2

1.1K 31 1
                                    

[12/17/2017, 1:48 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE"... ©Feenat Ja'afar 4_Kuka Naina ta fara mishi, tana nuno mishi kofa,lallashin duniya taki shiru, kofar ya bude,tare da ruko hannun ta, hanyar dakin Laila yaga tayi, sakare yai yana kallon ta, a hankali ta fara buga kofar," Momma!Momma!!.. Kamar a mafarki take jin Nainan,dago wa tai,tare kasa kunne,bugu ta cigaba da yi,da sauri ta tashi ta goge fuskar ta, tana bude kofar Naina ta rukun kume ta,dukawa tai ta dauke ta,tadan sachi kallon shi,da sauri yai daki, mamakin shi d'aya,Naina,yasan ta sarai, ko taga mace,sai dai ta kira ta da Momma daga nesa, amma ya rasa meye gamin ta da Laila, har take kuka a kanta. Kitchen taje,pidan ta d'akko,suka zauna a parlour tana bata,ai kwa yunwa take ji,amma baban yace ba yanzu ba,tai murmushi tare da shafa kanta,tun ganin farko,Naina ta shiga ranta farad d'aya, ko ba komai,ganin Nainan na sata cikin nishadi,ta Sani Naina yar uwar tace,dole jinin ta nata ne,tai alkawarin kula da baby Naina tamkar yarta, ta dauke ta, sai dai Yarinya ta make kafada,baya take nuna mata,murmushi tai tare da cewa"Bamboo?.."
Ok,bari na dau zani,sai ta kara make kafada,ju ya wa tai,tuni kwa ta dane bayan, dankwali ta sake daure ta dashi,kan ta dau pidan tai kitchen, wanke shi tai, tana kallon yadda aka jere ma Naina kayan abinci,da halama shi bai San ta girmi wannan ba,ta kada kai, dole tun yanzu ta fara cin abinci. Kan kace mey,Naina taji dumin baya tai bacci, sanin ba wani taro akai na auren su ba,tasan babu mai zuwa gidan ta yau,tea ta daura,ta duba store, akwai duk abinda take so,sai ta daura dankali,ta koma daki, dan kwantar da Naina,,a hankali ta kwanta, kan ta kwantar ta, kuka ta fara cikin bacci, a hankali ta fara jijjiga ta, sai ta koma. Wanka ta shiga a gurguje kan dankalin ya nuna, ta fito ta shafa mai,ta mirza powder fara da man lebe,kullum kwalliyar ta kenan,tun shekara biyu data wuce. Attamfa tasa, ta yafa dankwalin ta,kitchen ta koma,tuni ta dukufa aiki,kusan 9 ta gama,ta fito parlour, yana zaune ya hakimce,fuskar nan kamar bai taba dariya ba,dining tai ta ajiye abincin, ta dakko cups,Baba mai gadi ta kaiwa nashi,sai yanzun ta kula ashe ihun karen jiya a gidan ne,ciki ta koma, taji bugun kofar Naina da dan kukan ta,kan taje har ya rigata,hannu yasa ya dauke ta, rike take da zanin goyon ta,sai take nuna mishi,karba yai tare da hulla shi kan kujera,Laila na kallon su,ta duk'ar da kai,baby Naina ta kara dakko dankwalin, bamboo take ce mishi,amma bai gane ba,sai ta fara kuka,tashi yai yana dan jijjiga ta, bai san mey ke damun Naina ba a satin nan,rigima kawai take, yasan kuma ba halin ta bane,ya makawa Laila harara,tamkar ita tasa mishi ita kuka,ita kuma ta fuskanci abin da Nainan ke so,sai ta kara tausayin ta,bataji dumin uwa ba. Zame wa ta fara,halamun ya sauke ta, sai yai kitchen, dan ko wai yunwa take ji,yana dire ta tai waje,biyo ta yai,sai yaga tai wajen Laila, tana zuwa ta mika mata dankwali,"Bambu,murmushi tai,tare da hadiye hawayen ta,ta dauke ta ta saba a baya,tare da daura dankwalin, sai ta tuna mishi da wata rana a chan baya lokacin Naina nada ciki,yasa mata kara min filon su Wai ta goya ko zatai kyau da goyo,murmushi take mishi,kan ta duka,"Daura min babyn