BABI NA BIYU

1K 126 1
                                    

[3/12, 1:41 PM] ~Mamu gal 💞

BAKIN GANGA
By
Mamu

<<< 2>>>
***
Zaune suke a kujera mai d'aukar mutum d'aya, suna farantawa juna rai, cike da soyayya mai tsayawa a rai.
Sosai ta k'ura masa ido, wannan sajen na mijinta, ba k'aramin d'aukar mata da hankali yakeyi ba.
K'ura masa ido tayi k'irrrr, a k'alla na minti uku, ta shagala sosai da kallonsa, sai ji tayi yana hura mata iska a ido.

Firgigit ta dawo hankalinta, fuskarta cike da murmushi, ta furta masa kalma mai tsada a birnin masoya.
"I love you."
Zama ya k'ara gyara mata a jikinsa, yace "I love you too."
Har yanzu murmushi ne kwance a fuskarta, ta k'ara furta masa "I love you more." Tana lumshe ido.
Zaro ido yayi kad'an, yace "No, I love more Sweetheart.

Jin tana k'ona hannunta ne da tukunyar da take girki, yasa tayi firgigit ta dawo daga duniyar tinanin da ta fad'a, na rayuwarsu ta baya da mijinta.

Lokacin suna cikin gurzar amarcinsu, wannan Moment yak'i gogewa a brain d'inta.
Kuka takeyi sosai, idan tana tunawa da yadda mijin nata ya juya mata baya, yak'i d'aukar k'addarar da Ubangiji ya d'ora masu.

Tayi kukan ta har saida ya ishe ta, chan kuma wata zuciyar take ce mata
"ke Hamida ki rufawa kanki asiri wannan kukan zai iya janyo miki rashin lafiyar nan taki ya tashi, gashi baki da ko wanda zai miki sannu."
Ta kuma cewa
"Hmmmmmm! Lalle Ni Hamida na yarda da wannan Karin maganar na hausawa, 'NAMIJI BAKIN GANGA' ne, a ko'ina ka buga zaqi zaka ji, idan kuwa ya juye maka, sai yafi d'an kunama zafi."

Murmushin takaici ta fitar, ta juye girkinta a cikin Warmers, ta shirya komai a inda ya dace.

Ta b'ata lokaci sosai, wurin wankanta da shiryawa, ta dawo falo ta zauna, ta cigaba da kallonta, rik'e da carbi a hannunta tana ja.

Bata fi minti sha biyar ba, taji dawowar mai gidanta.
A nitse ta tashi, tayi masa sannu da zuwa, ba yabo ba fallasa ya karb'a, ya shige ciki.
Jiki a mace ta bisa har d'akinsa, wanka ta samu yanayi, sai ta fitar masa da kayan da zai saka, ta zauna zaman jiransa a bakin gado, tare da rafka tagumi.

"Bana son wad'annan kayan, kinsan duk ba su nake ra'ayi ba."
Hargowarsa ce ta dawo da ita daga duniyar tinanin da take.
"Kayi hakuri, wanne zan Ciro maka?"
Ta mik'e zuwa wurin drawer kayan sawarsa, tana tinanin, yaushe ne zata yiwa mijinta abinda zai faranta masa rai?

Da zafin nama ya tureta gefe, tare da nuna mata k'ofa.
"Fice min malama, ba abinda kika iya, baki San komai ba na farantawa miji, marar tarbiya kawai."
Da sauri ta juyo har tayi rabin fita d'akin, a gabansa ta tsaya.
"Yanzu nice marar tarbiya Hudu?"
Ta k'arashe maganar tana kuka, mai cin rai.
"Lalle banyi mamakinka ba, saboda kai ne Wanda bai San k'addara ba, har kake neman kirana da wannan suna, any way, Nagode."

Da gudu ta fice a d'akin, ta fad'a nata d'akin, Wanda suke opposite da nashi, a yau tana dana sanin auren mutum mai Hali irin na mijinta, Wanda bai San kowacce k'addara ba, mai kyau ko akasin haka, da Allah yake d'orawa bayinsa ba, domin jarabawa.

***
ASALIN LABARI.....

Don't forget to hit d star 💥 mai kalar ruwan lemu.

Mamulle🙌

BAKIN GANGAWhere stories live. Discover now