RAHMA

1K 33 14
                                    

[9/15, 5:34 PM] Aunty Queen Mermue: *RAHMA*
         _(Daddy's girl)_

*Na*

            *QUEEN MERMUE*

*Vote on Wattpad, #2Auntyqueen*

*25*

Abin ya bawa Fajir haushi dan haka ya daka mata tsawa,
"Salma! Wai meye haka? Ko kin fara fita hanyacinki?"
"Eh dole kace na fita hayyacina dan kasan me kake son aikatawa toh Wallahi ba a gidan nan ba, babu yanda zakaci amanata a gaba na,"
Tsaki yaja mata ya nufi hanyar ita kuwa ta bishi tana yayyafa ruwan masifa,
Rahma duk tana jinsu, dan haka abin yayi mata dad'i, indai rigima ce ai itace kan gaba.
Tun da la,asar take rigima duk inda Fajir yayi bibiyarsa take,
Ita Daddy take son gani, gashi idan ta Kira sai yace yana aiki zai Kira ta,
Haka dai Rahma tayi sati d'aya curr cikin amarcin ta babu wani abu da ta fahimta illa cewa Fajir Matar sa d'aya kuka ita kadai ce agaban sa, wato Salma,
Yau Rahma ta kammala amarcin ta dan haka girki ya koma hannu Salma, wadda tun safe ta fita, itace bata dawo ba sai maraice sosai, tasha kwalliya iya kwalliya, da dare kuwa bayan sun ci abinci ne Fajir ya nemi yin Magana da su,
A falo suka koma suka zauna, bayan yar guntuwar addu,a da Fajir yayi suka shafa ya kalli Salma ya fara da cewa.
"Salma kamar yadda mukayi magana da ke, Rahma k'anwar ki ta ko'ina so kamar yadda aka bamu amanar ta Ina son kiyi kokari kiga kin rike amanar,"
Salma ta sakar mishi wani kallo irin na haba Honey,
Kana tace"ai wannan ba komai bane matuk'ar ba ita ta canja matsayin ta ba,"
Dariya yayi ya dan rungumota sannan yace,
"Toh maganar girki Kuma fa? Kwana nawa kike so ayi,"
"Girki?"
Wani irin janye jikin ta tayi cikin Isa tace,
"Dama dan maganar girki ka taramu anan? Ni dince zan wani raba girki da wannan?"
Ta nuna Rahma da hannu, Rahma da tun fara zancen bata ce komai ta mike tsaye ta kama hannun Salma da ya nuna ta, Salma ta tizge hannu ta,
"Bari kiji Salma, wallahi kika kuskura kika kara nunamin hannu anan sai nasa an karshi kuma ayimiki korar walakanci a garin nan, and maganar girki da fari na so nace bana bukata dan ni ban iya ba koma bana son wahala ko ordering abinci bana so, but now Ina son yin girkin kuma dole arabashi dani,"
Fajir ya mike a hasale yace,"ke Rahma kinsan wa kike gayama wannan maganar? Toh wai ma ke zaki kore ta a garin ne? Bana son rashin mutunci duk abinda Salma ta yanke shi za,ayi,"
Cikin jin dadin sabuwar rigimar da ta barko Rahma tace,
"Yah? Dama baka san inada wannan ikon ba? Salma matar ka ko? Bakada labarin K'anwar Miji zata iya korar matar sa, bale iri na da nake da karfin ikon da baka dashi!"
Hannu yakai zai mare ta, nan take kuma yaci birki,
Dariya Rahma tayi tace,
"Koma meye Girki sai nayi shi yanzu haka kuma ni zanyi shi,"
Daga Fajir har Salma Ido suka tsora mata, Shin tasan girkin da ake nufi?ko kuma ita dahuwar abinci take nufi,?
Basu iya bawa kansu amsa ba sai zuba mata Ido daza suyi dan suka me take nufi,
Daga haka ta haura upstairs, Salma dake tsaye sankare ta kalli Fajir tace,