toh,da zumudi yasa mata filon,tare da sa towel,ta karba ta daura,yace "kai kinyi kyau da goyon, ya tuno yadda take murmushi, da sauri ya koma kitchen, dan gudun kar hawayen shi ya zubo gaban Laila, daki ta koma,tana jijjiga Naina,sai ta samu kanta da bata story,ita dai tai lumii a baya tana jin ta,ido warai ba bacci. (10am)ta fito,jin yunwa ta fara dibar ta,rabon ta da abinci tun jiya da yamma, turus tai ganin shi a parlour,kwai ya soya yana ci da bread, ta kalli abincin kan dining,bai ko taba ba,ta dai fita, amma tuno da nasihar iyayen ta yasa ta daure," Abban Naina ga break fa,,banza yai da ita,ta rintse ido ta kara maimaita mishi,a wulakance ya kallo ta, yarinyar akwai tusa kai,"ki ma bar tusa kanki a wuri na da y'ata,mun saba yiwa kanmu komai,,kai tai kasa dashi,hawaye kusa,tuni ya fara ambaliya,"ba kince kinji kin gani ba? Ya kada kai "Ya miki kyau. Cigaba yai da cin abincin shi,bai ko kara tanka mata ba,kai ta kada, kan ta goge hawayen ta, dining din taje,ta zauna,tea ta hada,ta sakko Naina da dabara, ta bude flaks din,dankalin ta zuba,kan ta daura kwai,tadan gutsuro takai bakin Naina,kallon ta take,baki a hannu,dan tasan ba cimar ta bane,murmushi tai mata,kan a hankali ta cire mata hannun a baki,takai kwan bakin ta,bude baki tace tai da turanci, dan ta fuskanci yafi mata akan Hausa,da mamakin ta sai taga tana ci,shayi ta dan zuba a wani cup din,ta dangwali da bread,tuni Yarinya ta hau ci,harda keta,tadan kware kadan,tea ta dakko zata bata dai dai ya juyo dan jin tarin Nainan, da sauri yai woo wajen,bata ankara ba sai ji tai yai fachali da cupn,a tsorace ta miki,ya sunkuci yar sa, da masifa ya kallo ta, " Bana bawa y'ata kowanne kanje kanjen, ki fita harkar ta... jikin ta har karkarwa yabke tana hawaye,bata saba ai mata tsawa ba,amma a yau kadai ta shasu,tuni ta fara jin tsoron sa,baby Nainan ma kukan ta fara,dan ba tasan Abban ta da tsawa ba, asali ma ita ba ya mata koda hayaniya, yau sai lamarin ya tsoratar ta. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:49 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE"... ©Feenat Ja'afar 5_Kitchen ya shiga,ya dau abincin berry,(karyar shi)ya tafi kai mata,,abincin da bata ci ba kenan,tai daki,kuka take son ranta, mey yasa iyayen su basu gano matsalar dake gaban ta ba? Yanzu a haka suke tunanin zata bishi wai har ta mantar shi Laila? Shin ita sun manta da tata damuwar? Ko so suke bakin ciki ya kaita lahira? Koda yake ba laifin su bane,hoton Mas'ood ta dakko,"laifin kane Mas'ood,laifin kane da baka cika min alkawarin mu ba,gashi nan a tulo ni a ara'ha..kuka ta fashe dashi,turo kofa taji anyi, Naina ce,da sauri ta ajiye hoton tare da goge fuskar ta, ta kakalo murmushi,kallon ta Nainan take,kamar mai fahimtar abinda momman nata take ciki"Momma" sunan ta ta kira,tare da zuba mata ido,hannu na baki,hannu tasa ta dau Naina,Allah yaga,ganin Naina na sata farin ciki,da tai alkawarin bazata kara taba mishi Y'a ba,amma babyn tausayi take bata,duk yarinyar (so cool),ba dan kiciniyar nan ta yara,ta shafo kanta da murmushi, an mata wanka,sai dai ba kwalliya, powder ta dakko da kwalli, harda jagira,ta zizara mata express, mudubi ta dakko,ta nunowa Naina,Wai ta kalli kanta,hannu ta cire tana kallon madubin,sai ta hau washe baki tana dariya,mudubin ta dauke,a hankali ta