Azeeza episode (8)
"Toh yi maza ki sako lalatattun kayan ki kizo ki rufe wannan fuskar taki ki fita.."
"Tohm" nace ,na wuce naje na sako kayan na karba kudin na fita ..
Nidai ban san me ya faru ba,se hafsatu ta shifo a fusace tana kuka..
"Inna ya akai wannan ifiritun ta fito bayan ina tare da me sona?"
"Lemo na aiketa ta siyo bakigan ta kacha kacha ba?"
"Ai gashinan kinsa yana tambayar wai wace ita..wai ta mai."ta fada da kuka
Innalilliahi wa inna ilaihi rajiun..
Nasan yau nagama yawo a gidana nan..
"Zo nan ke "..inji Inna
"Inna kiyi hakuri wallahi yadda kika ce nayi haka na yi ni ban ma kalle su ba ,kuma suna mota ma wallahi Allah inna ban gansu ba.sedai in ita ne ta ganni."
"Oho kina nufin na maki karya",said hafsatu
"Inna kiyi hakuri.."
Kafin na karasa har ta fara dukana.duka ko na gaske na sha shine har hannuna ya sama matsala amman ban san mene ya sama hannun ba..Tashi nai na tallafi hannun na fita batare da nasan inda zanje ba..(zuciya ta dai na fada mun nayi tafiyata daga gidan kawai)
Ina zuwa gate sabitu ya tsayar dani..
"Ina zakije a na sallan isha'I haka.."
"Hannu na ne yake ciwo sabitu,inaso naje chemist."
"Muga hannun.."
Na daga hijab ina da kyar yana ganin hannun yayi salati yace
"Wannan ai da kyar in be goce ba.."
"Innalilliahi wa inna ilaihi rajiun..goce wa kuma ?"
"Ba lokacin magana,kitaimake ni kar kice na taimaka maki wallahi mahaifiyata nake ji,in na taimakeki korata za ai kuma a lalata mun suna shiyasa amma kiyi hakuri komi nada lokacin sa."
Anan ya kwatanta mun wani gida acikin unguwa da ake gyaran targadi,karaya da sauransu.
Ya kuma kawo 1000 naira ya ban yace inje a ga mene a hannun.Bilal
Zaman Abuja yaki wa bilal dadi,saboda haka ya tattaro kayansa ya dawo kano ta dabo.A daddafe ya yayi 1 week a Abujan ya dawo tun sanda ya dawo yake yawo tsakanin unguwar tasu Azeeza da gidansu..
Da safe da rana da dare yake zuwa ko Allah zesa ya ganta,amma inaa..shiru kake jiYauce ranan da ya ware ta musamman ya tsaya tun karfe 6:00 na yamma yake gurin gidan har sallah anan ya runga yi.
Yana son sanin tana nan ko dai bata nan.ya gaji ya gyara seat in motanshi da niyyan ya tafi tunda dare yayi,kawai se ya hangi wata ta fito daga gidan tayi right.
Alhamdullilah ya rabb!
It's her,she's the one wallah,its the night Angel..ya fada yana murna
Se ya bita a hankali saida tayi dan nisa da gidan sannan ya yi mata horn,ko motsi batayi ba baranta na ta juyo.
Se yayy parking ya fito ya zo daidai ita tana tafiya.
"Assalamu alaiki.."
"Wa'alaikassalam"..ta fada amman in ba ka kusa baza ka san ta amsa ba.
"Ke ina zaki da daren nan?,ban hanaki fito wa ba?"
Se a lokacin ta daga kanta dan ganin wannan mutumin me kama da Mr.nice guy inta..
YOU ARE READING
Azeeza (the lucky orphan) ✅
General FictionA story about a girl called Azeeza that find her self in a terrible situation with regard to her step mom and step sister,but there was a turn of table and it happened that she finds the love of her life ...