[12/17/2017, 1:59 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 26_A hankali ta bude tana kallon abincin, sai ya sa mata,,tuni ta fara ci,yana bata,har sai da ta fara girgiza mishi kai halamar ta koshi,,Hajiya da ta leko a kitchen jin shirun parlourn, ta kada kai da murmushi ta koma ciki,tana Allah yasa hasashen ta ya zama gaske. Da dare sun hallara ana fira,Abba ya kallo Nainan da duk ta sauya,ba shagwaba yau...yai murmushi,"ni banga autar Hajiya na murnar ganin yayan nata ba fa Hajiya? Ko itama fushi take? Kallo ta Faruq din yayi,duk ta sauya mishi. "Atoh fushi ta ke,yazo ba Notice,koh Naina? Kai tai kasa tana murmushin. Har su Abban suka bar parlourn TV kawai ta tsirawa ido, ba magana.. Gogan sai neman fassara ta yake,amma da sun hada ido sai murmushi kawai. Matsowa yai wajen ta,,ta dan kalle shi,,"K'anwa ta..kai ta dago tare da amsawa a hankali,,"Naina da gaske fushi kike dani? Kai ta girgiza,,"toh kalle ni na ga,,kasa dagowa tai,sai dai murmushi take,,"OK. Fushi ne? Da sauri ta dago tana kada kai,, kallon ta yake,ido kamar mai fara jin bacci.. "(You know?) Kullum ina tunanin Naina ta,shine dalilin da yasa nace zanyi ba zata,dan ganin yadda kikai missing din yayan kin,, kallon shi take ba ko kiftawa..yana nufin itama yana tuna ta? Ko shima yana mafarkin ta?...katse ta yai"ba kiyi murna da gani na ba Naina? Kai ta girgiza,,"na yi..yace "sosai? Kai ta kada,,yai murmushi,"nima nayi,musamman da na ganki a uniform,,murmus
hin ta ne ya karu,,ya cigaba,kin san mey? Kai ta kada,,yace toh ta kalle shi tukun..kallon nashi tai,,ido lumshe yace "sun miki kyau.."sosai". Kasa tai da kai,tana murmushi,, sai jan ta da fira yake,so yake ta saki jiki dashi,,"ba kice min ya makaranta ba? Na gama? Hutu nazo? Ko aure ba?..da sauri ta dago tana kallon shi,,a zuciyar ta tana"Aure?..kaddai da aure yazo a daura mishi ya koma?.."Umm Naina? Katse ta yai,kai ta kada,kan tace"a a,,yai murmushi,"saurayin ki nawa? Da sauri ta kalle shi,, kan ta girgiza kai,,tana kallo yai murmushi, kan yace"good,,kallon shi kawai take,kamar ta fashe da kuka take ji..ba tasan lokacin da tace"kaifa? Sai kuma ta duk'ar da kai..tana juyo sautin murmushin shi,sai ta rintse ido.."ta wa d'aya ce..."Ba ka kwanta ba har yanzu? Hajiya ta katse su,,kai ya kada,kan ya tashi yana kallon Nainan,,"sai da safe Hajiya,,kai ta kada mishi tana kallon Nainan.. Tashi itama tai,kamar wanda k'wai ya fashe wa a ciki ta kashe TV.. Ba tare da ta kalli Hajiyan ba ta mata sai da safe..da kallo ta bita har ta kule,kan ta k'ada kai ta koma sama. Gado ta zube tare da jawo pillow,sai ga hawaye,, tsawan shekaru tana D'akon Son ya Faruq, in ya kira kamar abin kirki sai sun gaisa,ashe shi yana chan ya samu yar Thailand, ita kwa taki kowa..mirgina wa tai tare da matse ido hawaye ya zubo,ya kamata ta fuskanci zahiri,masu son ta da yawa, yanzu kam,yadda yayan nan ya dawo tasan ya mata nisa...sai hadaddu masu degree ko masters yan uwan shi,ba ita da sai yanzu ma ta shiga aji biyu a Nursing school ba. Haka dai da tunanin tai bacci. Shima a gun shi hakan take,tun da ya shiga wanka yaga ruwa,sai ya tuna yadda dazun Naina tai,ta bala'in kara mishi girma, ga k'yau da ta kara da nutsuwa..gata cikin karatun da yafi so tai a rayuwar shi har da uniform,wato Nurse,lokaci yayi da zai gabatar da son shi ga Naina,duk da ya gano tabbas tasan inda ya dosa. Da tunanin ta ya kwana,yana Allah-Allah gobe tai ya kai kanshi ga Naina.. Washegari da safe Jumma'a batta komai,malamin yai tafiya,kuma double ne. Suya take tana dan duba littafin malamin,, rigar bacci Cotton ce a jikin ta fara mai hannu iya g'wiwa, a gaban rigar an rubuta"what is Love?a jiki da fenti pink.. Zani ta daura kai,da kalabar ta yar kullum har gadon kafada,ta daura hula pink. Hannu ya harde yana kallon ta,yadda take karatu da hannu d'aya, hannu d'aya tana juya suya,,murmushi yai,kan ya karasa,,"ke d'aya? Zabura tai,har littafin na faduwa,dan ko sallama bai mata ba..kirji ta dafe ido a rufe,ta bala'in tsorata..kallon ta yake kan yace"(am sorry).. Duk'a wa yai ya dakko mata littafin,"kin fiya tsoro Naina..plantain ta kwashe dake neman kone wa,ya matso tare da daukar d'aya. Littafin yake duba wa,tai mishi ina kwana..kallon ta kawai yake da wani yanayi.. "Kin gama ne Naina? Hajiya ke magana ta parlour,daga nan inda take tace"saura kadan. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar 27_Ta dan sachi kallon shi,a kasa kasa yake kallon ta yana murmushi, sai itama ta k'akalo,,Parlourn tai yana binta a baya da flaks din tea,,suka jera ita dai kallon shi kawai take. Hajiya ta sakko"ka dawo ne Baba na? Kai ya daga,kan yace"ina Abba?koh bai tashi ba? Kai ta kada, yanzu ya gama jin radio ya koma,,Naina ta kallo,"sannu auta,ki hawo mana da namu sama,saukar nan yau wahala take ban,kai ta k'ada,kan ta koma kitchen ta debo plates,, zama taga yayi yana zuba tea,ta debi nasu Hajiya a flaks da sauran abun bukata tai sama. Samu tai ya hada musu tea yana zuba plantain da kwai ya sha sidin din gwangwani,a hankali taja kujerar ta zauna, ya dan turo mata nata, tadan yi yake,kan ta hau juya shayin,,"ki sha man,,kai ta kada kan ta deba a chokali ta kai baki,,plate d'in ya matso gaban ta,"bissmillah,,ci kawai take ba dan dadi ba,duk ya kan tsare ta da ido. Da yamma tana bayan gida ita kadai,littafi take dubawa,yamma da safe sune lokutan karatun ta. Taku taji ta gefen ta,tadan kalli wajen,shine janye da kujera fara yana mata murmushi,"sai kika gudu ina neman dan fira? Murmushi tai,da zai gane zaman su daga nesa zai fi kusancin su sauki a gunta,da yai nesa da ita..kai ita dama bai dawo kasar ba ma yafi mata alkairi.."Naina" kai ta dago tana kallon shi, tare da hadiye kukan ta..Ruwan da ke gabanta ta dauka zata kora ko ta samu sa'eda.."I Love You Naina...tari ta fara ba na wasa ba,sakamakon k'warewar da tai da ruwa,,tuni ya rikice,tare da kara tsiyaya mata ruwan ya bata,karba tai tana sha tana kallon shi,,Allah dai yasa ba mafarki take ba kamar yadda ta saba..murmushi yai tare ciro abu a aljihun shi yana kallon ta,,"na baki mamaki koh Naina? Kai ta k'ada halamar a'a,, tashi yai daga kujerar ya dawo kasan dardumar da take.."Naina ke ce kadai abar so na har kullum,,kallon shi take ba ko kiftawa baki sake,,shikam ganin haka yasa ya cigaba da tuna mata sirrin ranshi.."Yanzu kam,nasan lokaci yayi da zan sanar ki,,Naina, kaza,Naina kaza,kan ta farga har hawaye ya wanke mata fuska dan farin ciki,shikam tuni ya tsagaita yana duban ta,murmushi take,amma kuka take..dame zai fassara hakan? "Naina baki so na? Kai ta girgiza tana goge idon,,yace"kukan fa? Tashi tai ta dau hanya,binta yake,har ta kule,ya dawo kan littafin ta da cup din.. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:00 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 28_Kofar dakin nata ya tura bayan ya k'wank'wasa ta bashi izini,jin ba'a karaso ba yasa ta dago,hannu a harde yake kallon ta da littafin..sai kunya tazo mata hadi da murmushi, kai tai kasa dashi tana dan murmushi, labarin zuciya, Wai a tambayi fuska,tuni ya sau ajiyar zuciya,da k'warin g'wiwar shi ya karaso dakin,a gefen katifar ya zauna yana kallon fuskar ta. "Naina" tace "uhm,littafin ya miko mata,tadan kalle shi kan ta karba...fulanci ya fara mata"Eemi yiduomaa Naina"(I Love you).."uhmm,,(say something.. Please Naina) Murmushi take na farin ciki,tama rasa bakin bashi amsa,yai ta zaman jiran amsa,sai dai kunya ta hana ta bashi... Tashi taga yayi,bai sake cewa komai ba yai kofa zai fita..da sauri ta dago kai tare da cewa"Hamma"... A hankali ya sau kofar tare da tsayawa.. Ganin bai juyo ba yasa ta tashi ta taho kusan kofar,tai dai shiru,sai ya juyo yana fuskantar ta,,kai kasa ta dan dago,sai ta kara kasa da murya da kallon ta zuwa hannun ta da take wasa dashi,,yace"uhm,ya ne toh? Kai ta dan sosa, kan ta juya mishi baya,zuciyar ta sai bugawa take,a hankali tace"Eemi yiduomaa sarai Hamma(I Love you too)sai ta rintse ido bugun zuciyar ta na karuwa,, amm... Da sauri yace"Gaske? A juyan ta kada kai,sai kuma tai kan katifa tare da daura kai cikin kunya tana murmushi. Gefen katifar ya dawo ya zauna,baki har kunne..yana son kunyar nan ta Naina,musamman shagwabar ta na burge shi,hannu ya kai zai kama nata,da sauri ya janye yana rintse ido,,yasan yanzu sai yai lefi wajen Allah,,sunan ta ya kira,,sai ta amsa ba tare da ta dago ba. Abu ya ciro a aljihun shi,kusa da hannun ta ya ajiye mata yadda yasan taji, a hankali ta dago,karamar akwati ta gani ash da zanen heart a jiki,,dan tashi tai ta dauka,a hankali ta bud'e, tai mata kyau,tasan abun ciki ma zai kyau..sai dai wayam! Ba komai ciki. Kallo shi tai da halamar tambaya, sai ganin tai ya ware wata hadaddiyar sarka mai kama da English Gold da kamar heart a jiki da harafin"I. U",har heart din sai yai making"I Love you.. "Ga tsarabar ki...en tukuicin so na Naina,,(please marry me),dan ke na kasa karasa PhD na fa,aure nazo sai mu koma tare..murmushi tai idon ta na kan sarkar,kai tai kasa dashi,kan ta kada kai halamar yarda da zancen shi. Tun fa daga nan aka baje kolin soyayya a gidan Hajiya,,ranar data tabbatar da hasashen ta ranar Faruq din ne ya sanar ta da kanshi ba ko kunya...murmushi tai,dan ido dama ta zuba musu taga iya gudun ruwan su. Tunda ta sanar da Abba,sai yaso finta murna,dan duk Familyn kusan hadin gida ne,amma na Naina da Faruq yafi na kowa kusanci. Tuni zance ya watsu dangi a bakin Aunty Salma... Ganin fitsarar da Faruq yake gwadawa a gaban kowa yasa Hajiya tunanin aurar su ta huta,,dan abinci Naina,firfita,Naina,fira Naina,unguwa Naina.. Alhaji yai murna dajin auren,dan su kadai suka rage musu a yaran su,sanan tasan Naina ta isa zaman gidan miji, tunda shekara ashirin take neman shiga. Tuni aka tsaida rana wata biyar. Umar ne ya kalli Faruq dan dariya,,"tun da kazo garin sai yau da taka ta kwaso ka zaka neme ni..Faruq yai murmushi,"kai hakuri mutumin, kasan kai kadai ne gare ni a nan kusa,,harara yai mishi,kan yace"a wa ka ke tunanin yi kana dankare a d'aki kamar mace? Ai budurwa ma nasan sai dai kai ta cikin gida..nima na kasa yar ka ne,amma Aboki abun nema ne fa..tam. Shidai Faruq jin shi yake,shi hayaniya ce bai so ba wai abokai ba,sannan ya saba rayuwar cikin gida,in kwa a makaranta ce toh hostel. "Yanzu dai kai hakuri ka tayani nema, dan banson shigar kudin nan ba tare da na kama gidan kaina ba,,kallo shi yai,"kace saura wata biyar? Kai ya kada mishi,,"toh ka bani kwana biyu,zan ma cikiya.. Bayan kwana biyu ranar suna zaune parlour shida Naina,yau firar ta kurame ce da murmushi,,wayan shi ne yai katse su,ya dauka,Umar ne,hannu ya daga mata halamar zai amsa waya,sai ta kada kai,, cewa yai ya same shi a waje. Umar aboki ne d'aya ga Faruq, tun tasowar su suke tare,duk da abotar a gun Umar din tafi k'arfi. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:00 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 29_Gida ya kai shi in completed, sai dai har roofing anyi, gashi ba laifi da dan girman shi,,ga tsakar gidan babbab sosai..sai dai a yadda yai bayanin kudin ne yaji ina..ga unguwar ba jama'a shiru shiru dai dai yadda yake so..wajen Abba suka je ya sanar mishi,tare da Abban suka zo yaga gida yayi,kuma shi bai mai kudi ba ma,,shi Faruq lokacin yace yana da rabin kudi,Loan Umar ya bashi shawarar dauka,tunda Abba ya dauke mishi lefen da sauran yayyen shi,,sanin yana aiki,yasa yayan shi Abbakar wuce mishi gaba,dan a Bank yake aiki. Ba a dau lokaci ba aka hau plaster. Tuni shirye shirye ya bun kasa. Shin Ina Laila... Ciwan cikin Mas'ood karan nan ya kara tashi,duk da bai wani tsanani ba kamar kan auran su,sai dai ita gani take daurewa kawai yake,,duk da a hakik'a dauriyar kawai yake,dan yasan Laila da rikice wa,gashi komai ya kusa zuwa mata karshe. Tunanin shi,likita yace in yai aure zai daina ciwan,sai dai gashi shiru...Allah da ya taimake shi ma ya kammala koman shi. Kan wani lokaci ya mur mure kamar bai cuta ba,abu kamar iska. Rigima suke zasu fita, akan lalle sai yasa shadda tunda itama yau attamfa tasa..chakulkuli ya fara mata yana"kina son na wargaja fitar nan ne kila? Rana dariya tana sa mishi rigar,daina wa yai tare da zuba mata ido,,batai aune ba taji ya jawo ta ya kank'ame kam,,"ina sonki da wa my interpretè..mu zauna a haka pls..kara kank'ame shi tai itama,tana g'wada mishi kaunar ta gare shi,duk sai jikin su yai sanyi, ji yake kamar wataran za'a kwace mishi Lailan shi,,a hankali ya zaunar ta a gado, tuni ya fara mata kirarin nata,sai dai karan nan ta kasa dariya kamar kullum,ido kawai ta zuba mishi tana kallon shi,,"kimin alkawarin zama tawa har abada Laila..ya kamo hannunta tare da matse su,,"Laila ji nake kamar watarana zaki bar ni ne yau...da sauri ta hado shi da jikin ta tana shafa bayan shi,,"Laila taka ce Maj'nu.."dan Maj'nu kadai aka hallacci Laila,,daina ma fadar haka...ido rufe yace"alkawari? Kai ta k'ada"alkawari.. Dago ta yai,sai ta ga fuskar shi hawaye..tuni itama nata idon ya ciko,, kallon ta yake ba ko kiftawa, sai ta sa fuskar ta a tashi tana goge mishi ido tare da girgiza kai,,murmushi ya k'akalo,tuni ta fara sashi nutsuwa da salon ta,ba aje ko'ina ba har sun fara dariya kamar ba su ba. Hula ta daura mishi a kan,tare da juya shi mudubi ta kwanto a bayan shi suna kallon juna ta mirror,,tace "perfect" murmushi yai tare da juyo wa,kugun ta ya ruko yana sauke ajiyar zuciya,,"Laila ce mudubina ko kin manta? Hannu ta daura akan button din wuyar rigar tana gyara wa,"Maj'nu kuma mudubin Laila of course,,"kai kyau a shaddar Booohot,.ta ja mishi kumatu,,murmushi yai tare da matsar ta yana kallon ta daga sama har kasa..sai ta rike skirt din tana dan yin gefe da gefe tana fari da ido,,"da za ace na zabi miss Universe.. Ya rike haba,"I think ina da ita a kasar mu,sai tai fari da ido..ya cigaba yana matsowa,"a gidan nan,wato wify na...yakai hannu zai kamota ta zame tana dariya tare da daukar gyale tare da daukar takalmi,,"Allah attamfa na miki kyau..kai ta kada,kan tace"I know.. Kaima Shadda na maka kyau,,sunkuya wa yai yana daura mata buckle din takalmin hill,,kan shima yace"I know.. Murmushi tai,data tuna ranar haduwar su ta biyu. Haka suka fita gari, kowa ya gansu gwanin sha'awa, da kayan Arewa a jikin su,sai suka fita daban. A yanzu damuwar ta d'aya"ciki" kamar ruwa a jallo take sha'awar ganin ta da ciki. Shekarar ta guda! Kenan da aure,zaman gama sauran watanin ta yake su juyo gida. Wataran har mamaki take bashi,don duk randa ta bushi iska sai tace sai sunga likita,,sannan kullum zancen d'aya ne,"kalau suke" Yakan ce mata lokaci ne,kar ta damu. Cikin wasa tai da kayan ta,yai tsini kuwa kamar na gaske,parlour ta fito tana dafe baya irin na masu cikin gaske,waya yake,sai ya sau baki yana kallon ta, sallama yai da Zunnu kan ya hau mata sannu,kai take daga mishi dak'yar kamar gaske shima ya biye mata,,ta bankaro ciki zata zauna,da sauri ya sa mata pillow,,dariya ta gimtse, tare da fadin"thanks" sai ya kallo kafar, ya d'uk'a yana dan mammatsa mata kafar,, da kalar tausayi yake kallon ta,"sannu maman Baby,,kai ta daga tana lumshe ido..." kin lura da kumburin kafar ki kuwa? Ido ta bude,tare da girgiza mai kai,,kamar wani bawan ta haka yake matsa kafar,tuni tai baya harda fadin"wash..yauwa...better..daga saman K'afa ya dawo g'wiwa, da sauri ta bude ido hadi da mikewa tana sosa gun...jin hannun shi har zuwa cinya hadi da kai baki ya sau mata cizo kadan..sai ga ciki ya zubo,dan gown ne jikin ta,da sauri ya tare yana"ya zaki hullar da babyn k..bai karasa ba ganin tana kokarin daukar cution tana sai ta rama,d'aki yai yana mata gwalo. A haka rayuwar gidan Laila da Maj'nu take,ko anyi fada,a take za'a shirya,k'warai zasu baka sha'awa musamman in ka zauna dasu. ~~~~~~~~~~~~~ A Nigeria biki ake shirya wa na ban mamaki,bikin yan autan Hajiya biyu. Yau a ainashin gidan su Nainan ta kwana,tun bayan girman ta,in ka 'kalle ta babu wani sabo tsakanin ta da Umman ta,dan k'awaici take mata na y'ar fari mace a gun ta. Kwanan ta biyu,amma kamar a k'aya take zaune,burinta ta koma kusa da Hajiyan ta da Hamman ta. Duk da kullum sai ta ganshi a gidan,sai dai ya wayen ce da gun Inna Bilki yazo. Yau aka shaida auran Faruq da Nainan shi,bisa sadaki kadan,mai albarka,, duk kunyar Naina,a yau kam ta kasa boye murnar ta a fili,,sai dai in ta tuno rabuwar ta da Hajiyan ta tuni sai ta shagwabe fuska. Yanzu haka Lalle ake mata,amma tana kwance kan Hajiya ta mika hannun,Aunty Salma ke musu dariya,,"ki ma fa mike Naina,dan rabuwa ta zama dole. By Feenat Ja'afar. ®NGR WRITER'S ASSOCIATION (NWA)