fara mata chakulkuli kadan kadan,dariya suke,Nainan sai wutsul-wutsul take da K'afa,,tuni ta manta da wani shan hannu,a yau d'aya babyn fara'ar ta ta karu,, bai kara bi ta kansu ba yai daki,,ya rasa mey ke damun Naina yau,zaman mint Biyar bata yi dashi sai tace"Momma ". Sai azahar ta fito daura na rana,ganin markade a fridge, kawai sai ta daura taliya,ta hau suyar miya, Naina na zaune tana kallon kai kawon ta,tashi tai tazo ta jingina da jikin ta, tai murmushi, Naina na son ta,itama kuma tana son ta. Ana kiran la'asar ta kawo abincin parlour, nasu ta zuba musu daban,ta ajiye mishi nashi a saman table, ta dau na baba ta kai mishi,dai dai ya sallame," aa,sannu Hajiya,tai murmushi, "yauwa Baba,kasake ya tsaya kallon ta, Allah mai halitta, tun safe yake mamakin kamar ta da marigaya,kirkin su gashi d'aya,na Berry ta dauka zata kai mata,Baban yace" a kawo na kai,murmushi tai,"aa Baba bari naje,hannun Naina ta rike,tai wajen Berry,Naina take kallo,kan ta kalli baba da biyo su,sai dai gaban ta sai faduwa yake yi,dan tana tsoron kare a rayuwar ta da kuliya. Sai da Berryn ta bari tazo kusa da ita,data sau mata wawura da wani haushi, bata san sanda ta hular da abincin ta dau gudu ba,Naina sai dariya take,gudu take tana wai waye,tana zuwa parlour ta gabze mutum,tai baya zata fadi ya riko ta,ilahirin jikin ta karkarwa yake, sai dai tana ganin shi ta sau hawaye"Dan.. Allah kaiyii hakuri,,yau ta kade,ashe shi ta bige,hannunta take kallo data rike,yace"kina hauka ne? Ko bakya kallon gaban ki,da in'ina ta nuna mishi hanyar backyard "K'are ne.. Wani uban tsaki ya sau mata, kan da gangan ya sau mata hannu da karfi,sai kwa ta kasan tiles,,bin bayan shi tai da kallo,kan ta kar kade jikin ta tadan leka. Baby Naina take nema,sai gata da Baba sun taho,dariya taga tana yi,wato ita bata tsoron k'are? "Hajiya na zata kamar Ku da Marigayi ya zaisa ta zata ita ce,ashe na manta kamshi suke bi,,murmushi ta kakalo," Zamu saba kwanan nan,ta karbi Naina,murmushi yayi,lalle fa,a kina gudun zasu saba. Abinci ta zuba musu,sai ta dau taliya d'aya ta daga sama,a hankali sai ta zuka,Naina na kallon ta tana dariya,sai itama ta fara k'waikwayen irin nata,ganin zata ci yasa da wasa ta fara ciyar ta suna dariya,,jin bude kofa ne yasa ta mike a tsorace,kallon Naina yake,ganin yadda ta tankwashe K'afa tana zukar taliya,juya wa yai kitchen, ta sau ajiyar zuciya, dan ta zata wani sababin zai mata na Naina na cin abinci. Da dare ya dau yar shi sukai daki,lallaba ta yake tai bacci,sai dai Naina ido kir taki bacci,da da ne,8 ta jima da bacci,amma yau kawai ta zuba mishi ido,tunanin sauyawar Naina yake yau d'aya, ji yadda ta zage take dirka dariya,wanda ko shi bai taba gani tana yi ba,asali ma yau in ba yanzu da ya dauke ta ba baiga hannu a bakin ta ba,toh mey hakan yake nufi? ,,"Papa,ta katse mishi tunani,kallo ta yai tare da shafa kanta,"My Naina,(what's wrong with you?) Kallon shi take,kan tace"Momma". Da mamaki yake kallon ta, kan ya furta"Momma? Lalle, toh mey matar nan tai yar shi a cikin sati d'aya? Dan tun ganin ta na farko take kiran wannan Momman,,karshe dai ta dame shi sai da ya bude mata kofa ta fito,tana parlour ta hada tagumi,ko buda kofar su ba taji ba,Naina taji a jikin ta, da fara'a ta kalle ta,bambu take ce wa,kai ta kada mata,kan ta ware