BABI NA UKU

889 83 1
                                    

[18/3/2017]

BAKIN GANGA

 By
Mamu
  

****

       <<<3>>>
Misalin k'arfe shida na Yamma (6:00pm),Tafe take sanye da Uniform na islamiya, da jaka ta rataya a kafad'a mai dogon Hannu, a natse take takonta, ta nufi hanyar gidansu. Da ka ganta kai kasan daga Islamiya ta fito.  

   Tafiya take sauri-sauri kar dare yayi mata a hanya, ga magrib na gabatowa, kawai ji tayi ruwa ya watso mata a jiki, dubawar da zata yi, taga ruwan da suka kwanta a kasan bakin titin layin su ne, wata mota ta fallatso mata a jiki.
     Ta d'aga kai ta kalli motar da ta watso mata ruwan, taga wanda yake cikin motar ya samu wuri yayi parking amma bai fito ba, yayi zaman sa yana shan AC abinshi, bin motar tayi da kallo na d'an lokaci, sannan ta ci gaba da tafiyar da take, ta nufi hanyar gidan su bata ce k'ala ba.
 
Shi kuma ganin hakan da tayi yasa mamaki ya cika shi.

     Shigar ta gidan keda wuya Mama Larai ta hau salati
  "La'ilaha illallahu ni Larai, yau me zan gani? Hamida yau kuma wasan k'asa kika koma kina yi tsofai-tsofai da girman ki? Kaicho Hamida wallahi Uwarki dai bata yi sa'ar haihuwa ba Hamida."

     Hamida da tunda mama Larai ta fara magana siraran hawaye ke ta zarya a kumatunta, dama tasan abinda zata tarar kenan.

     'Hamida cikakkiyar budurwa wacce bata wuce shekara 23 da haihuwa ba, yar asalin garin gusau ce (zamfara) mahaifiyarta ta rasu tun tana da shekaru 3 a duniya, bayan rasuwar mahaifiyarta ne, mahaifinta Mal Sale ya k'ara aure inda ya aure Larai yar mak'otansu, wadda tun mahaifiyar Hamida tana raye suke mutunci da ita sosai asali ma la'akari da hakan da Mal Saleh yayi ne yasa ya aurota, domin ta zamo Uwa a gun Hamida.

   Sai dai inaa! Larai ta zamo masa k'adangaren bakin tulu, yana gani take musgunawa Hamidarshi daya fi so fiye da komai a rayuwa, amma ba yanda zaiyi.
  Mal saleh Family, za'a iya cewa they are from a middle class family (Ma'ana su ba masu kuddi ba suba talakawa ba).

    Dai-dai gwargwadon hali yana kwatanta masu. Hamida tana da kanne biyu, domin kuwa Mama Larai ta haifi yara biyu bayan auren su, mace da namiji, Imam da Iman.
 
  "Mama wallahi ina tafiya ne wani mai mota ya watsa min ruwan dake kwance bakin titi."
   Hamida ta amsata fuska cike da hawaye.
 "To Hamida gani yayi kin masa kama da bola, ba dole ya watsa miki ruwan ba, yo miye marabar ki da bolar ne, ai ni wallahi yamin dai-dai, don wallahi da zan ganshi koda bani da abinda zan bashi zan  masa godiya, had'e da saka mishi albarka, tsinanniyar banza kawai, ni ki wuce zuwa d'ora min abinci kinji. Azzaluma shine ki kai zamanki wurin yawon iskancinki, don kar muci abinci ko? To wallahi idan zaki kai isha'i baki dawo ba ki sani sai kin dawo kin d'ora shi."

Inna Larai ta idar da fad'anta tana huci, ita a dole an b'ata mata rai.
      Da taga duk bai mata ba, Ta dauko butar da ke gefenta ta jefe Hamida da ita.

**
Do vote n comments

Mamulle🙌

BAKIN GANGADonde viven las historias. Descúbrelo ahora