[12/17/2017, 2:06 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 30_Da dare aka tattara aka kaita, rabuwar Naina da Hajiyan ta in ka gani gwanin ban tausayi,ta shaku da ita matuka,yadda take manta bama ita ta haife ta ba,,shi yasa daga kan Naina ta daina rukon yara,duk da gata da jikoki yanzun ta ko'ina. Bayan kowa ya watse an barta daga ita sai halinta,wayan ta taji tana kara,a hankali ta janyo ta,"6s Laila U.K" taga a rubuce, murmushi tai,ta kalli agogo kan ta daga,,"amarsu ta ango,ta Faruq ikon Allah. Murmushi tai mai sauti,wanda yasa Laila fadin"Umm Umm,yau dadi fal ranki? Karon farko Naina ta tanka,"sosai,ya Maj'nun ki? Tace"Lafiyan shi,,toh ya angon namu? Ko baya kusa? Kai ta daga jin sallamar shi a parlourn, gyalenta ta kara ja,ya kwanto fuskar ta,kan ta bata amsa,,zuba ta fara mata,kamar kullum murmushi take,na Umm tace Umm,ganin Faruq din tsaye yasa ta kara kasa da murya,,"rabo na da ganin ya Faruq fa kusan shekara biyar, har na soma manta kamanin shi.."hello? Ko angon ya zo ne? Murmushi ta sake,ba baki,kashe wa tai tana mata tsiya. A hankali ta dago,ta gyalenta ta hango shi,fuskar nan kamar gonar audiga, Shikam,bacin ga Umar,yana ga ba sai an sai mai bakin mata ba,shi kadai ya wadatar. D'akin ya tako zuwa kan gadon,zama yai yana facing nata da murmushi,,a hankali yasa hannunshi duka biyu ya daga gyalen nata,dagowa tai tare da sau mishi dan murmushin kunya,duk'ar da kai tai kasa,,sai ya dago habarta a hankali yana kallon fuskar tata,ido ta rintse a hankali hawayenta ya zubo,sai dai murmushin fuskar tata bai gushe ba,tuni yaga kamar an kara 'kawata mishi Nainan tashi. Duk abinda ya kamata su gabatar sunyi, yana ga baida matsala wajen tambayar Naina komai,dan shi sai dai ya ba wa wani, ka'r tasan ka'r ne. Daren Naina da Faruq kam, mai wuyar fassara ne,duk wani dangantaka ya kawar ta gefe,duk da a cikin rakin nata harda hakan tamai tuni,abun kam ba'a cewa komai,sai dai musu fatan zuri'a mai albarka. Washegari ita kam ras ta tashi,sai dai dan abin da baza'a rasa ba,a gaban madubi take,k'warai tasha mamakin yadda bataji abinda ake lissafo wa ana sha na wahala a daren farko ba,,murmushi tai,dan tuno da tsiyar Laila ta jiya. Agogo ta dan juyo ta kalla,jin shiru bai shigo ba tun dazun..kan ta kalli kofa jin ana kokarin budewa,,kai ta juyar kasa tana zira awarwaro da murmushi a fuska na kunya..yau batai tunanin zata ma iya kallon shi ba,amma tun asuba suke hada ido,,bata nufa ba taji ya sakalo hannu ta bayanta tare da ruko hannun ta. Kanshi ya daura a kafadar ta yana kallonta ta mudubi,tai k'yau abinta irin k'yau na amare. Juyo da ita yai,kanta na kasa tana murmushi, sai ya zaunar ta a gado, shi kuma ya kishingida tare da daura kai cinyar ta yana kallon fuskar ta..Dan kallo shi tai,kan ta mai sannu da zuwa..murmushi yake kawai,ba amsa,duk sai taji ta takura,hannun ta ya kamo yana kallon b'aki da jan lallen hannun ta. Yaja wata ajiyar zuciya, ji yai tamkar ana kara rura son Naina a ranshi daga jiya zuwa yau,yana son wannan dan murmushin nata mai cike da kunya. Ta ko'ina Naina tai mishi,musamman ta bangaren kamun kanta da tsananin kunya. Cikin nutsuwa kamar mai rada ya fara mata magana,kirari yake mata wanda tun fara soyayyar su ba ta taba ji ba,,take taji yana fasa mata kai,ji take tamkar ita kadai ta rage a wannan duniyar d'iya mace,,tuni sai ga hawayen dadi ya taru a idon ta ...fadi yake......"Ya Ruhii, "Habebtee K'albi" "inte Hayatee" "Wa Nurul aèini" "inte Omree" "ahh! Ya Helu(oh! Beautiful).."Muhibbi of the eyes full af tears..... ..... Sai kuwa hawayen da ya taru ya zubo yarrr.. Sai fuskan shi,,Faruq karshe ne,a fagen soyayya daga jiya zuwa yau Naina ji take kamar ita din sarauniya ce..lalle dole tai godiya da Allah da ya bata yayan ta a matsayin miji. Sai 12 ya bar gidan,shima dan ya ga yan uwa sun fara zuwa ne. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:06 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 31_Rayuwa yake gwada ma Naina tamkar ba gobe,,duk da wani abun in ya mata,takan wuni kunyar shi,shikam ko a jikin shi,wai an tsikari karkausa. Da dan guntun tarairaya da irin soyayyar da take karanta wa a littafin Hausa ta iya rike Faruq,, tuni kuwa ya sake sakar mata akalar zuciyar shi. Sati d'aya tai ta koma makarantar. Ko wata biyu ba ai ba ta san tana da shigar ciki. Sai dai tai shiru dan ganin ba mai laulayi bane. A U.K... Karatu Laila take ba kama hannun yaro,dan yanzu da aski yazo mata gaban goshi sai ya fara zafi,gaba d'aya burin ta taci exams din nan suyi su bar kasar,, dan tuni ta fitar mata a kai,ta gaji da yawo,, daga makotan ta sai gida sai makaranta kullum..Wai a hakan ma (18 month programme)ta dauka,da tabi ta Maj'nu da tuni 3years zata dauka. Rub da ciki tai tana solving wani formula,gaba d'aya ta tattara nutsuwar ta gun formular,yayin da Maj'nun ta ke kitchen hada mata "coffee". Kira ta kwada mishi da muryar shagwaba, kan yazo ya agaza mata. Sai gashi da tray dauke da kofuna biyu da coffee a ciki,,tashi tai ta dau nata tana mishi sannu tare da dan manna mishi...a kumatu,,yai murmushi tare da janyo kujera. "Yauwa My,ka gane? Allah na kasa gane ta ma ya zan solving wannan,, tashi yai tare da zama kusa da abinda take nuna mishin ganin yau ba wasa a lamarin nata. Tuni ya hau war ware mata matsalar ta wani formularn ba tata ba,sai ma taga dayar tafi sauki,,kallon fuskan shi take yi,duk da tace ta gane,har ta mishi ya gani amma bai daina mata bayani ba,,murmushi take lokacin da yace ta gane? Da k'arfi tace"Yes sirrr!!! Kai ya jijjiga,yasan tunda ta fara haka shikenan karatu yasha ruwan kanwa,, coffeen shi ya dauka ya sha,,tambayar shi take ina zai yi aiki in sun bar nan?yai murmushi, "Laila,kasar mu ta gado, InshaAllah nan zanyi aiki dan a karu dani,,tace"toh su momy fa? Coffee ya kara kurba kan yace"ai suma ba zaman k'watano zasuyi ba,kila kan mu koma ma sun koma Kano. Tai jim,gaskiya a yanzu burin ta su zauna kusa da mamy,,tai bala'in kewar su. Da taimakon Allah da taimakon Maj'nun ta tai jarabawa lafiya,tuni ya fara musu shirin tafiya,dan ba'a jima ba ta karbi sakamakon gama BSc Nursing dinta in Deploma. A k'watano suka sauka,duk iyayen sunyi murnar ganin su,barin mamy,ganin gashi har ta samu abin nema, ga ta kara cika mata ido. Watan su guda suka sauka Kano gidan su momy na chan. Shopping suka fito da yau a motar Abban ta gidan,in ka gansu ka dauka har yau a U.Kn suke,sanye take da farar rigar sanyi mai gashi gashi iya g'wiwa da wando baki.. sai ta nada gyale ya dan sauka bayan ta,da wani uban hill fari,ta maka wani uban su sunglass baki,light makeup tai dan pink jan baki..Gogan nata ma yasha kusan shiga irin nata,ya daura abu a wuyan shi kamar necktie babba,ka gansu kamar wasu yan chan. By Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 2:07 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar 32_Mota yake koya mata a tsakar gidan,bakin nan har kunne,tuni rawar kanta ya karu,dan yau har ya bata gwajin rike hannun shi suna tukawa a hankali. Washegari yana bacci da safe ta gama girki ta dau mukulli cikin sanda tai waje,,kunna motar tai,tukun ta fara kokarin tada ta kai na rawa, ko mai ta danna? Kawai ji tai mota ta debeta ta baya,tuni ta fara ihun kiran ta kasa controlling komai,tuni jiki ya fara karkarwa,, kamar a mafarki yake jin dirin mota acikin gidan,a zabure ya mike,sai dai kan ma ya fito yaji karar bugun abu a tsakar gidan.. "Laila" da gudu ya karasa wajen da ta buga motar kan ya bude yana kiran ta,ilahirin jikinta karkarwa kawai yake bata cikin nutsuwar ta,ga rawar kai,ga shegen tsoro.. Motar ya kashe da sauri ya fito da ita ya fara jijjiga ta da nufin ta dawo,jin irin sambatun da take na tsoro yasa ya fara duba ko taji ciwo ne,,sai dai ita har yanzun taki shiru,sai da ya rike kafadunta ya jijjiga da tare da cewa"Laila"da k'arfi kan ta dawo,kuka ta fara,dan ta bala'in tsorata,kira take yai hakuri bazata kara ba..lallashin ta yake akan ya isa,amma sai kada kai take,ganin kukan yana yawa yasa ya ciccibe ta zuwa cikin gida..Maimakon yai mata fada,a a,shi tausayi ma ta bashi,kamar yar baby ya kwantar ta yana lallashi.. Kira yake"it's Ok,,dakyar ya samu tai shiru ta nutsu sosai,wunin ranar cikin nutsuwa tai ta,duk sai ta bashi tausayi,sai dai tun daga ranar take dari dari da koyar mota. Yau kimanin watan su biyar da zuwa Kano,wanda tuni Mas'ood ya fara aikin shi da Lailan shi gu d'aya,, yai farin ciki sosai da suke asibiti d'aya,,zo kaga abu gun su a asibiti. Ana strike yau na doctors da Nurses,hakan ya basu damar shirin zuwa ga dangin Lailan Adamawa a satin nan. D'un d'umi_d'un d'umi suke a tsakar gida,turn na Laila ne,lallube take na neman shi yana zille mata,suna dariya,jin shirun shi yai yawa yasa ta fara laluben shi da gaske tana kira,hannu yake mika mata dafe da cikin shi dake mishi wani azababben ciwo,, Kunce daurin idon take da mitar ta fasa tunda bazai tsaya ta kama shi ba,,sai dai a yadda ta ganshi a kasa rike da ciki yana mika mata hannu yasa da gudu ta nufe shi,,"Maj'nu.. Mas'ood, mey ya faru?Duk ta rikice,, Jijjigashi ta fara,dan tasan bai fiya mata irin wasan ciwo ba,,tuni idon ta ya fara hawaye tana jijjiga shi, kokarin furta abu yake mata amma ya kasa. D'aki yake nuna mata,a hankali ta kama shi dak'yar suka mike,da sauri taje dubo maganin da aka bashi a U.k ta dakko ruwa,,tana kokarin bashi ya fara kela amai,tuni ta kara rikice wa,kuka take tana rurruko shi,,duka basirar ta kare,,kawai sai ta dakko waya ta maka wa Momy kira Cotonou,, da kuka take su taimake ta Mas'ood,, dak'yar momyn ta samu ta nutsar ta kan tai ma makotan su magana. Duk da itama daurewa kawai take momyn,amma tasan ciwan Mas'ood mai tsoratar wa ne,bare ga Laila. Allah ya taimaka aka kaishi asibiti da taimakon makotan su momyn,duk ya gama galabaita. Kwanan su biyu su momy suka karaso, sai dai ko su karan nan ciwon ya basu tsoro,dan har yau bai dawo d'ai d'ai ba. Ido ya bude yana kallon Laila dake rike da hannun shi marar drip,ta daura kanta a kan katifar tana kallon shi,sai dai a zahiri ta lula tunani ne da dan guntun hawayen ta wanda bata ma san ya farka ba. Daga mai jinyar,har mai zaman jinyar sun lalace a kwana 2,duk da a hakan ma yan uwan baban su Mas'ood din suna matsa mata taci abinci ta bar tunani. Gaba d'aya sai ta bashi tausayi,, hannun nata ya dago hade da hannun nashi, da sauri ta dawo hankalin ta tare da mai murmushi. Bakin shi ya kai hannun nata,da sauri ta rintse ido ta soma hawaye, kai ya fara kada mata,sai ya janyo ta gaba d'aya ta hawo gadon, kanta ya daura a dai dai zuciyar shi,ai kamar mai jira sai ta barke mishi da kuka. "Shhhh,it's Ok Laila..dak'yar ya samu ta daina kukan da sambatun kar ya batta. Ajiyar zuciya take, irin na wanda yaci kuka sosai,ta kurawa fuskar shi ido,,murmushi yake mata tare da shafa bayan ta. K'wank'wasa kofar akai, a hankali ta tashi a jikin shi da fadin Bissmillah. Momy ce da K'anwar ta da k'wando a hannun ta. Tashi Lailan tai daga kujerar,da sauri momyn tace ta zauna, duk tausayin su take,tasan ko ba aure,Laila da Mas'ood akwai shakuwa a tsakanin su. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:07 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 33_Sai da yai kwana 5 aka sallame su,tun achan sun rasa musababin ciwan na Mas'ood, suma yan uwan shi doctors na nan suma sun rasa cutar,kai wai sai suka duk'ufa mishi adu'a. Su Naina dasauran yan uwa duk suna ta kira mishi sannu. Zaune suke a parlourn da momy sunyi bak'i an jingina mishi pillow,, Dr Auwal ne da matar shi,bayan sun gaisa momy ta basu gu,Laila suke ma tsiya lokacin da take tsiyaya musu ruwa. Murmushi kawai take tana kallon Mas'ood din,"sister Laila gobe fa zamu wuce inda muka fi k'wari,,murmushi tai,tana ya gaida mutan chan,nan yake sanar su burin shi na son komawa dan dama Horsemanship ya kawo su Kano,yan Adamawa ne. A Adamawa. Zaune take a kasa kan tuntu,taci dauri, ganan cikin ta dan (8month) a gaba,ta dan dafa kasa,zanen ta yake yi,wanda duk randa ya bushi iska sai yace ta zauna, haka zai zana ta kamar ka kirata tazo. Dafe da kugu ta tashi,da sauri yazo ya kamata,"in ina kusa na fada miki kina min magana in zaki tashi,kai ta kada mishi tana murmushi, kan taje gun zanen, a hankali take shafa shi,kamar hoton ta ya lika, tsugunawa yai gabanta kamar mai neman gafara,kunne ya kai kan cikin ta,ya hau shirmen shi kamar kullum ga cikin,in tace ai shi kadai yake abinshi,yakan ce babyn na jinshi.Kanshi take shafawa tana murmushi. Wayan shi ne yai kara,tun da ya fara maganar ta fara yatsina fuska,don jin zai fita,rarrashi ya fara,kan tai hakuri,wani ne ya bashi aiki,zai je su duba filin. Kai ta k'ada mishi,da murmushi ya hada goshin su tare da bata...yai kofa,,tana ganin ya kai kofa ta fara wash Allahn ta... Hararar ta ya juyo yana yi cikin wasa,yasan na karya ne,kai ya langwabe mata yana hade hannun shi waje d'aya. "Naina pleassse... Kafada ta make,halamar taki,ita kawai in bata son yai nisa yanzu zata tada ciwan karya. Dak'yar ta barshi da lallashi ya fita kiran. Washegari Hajiyan ta tazo,kan batu d'aya na su tafi gida ta haihu a chan,amma fir gogan ya hana,da Hajiyan ta fara mishi fada kuma Nainan zata hau langwabe kai cikin shagwaba, yauma hakan ta faru,Hajiyan ta kada kai,ya ta iya mata,haka ta hakura ta k'yale ta. Sai dai sun nemi in haihuwar ta kusa sai inna Bilki tazo ta zauna. Ciki ya rike yana kiran "help me Laila.. Kokari take taje gare shi a saman kujerar da kukan ta,kan ta karasa har ya fado kasa. Kwala ihu tai tare da kiran "Mas'ood"...a firgice ta tashi daga mafarkin tana neman shi,baya kan gadon,da sauri ta yaye bargon tai gefen gado da sauri,,da gasken shi ya fadi rike da ciki ba mafarki ba..Tallafo shi tai da salatin ta tana kira,sai dai ganin kumfar da ke fita ta bakin shi yasa ta kwala ihu,momy take kira,sai dai ina,bama wanda yaji ta,ita kuma ba abin ta tashi ba ya rukunkume ta,,hannu tasa tana goge mishi kumfar bakin nashi,,kuka take tare da girgiza mai kai,,fadi take"Stay with me"please...zama tai dirshen a kasa,tare da janyo shi jikin ta tana kuka tana kallon kofa,, zuwa wani lokaci ya dan lafa mishi,,hawaye ke gangaro mishi a ido yana kallon ta..karan nan bai hanata kuka ba,sai ma murmushi da yake yana shafo fuskar ta. Maganganu ya fara mata wanda tuni ya kara karya zuciyar ta,ji take dama cutar nan ta Mas'ood ta dawo jikin ta, bata iya jure ganin wahalar shi duk randa ta tashi. Ta tuna alkawarin da ta mishi kawai yake fada,bazai iya in ba ita ba,kar ta barshi,,rungume shi ta kara yi tana k'ada mishi kai da kuka,,tare fa fadin tai mishi,,shima yai mata alkawarin bazai barta ba duk rintsi... Murmushi yai,shi kadai yasan mey yake ji..kai kawai ya daga mata tare da fadin yana son ta(Laila Maj'nu),ta rike a ranta. Kai ta kada mishi,tare da fara sumbatar ko'ina a fuskar shi,ta kasa tsaida kukan ta, kamar yadda a karo na farko Mas'ood yaga tana kuka bai hanata ba. Da jan jiki ta mika hannu ta dau wayar shi a bed side,,fada mishi take