INDA RANKA... KASHA KALLO

8.4K 443 4
                                    

*😳INDA RANKA....😳*

Billy Galadanchi

HASKE WRITERS ASSO.

Wannan littafin kacokam na sadaukar dashine ga Kawar Alkhairi kuma babbar Aminiyata *CUTEST ZARAH BUKAR*

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai,ina roqon Allah yabani ikon rubuta Alkhairi abinda zai amfaneni duniya dakuma lahira yakuma Baku ikon daukar darussan dake cikin wannan littafin Ameen...

Vote me on wattpad@68Billygaladanchi
01

Zara zonan! Ta fada a tsawace cikin Isa dakuma nuna cewar itadin yar wanice kuma ta Isa da zaran,mikewa zaran tayi cikin mutuwar jiki dajin zafin Abinda Aina tamata agaban friends d'inta taje dab da motar ta tace "gani Aunty Aina" wani mugun kallo ta wurga mata sannan ta dauke kanta ta mayarda dubanta zuwaga sitiyarin motarta sannan tace cikin daga murya

"Dan uwarki zarah kan nabaki kayan jikin kinnan ya mukai dake? Ban sanar miki karki kuskura ki shigo dasu jami'a ba?" Langwabe kai zarah tayi hawayen datake kokarin rikewa suka zubo ta furta cikin dacin rai

"Aunty Aynah duk kayana dana wanke ruwan Sama ya gama jiqasu ba yanda na iya dole na saka wannan gashi inada test dole nazo school" tabe baki tayi sannan ta manna uban shade a fuskarta daya kusa cinye Rabin fuskar ma tace tana mai bawa motar wuta

"Mintuna biyar idan baki bar jami'a annan ba wulakantaki zan wlhy"

"Aunty Aynah dan manzon Allah kimun rai wlhy test zanyi yanzu ina gamawa zan wuce" wani hatsabibin murmushi tayi sannan tace tana mai taunar cingam dake bakinta

"Hmm zarah kenan,kinsanni sarai idan nai hukunci bana sauyawa saidai na baki option, koki Koma gida yanzu kokuma idan kin zabi yin test idan kin kammala kije gida da kafa" da sauri ta 'dago ta kalle ta ce

"Kiyi hakuri Aunty Aynah yauma Na tashi da ciwon kafa da hannu sakamakon ruwan da aka tsula jiya" cikin fusata tace

"Zarah! Amma kinsan bana sauya hukuncina ko? Kuma Sanin kanki ne bana hakura idan nayi niyya saina yi,sabida haka kizabawa kanki wacce zata fiddaki"tana kaiwa nan tafigi mota tayi gaba abinta,sarai kawayen zarah sunji me take cewa amma sabida su sassautawa kawarsu wannan tozarcin sasukayi kamar basu ji komai ba,jiki a sanyaye tazo ta zauna a mazauninta tana nazarin handout dake hannunta babbar kawarta Jidda ce tace da ita

" saura mana mintuna biyar zarah muje lecture hall kawai" kallonta tayi ido cikin ido ta rausayar dakai sannan cikin dashashiyar murya tace

"Muje" a takaice sosai jiddah ta fahimci ran kawarta a jagule yake wannan ne ya sanya taja hannunta sukayi wa sauran kawayenta sallama kan cewar saisun karaso,suna cikin tafiya suka hadu da Aynah da Kawar ta khairi suma zasuje nasu lecture hall din wani gwatsine fuska khairii tayi tasha gabansu batare da wani tunaniba ta wanke zarah da lapiyayyen Mari sannan cikin isa ta nuna da d'an yatsa

"Wato ke tsabar jahila ce sabida ace kuna sharing kaya da Aynah dimples shine kika sako kayan data gama yayi kika shigo jami'a ko? Dan babarki dimples sa'ar kice koso kike kice sabida kuna amfani da sunan uba daya kedin daya kike da ita,to bari kiji wlhy kozaki mutu test dinnan bazaki yishiba banza jaka gida zaki Koma ki sauyo kaya" dafe wurin da aka maretan tayi cikin mutuwar jiki tana zubdah kwallah tace

"Aunty khariyyah kiyi hakuri lokaci yarigada ya kure baifi mintuna biyar ashiga test dinba ina kammalawa zan wuce"

Shaqo wuyan rigarta tayi tace "ke kin isa ina fada kina banza dake yar kauye jaka mara usuli wlhy sai idan kin canjo kaya zaki Shiga lecture hall din nan" kuka tasaka yayinda kawarta jiddah ta sha gaban khairi cikin fusata ta furta

"Ke dinan baki isa kin hanata rubuta wannan test dinba wlhy indai ina numfashi saita rubuta kuma bazata je gidan canjo kayanba kune jahilai dabaku San girman mutane ba kuma wlhy karki kuskura Ku kuma marinta bakauya kawai" sororo sukayi suna kallonta yayinda ta figi hannun zarah dake rusa uban kuka sai hall din,a daddafe aka karasa test din domin kuwa zarah dakyar tayi question biyu acikin ukun,tana fitowa direban dake daukarta na karasowa sallama tayiwa jiddah tashi ga motar yana shirin tashin motar Aynah ta iso wurin ta dakatar dashi ta rike kugunta da hannayenta duka biyu ta murtuke fuska sannan ta furta cikin isa

"Zarah ya mukai dakene dazu? Ban sanar miki idan kika kuskura kika rubuta test dinnan ba a kafa zaki je gida?" Shiru tayi banza da ita bude murfin motar tayi ta fincikota iya karfinta ta wullah ta waje tafadi a wurin har tana buga goshi da dutse a take goshin ya fashe sai jini,ta kalle ta tace

"Zangani idan da albashin aikatau da uwarki keyi ana biyanta aka hada aka siyi motar nan kaikuma tanko idan kanaso kaci gaba da aiki a gidanmu inga ka bar nan yanzu" Jan motar yae yayi gaba abinshi,ita kuwa tana shewa tabar wurin yayinda daukacin mutanen dasuke wurin ke la'an tarta a haka jiddah tazo ta sameta da sauri tayi kanta,aikuwa tafada jikinta tana kuka,mota jiddah ta janyo kirar Mercedes Benz hadaddiya ta taimaka mata sukaje chemist aka mata dressing wurin daga nan tawuce tayi dropping nata a gida ta wuce cikin tsananin jin zafin abinda akayiwa Kawar tata....

Mom Nu'aiym

INDA RANKA...KASHA kALLOWhere stories live. Discover now