"Toh billahil azeem bazan yarda ta kwana anan ba, saidai ta koma part enta, ai girki na ne taya zata kwana a d'akin ka? Saidai ka zaba koni ko ita,"
Fajir da kansa ya dauki hayak'i yace, "haba ke kuma Salma kin dai ga Rahma k'aramar yarinya ce meyasa zaki dinga biye mata, and ai ba, adaki na zata kwana ba,"
"Oh dai kowacece babu ruwa na idan naga zata kawo min matsala sai dai na bar gidan,"
Fajir ya riko hannunta da ta dora akan kunkurun taya jawota ta fad'a ajikin sa yace,
"Haba Honey akwai wata da ta isa? Kiyi hakuri kinji da an koma Hutu a school zan maida ta tayi master's kinga bazata dame mu ba,"
Nan dai ya shiga yi mata dadin baki kana ya sunkuceta suyi d'aki,
Rahma baiwar Allah, tana shiga ta dauki wayar ta dake charge ta Kira Daddyn ta, da kyar ta samu  ya daga, korafi ta shiga yi masa na rashin kiranta da yake hakuri ya bata, nan take ta shiga tambayar sa dalilin kiran sa cewa girki take so tayi gobe me yake ganin zata girka,?
Dariya yayi kana yace, "iyye 'yan mata na, har an san ayiwa Miji girki,"
"Kai Daddy shi girkin?"
Ta fada tana dariya, Daddy yace "toh abinda ya kamata yanzu ki bari da safe sai Ki Kira Mamarki Sadiya ko Fadila nasan zasu koya miki, and zan turo Islam sai ta tayaki,"
"Toh Daddy idan nayi na aiko zakayi testing?"
"A,ah bawa Mijin ki dai, in kika zo nan sai kiyimin nawa,"
Suna kammala waya Rahma ta shiga kwadawa Mama Sadiya waya, lokacin kuwa sha d'aya ta kusa, sai da ta kusa katsewa Mama Sadiya ta dauki wayar,"
"Rahma lafiya da daren nan haka?"
"Uhm Mama barka da dare,"
Cikin kaguwa dan taji dalilin kiran ta yanzu tace, "barka dai ya akayi?Ina Fajir ne?"
"Maaa dama girki zanyi gobe shine nace wane irin zanyi?"
Dariya Sadiya tayi Sosai kana tace,
"Oh su Daddy's girl ansan dadin aure hada girki za,a koya?"
"Kai Mama wane Dadi? Kawai dai Salma ce tace baza,a bani girki ba shine ni kuma nace sai nayi,"
Mama Sadiya tace,"kamar Yaya baza,a abaki girki ba? Kwana nawa kuka tsara yanzu?"
Rahma ta dan ware Ido tare da tabe baki tace,
"Ni fa tun zuwa na bana girki shine tace yau girkin ta ne, da Ya Fajir yace ya zamu raba girki tace ita zata dinga yi nikuma nace nima zanyi,"
Mama Sadiya sam bata fahimci zancen Rahma ba, dan haka tace gobe zata biyo gidan kafin su wuce dan banda gobe zasu wuce Washington, haka dai sukayi Sallama ita kuwa Rahma ta shiga yanar gizo dan neman mafita,
Salma kam taji dadi ganin yanda Fajir ke rawan kai akanta kamar zautacce, yanda yake going round akanta kamar mayunwacin Zaki, haka ya k'ara tabbatar mata da Martabar ta.
Da safen ma basu fito ba sai sha biyu, suna can suna cin zallar amarci,
Rahma kuwa 11nayi sai ga Islam tazo, nan suka shiga kitchen da yake Islam ta dan iya girki dan haka itace a gaba, kuyangin gidan kuwa dama duk inda Rahma take basa zama saboda umurnin ta.
Farar shinkafa suka dafa sai miyar nikakken nama da ganye, tayi kyau sosai kuma tayi test, Rahma taso su k'ara Islam tace ta gaji da yake ita ko akwai son jiki,