bari ta kira momy,ga Abba ya koma. Murmushi kawai yake mata, har ta fara dailing numbern momyn.. Itama momyn dai dai ta tashi tai alwala zata tada sallah sakamakon mafarkin ta,taga wayan ta na haske,,wajen ta tafi tana karasa sanya hijab dinta. Ganin Mas'ood a rubuce ta matukar tsorata.. Da sauri ta dauka,sai dai tana dauka taji Lailan na kiran Mas'ood din cikin kuka,,kiranta take,amma ina.. Da sauri ta bude kofa tai d'akin nasu sai ga Lailan ta fito zatai kitchen da gudun ta,binta tai da kira har kitchen din ta dau ruwa,sai a sannan ta kula da momyn. "Laila mai ya samu Mas'ood din? Da sauri ta ruko hannun momyn cikin kuka,"mom Mas'ood.. nuna mata hanyar d'akin nasu take,sai dai maganar ta makale,ji tai numfashinta na sama sama,kawai sai ta ja hannun momyn,rike da ruwa da kofi. Tari suka tarar yana yi,ga nan kumfar dazun ta dawo,da gudu momyn ta karasa tare da tallafo shi tana kiran shi,,kan ta kallo lailan da tai turus baki sake tana kallon su hawaye na zuba.."Laila ban ruwan nan...a tsorace ta kallo momyn,takowa take kamar zata fad'i tana furta Mas'ood.. Ruwan momy tace ta bashi,bari ta kira su kaishi asibiti. Hannu na kar-karwa ta tallafo shi,duka ruwan baya zuba mishi,harshe ya karye,a dai dan karatun ta,tasan wannan gab'a ce ta mutuwa.. Kai ta fara girgiza mishi tana sambatu.."kar kamin haka Mas'ood..''kar karya alkawarinmu dakai Maj'nu.."kar muyi haka da kai.... Momy ce ta shigo,tana sanar da makociyar su,,turus,taja ta tsaya,ganin yadda Lailan ke sambatu,ga Mas'ood din idon shi kanta bai ko kiftawa, da ta karasa tana kiran Mas'ood din.. Hannun shi ta daga,sai taga ya sake,,jijjiga shi ta fara,tana kiran shi,, kallon ta Lailan take,tana kallon Mas'ood din dake kallon ta,,take taji K'wak'walwarta ta daina aiki,idon ta tsaf ya kafe,,bakinta ya mutu..kai kawai take iya girgiza wa momyn. tashi tai tana ja da baya jin..momy na kiran"innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un.."Mas'ood..." Mas'ood... By Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 2:08 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 34_Kunne ta toshe,lokacin da taji an tokareta ta baya,idon ta kamas,,naiman kukan take,sai dai tunanin ta ya kasa bata shi,kallon momyn take,kuka take tsakanin ta da Allah ta rukunkume gawar a jikin ta,k'wata k'wata bata ma jin mai take cewa..nata kawai ido. Buga kofar da ake ne yasa momyn tashi,tasan makotansu ne,wajen Lailan tazo,daga ita sai riga doguwa ta bacci, hannunta ta kamo,duk inda tajata nan take yi,sai dai idon ta na kafe a Mas'ood... zani ta dakko da hijab ta daura mata,ta zira mata hijab,kan ta fita bude gate. Har d'akin suka shigo shida babban danshi da maman su,tsohon likita ne da yai retired. Duk wani dube da ya kamata ai yayi,Mas'ood d'ai ya rigamu gidan gaskiya. Take ya kira Abba,wanda shirin shi gobe zai nufo su,ashe ba rabon zasu gana.Haka suka karasa safiyar su da jimami,sai dauriyar Laila suke gani da kara bata baki,sai dai ita bata ma san sunai ba. Washegari karfe goma aka fito za'a kai shi,da ido kawai tabi makarar,har yanzun mikis ba kuka... Abban nasu ne ya fadowa Abban su Laila, inda ya bari suyi booking dasu Zunnu. Sai ya fadowa yan Adamawa,sai gasu a ranar mazan da wuri,su biyar, Faruq, da yayan shi da uncles nasu biyu,sai yayan mamy,matan ne kusan yamma suka karaso. Sukam mazan a ranar sukace zasu juya,Faruq ya bar Naina,su kuma gobe Aiki. Tun suna ganin dauriyar Laila suka fara tsorata da lamarin ta,komai sai ana agaza mata take,alwala,sai an kama hannunta ana magana tukun ta fara,,yanzu su burin su tai kuka koh ta ware,amma ina,sam kukan yaki zuwa,abinci yadda suka sa mata a baki haka take hadiya. Washegari su mamy suka zo,bayan sun gama gaisawa dasu momy sukai d'akin Lailan. Tana k'wance a cinyar Hajiya,tofa mata adu'a suke, dan a tunanin su ko ta zauce ne,da ido kawai take kallon su.. Zama mamyn tai a gabanta,tabbas tasan haka zata iya kasancewa da Laila, kila kam ba'a hankalin ta take ba. Kanta ta dafa,kan ta kira ta,"Laila" a hankali ta dago tare da kallon mamyn, tasar ta Hajiyan su Faruq tayi, kallon mamyn take ta kasa mata magana,,bayani su Hajiyan suke wa mamyn kan Lailan,kallon ta take da tausayin y'ar tata,,kafad'unta ta kama,kan ta fara jijjiga ta,"Laila"..tai shiru,sai ido take sa mata, "Laila".. Da k'arfi mamyn ta k'wala mata kira tare da girgiza ta,take ta tsorata tana kallon mamyn,sababi aka fara ma mamyn,kan daga zuwan ta zata rikita ta.."mamy''... Da sauri suka k'alli Lailan jin tai magana,, sai ta hau sambatu kuma,hannun mamyn ta rike,"mamy Mas'ood.. Hannu take yarfe wa,kamar irin yarannan in sun so abu,sai ga nan hawaye wani ma bin wani,,"mamy ya barni,,, hannun mamyn ta kara janyo wa,tana son magana numfashinta na yin sama.. Ruwa Hajiya tace a kawo da wuri,jin kukan Lailan yasa Momy zuwa da sauri,,ai tana ganin momyn ta kara barkewa da kuka,,kirjinta take nuna musu,sai numfashi take ja tare da yarfe hannun ta,,da k'yar ta tattaro kalmar da take son fada,"momy mutuwa zanyi,, a.."A."Allah mom.."wayyo Mas'ood...kamar mai Asma ta fara,tuni kuka ya dawo musu sabo,,tausayin ta ya rufe su,, duk suna kanta sun rufe ta,Aunty Salma ta bada ruwa,ina,ana bata tana tankwabar wa,,kawai kira take mutuwa zatai tare da kokarin jawo numfashin ta dake barazanar dauke mata. Tashi Mamyn tai tabar d'akin, bataso ganin mutuwar y'arta a gabanta ba. Kiran Abba momy tai. Ba'a jima ba saiga su Abban su Mas'ood din sun shigo da doctors biyu abokan Mas'ood da suka zo gaisuwa. K'warai sun san Laila da Mas'ood, ko a su,basu da sunan kiran su sai"La'ila Maj'nu''... Abban d'ayan Doctorn ya kallo,,"ina ga Alhaji ku k'yale ta tai mai isarta,don yanzu bazataji lallashi ba,sannan da damuwa,kar mu bata magani ta haddasa wani abun. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:08 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 35_Sai dai duk yadda suka zata abin ya gagara, karshe sai asibiti sukai da ita.. Tabbas Mas'ood mutum ne harda guda. Duk mutuwar shahidai yai ta ciwan ciki. Kuka reras Faruq ya tarar tana yi a parlourn, dan yanzun suka gama waya da su Hajiya..tabbas ta tausayawa Laila, dan tasan sun shaku matuka da Mas'ood. Lallashin ta ya fara,tare da bata baki kan duk'kan mai rai mamaci ne..cikin kukan take tambayar yaga Lailan? Yace"bai samu shiga ciki ba shi..ta sunkuyar da kanta kasa..habarta ya dago tare da girgiza mata kai yana goge mata hawayen"Naina dole akwai mutuwa..kallo shi tai,tare da rukunkume shi,,"bana fatan ka tafi ka barni, Allah kar ya nunan ranar,,gwara ni n..."Naina" cikin tsawa ya katse ta,"(please) kasa tai da kanta,dan subutar baki tai,"ba'a wasa da mutuwa.. "Ki cire min wannan cikin wasa..tuni zuciya ta motsa,har ya tashi ya bata waje. Da kallo ta bishi,tasan yau kam sai tai da gaske. Har tai bacci bai dawo ba tara.. Ita kam tuni tai uku. Sai dai da ya dawo ya tasata a gaba,tunani ya fara kan ya ma zai kasance ba Naina? Da sauri yai istigfar ya kwanta tare da zuwa gare ta sosai. Kamar kullum tunda cikin ta ya girma saita tashi cin wani abu cikin dare. Motsin tashi take,duk yai mata dabaibayi,ido ta zuba mishi,tana tuna wani abu. Warai ya bude idon shi a kanta,sai ta marai rai ce mishi,,ya gano mey take nufi,dama da zai kwanta sai da ya shigo da shi,tashi yai ya hada mata cornflakes da madara kan ya dawo gadon,sai binshi da kallo take,har yanzu fushi yake. Zama yai yana juya mata,sai kokari take su hada ido amma yaki, debo wa yai kamar kullum yana bata a baki har ta gama,kan ya dauke ya sake kwanciya. Yau ko dan kirarin da take ji ya sata bacci bata samu ba. Washegari zata awu,ta gama shirin ta ta yafa gyalen ta kato ta fito parlour,yana zaune jiran ta,,daga inda take ta tsaya taki zuwa ta su tafi,sai ya kallo wajen jin tana dan kiran washh! Da k'arfi,juyo wa yai kan ya dauke kai,da taga wannan bazai ba,sai ta fara kukan b'aci,harda buga kafa bata ko jin nauyin cikin ta.. Dolen shi ya tashi kan tai mishi ta'asa. Hannu ta daura kan kunnen ta,halamar yai hakuri.. "(Ok,) amma Naina please, wasa irin wannan ban son shi..kai ta daga mishi,sannan sai ya biya bashin jiya,sai yai murmushi kan matso tare da dago habbar ta ya fara mata,"Ah Naina" Ya Bajat Al-Ruhh"Habebtee,Hayatee(my Love,my life) " soul of my soul" the most beautiful I have ever seen.. Murmushin ta ke karuwa,yayin da take kara jin fasuwar kanta,kai ta kwantar a jikin shi,tare da sakar ajiyar zuciya. Yau kimanin sati uku kenan da rashin da Laila tai,rashin da take ga bazata iya maida ko da rabin gurbin shi ba,sati biyu tai a asibiti, ganin kullum allurar bacci kar tazo tai mata illah a gaba,Abba yasa a sallame ta. Babu yadda zakai ka gane Laila in ka ganta, duk ta sukurkurce,abu kadan kuka,koh Laila tashi kici abinci akace yanzu zata fara hawaye. Kullum sai nasiha momy take mata,akan adu'a yafi bukata. Jingine take a gefen gado da charbi a hannun ta,wajen da Mas'ood ya rasu take kallo,sai ga hawaye.. Duk ta rame, ta kode, sai ido. Abinci Naina suke ci da Faruq,yau sukai zai d'akko Inna Bilki dan zama dasu ko da ya fita office. Taci kwalliya irin wacce tun kan cikin ta ya tsufa rabonta da irinta. Murmushi take aika mishi mai tsadar gaske, shikam gogan duk ya sukukurce mata.Fadi take"so nake na haifo baby mai kamar ka Hamma...Abinci take bashi da chokalin hannunta tana mishi tadi baby. Wanda ada,in yana yi sai dai tai murmushi cikin kunya,sai gashi yau ta badawa idonta toka. Chak! Ta tsaya da bashi abincin tare da yatsina fuska,,sai dai ta daure, ta kara diban wani ta kai bakinshi,sai dai kan ya karba ta sau chokalin kasa tare da rike kugu da "washh"..hararar wasa ya mata,kan ya dau chokalin ya cigaba da ci..dauriya ta fara,sai dai tuni har ta fara zufa. Sai da ya koshi ya zuba ruwa yana kokarin tashi ta kara Fad'in"wassh d'inta na biyu ne yasa ya kalle ta,,shi take kallo,fuska a marai rai ce..yace "please Naina,let me go..kai ta girgiza mishi,sai ta kasa magana. Key ya dauka na mota tare da kunna mata TV,"kin fiya rigima da neman tsokana, Oya, zu ga nan kallo ki fara yanzu zan dakko ta na dawo..(give me a hug) ya ware mata hannu,sai dai ita kasa take kallo dafe da baya. Ganin bata da niya yasa yace shi toh ya tafi,dan in ya biye ta ba zaya na fita ba. "Hamma" ...a hankali ta furta,yana tafiya yace"yanzu Hamman zai dawo,har da dan gudun shi yai waje. A hankali ta sakko a kan kujerar dining din,jin abu na bin kafarta,tabbas tasan haihuwa ce,duk da saura week d'aya EDDn ta ya cika. Baki ta rufe,jin ta fara nishi, wanda tasan labour ke tafe,a iya sanin da tai wannan gabar kusan fara labour ne,sai dai batajin duk da tana Nurse, zata iya karbar haihuwar kanta da fari. Hawaye ta fara,tana kallon kofar da Faruq d'in ya bi ya fita...sai ta rintse ido,yau ga ranar labourn gaskiya amma dake ta saba na wasa Faruq bai kula ba. Da tata tai wajen TV ta ciro wayan ta a chargy,ta dan tsaya tana numfashin waje,kan ta fara dailing numbern nashi,, shiru taji, tana dubawa taga ansa mata"user busy.. By Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 2:10 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 36_Baki ta cije,tare da zata dafa kasa,cikin ta taba, taji tabbas komai yai kasa..wayan ta kara dauka,tana dan nishi a hankali na waje,,har yanzun line busy,da yasa waiting call da zaya ganta.. Yau d'aya, tai nadamar wasan naguda,,kaichon ta,adu'a ta fara karanto wa,tuni zufa har ta bai baye ta,ga karar TV,ga azabar ciwo,ga baya ya rike. Hajiya ita ta fado mata,da sauri ta dau wayan,ringing take ita shiru ba'a dauka ba,,tuni sai ta barke da kuka,meye ranar wannan? Ga dry labour take... "Assalam Alaikum, Naina,lafiya kike kuka? Da sauri tace"Hajiya ki taimake ni,zan mutu.. Tuni ta ruda ta kira take "ina Faruq din? Ina kan tai magana ta fara amai,da sauri Hajiyan ta ajiye wayan tai d'aki. Kan su karaso tuni amai ya gama galabaitar,Hajiya ce da driver, ganin ita kadai ce yasa ta shiga makotan ta na chan gaba da ita. Wayanta ke ringing, ta kuma san ringtone din Hamman ta ne. Hannu na karkarwa ta dauka. "Ya akai? Gani ga Inna,tana ta tsiya wai sai yau,da mu bari sai kin haihu na dak..."Hamma" cikin kuka ta katse shi,,take Y'aji gaban shi ya fadi. "Naina(,are u ok?).. Kai ta kada mishi,"ka yafe min Hamma..tuni ta fara kakarin amai,Inna Bilki dake kallon yanayin shi ta fara''Lafiya? Ina ai tuni yai hanyar waje,da sauri ta ruko shi,,"Faruq,lafiya? Duk a rude yace"Naina,,inna mu tafi,ko ki bari naje na dawo. Shigowar su Hajiyan ne yasa ta kallon kofar a galabaice,"Innalillahi, Naina? Sannu,ina Faruq din? Subhanallah,, ga irinta nan ai,fir nai dake ki dawo gida dan gudun irin wannan bacin ranar,amma kikai ta biye mishi..kamo ta take,sai fada take,"ga yanzu nagudar ta tashi bayanan. Kai kawai take k'ada ma Hajiyan,taya zata fara sanarta laifin ta ne ba na faruq ba? Ciccibar ta suke,sai dai komai ya sake mata dan galabaita,,wayar Faruq din Hajiya ta fara nema, dan ita tama manta bata fada mishi ba..gasu a hanya kawai yace.. Tuni tausayin Nainan nata ya rufe ta,ruwa ta dakko ta bata marar sanyi, kan ta hau gyara wajen. Ba a fi minti 5 ba suka zo shi da inna. Amai ya samu tana ta kwarawa,da gudu yai gunta yana kira,ganin yadda duk ta rak'wark'wabe a abinda baifi minti arba'in ba. "Hajiya muje asibiti,,kai ta k'ada mishi,"dama kai muke jira,ganan ranar da banson zuwanta. Amma ku yaran zamani baku hango abinda ake hango muku. Shidai baya ma jin mai take fada,kawai ta Nainan shi yake. A asibiti sai fama suke da ita,dan ta kai karshen cm,ganan baby na kokarin fitowa amma uwar ba ta da k'arfin nishin.. Ga suna gudun kar tasha ruwa babyn.. Roko yake ma in charge din kan ya barshi yaje ga Matarshi, sai dai sun sanar shi ba hali,don ba ita kadai ce a laboun ba. Hakuri Hajiyan da Inna Bilki suke bashi. Zani akace su kawo,aiya,su duk sun manta wannan ai,,gidan yace zaije ya d'akko, sai yace wa drivern su Hajiyan kawai ya tafi,daga nan ya fado wa ainashin gidan su Nainan. By Feenat Ja'afar. [3/3, 12:10 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 37_Akalla ya dauke shi kusan minti goma sha biyar,duk da gani yake shi ba wanda ya kaishi sauri,Rio ya dakko da kayan baby aciki unisex, dama suna ciki abinta, sai kayanta set biyu da zani spare kamar yadda Hajiya tace. Fatan shi yasa yana zuwa ta ware.. Sai dai gaba dole su guji wasa irin wannan,ko dan gudun afkuwar matsala. A yanayin da ya gansu a kofar labourn,take y'aji zuciyar shi ta tsinke, duk ganin shi yasa sun fara dan saita kan su. "Hajiya ya Nainan? Ga kayan...inna Bilki ce ta kasa danne kukan ta. Da sauri ya saki kwandon kasa. Ido ya zuba musu,sai ga nan likita ya sake fitowa. "Yauwa bissmillah.. Hajiyan yake kallo da inna,sai tai saurin kawar da kai tana goge hawaye. Yana barin gurin inna ta fara fadin"Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un..ni Bilki Shikenan kuma. Hajiya ce ta fara lallashin ta,ganin jama'a har sun fara basu bakin "sai hakuri. "Wayyo Naina" Allah ya jikan ki..kuka itama Hajiyan ta fara,ganin Inna na kara karyar mata da zuciya.. Waya ta dauka,kan ta kira Abban da Aunty Salma. Nainan ta guda,tamkar ya dubu ce..kofar take kallo,tunawa da Faruq.. Wane hali yake ciki yanzu? Ya yayi da ya riski rashin Nainan? Tafe yake yana hada hanya,da sauri sukai kanshi zasu rike shi ya daga musu hannu.. "Faruq kai hakuri,,duk dummu na chan ne,cewar inna.."kai ya k'ada.. Kan ya zauna a dandamalin kofar. Gani yake karya Dr ya fada mishi. Shin zaya gaskata likita ne? Ko kuma zuciyar shi?.. Kukan da y'aji a kanshi ne yasa ya dago,Aunty Salma ce da Maman Nainan sai Abban su da Abban Nainan..da mamaki yake binsu da ido. "Ba fa gaske bane Aunty Salma..kai yake kada musu"kuma daina zubda hawayen ku..,"Naina nasan bata mutu ba..zamuyi Shari'a da duk wanda yace ta mutu wallahi.. Likitan nan mai rabani dashi sai Allah..