Part One: Chapter 5

95 6 0
                                    

GOMBE:
Qarfe 4:00am Meemah ta tashi daga bacci Wanda hakan yazame mata jiki. Tashi tayi tafita tayo alwala tadawo, wani wuri nagah tanufa wanda Sallaya ne ah wurin sai Hijab dakuma Qur,an. Hijab in tasaka tatada Sallah, sai da tajeri raka'a 6 kafin ta xauna tasoma karatun qur'an na haddan ta wanda ynxu saura musu izu 3 su sauqe Quran. Bayan ta idar ne taji Ana kirayen Sallahn fajr, hakan yasa ta miqe tayi Raka'atul Fajr Kafin tayi sallahn asubah. Ta dade tana adduan Allah sauqi mahaifiyar ta lafiya, Tayi wa kanta da Er uwar ta sai baban ta, daga qarshe tayi wa qasa baki daya ta shafa, Tashin arfah tayi tace tatashi tayi Sallahn asubah. Nan tamiqe ta koma baccin ta. Arfah mah alwalan tayi ta tada Sallah sai datayi Raka'atul Fajr kafin tayi Sallahn asubah, itama ta dade Tana addua kafin ta shafa. Dauko Quran inta tayi tayi bitan haddan ta kafin tabi sahun er uwar ta sukaci gaba da bacci.
   Ammi ce ta tashi wuraren 6:30 taje tatada su suyi aiki kafin su shirya makaranta, tashi sukayi kowa yakama yin nashi aikin, Wanda in har ba weekends bane tho shaara da wanke wanke kawai sukeyi, Amma in weekends ne har girki sukeyi. Tashi sukayi suka fita kowa yakama aikin shi, Arfah itah shaara takeyi yayin da Meemah kuma ke wanke wanke, Umma koh ruwan zafi ta daura cikin Babban tukunya Wanda zai ishesu dukan su suyi wankan. Bayan sun kammala ne kowa yashiga yayi wanka. Bayan sun shirya ne suka fito sukayi wa su Mama sallama suka kama hanyan makarantar tasu me suna ORJI wanda yanzu haka suna SS1 ne ah karatun su.

