da cin mutunci amma ko kadan bata tab'a gajiya da yi musu nasiha ba.
   Kwalllahr daya yita rik'e wa ne ya zubo yayi saurin goge wa ya na kai duban sa ga su Nabiha da suka had'a wani uwar  tagumi daga inda suke zaune...ba abunda ya iya furta wa sai "innadillahi wa'inna ilahir rajiun"!

"Take heart kai babba ne, kai zaka lallashi k'annen ka ayanxu bcos they will need u now fiye da kowani lokaci arayuwar su" tana kai wa nan ta wuce, Nabiha ce ta tashi da sauri zata bi bayan ta jin ya k'ira sunan ta yasa ta tsaya wa ta juya a hankali kamar Mara jini a jiki tana kallon sa sai kuma ya kasa cewa komi alokaci guda kuma ya kawar da idonsa akanta.

Bai Ankara ba sai ganin su duka yyi a gaban sa , ba tareda ya furta musu komi ba suka fahimci abunda yake faru wa saboda yanayin sa ya nuna. Maryam ce ta shiga rera wani sabon kukan ba kakkauta wa, Nabiha ta jawo ta jikin ta tana lalashin ta amma ina kukan yaci karfin ta, ta kwace kanta ta koma can gyefe ta had'a kai da bango tana cigaba da kukan ta wannan yyi matukar tab'a zuciyar Hamdaan saboda mutum ne mai tausayi kuma bashi da wani tashin hankali kamar yaga mutum na kuka mussamman 'ya mace.

Nan tayi durk'usau ta had'a kai da gwuiwa, ji take kamar ta Kurma ihu, rayuwar su da umman sune yyi ta dawo mata, bayan Allah basu da kowa sai umman su dan tun rasuwar Abban su 'yan'uwansa sukayi watsi dasu, ba abunda ya saura musu na daga gado sai d'an gidan su da suke ciki ayanxu. Ummah ce gatan su, daga d'an kudin aikin wanke2 da take yi suke samu su ci har a biya wa maryam da Umar kud'in makaranta. Maryam na ss3 yanxu zata zana paper inda Umar ke aji  biyu a sakandiri ita ko Nabiha ta gama secondary tun Abban su nada rai, rashin Wanda Zai d'auki nauyin ta zuwa jami'a yasa ta hakura da karatun take talle dan ta taimaka wa umman su da hidimomin gidan.

"Ki daina kuka, ayanxu addu'ar ku ummah tafi buk'ata Allah yaji kanta yasa mutuwa ta kasance Hutu agare ta"  jin muryar sa daf da kunnen ta yasa tayi saurin d'aga kai sai ganin shi tayi a durkushe agaban ta, hakan yasa taji wani iri ta d'an ja baya Sannan cikin raunaniyar murya tace
"Ba kuka nake yi ba kuma ma bazan tab'a yin kuka ba saboda bashi umman nah take buk'ata ayanxu ba hasalima addini yyi mana Hani da haka, tafi buk'atar addu'a ta shine abunda kadai abunda zan iya yi mata ayanxu Allah ya jikan ki ummah na yasa aljannah ce makomar ki" ta k'arashe maganar cikin muryan kuka amma kuma ko kad'an Bbu hawaye a fuskanta. Ta sake had'a kai da gwuiwa tana sauke numfashi mai sauti...

Rashin kukan ta yyi matukar bashi mamaki , gaskiya bai tab'a ganin yarinya ashekarun ta na yanxu mai tawakkali irin haka ba.
 
"Dan Allah kiyi kuka ko zaki ji sauk'i a zuciyar ki, rashin kukan na iya miki illar" ya rad'a idon sa tsam akan ta

"I won't! Bazan yi kuka ba nace maka" amma ina sai data fashe da kuka mai sauti, ko kadan bai nemi  hana ta ba duk da kuwa wani b'angare na zuciyar sa yaso yin haka dan he hates it wen a woman cries,  sai data yi mai Isar ta Sannan tayi  shiru. Tana d'ago kai ta sauke akan jajayen idon sa, hanky taga yana mik'a mata tasa hannu ta karb'a kana ta goge hawayen daya wanke mata fuska Sannan ta mayar masa.