(sorry 4 your lost)..Kalmar likitan yake tunawa. Likita ne ya fito da Nurse biyu,rike da baby a koren k'yalle suka bawa Hajiya kan suka dau rion suka cire zani. kallon Drn yake,wanda ke wa su Abba bayanin za'a a fito da gawar wai reception... A fusace ya mike,tare da kama kwalar rigar Drn.."ba kaji mey na fada maka aciki ba koh? Da sauri su Abba sukai kanshi,,"ni zaka raina wa hankali? Dama dan haka kaki bari na shiga?..Kokarin bambare shi Abban ke yi da fada,sai dai shi kamar wani mahaukaci yake masa masifa..shiru likita ya mishi,dan yasan duk a cikin shock ne na rashin Matarshi.. Dak'yar suka bambare likita,"ka dawo hankalin ka, mutuwa ajali ce..tanan ne ajalin Nainan ka.. Ina so kai saurin jawo imani kasa tawakalli a ranka Faruq.. Cewar Abban Nainan. Murmushi yai musu,tare da ja da baya yana k'ada kai,Abban Nainan zai bishi Abba ya rike shi, sai kan su aune har ya bar harabar gurin, kiran shi suka fara, tare da bin bayan shi,tuni ya shige mota yai reverse..sai dai suyi fatan ya sauka lafiya. A parlour ya tsaya,mai gadi ya bish da kallo,jin ko kashe mota bai ba kuma ya shigo kamar ba a hankalin shi ba. Kan Table d'in ya kalla, awa biyu dazu suna kai tana bashi abinci a baki..oho? Dama wannan murmushin yaudara take mishi? Dama tafiya zatai ta barshi ba koh sallama? Tvn ya kalla, a channel da ya bar mata har yanzu shine. A hankali ya taka kan dining wajen kujerar data zauna,ko kayan abincin ba'a debe ba. Kofin ya dauka,wanda tasha ruwa dashi,ganan shatin bakinta akai, jambakin ya fito..hawaye y'aji ya zubo mishi,bai san lokacin da ya daga kofin ya kwadawa Tvn ba..sai yai kasa ya tarwatse.. D'akinta ya nufa,komai tsaf-tsaf..sai kamshinta ke tashi,wai fa Shikenan Nainan shi,kamar anyi ruwa an dauke.. A gadon ya zauna,hawaye wani na bin wani..ya kai hannun shi kan bedside inda hotonta yake a dankaramin frame na auran su. Murmushi take kamar ka kirata ta amsa. By Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 2:16 PM] Feenat Ja'afar: [3/4, 12:45 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 38_Zamo wa yai kasa ya zauna a kasa...kamar wani mace haka ya dinga kuka baji ba gani.. Mey ya rage mishi a duniyar nan na jin dadi in ba Naina? Zuciyar shi tafasa kawai take,amma ya kasa ko k'wak'waran motsi bare ya koma ya ga gawar Nainan. Kofa yaji an bud'e, ba tare da ya dago ba ya fara shi a barshi,kar a bashi hakuri..Dafa shi akai ana jan hanci,halamar kuka,"Faruq, ka kasance cikin masu dauk'ar K'ADDARA.. Ka dauka K'ADDARA CE ta rabaka da Naina,,ka kuma gode Allah da yai maka k'yautar wata Nainan... Da sauri ya dago,tare da kallon Hajiyan,kuka itama take,don ita a ganin ta ba mai gwada mata son Naina. Kafafun Hajiyan ya rukunkume tare da daura kanshi,,"Kenan ta mutu da gaske Hajiya? Da gaske ta tafi ta barni ba ko sallama? Meyasa zatai haka Hajiya?.. Kanshi ta fara shafawa.."Faruq mutuwa ba ruwanta da sallama..ita kanta Naina bata mata sallama ba bare ta sanar ka.. Yanzu abu d'aya tafi bukata a gunka Baba na,"adu'a".. Dak'yar ta lallasheshi suka fito parlour,Aunty Salma na rike da jaririyar hannun ta a baki tana tsotsa. A carpet din ya zube gaban Aunty Salma,tare da mika mata hannu..Hajiyan ta kalla,kan ta mata da kai ta bashi..Ido kawai ya zubawa babyn,kamar shi sak..wato Babyn ma bata bashi mai kamarta ba sai kamar shi kamar yadda tace? Da sauri ya mika wa Aunty Salman, kan ya tashi,sai y'aji y'ar ma haushin ta yake ji.. Binshi suke a baya sai hada hanya yake kamar bugagge..wajen mota ya nufa,kan ya tsaya tare da juyo wa. "Ina Nainan? Hajiya ce tace ya shiga baya tana gida..Aunty salma ta jasu har gida inda Gawar Nainan take. Kallon ta yake,kamar mai bacci..fuskar nan tai fresh,kamar ka kira ta bude ido.. Shi yai wa Matarshi wanka,da taimakon su Aunty salma aka kimtsa ta,sai mak'wanci...gaba d'aya ya tattara ko zama wajen makokin bai ba yai gida..a d'akin Nainan ya yada zango,Shikenan ya zama maraya marar Naina kusa.. Da dare kuma sai ya kasa bacci,ga kukan Berry,ga nashi kukan,sannan kuma sai kawai yake sake marmarin kallon babyn..Alwala ya tashi yai, kan ya hau sallah, yi kawai yake bai ko sanin adadinta..shidai burinshi takai ga Naina. Washegari ko gari bai gama waye wa ba yai gidan su..a fafur sai an bashi y'ar shi..dama sai kukan yunwa take,sai dabino da zam zam suka bata..ga ba mai karamin goyo kusa.. Maman Nainan ce,itama kuma ta yaye..Abba taje ta fadowa abinda Faruq din yace..sai suka sakko tare,yana rungume da babyn ba halamar zai bada ta. Hajiya tace bazai yu a bashi ba,nan ya tasasu ya soma kuka..kan ita kadai zaya gani y'aji dadi.. Gudin kar su tada rigima yasa Abba yace yaje,, direct asibiti ya nufa da ita..kan su rubuta mishi baby food din da zai mata. Da rana sai ga Inna Bilki,ba yarda zai yi haka ya bata d'akin Naina ya koma nashi. Yai ma babyn huduba da Naina karama.. Haka suke renon baby Naina da Inna Bilki,koh zaman arba'in batai ba ta bar gidan..dan kan ma ta tashi yai wa baby wanka,sannan da y'ar shi yake kwana. Agun Laila kuwa,ko kusa basu fara fada mata mutuwar Naina ba..dan a kullum ita mutuwar Maj'nun ta sabuwa ce..duk ta rame,tai wani iri,babu wannan rawar kan sam yanzun..momy tayi tayi ta dawo da abin yaci tura.. K'warai tana mamakin soyayyar Laila da Mas'ood.. Gashi ko dan babyn da take bidar samu Allah bai rubuta zata samu dashi ba...Babban abinda yafi kara sata kuka kenan,wato rashin samun Photocopy na Maj'nun ta. Har ta gama takaba Laila taki d'ai d'aita..duk da takan yi wa momy dan murmushi in tana mata magana. Kallon zunnu kadai ke kara tuno mata da Maj'nun ta,dan yaron suna kama ainun da Mas'ood.. Sai dai shi surutun tsiya gare shi. Sai lokacin suka tattara suka koma Cotonou.. Nan fir taki barin gidan Momy,sai dai su tuni suka fara tattarawa zasu bar k'watanon. Dak'yar ta yarda da bada baki ta zauna a k'watano.. Sosai take bawa mamy tausayi.. Laila na da makon a So..ga ba wani k'awayen azo muga gare ta ba..haka Mamyn ce dole ta zama K'awar Lailan. Duk wani abinda ta sani shi zata mata..ta aika a siyo Indian film,sai dai har a gama bata tunanin tana fahimta..komai ya fice mata a rayuwa..Yunus da babyn mamyn data haifa kawai ke sata kaga har tana musu dariya..daga nan sai ta bige ya zama kuka. By Feenat Ja'afar. [3/5, 12:22 AM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 39_Shekaru biyu kenan duk dun su da rasa masoyan su..a karan nan Abban su Lailan yazo Nigeria dasu Lailan..da zummar zata gidan momy kano..sai dai shi da abinda ya kawo shi..dan tuni sun gama yanke hukuncin hada su aure..tunda duk zani ce ta tadda muje. Dajin labarin ta hau kuka a d'akin su na da ita da Naina. Aunty Salma ce ta shawo kanta bisa sharadin da su kadai suka sanshi. K'warai mutuwar Naina ta girgiza ta,hakan yasa jikinta ya kara yin sanyi.. Sai dai ganin Baby Naina taji wani irin farin ciki..a bagaran Faruq kadai tasan tsugune bata barta ba. Duk rayuwar ta zuwa mutuwar Maj'nun ta ta bawa Maman Nana.. Sai kuma alakar su zuwa inda auransu ya kasance. Kuka sosai Maman Nana take,tabbas yanzu ta gane rashin sakin jikin Lailan..kw'arai ita kanta taji mutuwar nan,bare Lailan..nan firar ta kare da alhini. "Lalle ne Laila kin fuskanci kalubalai cikin rayuwar ki,sai dai duk duk'kan abinda ya wakana duk dunsu rubutacce ne a K'ADDARAR Ku Laila.. Murmushi tai kan ta k'ada kai,"k'warai K'ADDARA CE maman Nana..ta goge hawaye.."dan banda K'ADDARA ba abinda zai rabani da Mas'ood. Kafadar ta Maman Nanan ta dafa,"ki kara hakuri..Allah kadai yasan abinda wannan K'ADDARAR taku take nufi...nan tai ta bata baki,har tai shiru ta bar kukan. "Amma a zahiri duk kuna kama da Naina Laila keda Faruq din..Allah ya jikan Naina babba..Ta hadiye kukan ta tare da fad'in "Amin. Sai bayan magriba ta rako su gida kan ta koma,har zuciyar ta tana tausayawa rayuwar su Laila. (7pm)aka fara Tom and Jerry ta kunna ma Naina tai d'aki. Wanka tai,dan zafin da ake na gari, kan ta sa dan skirt pink da ratsin yellow da riganshi mai kamar singlet yellow, gashin ta da ruwan wanka ya dan taba ta baza shi bayan ta dan ya huce,parlourn ta fito,a tunanin ta ko an gama Tom and Jerryn. Naina na ganinta ta fara bata labarin abinda akayi, tai murmushi tare da shafo kanta. A kasan carpet din ta zauna kusa da Nainan tana biye mata har aka gama. Gashin ta fara bazawa iska na shigar shi yana tashi,,kallon ta Nainan take,sai itama ta matso tana tayata tana dariya. Tura gashin gaba ya zubo har kirji sai hargitsa mata take,ita a dole gyara ne. Tsaye yake kamar kullum sallamar aciki ba mai ji,kallon su yake yana dan yin murmushi,sai ya samu kanshi da kallon yadda iska ke k'ada gashin gefe dan murmushin fuskar Lailan ya fito. A zahiri Laila tafi Naina gashi sosai,yana matukar son gashin Nainan a haka kuma a tsefe... "Papa"...da sauri ta dago kanta gashin yai baya ya bazu tare da kallon kofa..tuni ya gintse fara'ar.. neman abin rufe kai take babu,tashi take kokarin yi,Naina ta rike ta wai "A'a. Sai tai kasa da kai gashi zama ma yayi maimakon ya wuce d'aki. Labari da dan guntun yarenta take bashi na Jerry tana daga zaunen tana dariya,yayin da hannun ta ke kan Lailan kamar wata makitsiya. Kamar an tsikare shi kuma ya mike yai ciki. Hadari yau suka tashi dashi a garin,goye take da Naina tana aikin abincin dare tai bacci. Zuwa tai ta kwantar ta kan ta dawo ta zuba komai ta gama tare da ajiye mishi nashi ta dau nasu dan ruwa aka fara kamar da bakin k'warya. Karar shigowar motar shi taji da sauri ta fara hadawa tai ciki gudun kar suci karo. Ta juya kenan zata bar kitchen d'in akai kit suka dauke wuta. Da sauri ta koma kitchen d'in a tsorace,tsoro biyu ya hadu,ga dauke nepa,ga zuwan Faruq. Gashi duk gari ya danyi duhu sosai. Da sanda ta fito dan hasken walkiya na haska gaban ta,wata walkiya akai mai k'arfi sai wata cida mai karar ta biyo baya,a tsorace ta sau plate d'in da nufin guduwa d'aki taji an ruko ta. By Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 2:18 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 40_walkiya akai,kan ta waro ido waje, sakamakon ganin wanda ya riko ta fuskar nan ba annuri. "Kai hakur...shiru tai jin ya hankadata kan kujera ta d'ayan gefen,kan ya dakko wayanshi ya lalubi remote d'in kunna fitilar sama mai chargy da wuta..takurewa ta kara yi a kan kujerar. D'aki ya wuce,tadan saci kallon shi,ajiyar zuciya ta sauke,kan takai dubenta ga fasheshen plate d'in da abincin.. Mey kenan hakan yake nufi? Karta taka ne ko tsabar tsanace yasa shi hankadata? Kai ta k'ada, kan tai kitchen d'akko parker da tsintsiya ta k'washe kan ta zubo wani tai d'aki. Zulumi take had'e da lissafi, in bata manta ba watan ta ya wuce da kwana 3,calendar wayanta ta bud'e tana kara lissafi..uku-uku taji gabanta na duka,mai kenan hakan yake nufi? Ido ta zubawa Naina kamar mai neman amsa. Itama itan take kallo,ganin yadda momman ta ta duk ta fita hankalin ta.. Tun shekaran jiya take jin dan cramp da dan bloating k'adan,amma a tunaninta period d'inta ke hanya, tuno da yawan discharge da take kwana biyu ya kara tada hankalin ta,(am I pregnant?)... Zumbur! Ta mike tare da yin gaban madubi,ta fara checking d'in kanta da kanta,amma yanzun is too early ta gano gaskiyar lamari,cos duk wani early sign na ciki tasan yana kama da pmc a time.."Ya ILAHI..kai ta dafe,ji wata K'ADDARA? A zuwa d'ayan? Da sauri ta girgiza kai,"inshaAllah ba haka bane.."toh in hakanne ya zakiyi Laila? Cewar zuciyarta..kai ta girgiza, tana mai fatan ba ma shi d'in bane. Komawa tai ta zauna a bak'in gado tare da dafe duk'kan hannunta a kai..hannu taji an ruko mata,sai ta dawo hankalinta tare da k'ak'alo murmushin dole,sai ta d'au waya tare da d'aura kan Nainan a cinyarta. Maman Nana ta kira,tana tambayar ta chemist a kusa. Da Naina suka fito wajen Baba maigadi,ta bashi dari biyu da takarda kan sakon yana rubuce.. Ba'a jima ba ya dawo da sakon strip d'inta,sai jiran g'waji. Parlour suka zauna,ta duba agogo,tasan duk inda maigidan yake yana hanya yanzun,wunin ranar nan a chunkushe ta kare ta. Rike take da strip d'in a hannu tana hawaye,sakamakon ganin pt capital Positive.. Mey ne ne abin yi? Aunty Salma..ita ce wacce ta fado mata..tasan yanzu dai kowa yai sallar asuba,ta sauke ajiyar zuciya tare da goge hawayenta,bugu biyu ta dauka,,ba ko sallama tasa mata kuka tana tsara mata.. "Aunty Salma kin dai san alkawarin mu,yanzu ga wannan cikin, ga ina tsoron abortion.. Please help me.. Ajiyar zuciya ta sauke,"ni ai bansan ta inda ma zan fara ba Laila? Garin ya hakan ta kasance?..da kuka ta katse ta da"tsautsayi ne.. Aunty Salman tai jim,dan ita a tunanin ta Laila ta manta da wani alkawari ta rungumi K'ADDARA.. Ashe tana sane,jin irin kukan da take yasa ta fara lallashi,'' Kinga, kar kiyi komai,anjima in gari ya waye ko da yamma zan zo,sai musan na yi, Kai ta k'ada mata,tana fatan Allah kaimu lokaci. Kitchen ta wuce, kawai ta jirge kayan tana wanke su baji ba gani.. Har na k'wali take wanke wa tana hawaye,a tunanin ta ko zata samu sauki. K'warafniyar k'wanika yaji a kitchen lokacin da yake dawo wa a masallaci, tsaye yake yana kallonta da mamaki,da sauri-sauri take yi kamar mai neman huce haushi a kansu,, duk saman sink d'in ya cika da k'wanika..kuka tasa mai sauti,tare da tsayar da wanke wanken,sai da tai mai isar ta tukun taci gaba. Har zai mata magana kawai sai ya wuce d'aki. Sha d'aya da wani abun Aunty Salman tazo,lokacin tana zaune ta zubawa TV ido,Naina da Papan ta suna kan dining yana karyawa, shi dai ya rasa mey ke damun ta,ya fuskanci kamar bata a hankalin ta. Shayi ya kai b'aki yana kallon ta. Ajiye wa yai da zummar tambayar ta Aunty Salma tai sallama,suka gaisa da Faruq. Tsaye ta mike ido ya cika da k'walla, kan ta tako tare da rike hannun ta. Shi dai da ido yake binsu,ganin zata sa mata kuka yasa ta ja ta d'aki. "Ai Laila sai ki tona mana asiri,,ki shiru kan ya ji ba'asi mu samu mafita..kai ta daga tare da share hawaye. "Kiyi hakuri Laila ki d'au wannan cikin,kar mu kai ga yin kisan jariri..yanzun lissafi zamuyi,,kai ta k'ada tana sauraron ta. Suka gama kulla abinda za ai kan ta tafi. Hatta Naina rasa gane kan momman take k'wana biyun nan,bare gogan. Ko sati ba sake da faruwar haka ba ta fara fita haiyacinta. Laulayi ne mai zafi ya dirar mata,da ga shiga yin brush ta fara kela amai,gaba d'aya karfin ta ya kare,da k'yar ta jawo jiki ta koma d'aki ta hau gado tare da jawo Naina. Laila uwar Lang'wai,tuni ta fara hawaye dan jin wahala. Lalle ta yarda da zancen Maman Nana,kan auran su kam K'ADDARA CE. Tunda gashi a zuwa d'aya tal! Ta roro ciki.. Hawaye ta fara,tuno da Maj'nun ta,tsawan kusan shekara biyu tana nema Allah bai nufa ba a auran su. Lalle ta yadda da cewa wannan cikin ma wata sabuwar K'ADDARA CE a gare ta. Sam duk sonta da haihuwa bata ko murna da samun cikin. Abincin da bata daura ba kenan,Allah ya sota gogan ya tafi Abuja,daga ita sai Naina. Dawowar shi kenan daga tafiya ya jiyo kukan Naina a d'aki,kuka take ba kadan ba,wanda yasan ba lafiya ba. Momma take kira,da sauri ya tura kofar,rike take da ciki tana kuka Nainan nayi,amai take son yi ta kasa,ba abinda ya rage da zata zubar a cikin,ga wani jiri dake diban ta da azababben ciwan kai,mura,duk ita kadai. Bata da ko karfin janyo Naina bare ta iya tashi,ga Naina ruwa take so..ga kukan taki kula ta,sannan ko kadan bata son ganin kukan Lailan. "Oh God..kai ya dafe,kan ya ajiye jakar shi yai wajen da sauri,gaba d'aya gani yake kamar Naina ce yayin ciwan labourn ta. Bai wata wata ba ya kinkikme ta ya daura a gado..ruwa ta fara kira,da sauri yai waje,tasowa Nainan tai itama ta hau gadon,sai gashi da gurar ruwa da cup,ya tsiyaya mata zai kai bakinta tai wajen Naina da ruwan,,sai ta koma tana sauke ajiyar zuciya. Kallonta yake ganin a k'wana 2 yadda ta kare,anya yana adalci kuwa? Tunda ya tafi bai kira ya ji lafiyar su ba,sannu yai mata ba yabo,ba fallasa,ya goge inda ya baci,kan ya d'au Naina suka fita, motar shi gareji ya mika ta yanzun,bare ya kaita asibiti. Waya ya ciro, jin ana kiran shi,"Dr Auwal" ya ga an rubuta,sai ya d'auka, akan aikin shi suke magana,kan ina zai same shi? Yace yana gida. Fita yai dan shigo da shi,yana ta mishi tsiyar sam yaki su,"wai sai d'ai muji ka sake aure ba ko g'aiyata,wanchan ma har madam ta rasu bamu gana ba.. Murmushi yai kan ya tuna da Laila,"ai hakuri boka na turai..Afuwan. Ya k'ada kai,"toh ina amaryar? Ko sai mun yanki ticket? Kai ya k'ada,"tana d'aki, ka duban ita ma please, kan muje asibiti, yanzu dawowa ta na tarar ba yanda take,d'akin ya shiga,lokacin taja bargo tana rawar d'ari,, kai wannan fa itama akwai langwai,yai dan karamin tsaki,kan ya dau dank'wali ya mika mata,"ki g'yara za'a duba ki yanzu..da k'yar ta yafa dafa k'wancen da take. Da sallama suka shigo, Ya d'akko mishi kujera ya ajiye kusa da gadon,kamar tasan mai muryar nan? Juyo wa tai dan jin ya sake ambartar "Sannu madam...baki sake yake kallon ta da mamaki,sai ta k'au da kai tana hawaye,hannu ya nuna ta dashi yana kallon Faruq,"sis Laila.. LailaMaj'nu.."ikon Allah,ko ba ita ba ce? Kasake Faruq d'in yai yana kallon shi yake da mamaki hadi da halamar tambaya. By Feenat Ja'afar. ®NWA. BANI NA MUTU BA Ana ta kira na dan jin wai shin da gaske ne Feenat Ja'afar na mutu? Little sis nace ta rasu. Na gode k'warai