dankwalin ta,duk yana kallon su har ta goya ta tai daki. Kan sati wata iriyar shakuwa ce ta shiga tsakanin Laila da Baby Naina,abu d'aya ne matsalar su,tsangwamar mai gidan,abu kadan tsawa,komai tai ba gwanin ta,abinci kwa yadda ta ajiye haka zata dauka,sai dai a bawa Berry... Iyanzu baby Naina abinci take ci taki(Baby food's),ga wata kiriniya data fara koya da shagwaba, abu kadan goyo,kuma ko shi ya zauna yanzu zata fara tumurmusa shi halamar yai mata wasa,tun abin na bashi mamaki ya dawo bashi tsoro, dan gani yake a gaba Naina zata iya manta shi sai Laila,shi yasa ya kudiri a niyar dauke ta a gidan gaba d'aya ta koma wajen Hajiyan shi. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:49 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE"... ©Feenat Ja'afar 6_Washegari ya tattara kayan ta a karamin kit, yazo dakin tare da kiran Nainan,a kitchen yaji kiriniyarta,yai chan,tana ganin shi ta taho ta rungume shi, tuni gaban Laila ya fara bugawa,kai ta sunkuyar,a rayuwa bata taba cin karo da mutumin da take tsoro ba kamar Faruq,bata kaunar kallon fuskar shi marar annuri da tsabar tsanar ta. " ina kwana?..a tsorace ta fada,(as usual)yauma ko kallo bata ishe shi ba,,yar shi ya zara,ya rataya briefcase din shi,dayan hannun Naina,d'aya yana kokarin daukar kit,kallon shi kawai take da mamakin yadda zai yi da Kit din,sunkuya wa yayi jakar ratayen take kokarin fadowa,da sauri ta taho dan agaza mishi,kit din ta dauka,da niyar bashi,wani mugun kallo ya mata,da fada fada yace"na sa ki ne?, a zabure ta hular da kit din tai baya, Naina ya sauke,tare da crossing briefcase din yai bayan shi da ita,ya dau Naina kan ya dau kit,da harara ya bita a maimakon sallama,baby Naina harda mata bye bye.. baiwar Allah,kanta duke tana hawaye,,tana jin tashin motar shi tasau kuka mai cin rai,anya ta taba ganin wanda yake cikin kunci irin ta kuwa?..tana komai dan kyautata mishi,amma kullum sai dai a bige da k'yara,a Da!in ance zata shiga irin rayuwar nan tabbas zata musa,lalle duniya juyi ce. A gurguje ya sauke Nainan a gida kamar yadda ya saba in zai je office, sai dai karan nan Hajiyan baki sake take kallon shi,daga gaisuwa yace yayi latti sai ya dawo,Kallon kayan take da mamaki,kai Allah ya kyauta wa faruq, waya ta dauka ta kira Aunty Salma,kan tazo in bata komai.(11am)tazo kiran Hajiyan tasu,ganin Naina itama tai mamaki,,gashi sai rigima take ita wai"Momma". bayan sun gaisa Hajiyan take cewa"Yaran nan kuwa salma kalau suke zaune? Aunty Salma tai tsamm, dan tun bayan bikin ba wanda yaje in banda Umman ta,suma sallama suka mata,"Hajiya ya kamata kam na leka yau kam,Naina ta kalla,"amma yarinyar da gani tana samun kula a wajen Lailan,dan da ba haka kuzarin ta yake ba,,kai, bari yanzu ma na kaita da kaina,kai Hajiyan ta kada mata,tana mai fatan Allah sa baya cutar yar mutane. A waje tabar motar ta,dan haka bataji dirin mota ba,da sallama ta shiga parlourn,amma Laila shiru,gata kuma a parlourn,kanta Aunty Salma taje,in banda ajiyar zuciya ba abinda take, ganan idon ta a kumbure halamar taci kuka,kiran ta da Naina take tana jijjiga ta ne yasa ta firgita, a zaton ta ko shine,ganin Aunty Salma da sauri ta hau goge fuska da kakalo murmushi,sai dai ita karyayyen zuciya gare ta,tuni hawayen ya dawo sabo,kara matsowa Aunty Salman tai,tare da rungumo