"No, keep it... Ku shirya na mayar da ku gida dare yyi gobe da safe sai mu dauke ta zuwa gida dan ayi mata sutura"
    Bata ce dashi komi ba tayi gaba, maryam kam Sam tace baza ta tafi ba sai dai abarta ta  kwana agurin, sai data ga ran yayar ta na shirin b'aci Sannan ta hakura suka wuce.

Daren ranan Nabiha bata rintsa ba ko kad'an damuwar  duniya duk yabi ya ishe ta ,yanda rayuwar su Zai kasance take tunani amma idan ta tuna akwai Allah sai taji d'an sanyi aranta.
    Daga b'angaren Hamdaan ma haka abun take ya d'au lokaci mai tsawo yana tunani, yanayin da zasu kasance aciki Kawai yake tunani....

*****
Sai Karfe 1 na rana zarah ta rintsa, tana tashi ta fad'a toilet ta watsa ruwa kana ta fito  cikin usual dressing din ta wato Riga da wando, ko kadan bata bi ta kan sallolin da ake binta ba ta sauk'a ka. Mommy ta tarar a dinning da Walid zasu ci lunch, Mairo na kokarin serving dinsu.

"My sweet mommy and cute little bros" ta fad'a tana murmushi
 
"Yes big sis" Walid ya amsa mata kana ya cigaba da cin abincin sa

"Ke baza ki tab'a chanja hali  ba koh?!
Mommy ta fad'a ranta a b'ace amma ko kadan hakan bai damu zarah ba, cikin muryan shagwab'a tace " haba momma mai kuma nayi yanxu, u always blame me, wallahi daz why nake yin daddy"

" Hmm Bana ganin laifin ki ko kadan sai ma laifin shi daddyn naki daya daure miki gindi kike duk abunda kika ga dama, wai ace kullum ke bakya dawo wa gida sai dare yyi nisa kuma ki dawo cikin maye, wannan takaici da me yyi kama"

"Ni dama ba'a wani so na agidan nan, anfi son walid" ta fad'a bayan ta kai lomar abincin da Mairo ta zuba mata.

"Kinsan dai yanxu daddyn ki ya tsaya takarar gwamna a garin nan kuma by all indication Zai ci insha Allah so ppx don't do anything that will tarnish his image kin ji koh?"

Bata ko amsa ba ta cigaba da cin abincin ta hankalin ta a kwance.
Tana gamawa ta koma d'akin ta abunta..
  "Ya Allah ka shirya min zarah na" cewar mommy
 
"Amin!" Walid ya amsa

Murmushi Kawai mommy tayi "wai ace yaro d'an shekara goma har ya fi zarah hankali da nutsuwa ita da take Neman shekara ashirin da uku a duniya" mommy ta raya aranta tana kuma k'ara addduar Allah ya shiryar mata da yar'ta.

*****
Tana kwance bisa gado, Hasim ne ya fad'o ranta tayi wuf ta tashi ta d'auko C.card dinsa nan ta shiga saka numbar dake jiki a wayan ta, tayi dialing ringing na farko ya d'auka daga b'angaren sa yace

"I have dis feelings that it is that beautiful damsel zarah MB on d line"

Sautin murmushin ta Kawai ya iya ji kana ya cigaba
  " No smile is beautiful like urs, dan Allah ki Kar ki tsai  da murmushin kin nan dan yana sanya nishad'i"

Akaron farko tace " How did do u know that i smiled Ko dai kana kallona ne?

"Na Sani do u wish to know how, saboda inada hoton ki acikin zuciya ta"

Wani dariyar jin ddi ta sake, Hasim yayi mata, bayan gashi d'an gayu gashi ya iya magana...nan ta sake suka cigaba da hirar su kamar wasu masoyan da suka jima a soyayya bayan yayi mata tayi soyayyar sa kuma ta amsa nan a take.


Vote wally @wattpad waliyyamoraq
   

MASU DUNIYAWhere stories live. Discover now