[12/17/2017, 2:18 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 41_"LailaMaj'nu
? A hankali ya furta. Dr Auwal yace "Eh ba,,auf so sorry,yanzu matar ka ce ba Maj'nu. "Allah ya kara muku hakurin rashi kinji? Kai ta daga,tuni ya famo mata ciwo.. Shikam Faruq kallon su kawai yake. A yanayin ta kawai Dr ya gano bakin zaren,a yadda take basar da tambayoyin kuma ya gano tasan komai. Sai yai mata sannu suka fita. "Amm aboki,sai hakuri fa,in ba k'wari yai ba ba za a daina wannan yan morning sickness d'in ba,nasan zata taimaki kanta,bari zan rubuta allurori da magunguna. Da rashin fahimta yace bai gane batun ba? Murmushi yai,kan ya dafa shi,"madam na d'auke da K'anwa ko k'anin Naina,,,ya shafo kan Nainan. Shiru yai da tsabar mamaki,ciki? Ikon Allah,daga kuskure d'aya? Murmushi ya k'ak'alo tare da kallon Nainan shima. Yai abinda ya kawo shi suka biya ta chemist yasai musu,kan ya dawo dashi gida. Gaba d'aya sun sashi a duhu,mey yake nufi da aikin ta ne zata iya kula da kanta? Mey yasa ta fara kuka daga ce mata La'ila Maj'nu? Ina ya santa?... Da wannan tunanin ya bude kofar ya shiga,har yanzun kuka take,sai ya kwantar da Naina datai bacci ya dawo kusa da ita ya tsaya,ido ta rintse,dan a ganin ta duk shi ya jawo mata,hakan yasa ta kara jin bala'in haushin shi. "Sannu ga maganin,mey zaki ci? Ido ta kautar,kan ta fara kokarin tashi,da sauri yaje zai taimaka mata ganin tana cije lebe.. Kitchen ya shiga,ya hado mata tea a tray ya kawo mata. Tana jin kamshin tea d'in karnin madarar ya bigeta ta fara k'ak'arin amai,da sauri ya matsar shi yana ce mata"sorry.. A hankali tace mishi ita kunu mai tsami take so da b'akin shayi ba sugar. Kai ya k'ada, kan ya fita ya had'o mata,saura kunu,ina zai samu kunu mai tsami? Yana tsaye ta shanye ta bud'e ledar,allurar tsaida amai ta d'auka, da mamaki yake kallon ta,ganin tana zuke ruwan a cikin syringe d'in cikin K'warewa.. Baki sake yake kallon ta lokacin da take ma kanta allurar,kan ta balle su Vitamin B6 da sauran maganin Nausea. Dan satar kallon shi tai,ganin yadda ya zuba mata ido,,a ranta tana tunanin yau yan mutunci ne a kusa,,komawa tai ta kwanta, ya tattare kayan yai waje,ko zama bai ba ya mika jakar shi d'aki kan ya d'au jug a kitchen yai waje. Gidan Hajiya ya nufa,bayan ya karbo motan shi,sai sinne kai yake lokacin da yake fada ma Hajiyan abinda yazo nema wa Lailan kan ta ki cin komai sai shi. Murmushi Hajiyan take,fatan ta Allah yasa komai ya wuce a gun yaran,tunda gashi harda an samu rabo. Cikin sauri ta dama mishi kunun,dan ita kam bata rabo da garin kunun tsamiya, tsamiya ce kawai bata. Sai tasa ya ciro musu lemon tsami a bayan gidan inda suka shuka. Ta bashi tana fad'in"ban sa siga ba,dan kila a haka zata bukata,kai mata sannu,Allah inganta,, banda dauk'ar abu mai nauyi d'ai..tana murmushi, tace"ko dayake Nurse guda tasan yadda zata kula. "Sai dai Baba na ka taimaka mata wajen rage tunanin nan nata. Kai ya k'ada ba wai dan ya gane abinda take nufi ba. Tunanin shi wai Laila ma Nurse ce? Mey yasa komai na Nainan shi da Laila yake shige ne? Da wannan ya bar gidan,wanda bai san wa zai bashi amsa ba. Kusan magriba ya shigo,suna parlour kamar wasu marayu,shiru kake ji sai karar berry..Naina hannu na baki tana kallon momman da ta tafi tunani. Kwana biyu ba kodan wasan nan da take mata,in ja ganta itama duk tai wani iri,hannu da in ba bacci take ba yanzu bata tsotsa amma yanzu a kwana biyu ta dawo da shanshi. Cire hannun tai kan ta tashi tsaye tare da sa hannu tana goge hawayen Lailan, "Momma" ta kira ta tare da girgiza mata kai halamar ta daina kuka..kallon Nainan take,tana mamakin yadda yarinyar ke gane damuwar ta,sannan kuma ta hana kanta sukuni sai taga ta ware. Jawo ta tai,kan ta zaunar ta a cinyar ta tare da k'akalo murmushi.. Tace ta bata story? Kai Nainan ta k'ada, sai ta fara bata tarihin Maj'nun ta da French.. Jin wani yaren da bata taba ji ba yasa ta zuba mata ido tana kallon ta kamar mai koya. Na murmushi tai murmushi, sai itama Nainan tayi, ta zurfafa cikin bata labarin har bata san ya shigo ba,tunda shi ba sallama yake k'wadawa ba. A kan dining ya zauna yana sauraran yadda take fidda French kamar yar chan,duk da bai jin komai,amma d'ai yasan French ne,sai d'ai yawan ambatan Maj'nu da Mas'ood a zancen yasa ya fara dauk'ar inda ta dosa... Wayan shi ne ya dawo da ita,da sauri ta kallo shi,shikam ji yake kamar kar ta daina. Mtn ne suka kira,sai yai rejecting tare da tashi ya ajiye mata kunun, kai kasa ta mishi sannu da zuwa, da ka ya amsa, tare da mata ya jiki. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:19 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 42_Da dadi ba dadi ta kai wata uku, sai abinda ba'a rasa ba,sai d'ai maimakon abubuwan Faruq suyi sauki,ita gaba taga sun kara,a tunanin ta kodan ciki zai rage mata bambami da tsawa,sai dai kiris zai ga abu ya rufe ido ya zazzaga mata,duk da yanzu har ta ma saba da hakan,gudun kar ta jawa kanta Bp yasa sai dai tai ta mishi yaken dole,wanda shi a ganin shi wani rainin ne. Duk da duk fita zai tambayi mey take bukata? Ita abun nashi har tsoro yake bata,tamkar mai aljanu, yanzu kalau anjima ya burkice. Fresh Laban shi ta mayar abun shanta, wanda kan aje ko'ina har ta cike gurbin da har da kari,tai bul-bul da ita ta kara wani irin hasken k'yau. Gobe da safe zata fara Yuga,dan bata son tai kiba dayawa ga kuma ciki. Ya fita jogging ogan, ganin shima kwana biyu ya fara habbaka. Sanye take da wando Orange 3quarter na roba mai laushi, sai farar riga mai hannu siriri kamar vase,ta kama ta tsam,sai ta kama tsefaffen gashin ta ribbom fari da shima sai kara yawa yake da k'yau da cikin nata. Yi take tana nishi, d'ai d'ai ya dawo ya tarar ta tana ta karye karye da jiki a filin kusa da dining da different Yuga. Ilahirin jikinta yake kallo,dan cikin ya dan fito ya mata dass a gaba..tana da k'yau,zata dara Nainan shi kadan,musamman yanzu da tashen k'yaun masu karamin ciki..sau tari in tana abu yakan shagala da kallonta,sabanin yanzun da ya ji wani abu na tsirga mishi yayin kallon nata.. Baya ta rike tana dan fad'in"wash".. Sai tai kamar zaman tashiya, tai crossing kafarta tare daura hannu a cinyarta ta dafe kowacce K'afa,(Butterfly Pose). A hankali ta rufe idonta,sai ta ja numfashi kadan,sai ta dawo,kusan minti biyu yana kallon yadda take dan murmushi, shima sai ya fara yana kara matsowa cikin parlourn. Sauya position tai da tashi kadan kamar zatai rarrafe ta dafe kasa da duk hannun ta,(Cat-cammel pose)ba tare da ta kula dashi ba. Murmushi ya daina,ganin yadda yake ga kamar cikin zai zubo,bai san lokacin da ya fara sababi ba. "Cikin za ki fado dashi ko meye hakan?..da sauri ta dago tare da mikewa duka gabanta na faduwa,sababi ya cigaba wai zata zubar mishi da ciki.."oh,yanzu na gano ki,wato cikin ne bakya so? Ranar chan haka kin hau saman kujera a kitchen kamar wata yarinya kina tsaye wai Naina zaki d'akko wa abu,ga tiles,daga magana kin hau kuka, yanzu gashi kina son ki zobo min da cikin gaba d'aya ki huta koh?..karan nan kasa d'aurewa tai,dan ta fara gajiya da wannan bambamin,tuni ta k'ank'ance ido,, "Kaga malam,ni fa abinnan ya ishe ni wallahi,,ni fa ba yarka ba ce da zaka tasani gaba kullum kana min bambami fada...a zuciya take fadi, sai dai tasan ko giyar wake tasha bazata iya furta mishi hakan ba, ko ba komai yaya yake a gare ta,duk tana ginin shi yama manta da alakar dake tsakani su.. Maimakon haka ma,sai kawai ta sa mishi kuka mai sauti.. Baki ya sake yai shiru yana kallon ta.. Kamar kullum ya ja Aya bai ko karasa ba yai d'aki yana fad'in"ya miki k'yau. Y'ar baci ce yarinyar,da ya soma bambami zata hau mishi kuka. Yayinda shi kuma duk jarabar shi sai ya tsagaita ta,sai d'ai ya barta ya wuce,in tayi ta gama. Da,kallo ta bishi da matukar jin haushin shi...tayi imani idan ta rantse ba zatai kaffara ba,akan in Maj'nu ne bazai mata haka ba,kila ma sai dai ya tayata suyi tare,balle kuma abu take dan lafiyarta data Babyn,sai taji har babyn shima haushi yake bata. Da yamma ya karbo mata kunun ta na yamma kamar kullum,tun da safe rabon da ta fito parlour,dan tuni ta ajiye girki, ta tsani warin albasa da warin gas,da kanshi yace toh ya yafe,gaba d'aya yau gidan ya dau mata zafi,ga zuciyarta ji take a kusa take,wani irin bala'i take ji,shi yasa tai zamanta a d'aki,sai da taji fitar shi kan ta fito, gudun kar ta sauke a kanshi yau. Ita kadai a parlourn ta cika ta batse,kiris take jira ta sau kuka,Naina tun fita kunun safe bata dawo ba,fatan ta Allah yasa kar ta sauke a kan ta. Da gudu Naina ta shigo tana nuna mata ribbons da band na blue,da meat miss a leda,su iloka da taura Sai surutu take mata ba comma ba full stop. Aksar kuma akan papan ta,tsaki tai,ta tsani ko sunan shi taji,kai ita ko ganin shi fa bata son yi yanzun. Sai dai jin kamshin meat miss tuni ta kallo ledar hannun Nainan. Murmushi tai mata tare da fara kunce ledar,kamar taci babu haka take ci,Nainan kallon ta ma ta fara tana dariya, ganin har wani lumshe ido take,, Ido rufe tace"Oh my Naina..u r so uhmmw.. Da dariya Nainan ta k'yalk'yale mata,itama sai ta dara,tuni taji ta fara huce wa,Naina na daga d'aya acikin farin cikinta a yanzun. K'warai jinta a kusa da ita na sata farin ciki. Fuska ta g'imtse, jin kamshin turaren shi na bugarta. Ta bude ido suka sauka kanshi,kallon su kawai yake da murmushi,, suna hada ido ya wayen ce tare da ajiye jug d'in a kan table, kai ta d'auke, duk da tana son kunun,wanda a da yana ajiye wa zata d'akko ta zuba. A kujera ya zauna, sai yake kallon ta ganin taki tashi,kusan minti 10 bata koh kalli wajen ba,sai ya tashi ko zata d'auka in baya nan. Kusan shida ya fito daga shi sai singlet fara kal da shortniker,da iPad d'in shi a hannu yana kallon su. Ba halamar ta motsa a gun,sai d'ai Naina data kama mata Talking Tom tana yi a waya a kan kujera tana dariya. Suna hada ido tai saurin d'auke wa..sai dai yana zama ta kara satar kallon shi lokacin yana kallon kunun. Sai ya dawo mata yaro yau,da sauri ta d'auke kai tana dan tsaki a ciki. Bata nufa taji shi a kanta yana mika mata kunun,"ga nan fa kunun ki..dagowa tai,yana rike da jug d'in, fuskar ba yabo, ba fallasa,sai ta kawar da kai tare da girgiza wa. Baki ya ta6e kan ya ajiye mata tare da zama a kujerar dake kallon su. Sai dai har aka fara kiran sallar magriba bata kalli kunun ba,shi kuma ya rasa abinda yasa ya damu da tasha yau d'in..samun kanshi yai da lallaba ta,harda ce mata sorry,wanda shi bai ma san na meye ba. Ita kuma sai ta zata sorryn dazu ne,hakan yasa ta sha. Ya rasa dalilin da yasa yake son zaman gidan yau. Koda ya dawo a masallaci nan parlourn ya zauna,lokacin tana nafila Naina ta hau bayanta tana sujjada,dariya abin yake bata,sai kuma dan kanta ta sauka. Ya shigo yana kallon Nainan,tana komawa wata sujjadar da gudunta ta dane bayan tana"yeee".."Naina"......bai san ya sau mata tsawa ba tare da yin wajen ya sauke ta..Aiya tuni ta hau bori tana kukan an mata tsawa..sai turje-turje take wato ya sauke ta,da sauri ta sallamar tare da tashi zata fara mishi masifa akan ina ruwan shi,sai dai tuni shi har ya riga ta farawa"na fa fuskanci da gaiya kike wani abun, in baki son cikin ne kike neman yadda zai zube toh kiyi haife shi ni zan raine abu na..ya dagan gan zaki na kallo tana tsalle a gadon bayan ki amma ba zaki hana ta ba?..ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba,ga Nainan sai mikawa Lailan hannu take tana kuka.. A fusace ta kwaci Nainan,ba tare da ta ce mishi kom ba,,tasan d'ai tabbas Faruq baida lafiya. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:19 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 43_Baki sake ya bita da kallo har suka kule d'aki,, bai taba ganin bacin ranta irin na yau ba,ga wata harara da ta aika mishi..kai ya k'ada yai zaman shi tare da kunna TV,sai d'ai ko kukan Naina bazai bar shi jin komai ba. Sai ya rintse ido tare da dafe kai,gaba d'aya so suke su burkita mishi K'wak'walwa.. Yadda take yar shag'waba haka take son koyawa y'ar shi,"da gaskiyar ka ma sai ama kuka? Sai d'ai har aka fara Tom and Jerry basu ba kamar su..shiru kake ji ba ko kukan Nainan. In banda kallon kofar d'akin nasu ba abinda yake,kuma sai abin ya sha mishi kai. Sai yayi kamar ya bisu sai ya fasa,shi a ganin shi a kan gaskiyar shi yake. Bayan isha'i har yai shirin k'wanciya bacci. Sai juyi yake a gado.. Naina da Momman ta sun hana shi bacci,sai d'ai shi yafi bada na Nainan shi ne,yau ya mata haramiyar kallon Jerryn ta. Wajen sha d'aya ya fito da waya a hannu,ya kunna wutar parlourn,, a hankali ya kama kofar ya d'an tura, da mamaki ya ji ta bud'e. Waya ya haska tare da shiga, hasken farin wata ya hasko ta windown d'akin, ga labule a dage iska mai dad'i na kad'awa. A bakin gadon ya zauna,tare da haska su,"Oh Allah!..ya furta lokacin da yaga yanayin k'wanciyar tasu.. K'wachokam ta daura ta kirjinta kafafunta a kusan nata kafar, dak'yar ta samu a hakan ma tai bacci sai ajiyar zuciya take. A hankali ya kai hannu zai d'auke hannun Lailan sai ya ji tana magana cikin bacci halamar lallashin Nainan,har ya d'auke ta Allah yaso shi basu tashi ba,sai ma g'yara k'wanciya da Lailan tai. Gadon ya hawo tare da k'wantar da Nainan a hankali,sai ta dan fara rigima, juyi Lailan tai cikin bacci tana"shhh.. tare da dauro hannu kanta da zummar lallashi sai a hannun shi,lallashin hannun ta fara,sai a sannan ya kallo ta sosai,duk gashin ta ya bazu kan pillown,yar guntuwar rigar ta duk ta tattare, tuni ya kafa mata ido ba ko kiftawa. Yadda iska ke k'ada gashin yake kallo,a hankali ya tashi tare da gyara Naina. Wajen labulen yaje, tare da kara gyara shi,juyo wa yai,d'ai d'ai ta sake juyi zuwa rigingine,a yanayin da take dole yai saurin d'auke kai,,sai dai ina,tuni zuciyar shi ta hau buga wa da sauri-sauri,kamar ana janshi gare ta haka yake zuwa,a bakin gadon ya zauna,tare da kai hannu kan gashin tare da g'yara mata,idon shi yakai gun dake d'aukar shi tun dazun,hannu ya kai zai taba,sai d'ai ya rintse ido tare da d'aura wa acikinta..hannun ta rungumo duka a kirjin ta tare da fad'in"Naina"..a hankali ya hadiyi yawu tare da zuba mata ido. By Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 2:24 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE"
© Feenat Ja'afar.