ta tana lallashi ("it's Ok),kai ta hau girgiza mata,"Aunty salma bazan iya jihadin nan ba,ki taimake ni pls,,kuka take mata tana goge mata,tuni Naina ma ta fara,rungumo ta tai,karan nan bazata iya ba,barin ta tai tayi mai isar ta tukun ta takaita,"Laila,nasan kina da hakuri, dan Allah ki kara a na da, kiyi ta adu'a Allah shi zai shige muku gaba,ni kaina nasan Faruq ya sauya,amma Laila da ba haka yake ba,yanzu Faruq a burkice yake,tun bayan rasuwar Naina,Laila kodan Naina ki ci gaba da hakuri dashi,ki kara kyautata mishi ta yadda zai gane lalle ba Naina bace kawai matar k'warai, Laila kiyi hakuri ki dannne naki,nasan kinfi shi tawakkali,yanzu masoyan ku sunfi bukatar adu'ar ku sama da wannan, pls kiyi hakuri ki kara daure wa,ki rage tunanin Mas'ood, kiyi adu'a Allah ya masa Rahma,shine yanzu abinda yafi so,pls Laila, kodan Naina,, Nainan ta kalla, tare da shafa kanta,"Amin Aunty Salma,InshaAllah zan sadaukar ma Naina farin ciki na,amma ki tayani adu'a, kai ta kada mata,tare da musu sallama,tabar yara a gida. Fuska murtuke ya shigo gidan,lokacin suna kitchen daura girki, kitchen din yayi,ba ko sallama, "Papa, Naina tace,dai dai tana yanka albasa sai kwa ta yanke, tuni jini ya fara zuba,daga jin an ambaci sunan shi taji faduwar gaba,hannu ta fara yarfe wa,tuni hawaye ya fara mata ambaliya, ganin jinin kan tiles din shima ya tsorata,da sauri ya karasa,cikin fada ya fara" kina hauka ne? Ko bakya kula? Wace iri ce ke wai? Kuka ta fara,jin irin fadan da yake zazzaga mata,famfo ya bude,tukun yace tasa hannun ta,haka ya sau mata ruwan a hannu,daki yace ta biyo shi,ya dakko first aid box din shi,da fada fada yake goge mata ciwan, ita zafi ma yake kara mata,dan ba a hankali yake yi ba. Ba ko sannu haka ya barta a nan ita da Naina ya shiga bathroom, kai ta kada lokacin da take kokarin tashi,dakin duk a hargitse da takardun shi,duk da a share yake.. Wani lokaci ta tuna a baya,lokacin tana amarya suna kitchen ita da Mas'ood, ko wanne da efron jikin shi, tana yanka kaza wuka ta subuce mata,kara ta saka,ta tuno ba ta ma yanke ba,amma ya zaburo a rikice yana duba hannun, "Kin yanke,wayyo,baby ina ne?..murmushi take mishi,ya cire mata handgulf din,dayan hannun ta mika mishi, "nan ne,da sauri ya fara duba wa,tana dariya ta mika d'ayan "no wannan ne,harara ya sau mata tare da sunkucan ta,yana" ni koh?..kai take girgiza mishi,"aa sorry, yace "ai baki isa ba,da gudu tana hannun shi sukai daki, a gado ya dire ta,chakulkuli ya fara mata, tana ta kyalkyala dariya,"Maj'nu(stop it).. Dakyar suka dai daita tare da zuba wa juna ido suna murmushi,, kanta ta daura a kirjin shi,tana sauke ajiyar zuciya," Allah ya barmin Maj'nu na,ta fada da sanyin murya, kan kamo ta yai,tare da fadin "Allah ya bar min Laila ta,,(u know)in Laila ta yanke,toh Maj'nu ma dole ya yanke,everything na Laila,na Maj'nu ne,,murmushi tai,tare da shafo fuskan shi,"I love my Maj'nu,,murmushi yai,tare Shima da shafo fuskar ta," I love my Laila-Maj'nu,a nan suka lallace da faranta ran juna,an manta da nama,wani irin kuka ne ya kubuce mata,ta kalli hannun nata,"Ya Ilahi, a hankali ta furta "Mas'ood''...Mey kike min a daki har yanzu? A firgice ta dawo daga tunanin,kan ta gane ina take,tashi tai jiki a sanyaye,ta ruko Naina da hannu ke baki,indai kaga walwalar ta,toh Laila na yi. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:50 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE"... ©Feenat Ja'afar 7_Rayuwar kunci,ita Faruq ya nema wa Laila, duk randa ka ga ta wuni batai kuka ba,toh tabbata baya garin,a ganin shi da kora da hali zata bar gidan,shi ko irin sassaucin y'anuwan taka baya mata.. kullum bata gaba bata baya. Kimanin wata 3 da auran su yanzu,amma sassauci sai dai a wajen Allah, ga bata Qawaye ko d'aya a Nigeria, duk suna kwatano, wata makociyar ta Maman Mimi da ita kawai take zumunci. Aunty Salma ce tasa dole ya sai mata waya,ta sauya numbern Nigeria, da taji takaici sai ta kira gidan su sui ta debe mata kewa ita da Nainan ta. Yau an tashi da gyara sakamakon Hadari da ake yi,kurar jiya da dare take kadewa,dakin shi ta tura, duk da kota gyara sai an mata gori,duk yai kura,kwana biyu baya gari, takardun nan da kota gyara sai ya bazasu ta fara tattara wa,a drawer ta bude ta sa mishi,ta bude dayar ta kasan,wasu sketches taga, tamkar zanen ta,tahau duba su,harda mai tsohon ciki,tasan tabbas Naina ce,yayi kyau zanen pencil din kamar mutum,sai ta samu kanta da murmushi, zane iri iri,na baby Naina ta gani da kwanon abinci a gaban ta,sai ya fara zannen wata a kusan ta bai karasa ba,toh wacece? Tasan dai ba ita bace, dan anyi komai amma fuska bata gama fitowa ba, tattara su tai ta maida, ta ci gaba da gyaran ta,ta goge komai harda hoton Naina,kan ta shiga bathroom, ko'ina yai dau,kan ya dawo ya wargaza,ta sa turaren wuta tare da air freshener ta rufo mishi daki. Da la'asar karfe biyar suna zaune parlour ana dan yayyafi,Naina take koyawa "Alif B'a, tana yi da dan zakin muryar ta,kofar taji an bude,kamar kullum ba ko sallama,Naina na ganin shi ta tashi da gudun ta," oyoyo Papa,,jakar ya ajiye yai sama da ita yana dariya,"(missed you papa),ya sumbaci kumatun ta,(missed you too sweetheart).Murmushi Laila take musu,yana kallo ta da sauri ta mike tare da daina murmushin, "sannu da zuwa,kai ya daga mata yana kallon ta,sanye take cikin wani riga da skirt na kanti masu rawa,an musu adon net da stones, sun dan kamata kadan,kayan sun mata kyau,ta tufke gashin ta a tsakiya,a zahiri ita ko daurin zani bata iya ba,dan kayan ta duk English wears ne,sai attamfa ko les na riga da skirt,amma tun zuwan ta gidan ta ajiye, sai yanzu da damuna ta shigo ga zafi,mamaki ta ke kallon shi, yau d'aya ya amsa maganar ta,kamar wanda ya tuno abu sai ya dauke kai,Naina yake kallo,tana nuna mishi wai gyaran gashin da Momma ta mata,ya shafa kan,yana murmushi, daki sukai sai zuba take mishi,ido ta rintse tare sakar ajiyar zuciya,("thank God) yau ba'a sauke mata aradu aka ba,amma tasan a gyaran daki ko abinci za ai. Chan sai ga Naina ta fito da leda a hannun ta,dakyar take ja, wajen ta ta kawo,wai papa, cosmetics ne da tarikicen mai,kusan sati da cewa manta ya kare sai yau,sai dai ta shafa Johnson din Naina,sweets ne da tsaraba, ta cire ta bawa Naina,sai gashi ya fito," ina takardu na?da sauri ta mike,cikin in ina tace "suna drawer,kai ya kada, kan ya zauna a kan kujerar dining da laptop din shi,a hankali ta tako dan zuba mishi abinci,duk da tasan ba ci zai yi ba," indai ni ne na yafe,,amma ta dake ta cigaba da zuba mishi, sai dai ilahirin jikin ta karkarwa yake,a hankali ta dan kai gaban shi,dago wa yai fuska