MAHBUB:
Fitowan shi kenan daga wanka yana faman shafa mai yaji wayan shi na ringing,dubawa yayi yagah wanda yake qira BUDDY yagani ah rubuce nan ya daga "Hello" daga dayan bangaren akah amsa "Hello friend, Ya gajiyan hanya" "Alhamdulillah, ya naka gajiyan" Cewar Mahbub, "Yaushe xaka xo min ne kan" cewan Mahbub. Dariya Naseer yayi yace " Kar kadamu zanzo maka kwanan nan In sha Allah" "Okay sai kazo" daga nan suka kashe wayoyin su. Fita yayi bayan yagama shirya wa , T-shirt yasaka fari me Rubutun PlayBoy, sai Wando three quarter Wanda da kadan yafi kneel insa. Sai tashin qamshi yakeyi. Wrist watch ⌚️ inshi ya ke daura wa yayin dayake shigowa dining room in danyin Breakfast, zama yayi gefen Airah wacce ynxu take da shekaru 17 ah duniya, while sistern ta Hanifah kuma nada shekaru 19. Zaman jiran fitowan Iyayen nasu sukeyi kafin su sumo cin abinci. Yana cikin danna wayanshi ne yaji shigowan iyayen nashi, dago idanun shi yayi ya yana kallon iyayen nashi waenda suka shigo hannayen su Sarqe dana juna. Zama sukayi kafin yaran kowa ya soma gaidasu, Mahbub ne yasoma gaidasu "Good Morning Mom and Dad" Morning Son suka fadi ah tare "Good Morning swt parents"Airah da Hanifa suka fadi ah tare "Morning princesses" iyayen suka amsa musu daga nan kowa yayi shiru sai abincin su dasuke ci. Dad ne yasoma tashi yace dasu " If ka gama ka same ni ah Main parlor" nodding head nashi kawai yayi kafin Dad ya wuce parlorn. Mom ce tatashi tabi bayansa kafin, sai da yabata kusan 15min yana zaune bayan ya kammala breakfast inshi kafin yatashi yabi bayan iyayen nashi.
   Zama yayi ah qasa ta wurin qafan Mahaifiyar shi "Tho de dalilin dana ce kasame ni ah nan bai wuce tambayan da xanmaka baane "Ah inah kakeson yin Masters naka tun kace kafison kazo qasar nan kayi" "Abba dama nace Yola nakeson zuwa" " Tho Alhamdulillah In sha Allah duk lokacin daka shirya ka min magana zan nemamaka chan in" amsawa yayi da "Tho" kafin yatashi zai fita "A ah  son dawo ka zauna saura nawa maganan" Mom tace dashi " Tho batun aure fah yaushe zakayi?" Ta tambaya "Haba Mom dan Allah yaushe na girma ne,har yanzu fah ni yarone qarami....gaskiya nikan aure kan banshirya bah" yafada yana turo baki irin shagwaban nan "Tho kema Fatima banda abinki wannan yaro inah ya isa aure" Dad yafada "Hmmm! Haka zaku ce ai,nide kawai kana gama masters inka aure zakayi, kuma nagama magana. Tashi kaje Allah maka Albarka" tashi yayi yana me amswa da Amin kafin yayi hanyan parking lot dan yanason zagah gari. White Lamborghini Huracan LP640-4 ya dauka yafita. Be zarce koh inah ba sai gidansu abokin shi Hamza. Dashigan shi gidan qiran wayansa yayi, ringing daya biyu sai akayi picking "Hello" amsawa akayi ta dayan bangaren "Hello gani ah qofar gidanku" "Okay kashi go mana inah parlorn" nan ya bude qofan yafita yana takunsa. Qofan parlorn ya bude yashiga tare da Sallama ah bakinshi. " Assalamu alaikum" "Wa alaikumissalam, mutan Cyprus yau kaine ah gidan namu?" Maman Hamza tafada  "Wallahi Umma nice, Inah kwana" "Lafiya qlau ya Maman naka" " lafiyan ta qlau,tace mah in gaisheki" "Inah Amsawa, yanzu Hamza yashiga daki kaje yana ciki" hanyan dakin ya shiga ya bude yazo shigah kenan Hamza mah yazo fitowa sai suka bugi juna "Kai Malam inah zakaje ne baka kallon gaban ka?" Mahbub yafada yana me shiga dakin "Ha'a mutumin ai nazaci fita xamuyi, har kasa na changing kaya" "Nan kuma kai kasani dan nikan bah inda zanje" daganan ya gyara kwanciyan shi yaci gaba da danna wayanshi.

NASEER:
Bangaren Naseer kuwa bayan sun gama gaisawa da Mahbub bandaki yafada yayi wanka yafito yashirya ah cikin wani Shirt me rubutun Boss ah jiki tare da Trouser nashi.Fitowa yayi sai tashin qamshi yakeyi. Dining yanufa, yana xuwa yaga Abban shi yadawo "Assalamu Alaikum" "Wa alikumussalam" iyayen suka fada ah tare " "Welcome back Son" Abba yafada yana me rungume dan nashi "Kayi haquri ban samu daman dauko ka ah airport jiya bah, kasan aikin namu yanda yake" "Uhm" kawai yace yana me gyara xama ah kan kuje run Dining in "Good Morning Umma and Abba" "Morning son" sukafadi. Bayan gama breakfast inne Abba yamishi maganan inda yakeson yin Masters nashi " wai nikan Son wace qasa zaka koma yin masters ne kan?" Murmishi yayi daman ba cika dariya yayi bah "Abba ah nan qasan xanyi" Yafada yana me kallon Abban nashi " Bangane ah nan qasar bah, me qasar nan suke dashi daza su baka, kaje kanemi wata qasar kawai" daman yasan Abban shi da wahala ya yarda "Abba kayi haquri amma ni choice inah kenan" "Tho shikenan zan tura ka Yola kuma ah cikin gidan Governor in zaka zauna" "Tho shikenan Abba nan in ma yayi, nagode tashi yayi yabar musu parlorn. Part nashi ya nufah ya bude, ah kan gado ya kwanta yana tinan nin Mahaifin shi ace ka girma ah qasa amma kana qin qasar ka, Allah de ya kyauta. A haka bacci yaqara ebanshi.

Alhamdulillah here is an Update..baxan gaji da baku haquri ah kan jina shiru da kukeyi bah, Rashin wuta ne yake damun mu. Amma dan Allah ku cigaba da Haquri.
    Please VOTE and COMMENT

LAIFI NAH NEWhere stories live. Discover now