44_Kokarin zame hannun shi ya fara a hankali, da sauri ta kara runkumo shi har yana k'wantowa suna fuskantar juna,bugun zuciyar shi ya cigaba, ba ya son kara kuskuren ranar,amma kuma zuciya na ingiza shi,,hannu yakai bakinta yana zagaye shi a hankali,da mamakin shi yaga tai murmushi. Bai tsinke da lamarin ba sai da ya ji tana dan magana rad'a- rad'a a hankali, kunne ya matso dashi dan jin mey take fad'i..
"..(I know Maj'nu,, I know u love me,,buh please maj'jawo..) Sai ta sake murmushi hak'waran ta suka baiyana,a zahiri mafarki take su na a tare da Maj'nun tana mishi 6aci. ("I'm feeling lonely..) Sai ta dan sa dariya mai dan sauti..Hannun shi ta cika,tare da waro su tana yamutsa fuska cikin shag'waba ("would you please give me a hug...) Cikin marairai cewa tace ("pleassse..) Bai wata-wata ba kwa ya k'wanto, da sauri ta rukunkume shi tana zuba mishi godiya.
Yaushe rabon da a mishi haka? Tun Nainan shi nada rai,tuni sai ya kara lafewa kamar wani yaro ajikinta,wani sanyin dadi na ziyartar shi,burin shi ya d'auwama a hakan..
Tuni kuma sai ya fara sakar layi,jin irin kalaman da take zubawa acikin mafarkin, wanda tuni ya fara tuna mishi da wani moment achan baya.
Da kid'an ya sauya sai ta soma mishi d'an kukan shag'waba kamar yadda take mishi in suna tare,da mamaki kuwa shima sai ya fara mata irin lallashin da Maj'nu ke mata in suna a yanayin nan..tuni murmushin ta ya karu, har bata san ta fara mayar mishi da martani ba cikin yarda da a duniyar mafarkin ta take...kan ta tashi farga da reality har komai yai nisa,kuma da taimakon ta.
Ido ta fara juyawa a rufen tana son bud'e wa, a hankali K'wak'walwarta ta ainashin Laila ta dawo aiki,a tsorace ta bud'e ido zuciyar ta na bugawa da k'arfi sosai tana kallon siling.
Hawayen ta har yanzun yaki daina zuba..baccin shi yake abinshi hankali k'wance..Ta kai duben ta ga Naina,tana chan gefe hannu yana a baki bata ko juyi..ido ta rintse,wato ya shirya komai dama? Hatta k'arfin tashi ta ture shi bata dashi,"Ya Ilahi..ya Maj'nu zai mata haka? Ya zaizo ya taimaka mata wajen aikata wannan aiki? Ina hankalin ta yaje da har ta biye mishi?... Kai kawai take girgiza wa tana kuka..lalle ne a times soyayya ma takan kai ga yaudarar kai..a haka har aka kira sallar farko tana kukan takaici, gashi ta kasa tashi ta shiga bayi,baccin shi yake hankali k'wance...take ta rintse ido,K'watak'wata ma ta tsani ganin shi,,sai d'ai tana Allah Allah ta ga ya tashi yace zai sauke mata tabarmar kunya.
Mika yai a hankali yana d'an salati hadi da adu'ar tashi a bacci.
Da sauri ta rufe ido.
Jinshi rike da abu kamar hannu yasa yai saurin bud'e ido,sai a fuskar Lailan da yai mata dabaibayi,da sauri ya cikata tare da fad'in"Ya Salam"..Sai dai yanda ya ji shi yasa yai saurin cije labe,tare da fad'in("Oh! no,,not again Laila...) Inashi inashi ya soma hadawa a hankali yana dan kallon Lailan kamar nai son ta tashi.
Duben wayan shi ya fara,da sauri ya tashi jin shi akan wayar,sai ya kunna, Allah yaso shi bata fashe ba yadda ya d'anne ta. Fuskar Lailan ya haska na d'an lokaci.
A hankali ya sauka ta gefen Naina tare da yin wajen kofa a hankali.
Da ido ta bishi har ya fice,tuni ta hau kuka mai cin rai..yi take ba ko ji ba gani.
Sai da tai mai isarta kan ta tashi ta shiga bathroom ta sau shawer..dirzar jikin take da soso kamar wata mahaukaciya sabon kamu tana kuka..so take ta wanke duk'kan wani gurbi da tasan Faruq ya taba,ga kamshin shi duk ya dabaibaye mata jiki.. Tuni jikinta ya d'au Jaa yaji dirja.
Akan sallaya kuwa,harda rokon Allah ya kare bacin rana irinta yau.
Shikam direct bathroom shima ya fada,sai d'ai karan nan haushin kansa yake ji ba na Laila ba. Dan da kafarshi ya kai kanshi gare ta.. Yanzu ta ina zai fara nad'e taburmar nan tashi ta kunya da ya shimfida?
Sai tara ya dawo tun fita masallacin asuba.
Baiya ko son su hadu da ita. A kitchen ya ji hayaniyar Naina ga tea flaks a kan dining. Hmm yau an shiga kitchen kenan? Sai yai
d'aki da sauri gudun kar ta rutsa shi.
Har sukai break bai fito ba,gashi yau da yunwa ya tashi,yai wanka ya gama komai amma ya kasa fita parlourn.
Kar d'ai fa Laila ta samu lagon ka? Da sauri ya mike tare da d'aukar wayan shi ya ci kunu ya fice.
Suna parlourn, Naina ta kunce wa kai tana mata twist stick,gown d'in purple leas ne a jikinta,tai parking kanta da ribbons. Kamar kullum dank'walin na kan kujera,dan bata iya d'aura shi ba.
Kofar suka zubawa ido jin an bud'e ta.
Tuni Naina ta hau mishi good morning, yaro kenan,har ta manta abin jiya da ya mata,harda kitso take nuna mishi,shidai murmushi kawai yake bayan ya ce mata"morning Naina"..
Firr yaki yarda su hada ido da Lailan,wanda ita tunda ya fito ta kafa mishi ido,wallahi yau a yadda take jin masifar haushin shi jira kawai take taji yace "kulee..tace mishi"chass.
By
Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 2:29 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 45_Toh sai akai katari bai ce uffan ba,abinci ya bud'e ya d'an kalle ta,ta maida kai a kitson su ta barshi,ya d'an chakala kan ya tashi ya zari jug. Naina ta tashi wai zata bishi,dan ma sun gama. Da harara ta bishi,sai kuma ga hawaye ya biyo ba. A karo na biyu ta zama mai karya alkawari, alkawarin da ta d'aukar wa Maj'nun ta na zama tashi shi kadai,,yanzu da wane ido zata kalle shi ranar haduwar su? Ga har tsarabar sa6a alkawarin shi ta roro.. Motsin babyn cikin ta ne ya dawo da ita hankalin ta..da sauri ta kai hannu kan mararta,yau ne motsin shi na farko da ya mata ba a bacci ba. Sai ta rintse ido,ta ci gaba da kukan ta,har kusan sha biyu tana zaune wajen,bata taba jin ta tsani ganin farkon irin na yau ba. A haka Maman Nana ta cimma ta,ta jima tana tsaye amma bata san tana kofar ba,ita kuma ta dawo a unguwa ta shigo jin fitar Faruq d'in. Ciki ta shigo ta zauna tare da dafa ta,"Mom Naina..da sauri ta bud'e ido tare da goge hawayen nata,,kallon ta kawai maryam d'in ke yi cikin son sanin dalilin kukan,duk da tasan bazai fice akan Mas'ood ba.."sannu da zuwa maman Nana.. Sai ta k'ak'alo murmushin dole,gaisawa suke,sai ita maman Nana kawai kallon ta take,sai d'ai ta kasa d'aurewa,"ya kamata Mom Naina iyanzu ki jingine damuwa a gefe kodan abinda ke tare da ke.."ki fawwalawa Allah komai,shi zai miki maganin duk wani abinda zai miki shamaki..Nasiha take mata ba tare da san meye musabbabin kukan ba. Murmushi tai tare da girgiza kai,tana ga ko ta fada ba mai fuskantar yanayin da take ciki..amma rashin wanda zata fadawa ma abinda ke cinta a ciki kila shi ke kara mata damuwa. Sanar ma ta yadda wai ta tsani ganin Faruq a gidan take tana kuka.. "Wallahi ko kadan bana kaunar ya shigo na ganshi. Dafa ta tai tana lallashi kan ta gane wani abu,cewar "Ciki yana sa mace taji hakan,amma kuma Mom Naina sai kin daure fa kin cire Mas'ood kan zakiji dad'in zaman gidan nan..ni a gani na kiyi hakuri ki saita mijin ki sannan ki mantar shi baya,ki gane mey yafi so? Meye baya so? Sai kiga cikin k'ank'anin lokaci ya saitu ki mantar shi komai. Kallon ta kawai take,a ranta tana ganin ba zata iya ba,sannan a yadda take jin kanta yanzu kam..sai gyaran Allah...katse ta tai."Haka batun cikin nan kikai ta damun kanki.. Dan Allah ki rungumi mijin ki ko zakiji dad'in rayuwar ku..sannan ki cire damuwa. Murmushi tai mata,tare da girgiza mata kai,"maman Nana,bazaki gane bane,amma Faruq ya wuce inda kike tunanin shi,a da d'ai nai zaman saita shi,na juri wulakancin shi nai ta hakuri da mishi biyayya, amma yanzun..ta girgiza kai,"zaman jiran wa'adi nake ya cika..hakuri na ya kare. Baki ta saka tana kallon ta, kan tace"wa'adi? Kar d'ai ki soma tunanin kashe auran ki..murmushi tai kan ta kawar da kai gefe..ita kadai tasan mey zatai.. Katse ta kara yi tare da zummar waazi"ni sai nake ga kamar duu dunku baku yarda da K'ADDARAR data same ku bane shi yasa kowa ya kasa kallon zahirin abinda ke a gaban shi,,ni fa ganau ce,kar kice ina sa miki ido,amma ina ganin yadda kuke rayuwar ku ta ba ruwan kowa da kowa..nasha ina zaune Abban Naina ya dawo amma daga sannu ba ki kara komai,ko dan tarbar nan babu bare ki bishi d'aki,, banda abubuwan da ban gani ba ma..kuma laifin duk rabi naki ne..da sauri ta kallo ta,"laifi na? Ba musu tace eh, murmushi tai kan ta girgiza kai, kodan bata tona zaman da suke da Faruq bane shi yasa za ta ga laifin nata. "Ya Faruq ba'a mishi g'waninta ko kadan,ko d'aki na g'yara mishi sai ya g'wale ni ko yai ta mitar na mishi ba d'ai d'ai ba maman Nana,komai a tsawace yake min,wanda ni Mas'ood bai min wannan rainon ba sam, amma na daure,, yanzu tun samun cikin nan komai ya kara baci,abu kadan zanyi ya hauni da fada,sannan Babban abin bakin cikin ma wai yadda karara yake nuna min wai ina bakin ciki da cikin shi,, toh meye abin bakin ciki a ciki K'ADDA... Da sauri ta toshe mata baki tana girgiza mata kai. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:30 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. Ja'afar. 46_"Kar ki farawa d'anki baki tun yanzun Laila.."ki yarda K'ADDARAR Alkairi CE ta kawo shi,ki k'yale shi in yana abun shi in yaso daga baya ki bishi da adu'a,wallahi rashin mafadi ne ke damun Faruq..ki zama mai nusar shi ke d'in. Murmushi tai kan tace ta ji bazata kara ba.. "Amma nasan ranar gobe kiyama ba ni da idon da zan kalli Mas'ood, dan na karya mishi alkawarin da na d'auka na zama tashi shi kadai har a Aljanna.. Baki sake take kallon ta,wallahi a wannan ambaton Mas'ood d'in har ta fara jin haushin ta, ita bata ga aibun Abban Naina ba, duk da haka sosai,dan duk suna da laifi ta rashin rike K'ADDARAR da ta saukar musu. Bata san lokacin da tace "Sai fa kin daina hangen Mas'ood zaki iya zaman aure a duniyar nan,dan maza kam kowa da irin yanayin tarairayar shi zuwa ga Matarshi.. "Dole ki sa a ranki Mas'ood kam a yanzun does not exist a duniyar nan Laila. Kai ta fara k'ada mata tana hawaye,"na sani da(He does not exist here with me,) "amma kaunar shi gare ni tana tare dani anda will never die,,nasan da baya existing a duniyar mu Maman Nana..kuka take ba na wasa ba,ta cigaba''nasani da yana a duniyar nan da ban tagaiyyara a nan ba.. "Da yanzu ba'a tulo ni nan inda ba'a kaunar ganin farin ciki na ba.."inda danayi laifi da banyi ba fada ne.."inda ko nayi kuka ba mai tarairaya ta sai kaina..A hankali ta tsagaita kukan tare da duk'ar da kai kasa,"(I wish u were here with me now..always.. And forever Maj'nu..) Tuni kuma sai ta karyar mata da zuciya,ganin yadda ta fara kuka ba ji ba gani. Faruq da ya tsinci maganarta ta karshe tuni ya fara tsanar wannan Kalmar sunan Maj'nun..a nan bakin Kofar ya ajiye ya juya ba tare da ya shigo ciki ba. Hawayen take goge mata da tausayin ta.. Tasan da rashin masoyi akwai ciwo.. Amma taya zata ganar da Laila adu'a yafi so ba wannan ba? Cikin lallashi ta fara bata baki. "Na sani da kinyi rashin masoyi Laila,amma ki sani yanzun ke matar wani ce ba Mas'ood ba,ba yadda za ai ki same shi kamar Mas'ood.. "Mas'ood yana chan a duniyar da rike alkawarin ki bazai mishi komai ba face ki d'aura mishi alhakin hakan.."yana chan Duniyar da adu'ar ki kadai yafi bukata ba alkawari ba Laila..ki sani ba'a rike alkawarin mamaci wanda baya kan turba, idan har kin yarda da cewa K'ADDARA CE ta Allah ta rabaki da Mas'ood toh ki yi biyayya ga mijin ki Laila..Kiyi godiya aduk lokacin da kika tuna Allah ya shafe Mas'ood a doran kasa Laila,Allah yana matukar son bawan shi mai yadda da duk'kan K'ADDARAR da ya saukar mishi walau khairan ko akasin wannan. Nasiha take mata tare da waazi. K'warai Ta mata nasihar da ta ratsa mata zuciya, take ta fara Istigfari game da abinda tai na rabuwar ta Maj'nun ta. Tayi alkawarin mishi biyayya har zuwa inda wa'adin zaman da ta diba zai kare. A hanyar raka M Nanan taci karo da jug d'in kunun..kawai sai ta k'ada kai tai ciki. Sai bayan magriba ya shigo,lokacin tana kitchen taga wuce war shi d'aki shi kadai,toh ina y'ar ta? Bata san wani iri bane Faruq,wai sallama sai ta gagari bawa Acikin gidan shi? D'akin nashi ta nufa,da zummar mishi sannu da zuwa kuma ina Naina har magriba. Ta jima kan ta murda ta shiga da sallama. Yana zaune rike da waya,wani irin kallo ya bita dashi wanda dole tai kasa da kai kan ya sau mata halin. "Sannu da zuwa.. Jin yai shiru tace"Naina fa? Magriba fa ta..cikin masifa yace"Y'arki ce? Da sauri ta dago kai tare da waro ido.."Oh kin gama kukan naki tukun zaki tambaye ta? "Mey yasa Maj'nun naki da zai tafin baki bishi kun tafi tare ba?..da sauri ta juya mishi baya tana toshe baki,ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba,sai da ya wanke haushin tas, kan yai doko kofar bandaki ya shige. Ba shiri tai d'aki ta kama kuka..sai dai karan nan kawai sai ta dauro alwala kamar yadda maman Nana tace mata,har kusan tara tana kan sallaya. Qur'ani ta d'auka,ta k'wanta a kan gado ta hau karanta wa,a haka har bacci yai gaba da ita. Ji tai kamar da mutum a kanta. Tsaye yake da baby Naina a kafadar shi tai bacci,ya zuba mata ido..a tsorace ta tashi tana duben shi. K'wantar da Nainan yayi ya nufi hanyar fita,sai kuma ya tsaya, "Zanyi tafiya gobe in Allah ya kaimu (7:00am)..yai waje. Lalle mukami, yau har sanar ta tafiya yake? Kullum sai d'ai ya mata note na ya tafi ko ya bawa Naina. Ta riga shi tashi,dankali ta debo manya,ta daura ruwan tea..ta fere da abun ferewa tare da taimakon chargern kitchen d'in, yankan chips ta musu,kan ta tsane shi a k'wando tasa gishiri da maggi. Ta juye ruwan tean a flask. Motsin tashin shi taji,sai ta zuba mai a fry fan sai rage wutar ta d'aura ta tafi d'aki alwala tare da d'aura 'Raka'atanul Fajr. Kan ya dawo a masallaci har ta gama had'a komai,ta zuba mishi tea dan ya huce. Tunani take ta ajiye a dining kawai ta wuce,sai wata zuciyar tace ta d'ai kai mishi d'aki. A tray ta d'aura tai d'akin nashi gabanta na d'an faduwa. Baya d'akin, a bandakin taji halamun yana brush,sai ta ajiye taje d'akko ruwan wanke hannu kan ya dawo. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:30 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 47_Tsaye ta same shi yana taje sumar kanshi da cumb,a yanayin da yake yasa da sauri ta k'auda kai zata juya tare da cewa yai hakuri,jikin shi ya kalla, bai san mey ta ga na bada hakuri ba. Tsayar ta yai da fad'in"no ki shiga. Kai duk'e ta ajiye ruwan kusa da abincin kan ta d'akko darduma ta shimfida mishi, kan ta zauna a raka6e. "Ina k'wana.. Kai ya daga kan ya amsa,"ga break..kanta duk'e har ya kusa gamawa,ta rasa mey ya hanata tashi,gashi duk ta takure..a zaton ta ba zai ci ba,tunda bai amsa ba..jin kamshin turaren yasa ta lumshe ido,yana matukar mata dadi..yana kokarin fita ya tada gen aka kawo wuta. Sai ya zauna yana kallonta,,ya bud'e plate d'in, chips da soyyayan kwai,yawu ya hadiye,dan sosai yake kaunar chips, wanda ya jima bai ci ba,ko yaje siya baya samun wanda ya mishi. A sace ta d'an kalle shi,yana ci yana duba system d'in shi,sai ta sauke ajiyar zuciya. Jakar shi ta gani,da halamar da ita zai tafi,ga nan takalmin shi ya ware su,a d'an dirare ta mike tai gun doster fara ta d'akko, kayan da taga kan gado ta d'akko zata sa taga cikin jakar ba yanda yake,ledar biscuit ne,harda robar lemon da yasha,ga nan takaddun zannen kacha kacha ba kintsi, sai ta futar su duka tana d'an kallon shi ko zai gwale ta,abinda yake yasa a gaba,amma yana kallon ta ta gefen ido. Tsaf ta shirya mishi jakar,takaddun tasa su a aljihun jakar. Ya gama ta debe k'wanikan tai kitchen dasu,da mamakin ta taga baifi uku ya bari ba,ta d'an ta6e baki,tare da cire hijab. Wanke kayan ta fara,ta cigaba da sauran aikin ta,daga ita sai rigar bacci mai hannun vase ta d'aura zani akai,sink take wankewa,yai tsaye yana duben ta,wani lokaci ya tuna a chan baya,yayinda Naina ya ritsata kitchen d'in Hajiya, kusan itama irin kayan ne jikin ta d'aure da zani..cup d'in da ya sha tea ta d'au zata mayar wajen zaman shi,"zan tafi na bar sako a d'aki...a tsorace ta saki cup d'in ya fad'i kasa ya fashe, ba koh sallama kawai taji murya... Shi kuma mamakin shi kusan haka Naina tai wanchan karan,kai ya girgiza, abin tsoro bai da yawa a gun su. Kai ta dago dan jiran jin mey zai ce. Ganin shiru yasa tai kasa da kai murya na rawa tace"Allah ya tsare hanya.. Kai ya k'ada, ba tare da ta gani ba yai waje. Ajiyar zuciya tai,kan ta k'washe wanda suka face,ta share tai d'aki dan rama baccin ta. Basu suka tashi ba sai kusan 10,shima Naina taji a kanta ta lafe kamar mage. Da yamma gidan Maman Nana suka sauka..tace"yanzu nake shirin miki waya fa,tai murmushi kan ta zauna,"gamu munzo toh,zanin ta gyara ma dauri sosai,halamun daga bata jima da fitowa a wanka ba,dank'wali take d'aura wa a gaban mirron parlourn ta,baki Laila ta saka tana ganin ikon Allah,abinda bata iya ba,d'aura dank'wali da d'aura zani.. Asali ma zanin ta biyu single na Holland d'in ta da Super,suma tunda aka d'inko su bata taba sawa ba. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:31 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 48_Murmushi Maman Nana tai mata ta madubin,ganin yadda ta zuba mata ido,juyo wa tai tana kallon Laikan.."Mom Naina hala nayi k'yau ne irin wannan kallo haka? Kai ta k'ada tana murmushi,"sosai kuwa, nifa abinda ban iya ba kenan,daurin dank'wali da zani..ranar chan har magana aka gogan wai kullum dank'wali yana kasa tarbiyar wata kasa.. Dariya maman Nana tasa,"kai Abban Nainan nan da kike ganin shi lumbu-lumbu..hmm,bari dai nai shiru.."a ki fada maman Nana,"wutar k'aik'ai ne..baki Maman Nanan ta rike,"ina kika koyi karun magana haka Laila? Tashi tai ta cire gyalen ta,"Maj'nu na ya koyan.. Wasa maman Nanan ta mayar,kan yanzu a baro aiki. "D'an kara yi na ga,ko dan so na da d'auri.. Ware shi tai,tace"da dank'wali d'aya sai kiyi d'auri 20,,ido ta waro"Allah Maman Nana? Murmushi tai,kan tace"ke d'ai zuba ido..zanin ta kunce,kan ta mata dalla-dallah,kan ta d'akko wani spire ta bata..basu sha wahala ba ta d'aura, sai d'ai wajen tafiya tana harde wa,sai da ta kama hannunta ta saita mata kan ta iya. Aka dawo dank'wali, shi dake yana burge ta taga mace tasha d'auri kan dare tai ta practice,har sai da Dank'wali yace wayyo Laila. Da ta bata labarin yadda sukai da ogan bai g'wale ta ba. A zuciyar Maman Nanan tace"da sannu zaki jawo shi jikin ki ma baki sani ba Laila,,amma a zahiri sai tai murmushi tace"yauwa y'ar gida na,ke d'ai fita hakkin shi,Allah baki lada, sai kuma ki kira kiji ya ya sauka koh? Baki sake ta kalle ta, "kira kuma Maman Nana? Kai ta k'ada"eh kira,ki d'aure, nasan bazai gagare ki ba Laila.. Baki ta tabe,"ni fa ban san meye numbern shi ba bare na kira,barshi kawai. Shiru tai,dan tabbas gyaran gidan su Laila sai ta sake d'aura damara,ace tsawan zaman su ba mai kiran wani? Wane irin halin ko in kula suke g'wada wa juna toh? Har suka zo tafiya tana ta nusar ta kan ta kara hakuri,tai juriya, wataran sai labari. K'wana biyu da tafiyar shi yau,a yadda ta lura bai wuce k'wana biyun, zafi ake a gari kamar mey,Allah-Allah take ta gama da aiki ta huta. Misalin k'arfe biyar suna a zaune a parlour. Wankan orange da jeans sukai,skirt d'in jeans ne jikin Lailan har kusan kasa,sai d'ai gefe da gefen an mishi tsagu har kusan g'wiwa,da riga Orange mai gajeren hannu ta kamata kadan,parking d'in gefe tai da katon ribbons fari da orange,cikin nan yai dan dass a gaba,sosai tai k'yau ita da y'arta,shimi orange ta sa mata,sai skirt din jeans mini,da d'an slipas d'inta mai k'yau orange ko dan ta saba d'an fita gun Baba mai gadi, hatta g'yaran gashi iri d'aya ta musu,ta zama yar bubbuka Nainan,sai tashin kamshi suke mai dad'in ji da duk gidan gaba d'aya, yau d'aya ta taba turaren wuta, har d'akin ogan yasha g'yara kan ya dawo ya wargaza tsari. Tashar larabawa suka kama,suna sauraron wakar yara ta tsuntsu, ta"Ausfoorun Faukash shajara" bin wakar Lailan take,dan tun tana karama tasan wakar nan,da mamakinta sai taji tana bin baitin wakar bai bace mata ba tana k'ada kai.. Sai Nainan itama ta fara binta da jagwalgwalo ta tashi tana irin yadda yaran suke,dariya Laila take mata harda rike ciki,jin yadda ta dage tana bin su "oshfuur!oshfurr!! tana rawa. A waje ya bar motar shi,ya d'akko kayanshi ya shigo gate d'in, suka gaisa da Baba mai gadi yana tambayar shi komai d'ai Normal? Tunda ya kusa isowa parlourn yake d'an jin sautin waka k'adan na tashi,bai san mey yasa yake d'aukin ganin su ba yau. Hannun Lailan ta kamo wai itama ta taso suyi rawa tare,ba musu ta rike hannun ta suna dan jujjuyawa irin na yaran masu wakar,sai tuntsurin dariya suke,,dan jin in tace"Ya Eosfoor" Nainan tace ita kuma"Ana Oshfoor'' inda ta rike ita kawai nan take fad'i..da ka gansu a wannan lokaci g'wanin ban sha'awa,, Kamar yadda mai gidan ya tasa su gaba yana murmushi tun zuwan shi,jin Naina na kiran kanta da "Ana oshfoor sai ya kara bashi dariya,Nainan shi ta zama tsuntsu kenan..a kan Lailan ya sauke kallon nashi, jin yadda take fidda wakar da harshen ta kamar ita ta rai ra ta tana make murya. By Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 2:31 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 50_Parlour sukai ta cigaba da hada mishi abinci a dining tana biyewa Naina da murmushi. Ba'a jima ba ya fito,da halamar ruwa ya watsa,akan dining d'in ya zauna,ginger juice take juyawa,duk da murmushi take amma kanta na kasa,sai ta hau serving nashi, ta siyaya mishi juice d'in a cup,zata ajiye ta d'an k'allo shi suka hada ido,sai ta kawar da nata tare da ajiye mishi ta je ta zauna kusan Naina. Da zumudi ya d'au lemon,sosai yana son shi,tun samun cikin ta yake samun alfarmar shan shi,d'an sosai ginger na taimaka mata wajen rage aman ta da tashin zuciya. Yana cin abincin yana kallon su,kan ya farga yaci da yawa, yau kam d'aya, duk gidan suna cikin farin ciki. Washe gari tana zaune ya aiko Naina da card na waya,,Momyn Mas'ood yau ta kira,duk da tace ita ta daina kiranta zata kira,d'an ganin yadda kullum da kuka suke rabuwa a waya,har sun saba da Baby Naina a waya. Suna gamawa ta kira Y'an Cotonou, nan Mamy take kara mata fad'an ta daina tunani ko d'an yanayin da take ciki,kai ta kada mata,nan ta sha firar ta da sauran k'annen ta. Kuka Naina take kan ta bata waya,dole ta yanke tare da bata tai d'aki watsa ruwa,Abban ta ne ya shigo,sai ta bishi sukai d'aki da wayar a hannun ta. Chocolate ya bata,sai ta bashi wayan ta zauna sha. Hoton kan screen d'in wayan ne ya d'au hankalin shi,Naina ce da Lailan suna dariya sun hada hanci ta d'auke su akan gado,hoton yai k'yau ainun,murmushi yai tare da shafo hoton,tana son Naina amma mey yasa ba ta son cikin shin? Sai ya samu kanshi da duba Gallery tare da bud'e Bluetooth da tura hoton. Yawanci Naina tafi yawa a hoton,wani yai dariya wani ya k'ada kai,mamaki yake yadda ta koyawa Naina tsirin iya D'aukar hoto,har number karan nan ya d'auka. Cikin satin d'ai anyi zaman mutunci ba hancini kamar ba su ba. Gashi ta fita zaga dangi sosai,har dare suna gidan su Naina Babba. Tafiya zai ana neman shi na k'wana d'aya, karan nan harda Naina aka gama komai ya tafi,a satin nan sukai da Dr Auwal tazo ya ganta. Zaune suke a parlour tana koyawa Naina karatun "I t-it,sosai take jin dad'in koyar da ita, d'an tana d'auka sosai har nan da nan ta iya,har mamaki take,dan ko kiran sallah in anayi sai kaji tana binsu,yau da gobe har ta iya,in k'wa tana karatun Qur'ani sai kaga tana kallon bakinta halamar tana son ta d'auka. Shi yasa take yawan sa mata wakar yara ta larabci d'an tasan gaba zata ita fidda ma'anar su. Wayanta ne ya katse mata tunani,sai ta daga tana kallon numbern, sabuwa ce,sai take tunanin d'auka, har ta yanke kan ta farga. Daga chan shi kuma yana tunanin in ta d'auka ma mey zaice mata? Sai d'ai ya kara dailing. Wayan ta kalla kan ta daga,,shiru tai da sauraron waye, sallama ya mata,da mamaki ta sauke wayar ta kalli numbern, tare da watsa ke ido,wai ko mafarki take. Jin an kara yi ne yasa ta amsa a sanyaye,"Faruq ne,kuna lafiya? Kai ta k'ada kamar yana kallon ta,"Umm, ina yini, ya hanya? Kai daga ji kasan ba sabo a ciki..amsawa yai tare da jingina da kujerar motar shi,"Alhamdullilah,ya Naina..Sai ta kallo Nainan wacce ta zuba mata ido,"ga ta nan..sai ta sauke wayan ta mika mata,tare da fad'in"Papa" da sauri ta karba ta fara mishi zuba,Nainan take k'allo da mamakin wai da gaske Faruq ne? Dama yana da numbern ta? By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:31 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 49_Sai yaga sun koma mishi kamar larabawan asalin,har waka ta kare tana mawa Naina dariya..chak ta tsagaita dariyar, jin wani irin motsi da babyn cikin ta yai 4 d first time,hannu ta kai kan cikin nata da d'an murmushi a fuskar ta,Allah yayi,ko yana tayasu farin ciki ne hala? Bata nufa ba sai hawaye taji yana neman zubo mata,a hankali ta nimi waje ta zauna tanawa Naina yake,sai d'ai kamar wata kuliya taji hancinta na shako mata kamshi irin na mutum d'aya, sai ta lumshe ido,sai dai jin Naina tace"papa" da sauri ta bud'e idon,shine tsaye sa6e da Naina,fuskar nan as usual.. Sai d'ai karan nan ya zuba mata ido kamar mai son karantar wani abu a fuskar ta. G'yale karami ta janyo ta rufa na kan kujerar,sai ta mike a hankali tai wajen su,kayan hannunshi ta karba cikin girmamawa,ba musu ya bata,d'an kallon shi tai a takaice lokacin da yake nufar d'aki. Su plantain d'in da Fresh Laban d'inta ta mika kitchen, kan ta d'au jakar shi da sauran kayan ta nufi d'akin. Da sallama ta shiga,Naina ta d'ane gado ta tsaya tana g'wada mishi wakar data iya yana murmushi. Kayan ta ajiye,kan ta mishi sannu da zuwa,kai ya k'ada, yana kallon fuskar ta, sai d'ai taki bari su had'a ido. "Ya gida? Da mamaki ta dago jin tambayar,sai ya basar,"Alhamdulillah, kawai tace,sai ta shafo fuskar Naina tai mata murmushi ta fice. Da kallo ya bita, har ta rufo kofar,"toh mey take nufi? Har yanzun kenan bata son cikin komai? Da wannan tunanin ya yarda tabbas cikin ne ya sa ta daina abinda take zauna goge hawaye,, zama yai kusa da Nainan,da murmushi ya kallo ta kan yace,"you what? Ido ta sa mishi tare da girgiza kai,sai ya sake murmushi, da fillanci yace"basshi kawai,,kai ta kara k'ada mishi. Sai ya jawo ta kusa dashi yana mai tambayar tana son baby? Baki ta wage tare da saurin cewa tana so,sai ya k'ada kai,yasan ko Nainan shi zata taya shi raino in Lailan bata so. Ido yace ta rufe,kamar in yaso mata bazata,sauka yai zuwa wajen kayan leda babba sai dai batta nauyi,sai ya leka fuskar Nainan ganin tana kallon shi,da dariya yace mata"(no Naina,no cheating, no cheating), dariya tai irin ta yara,sai ta kara rufe idon ta da hannun ta..a hankali ya zaro teddy babba yana dariya,da fillaci ya sake cewa ta bud'e,kamar mai jira tai sauri sauke hannu tana dariya,sai d'ai ganin teddyn yasa da k'arfi ta k'walla ihu tare da mike wa tana"yeee Jerry..Jerry. Hannu yasa a kunne yana d'an jin ihun nata yana mata dariya. Da d'an gudun ta Lailan ta shigo,d'an ko ita ta tsorata jin ihun Nainan,ya k'allo ta da murmushi, Naina na ganinta tai gunta da Teddyn mai suffar Jerry,sai rinjayar ta teddyn take,da hardaddiyar hausar ta tace"Momma,Jerry, Papa siyo min..''ki ga.. Duk'awa tai da fara'ar ta tare da shafa jerryn. Hannu ta daga wa teddyn tare da wara su "Hi Jerry.. Sai Nainan ta k'yalk'yala dariya,kai ya k'ada musu shima yana dariya,kan ya juya zai shiga bandaki, da kallo ta bishi,yau d'aya tun zuwan ta gidan nan da taga dariyar shi a bagas. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:32 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 51_Da Naina yai sallama,ba tare da yai mata ba,baki ta tabe. Washegari ya dawo, sai kuma yake wani kama kai kamar ba shi ba jiyan. Tashi sukai Naina na d'an zazzabi,sai rigima take mata,gashi ta rasa mey zata mata,taki cin abinci, ga jikinta zafi k'au..lallashi take amma ina, kawai itama sai ta hau mata kukan,,gashi tunda safe ya fita bai dawo ba,dole abun da bata son zata yi,wato kiran shi. Numbern jiyan da ya kira ta fara dailing. Jin yanayin yadda take magana yasa yasan ba lafiya ba.. Shi da bai ga Nainan ba da safe ya zata bacci ne. Tana kashe wa ta kara rungumo ta,sai kuma tai tunanin juko towel tunda zafi jikin. Tun fara goge jikin ta kara karar kukan tana kiran Momma,tuni sai ta bari ta d'au ke ta. Katon towel ta d'akko ta goya ta dashi,a hankali ta fara jijjiga ta sai zillewa take yi, tasan hadda dangwalolon Naina ma,amma haka suka fito parlour tana ta aikin jijjiga ta. Basu jima ba ya shigo gidan,sai d'ai yadda ya tarar Nainan na yi a bayan Lailan sai yai masifar kuluwa. Tuni ya hau sababi akan danme zata goyata suna dambe ga ciki,kaza kaza in ya shiga nan ya fita nan,kamar dama jira yake,,tsabar haushi ba tasan sanda cikin daga murya tace"wai ya kake so na mata kuma? Komai Ciki! Ciki!!.. Haba,a kaina aka soma shi? Kawai sai ta sa mishi kuka tare da kunto Nainan. Baki sake yake kallon ta,abinda yake gudu ya fara faruwa,wato raini, ita akan cikin nan ta rasa wane irin abu ne haka,"a lalle,kinga makwanci na ne,ba laifin ki bane. Sai kuma taji bata k'yauta ba,duk tsiya ya fita,gashi har murya ta daga mishi.. Nainan ya karba yai waje,wanda ta dan tsagaita kukan. Tunani yake tabbas d'an kwana biyun nan ne yasa Laila raina shi, amma zaya rike girman shi,ko dan gudun faruwar fin wannan. D'an tsabar ya nuna mata kuran ta yaki dawo wa da Nainan har dare. In banda juyi ba abinda take a kan gado,har ta gaji da leka parlour,ta k'wata kiran wayan shi yafi a kirga,sai d'ai bata san abinda zai biyo baya ba,ga tana son jin jikin y'arta ta,a haka har bacci yai gaba da ita,duk tsoron da take ji. A firgice ta tashi tare da kallon agogo,(11pm) ga wata yunwa da take ji,a hankali ta sauko tare da fita parlourn, ganan keys d'in shi na mota,taje gun abincin, yadda ta ajiye haka yake,sai ta juya tana kallon kofar d'akin nashi, a hankali tai d'akin gabanta na fad'uwa,ta d'an jima kan a hankali ta fara turawa, sai taji ta a bud'e,kuma wutar d'akin a kunne,ya ware A.C ga nan Nainan sai baccinta take. A hankali ta taka tana d'an leka fuskar shi, a rufe take,sai d'ai hannun shi d'aya na kan Nainan. A zahiri idon shi biyu,jin shigowar ta yasa shi rufe ido,so yake yaga gudun ruwan ta. Da sanda ta zaga bangaren Nainan kamar wata barauniya. D'an duk'awa tayi tare da dafa goshin Nainan, sai taji ba zafi,halamar zazzabin ya sauka. Sai ta kara k'allon shi,kan a hankali ta daga hannunshi tare da ajiye wa tana d'an cije lebe da rintse ido halamar tsoron kar ya tashi,hannu ta sa duk biyu zata d'akko Nainan taji an ruko hannun, da sauri ta dago tare da k'allon hannun. By Feenat Ja'afar. A bini bashi,nai bak'i ne yau