a murtuke,da sauri ta kautar da fuskar ta ta bar wajen, daki ma ta tafi kan ya fara sauke mata. "Papa,abinci,kallon ta yai,ya kalli abincin,shi ya zata ci zatai,kamar mai tunani, kuma dai sai ta dago ta ya daura akan dining din,shinkafa da taliya ne,sai miyar pepee chicken, chokali yasa badan yaso ba zai bata,sai ta girgiza mishi kai,hannu tasa ta dau zirin taliya takai bakin shi tana murmushi, kallon ta yake,yana kallon abincin, yunwar fa yake ji,amma dan taurin kai ya basar, murmushi yai kan ya bude bakin,sai ta sa mishi,ganin ya cinye ba tare da ya zuka ba kamar yadda suke da Laila yasa ta girgiza mishi kai, " papa cii''(see)dauka tai ta daga bakin ta sama sai tasa,a hankali ta zuke ta tana dariya,murmushi yai tare da kada kai,ruwan wankin hannun da Laila ta kawo ya ja,sai ya wanke shima ya fara yadda take,kan ya ankara har ya tashi da abinci sai nama,dan Naina taki ci,kallon shi kawai take tana dariya. Mamakin kanshi yake,naman ya fara ci,ya gutsura ya bata,sai ta girgiza kai. Ta fito taga basa nan,kuma ba (plate) din data zuba mishi,kayan ta debe,ganin ruwan yasa ta gane yaci abincin, baki ta tabe tai kitchen dasu,zama tai a parlour yau d'aya tai mar marin kallo,zeeAlwan ta bude,dai dai ya shigo Naina na bayan shi da plate a hannun shi yana mata wasa,yana ganin ta ya gintse,"ke,da sauri ta juyo tana raba ido,sauko da Naina yayi ya karaso, "waya fada miki ana kunna kallo a gidan nan? Ido yake zare mata tuni ya burkice kamar ba shi ke dariya yanzu ba,kuka ta fara tana Allah ya bashi hakuri, amma ina,sababi yake a ganin shi wani salon raini ne,shi tun bayan mutuwar Naina Tv sai dai yaga a wani gida,sai ita aka kawo ta da ita harda kara hada mishi (dish). " Salon wani rainin ne kuma haka? Hannu ya nuno mata," toh,ki kashe,tun kan na fasa Tvn nan a gidan nan, ya kuma zama rana ta karshe da za ki kunnan TV..Jiki na karkarwa ta tafi zata kashe,kuka suke harda Naina,jin sababin papan akan Momma,sai dai mey,ji sukai ance " Gidan mutuwa ne da baza'a kunna maka kallo ba? Da azama ya juya,dan jin wanda ke magana. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:50 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE " ©Feenat Ja'afar 8_Hajiya ce a tsaye take jin ikon Allah, da sauri Laila ta goge idon ta, tare da k'akalo murmushi, shikwa gogan yahau susa kai,parlourn ta gama shigo wa,"Sannu da zuwa Hajiya,,Lailan ta kalla,"yauwa sannu yar nan,tashi tai taje kitchen Naina na binta baya, kan ya gaida ta kai kasa,kai kawai ta kada mishi,sai ga Laila sun dawo ita da Naina, ruwa da exotic ta d'akko da cups, "Sannu Hajiya,ta zuba mata kan ta zauna gaida ta,,chan sukai shiru,kowa da abinda yake rayawa, Naina ce ta fara damun ta da Bambu sukai daki,kamar Hajiya jira take ta dawo kan Faruq," Yanzu Baba na haka kake tasa yarinyar nan a gaba kana mata sababi? Yaushe ka koyi halin da ba naka ba Faruq? Ko tausayin halin da itama take baka yi? Shiru yai yake ko tankawa,amma a ranshi tsabar haushin Laila yake ji,akanta yau d'aya yaga bacin ran Hajiyar shi,yai k'wafa a ranshi,tare da cewa,"Hajiya yi hakuri,,kallon shi take,tamkar ba Faruq dinta na da ba,bata taba haduwa da mai kulafuci irin Faruq ba,amma Allah yaga bazata zuba ido a cuci yar Jama'a ba. "Gaskiya banji dadi ba,ina son Faruq dina ya dawo na da,,kallo ai yana cikin