Saida suka ji fitowar Salma sanna Islam ta wuce part enshi,
Bayan sun gaisa ne yake tambayar yaushe tazo, nan take shaida masa Daddy ya turo ta suyi girki,
Tabe baki kawai yayi wanda saida yabawa Islam Mamaki,
Islam ta sauko k'asa a part en Rahma nan take gayamata zata shiga wajen Salma,
Rahma tayi caraf tace zata je,
Nan suka nufi part en ta,
A zahirin gaskiya Salma kazamar gida ce, akwai tsaftar jiki da kwalliya amma dakin ta ko pant ta cire saidai 'yan aiki su dauke, da farko Fajir ya hana 'yan aiki shiga bedrooms enta, ganin yanda cikin kwana biyu ta maida shi bola yasa yace su ci gaba da gyara mata,
Ta iya kwalliya kam amma gyaran gida saidai 'yan aiki suyi mata, ko panties enta sai sun wanke haka take loda su ta cire koda tana period ne, saidai masu wankin bayin su wanke mata.
Suna shiga suka fara cin karo da D'an kwalin ta a falo, sai kuma robar ruwa an barta a bude ta zube a carpet, Rahma tsabar iskanci yasa ta kama dode hanci bawai dan taji wari ba saidan tana gudun taji,
Ganin bata babban falon suka wuce ciki, nan suka ci karo da under skirt enta tare da skirt enta da alama dai tun a waje ta fara tubewa,
Nocking Islam tayi a kofar dakin ta daga ciki tace waye,?
Islam da ba shiri suke da ita ba dan munafika take kiran Islam ganin yanda Fajir yake son ta shiyasa gaisuwa ce tsakanin su, Islam cikin kosawa tace,
"Baki kikayi,"
Salma da bata gane ko su waye ba tazo daure da Zane a  kirji, Nonuwan nan kamar Wata Nagge mai shayar wa,ta bude k'ofar,
Ganin su yasa ta saki gutun tsaki tare da hade fuska,
"Ya akayi?"
Ta tambaye su, Rahma ko leke take tana hango tulin kayan da Salma ta birkito daga cikin wardrobe, da alama goge su a wanke amma tsabar k'azanta duk ta birkito su kasa acan gefe kusan madubi kuwa katanyar breziyar ta ce yashe ak'asa,
Rahma ta saki wata irin dariya lokacin da ta hango Bresiar,
"Oh my dear goodness abu kamar Cow?"
Rahma ta fad'a tana rik'e ciki tare da ja baya,
Cikin takaicih Salma ta juya ganin abin da Rahma take yiwa dariya cikin bacin rai ta kalli Islam,
"Me ya kawo Ku? Ko kuma tsabar rainin wayo ne,"
Islam da itama dariyar take son kwace mata bata san sadda ta sake ta ba,
"Ai nazata bola ce muka zo"
Inji Rahma, da gudu Islam taja ta suka ruga aguje suna dariya,
Suna sauka a main falon sai ga Fajir ya fito daga part en Rahma,
"Ina kuka shiga?"
Nan take suka saita kansu Rahma ta marairaice tace,
"Munje gaida Salma ne ban mayi niyar zuwa ba Daddy ne yace na dinga zuwa shine ta rufe mu da zagi zan rama Iskan ta hanani harda cemuna tayi 'yan Iska,"
Fajir yaji ransa ya baci shida yake so Salma ta bashi hadin kai su maida Rahma a matsayin k'anwar sa shine take namen har gidan su asan zaman da suke,
Nan ya nufi part enta baikai ga isa ba sai gata ta sauko ranta a baci,
Tana ganin sa ta fara Bala,i.
[9/16, 7:50 PM] Aunty Queen Mermue: *RAHMA*
             _(Daddy's girl)_

RAHMA!Labarin So Da kauna tsakanin 'Ya da mahaifin ta, Mata da Mijin ta.Where stories live. Discover now