RAHMA

1.5K 45 2
                                    

[8/19, 2:42 PM] Aunty Queen: *RAHMA*
       _(Daddy's girl)_

*Na*
           *QUEEN MERMUE*
_Exclusive writers forum_
        *AISHA ALI GARKUWA*
_pure moment of lyf writers_

*1*

Hayaniyar da tayi yawa ne tsakanin
Wa da k'anensa yasa yaran gidan suka fito suna kallon iyayen nasu,
Hakan yasa wata zantaleliyar Yarinya wadda bata haura shekaru ashirin ba tana dauke da tutsetsen cikin ta da yakai k'ololuwar girma, cikin yayi k'asa sosai da kaganshi kasan ya shiga watan tara,
Daga step en ta sauko zuwa falon k'asa da ake rigimar anan,
Ya Abdullahi ya kalli kanen nasa cikin tsana da haushi watsa masa tafin hannayensa tare da nuna k'anensa da hannu,
"Ko kadan baka Isa ka shiga tsakanina da mai martaba ba, kai din banza, munafika ko wane irin asiri ne uwarka ta masa akaina zai Karaya, dabba, kai har wani tsiya ne za,a bawa sarauta,! Toh Wallahi idan inada rai nine nan zan gajeshi yayinda kai kuma zan maida ka bawa a wannan masarauta,"
Kanen da aka mara wanda ya dafe kuncen, cikin tsananin bakin ciki ya kalli yayan nasa yace,
"Akan sarautar zaka mareni? Nidin? Nagaya maka Ina buk'atar sarautar? Tsakanina da kai Allah ya Isa,..."
Kafin yace wani abu yayan ya kara dauke sa da kyakyawan mari biyu,
Wannan Yarinyar mai ciki da gudun ta tazo tana Jan hannun sa,
"Dan sarki mutafi, kadaina irin fadan nan Ku kullun cikin rigima, meye amfanin sarautar, kazo mutafi mu bar gidan bana son rigima nidai,"
Cikin kuka da Jan hannun sa take fadin maganar, Yayinda Dan Sarki yaji duk jikin sa ya yi sanyi,
Ya Abdullahi ya watsa mata mugun kallon tare da cewa,
"Ke mitsitsiyar munafika! Har kin Isa kishiga wannan fadan diyar talakawa diyar bayi diyar makiyaya!"
Wannan zagin yayi mata zafi dan haka ta kalleshi Ido cikin Ido abinda bata taba yi ba, tace,
"Yaya Abdullahi Kazan rike girmanka, ni iyayena ba bayi bane, ka Kira su da talakawa amma su ba bayi bane kuma..."
Tassssss ya dauke ta da Mari, da gudu ta bar wajen ta nufi hanyar steps,
Dan sarki kuwa kallon yayan nasa yayi yace,
"Zan bar maka gidan kaci sarautar...."
Ihun matar suka ji wadda bata kai ga karasawa sama ba ta gauce ta gangaro akan step step en,
Da gudu cikin rudani Dan Sarki ya nufeta,
"Aisha innalillahi wa inna alaihir raji un,"
Cikin gaggawa ya dauke ta yayinda yaran suka kara tsagaita kukan su,
Daga ban garen da yake zuwa fita harabar bangaren akwai dan nisa, hakan yasa ajikinsa ta fara zubar da jini, cikin sauri fadawan dake yajen suka shiga salati, nan take daya daga cikin wasu securities dake gefe ya jawo mota ya nufu su,
Shikam dan sarki rungume yake da ita yana kuka, ita kuwa sai faman murmushi take tana rik'e hannayensa,
Kallon tayi cikin murmushin karfin hali, tace,
" Dan sarki na kadaina kuka, Rahma zata sauka akan mu, ka Nisanta  kan ka da mafisa, ka guje tashin hankali, ka neni Rahma ka so Rahma ka rike Rahma ka kadaita da Rahma, Allah zai baka Rahma nima yayimun Rahma!"
Cikin kuka da majina dasa hannun rigar alkyabbarsa da ta jika shakaf da jini ya goge fuska tare da kara rukenkumeta,
"Ayshana muna a tare Allah zai bamu Rahma, bazaki barni ba, zan dauke ki mu Nisanta daga masifa, zuwa Rahma, nayi miki alk'awarin wannan,"
Cikin ta ta k'ara rikewa tare da cije lips enta, nan take ya kalli drivern yana cewa ya k'ara sauqi,
Cikin lokaci kalilan suka Isa a Asibiti, nan take nurse suka turo gadon daukar maras lafiya,
Yana rike da hannunta, har suka Isa wani dakin da aka hanasa shiga,
Su kowa fadawan acan nan take wasu suka nufi fada suka sanar da waziri ciki tashin hankali waziri ya sanar da sarki, Jekadiya da wasu 'yan fada biyu Sarki ya tura suka nufi asibitin tare da fadawa shida,
To and fro yake abakin d'akin sai bayan five minutes likitan da yashiga ya fito, cikin girmamawa ya Kira Dan Sarki a office ensa, nan ya shaida masa matarshi bazata iya haihuwa ba ya cike takardun ayi mata aiki, bada bata lokaci ba aka shiga yin aikin,
Gaba dai wurin cike yake da fadawa sai salati da tazbihi suke,
Bayan kamar two hours likitan ya fito a wahalce,
Nan take D'an Sarki ya nufesa,
Hannun yaba sa tare da cewa,
"Congratulation, kasamu new princess"
D'an Sarki zubewa yayi k'asa tare da yin sujuda ga ubangiji sarkin Rahma!
Yayinda fadawan suka shiga kwadawa sabuwar gimbiya kirari tun kan su ganta,
Bayan wasu minutes aka turo Aisha zuwa VIP room enta, Jekadiya kadai ta shiga sauran suka tsaya abakin k'ofa,
Da kaganta kasan ta wahala nan take ta wani zubewa ta rame, ta fita hayyacinta,
Baibi takan 'yar ba ya nufi Maman babyn,
Baccin wahala take, nurse en kuwa bata shigo da babyn ba har saida aka shirya ta cikin tattausan kaya masu kyau,
Jekadiya ta karbi babyn tana faman kirari da yimata addu,a!
Kafin kace kwabo tuni asibitin ya dauki mutanen fada da yawa,
Aisha hours biyu ta dauka tana bacci, lokacin da ta farka D'an Sarki kawai ne adakin dan tuni an maida Babyn a falo da yake acikin dakin,
Zaune yake bakin gado ya tsura mata Ido, tana bud'e idonta ta hau faman yin murmushi,
Cikin tausayinta ya rike hannunta wanda ya bala,in yin sanyi,
"Aysha kin tashi? sannu ya jikin? Me zaki ci?"
Cikin murmushin kaunar mijin nata ta k'ara kame hannun sa, da kyar ta buda bakin ta tace,
"Mijina! Allah yabamu Rahma,mu gode masa, mu kaunci Rahamar sa Allah yayi mana Rahma abaki d'aya,"
"inshaAllah aysha"
"Nagode"
kawai ta fad'a,
[8/19, 2:51 PM] Aunty Queen: *RAHMA*
       _(Daddy's girl)_

RAHMA!Labarin So Da kauna tsakanin 'Ya da mahaifin ta, Mata da Mijin ta.Where stories live. Discover now