abinda suke debe wa mutum kewa,barin ma ita,,nan tai tamai fada,tare da sanar shi yai mata alkawarin kallo a gidan shi da lumana..kai kawai ya daga mata. Laila tace ya kira,dan tace ma driver ya jira ta,badan yaso ba ya shiga,lokacin tana jijjiga Naina a baya kamar mai shirin bacci,ranshi a hade yace" kizo parlour,kai ta daga,yai wajen Bala Driver. Hajiya tai yin duniya ta fadi abinda Faruq yake mata amma tace ba komai,sai ma ta kara da ya hana kallon ne dan tarbiyar Nainan,tadai jita ne kawai, haka ta tafi tare da jan kunnen Faruq din. Fitar Hajiya da kamar minti biyar ya shigo gidan,zaune take ita kadai ta kafawa TV ido,jifi jefi tana dan jijjiga Naina da idon ta biyu. Harara ya aika mata,kan yace"wani abu kika ce ina miki a wajen Hajiya koh? Kai ta sadda kasa,tuni idon ta har ya duru ruwa,"Wato kin rabani da y'ata,Hajiyan ma shiga tsakani na zaki da ita? Kai ta girgiza mai,"kai haku..da tsawa ya katse ta,"ban son jin muryar ki,kinyi nasarar karya min doka 3,kar kiyi ta 4.. kai ta daga mishi,tuni hawaye har ya fara ambaliya,,kashe socket din yai kan ya wuce daki,Naina duk tana binshi da ido, tabbas tamkar mamakin papan nata take yanzun. Mutsu mutsu ta fara tare da kiran Momma,kunto ta tai,tare da daura ta akan cinyar ta,,Allah sarki,sai tasa hannu tana goge wa Momman hawayen tare da kada mata kai,murmushi tai mata, tare da kokarin hadiye kukan ta. Tsakiyar Damina ake, suna kwance ita da Naina ana ruwa,ga sai cida ake,kai Naina take kada mata da gwarancin bata son karar tsawar da ake,murmushi tai. Rigingine ta kwanta, tare da daura Nainan a saman cikin ta tana dan shafa bayan ta tare da mata wakar "Rain!Rain,,lamo tai tana kallon bakin momman tare da saurara kamar mai hadda. "Rain!Rain,,go away,,come back another day,,little Naina wants to play,,, Jin ta ambaci sunan ta yasa ta kyalkyale da dariya,, a haka wasa wasa har tai bacci,a hankali ta kwantar ta,tare da tashi dayin bakin window,magriba ce,amma gari duk ya hade da bakin hadari,ga ruwan da ake kamar da bakin kwarya,,cikin ruwan take kallo tare da tuno wani lokaci a chan baya,ido ta rintse hawaye ya zubo,tare da kiran" Mas'ood ".. Sakar labulan tai,tare da fita daga dakin,kofar kitchen dinta ta bude,tare da futa ta backyard din gidan, shimi ce a jikin ta iya gwiwa, sakamakon zafi da take ji kadan,ta kalli wajen Berry,ta shiga gidan ta tai lum,, ruwan ta shiga,tare da ware hannu a hankali,ta daga fuskar ta yadda ruwan zai na dukan ta,tare da rufe ido,(feeling)ta fara tamkar tana a tare da Maj'nu dinta ne a ruwan. Da sauri ya shiga gidan jikin shi jagab,sai tsaki yake zubawa, tunanin shi,ya zai da motar shi data kafe a waje,ya kara tsaki kan ya wuce daki, kayan shi ya sauya zuwa JC mai garen wando,,parlour ya fito,tsit kamar ba kowa,sai yai kitchen don shan ruwa,ya daga gorar ruwan yana sha ya kula da kofar Backyard a bude,ya sauke ruwan ya tafi dan rufo ta,iska ce tadan kara bude ta,a hankali ya karasa tare da tura kofar ganin kamar da mutum a wajen,a yadda ya ganta sai ya tuno da Naina,mai son wasa a ruwa ce,ko tace suje suyi wanka a ruwan sama,,sama ya kalla,tare da kallon interlock din,ruwa sai zuba yake,(imagining) yake,sai yake ga kamar Nainan ce,yanayin su sai ya burkice mishi ya zama d'aya. By Feenat Ja'afar

KADDARA CEWhere stories live. Discover now