BABI NA ASHIRIN DA BIYU

2.4K 157 4
                                    

*😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

    "Abbin Muhammad gaskia da sake,wai kaga yanda Muhammad ya zauce akan mutuwar wannan zahran? Narantse maka kodani na mutu iyakar kukan dazeyi kenan,sosai ya diririce shiyasa nace dakai asiri suka masa" kura mata ido yayi sosai yana dan nazari kan yace

"Ummie Muhammad kinada tabbacin asirin suka masa,Wata kil fa soyayya ce kurun daga indallah" dubanshi tayi ta langwabe kai tamkar Wata er sha shida sanan tace da shagwaba

"Abbi gaskia nifa hankalina be kwanta dasuba,dafarko fa gun Aynah yake zuwa er wajen Muhammad shayau,tundafa wannan matar ta kyalle ido taganshi shinefa tashiga boka da malam ta rabashi da Aynah ta cura wannan yar kuma fa kaji,cikin Shege ce ita daga bakin Mamie naji wlhy uwargidan shi Muhammad shayau din" rungumota yae jikinshi ta wani langwabe sai kace baby sannan yace

"Ummie Muhammad me kikeso ayi yanzu?" Kara shigewa jikinshi tayi wanda ba karamun narkar mai da zuciya tayiba,wanna dalilin yasanya sam ya zama mijin Hajiya sai yanda tayi dashi,sannan cikin murya kasa kasa tamkar zatae kuka tace tana wasa da gashin gemunsa dayazama 2 colour Wato fari da baki

"Abbi ni so nake duk yanda za'ayi a nemar masa auren Ayna'u kan ka koma England, kuma a tirsasashi dole ya auretan,kaga dolenshi idan akayi auren ya rabu da waccen kuma musanya amasa adua a karya asirin" kwantar mata da kanta yayi saman girjinshi yafara Shafa kitson da akai mata a hankali sannan yace

"Darling kina ganin ba matsala idan akayi masa hakan?" Wani shagwabe wa tayi hadda hawaye

"Dear kasanfa yanda nasan Muhammad, sosai nakejin tsoron wani abin ya sameshi sam bazan so hakan ba,wannan kadai zakamun ya tabbatar mun kana kauna ta" packin nata yayi a goshi sannan a hankali yashiga patting bayanta yana cewa cikin sigar rarrashi

"Kedin er gatace maryama Kisani duk abinda kikeso hakan za'ayi sabida haka Ki kwantar da hankali,sanar dani yaushe kikeson ayi auren?" Kara narkewa tayi tace

"Dear banasan a shallake 2 month duba fa ka gani har gininshi yayi kura ba mata"

"Angama darling Ki kwantar da hankalinki yau dinnan zanje Gidan shayau mu tattauna..."

   Ba kowa adakin sun watse sun bar moh da cutynsa zahra,sam takasa daga wa ba ruwanshi da su momy ko motsawa tayi saiyaje sa sauri menene?" Baccine yafara daukarshi daga kan kujerar dayake zaune ya kasa ya tsare gani yake tamkar idan ya daga wani abinne ze sameta,bude idonta tayi daga baccin datake ta kura mai ido tanason taje tayi fitsri amma tausayinshi takeji bataso ta tasheshi kuma yama za'ayi tace dashi fitsari zatayi ai abin da matukar kunya,mintuna biyu ta kara taga kosu momy zasu shigo amma sam basu shigoba shikuwa sai minshari yake bare tace dashi yanata kiransu tasani baza'a rasa wani a waje ba,drip da aka daura mata ta kalla takuma gane zata iya cireshi ta rufe wurin yasanya ta cireshi tana jin jiri haka tafara dafa bango tanabi a hankali hartaka toilet din tayi fitsarinta lapiya lau,tajuyo tafito tana fitowa tacire silifas santsin tile ya jata tazube a wurin atake ta kwallah uwar kara wacce ta farkar da Muhammad ba shiri, sannnan su momy ma suka yo ciki da gudunsu,dagata yayi yana mata sannu suka mayadda itakan gado,sai tambayoyi yake mata

"Zahrah meyasa baki tasheniba wayace Ki tashi da kanki?, mesa baki kwallawa momy kiraba,inane yake miki ciwo?" Kura mai ido tayi ya matukar bata tausayi tace,tana Murmushi

"Tsorata fa kurun Nayi ganin na fadi,amma banji ciwoba,kai baka ganin yanzu naji sauki,daka ganni nan ko wasan  tsere mukai dakai nice zanyi winning" kowa dariya ya saka momy tace

INDA RANKA...KASHA kALLODonde viven las historias. Descúbrelo ahora