[12/17/2017, 2:33 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 52_Sannan ta sauke kan wanda ya rike hannun, k'allon ta kawai yake fuska ba yabo ba fallasa, sai ta shiga kokarin K'wacewa, yi take tana k'allon yadda yake kara matse hannun da mugunta, har ta fara k'walla, jin muguntar na yawa yasa da sauri ta hawo gadon da zummar gasa mishi cizo koh ya cika ta. Sai d'ai tana kawo baki hannun shi ya cikata tare da janyo ta duka gare shi,kokuwa ta fara na k'wace kanta,sai d'ai har ta gaji ba ko sassauci, sai kuma ta hau bashi hakuri tana kallon gefen Naina. Bakinta ya kai hannu tare da murda shi,da sauri ta sau karar zafi, "Ba bakin ki ya iya fitsara ba? Kai ta girgiza tana hawaye, ga cikinta ya takura, "sai da ita zaki iya bacci koh? Sai ta samu kanta da daga kai da sauri tana ci gaba da kokarin K'wace wa, shi kam sai ya sau hanya,kuka take harda zata barshi da Allah,amma bai ko saurare ta ba. Kuka take tsakanin ta da Allah, bata taba cin karo da maketaci irin Faruq ba, wato d'an yasan bata iya bacci sai da Nainan shi yasa ya bullo mata ta wannan hanyar d'an ya ribace ta? Toh mey ma ya tado ta a bacci? Tunda har bacci ya tafi da ita kamata yai kar ta tashi sai asuba.. Tashi yai had'e da bata rai,ya fara nad'e tabarmar kunyar shi kamar kullum,ba ko lallashi ya fara.. "Kinga d'au y'arki ki tafi in baza ki min shiru ba,ina son nai bacci". Banza tai dashi tare da juya mishi baya ta ci gaba da kukan ta,wani abin haushi kuma ta kasa bar mishi d'akin. Sai d'ai dake barawo ne bacci tana cikin shesshekar yai gaba da ita. Fuskar ta ya leka, sai saukar da ajiyar zuciya take,shi ya ma rasa kukan na meye? Hannu ya kai tare shafo d'anshi da y'in murmushi,Laila rigima. Sai chan kusan uku ta farka,komai ya cigaba da dawo mata a hankali, idon ta bud'e, tabbas a d'akin take har yanzun,sai d'ai karan nan Laifin nata ne,tunda ita ta kawo kanta har d'akin shi,kuma k'an gadon shi,mey yasa da ya ki sakinta ta hau gadon? Mey yasa banyi hakuri har ya gaji d'an kanshi ya sau ni ba?... Ai da ga'iya yai hakan ko ba ki ga ba? Cewar wata zuciyar, kai ta k'ada,bangaren Naina ta kalla,tai rub da ciki hannun nan a baki tana ta baccin ta,sai ta jawo mata bargo ta lullube ta,d'ayan bangaren ta juya,kamar ya shige mata haka yake kallon ta har yai bacci,tuni wani hawaye ya zubo mata na takaici, sai d'ai kamshin da taji kusa da ita yasa ta kalli gun,rigarshi ce kusa da hancin ta,a hankali ta kara kai hancinta jikin rigar tana shaka tana lumshe ido,wata jaraba kuma ta ciki,ta rasa mey yasa take son kamshin nan?kasa juyawa,a haka bacci ya kara gaba da ita. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:34 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 53_Kamar kullum kiran sallar farko ya farka, da mamakin shi sai ya ganta, bai zatan zata kai safiya a d'akin ba, hannu ya kai zai cire rigar ganin ta toshe mata hanci,yana fara zame wa ta kara ruko ta zuwa hancin cikin bacci,murmushi yai,tare da bar mata yai bandaki. A zabure ta mike jin kiran sallah a masallacin unguwar na biyu,hannunta ta kalla,ganin rigar shi da sauri ta jefar ta chan kasa,sai kuma ta hau kuka wai tana kintsa wa. Da sauri ya fito a bayin yana k'allon ta da mamaki, harara ta k'wada mishi tare da K'awar da kai ta cigaba da kukan ta. "Kinga Malama,tashi ki barmin d'aki,, ba d'ai kin samu abinda kike so ba?.. Da sauri ta kallo shi da mamakin wannan sharrin,sai taji kukan ya tsaya chak,,sai yai saurin had'e rai tare da nuna mata kofa da brush d'in hannun shi,"ki fita dama kan na dawo.. Sai ya koma bandaki.. Da k'allo ta bishi,sai ta k'ada kai,yana da damar cewa komai,d'an laifi kam nata ne,sai d'ai ta kare faruwar hakan a gaba. Ko takan Nainan bata bi ba ta bar d'akin zuwa nata,sai da tana wanka wani kukan ya dawo,ta rasa wacce iriyar K'ADDARA CE dake hadata da Faruq? Wannan ai shine A dake ka a hanaka kuka..Sam ta tsani Faruq k'wata-k'wata, duk ya kara fita a ranta. Fitowa yai yaga bata nan,ga nan ribbon d'inta ta bari a kan pillow,wajen yaje tare da d'auka, fari tass dashi kato sai kamshin gashin ta yake..."wannan fa shi ke sa ta kara raina ka Faruq,kana zubar da girman ka ne a gunta.. Tunanin fad'an da zuciyar shi take mai yake,"kuma fa haka ne,toh yanzu meye abun yi? Sai wata zuciyar tace dashi"ka kama k'anka kawai. Kai ya k'ada, tare da yarda da shawarar karshe,zip d'in jakarshi ya zuge,tare da sa ribbon d'in aciki. Da kuka Naina ta tashi tana kiran Momma,ko d'an dashi ta k'wanta? Jiya tun magriba take kukan momman ta amma yai burus,dak'yar da taimakon allura ya samu tai bacci kan su shigo gidan,sai kawai ya sa mata pampers kamar yadda yake mata da ya k'wantar ta,sai d'ai fa shi ya kasa baccin,yayi imani Laila zatazo neman y'arta komai dare, a sannan ne zai nuna mata kuran ta,sai d'ai kuma tana zuwan zance yasha bam-bam. Tana kitchen ta jiyo kukan y'ar ta ta,da sauri ta fito,har faduwa take, da sauri ta karasa ta d'auke abarta ta sata kafada tana lallashi,("oh my Naina,am so sorry.) "Kin tashi? Sai tai shiru tare da daga mata kai, goshinta ta ta6a,ba zazzabi, sai kuma ta hau mata surutun jiya,k'an tana ta neman ta,wani ta gane wani ta rasa mey ma take fad'i? Sai tai murmushi ta hau bata hakuri. Wajen pampers take nuna mata tana yi da fuska kamar tai kuka,wai allurar da aka mata,shafa wajen suke tai kitchen da ita. Kamar mai tsoron zuwa gidan haka suka zaune da Abban Nana a kofa suna firar duniya, har kusan tara da rabi,dake shima magananne ne bai ko damuwa. Lokacin da ya shigo sai ya rufe gate,d'an Baba maigadi da safe yake zuwa yaga iyalin shi kan ya dawo aiki. Fuska d'unkume ya shigo da sharbi a hannun shi, direct d'akin shi ya wuce d'an ganin basa a parlourn. Yadda ya fita haka ya dawo ya tarar, yau ko gadon ba'a g'yara mishi ba. K'wanciyar shi yai d'an komawa bacci. Bashi ya tashi ba sai shad'aya da wani abu,ga ba wuta d'uk zafi garin,wanka ya shiga,kan ya fito parlour. Da y'ar da uwar d'uk sun zuba mishi na mujiya,ita Naina tsoron allurar jiya take kar ma ya d'auke ta,yayin da uwar ke mishi k'allon tuhuma,musamman da ta ga ya wani had'e rai,kawai sai ta girgiza kai,mutumin nan akwai k'arfin hali. Sai d'ai za tai hakuri har zuwa wa'adinta ya cika. Tukun wai wani wa'adi ga Laila da bamu sani ba? Hala ko ku kun sani? By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 2:36 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 54_Sai d'ai bata san sanda ta gaishe shi ba ma,wataran takan mamakin irin zuciyar ta marar zuciya,, ko taso kartawa Faruq sai ta k'wa6e ta. Kawai sai ta k'ada kai tare da cigaba da yanke ma Naina farce. Da zai fita y'in duniya Naina tazo su fita ta mak'e kafada tare da lafewa jikin Laila.. Saboda ta tsorata da allura,kuma da gaske chan zai kai ta d'an akwai saura. Sai d'ai kan dare har ta manta taje wajen shu Washegari suna mota zai kaita wajen Dr Auwal dan ya mata scan,in banda surutun Naina ba kajin komai, shi ya zirawa hanya kawai ido, sai d'ai ya saci k'allonta ta gefe. Yayinda ita haushin shi kawai take ji tun shekaran jiya. Dr ya duba ta yai mata abin da ya kamata. "Baby d'ai yana lafiya, Aboki,tunani d'ai kawai madam zata rage. K'allon ta yai,kan ya k'alli Drn,"mun gode sosai. Dar Auwal ya k'alleta,"kin shiga second trimeter ki ba? Kai ta daga mishi, ya k'ada kai,"good,yanzu d'ai zaki kula da exercise, ko estate d'inku kina zaga wa, na san d'ai zaki kula da yadda ya dace,Oga bani matsala da madam d'in ka,sai nan da 7month sai ta dawo,time na 3rd trimestern ta..shidai bai gane wani abun. Har sun fita yace su jira shi,sai ya koma office,"yauwa,akwai tambaya,,likita ya g'yara tare da mashi dariya,"ina jin ka,,"ya batun goyo? Durkushe da sauran su,hope bazai shafi cikin ba? Dariya yai iya y'in shi Dr Auwal,kan ya tsagaita. "Goyo? No way.. kana tsoron 6ari ne hala? Da sauri ya k'ada kai, "toh imshaAllah an wuce gun, cos lafiyyayyan ciki in ya shiga second trimeter bama tunanin fitar shi,cos an wuce gurin,sai d'ai in Allah ya k'addarto faruwar hakan,and ina tunanin ka siya mata abin auna Bp,sannan Faruq,please! kana lalla6a Laila,wallahi abun tausayi ce,cos yanzu na auna Bpn ta ya kai inda bai kama ya kai ba at dis stage. Kai ya k'ada, yana ce mishi ya gode, sai d'ai shi ba ta batun bp yake ba,murna yake akan cikin,tai yadda take so. Tun daga ranar ko goyo sukai sai d'ai ya sa musu ido,wataran harda murmushi, wato tai komai,ba abinda zai samu cikin shi. Da Omar yake waya,kan yaki ya waiwaye su,yake fada mishi suna hanya d'ukansu. Bikin K'anwar Naina babba ake,sun hau busy,in ta shiga y'an uwa ko gidan Hajiya har bata son komawa gidan Faruq,gashi yadda ta kula kul'le yake son mata,d'an kowa yazo gidan ta sai yai mata mitar bata zuwa ko'ina, takan yi murmushi, bare da yanzu cikin ya girma sosai,ba wanda ta tsani gani irin Faruq, ga zuciyar ta kusa a kanshi, nan da nan zai abu ta fara jin haushi, amma d'uk tsiya zata ragawa Y'arta. Hakan yasa shima ya bud'e wuta, shi adole bai son raini. Waya take da Aunty Salma, in ka ganta abin ka tausaya mata, K'afa ta kumbura, ita kanta ta kara habbaka, d'uk da yanzun fruits ne abincin safe da daren ta,d'uk dan ta saita weight d'inta, amma yadda ta fuskanta ba wai a kibar bace, tsabar rashin k'wanciyar hankali ne da rashin iya tattalin ta. Shi yasa kullum in taga yadda cikin yai girma sai ta koka, d'an tasan da Maj'nu keda shi da kila azo k'allon su d'an tsabar tattali, har abada bazata gaji da fad'in tai rashin da bazata maida gurbin shi ba a rayuwa. Hawaye ta goge,tare da tashi ta fito parlour d'an jiran Aunty Salma. By Feenat Ja'afar. [3/22, 8:49 AM] Feenat Ja'afarí ½í¸: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 55_Kusan tare suka shigo da Aunty Salman,wanda shi yakan yi mamakin yawan zuwan ta kuma su kule d'aka,, yasha ya tambaye ta,sai d'ai tace mishi kawai"Ka lalla6a Laila..hala k'wai ce ita da zai lalla6a ta? Yanzu da baiyi da gaske ba ai da tuni ya ta ma gama raina shi. Karan nan d'akin shi ya wuce,sai d'ai bai san ko wace karyar take had'a mishi gun Aunty Salman ba. D'an baiga ranar da bazaije gida Hajiya bata mishi fad'an ya tausayawa Laila sannan ya lalla6ata su zauna lafiya. Kamar kullum suna tattauna mafitar su yazo zai mata sallama dama abu yazo d'auka, sai yaji Aunty Salma na lallashin ta.."na sani,amma ki kara hakurin cikar lokacin.. kai ta girgiza mata,"Aunty Salma bazan iya ba wallahi,lamarin fa ba sauki,ki kalla yadda nake kumbura fa..sai ta hau mata kuka,''nidai kiyi musu magana d'an Allah, wallahi nai kok'arin saita komai,amma ya wuce zato na.. Barin gun yai yana g'yada kai,yasan da wata a kasa.. Sai d'ai bari zai dawo. Aunty Salma tunani take,na ydda Laila bata mantuwa,tai tunanin ko ta hakura da wanchan nufin nasu,ko dan samun rabo,dan ta jima bata mata wannan maganar ba,sai d'ai tafi tausayin D'an uwan nata,d'an tasan sam bai kula da Laila ba,bare ya bata kulawar da zata mantar ta baya ba kamar shi,shi ba gashi ya ware abun shi ba,sai narka kibar jin dad'i yake. Sai dabara ta fad'o mata. "Amma Laila ya zakiyi da Naina? Da sauri ta dago tana k'allon Aunty Salman, sam ta manta da Naina,sai tace"da ita zanyi komai Aunty Salma.. Sauke ido tai kan Nainan,wacce kawai ta zuba mata ido,ganin yadda take kuka. Murmushi Aunty Salman tai,dan jin dad'in amsar Lailan,lalle ta yarda Laila d'anya ce,za ai saukin zira ta. Sai d'ai ta manta da Naina ba abar ta bace, kamar yadda mai ita yace,,sun bari akan yarda Lailan tace. A yadda ya shigo mata,tasan yau ba kallau ba,hakan yasa da sauri ta k'auda kanta daga k'allon shi, d'an in ya soma tsiyar nan toh fanshe wa yake akanta tasan. Sai d'ai kan ta gama zancen zuci har ya hau masifar shi,hannu tasa ta rufewa Naina k'unne tana hawaye. Da Fillanci yake mata masifa,sai ya tuno bafa ji take ba,sai ya dawo Hausa. "Ok,dama shi yasa kullum in naje gida an d'inga cewa naji tausayin ki nai miki kaza nai kaza? Ke y'ar mai saboda ba k'ya son fad'a koh? Toh wallahi ya zama rana ta karshe da zaki kara kai kara ta gida,in ba haka ba..."mey zakayi? Ka sake ni koh? Tashi tai a hankali,"d'an Allah Faruq ka sake ni toh,koh ka kashe ni ka huta, nima na huta, kowa ma ya huta da kai kara,ka ga sai naji dad'in zuwa ga mai so na,wanda yasan tattali na,yasan abin fad'a,yasan kuma wanda bashi ba,,wanda da shine kai yanzu a halin da nake ciki wallahi bani ba takaici,bani ba bak'in ciki,bani ba zubda hawaye.."Mas'ood zai wahala na samu madadinka a rayuwa,, kai ne d'aya, wallahi tamkar dub...ido ta waro,tare da rintse su tana hawaye,,ganin yadda ya daga hannu yana huci zai mare ta,d'an ta saddak'ar yadda ya d'akko hannun nan sai ya sauke su a fuskar ta. Sai d'ai da mamakin ta taji shiru,doka kofar d'akin ne ya sata bud'e ido,a kasa ta zube a dandamalin tiles tana rusar kuka..yadda kasan an aiko mata mamy ta mutu, gashi fur k'wana biyu taki kiran y'an gidan,ganin yadda kullum suke hadata da Allah akan tai zama na aure ta kuma bi mijinta s'au da K'afa. Kamar an tsikareta ta tashi dak'yar tai d'aki. Jaka ta d'akko katuwa trolley, ilahirin kayan ta ta jide,ba na baby ko d'aya, wai kuma sai ta fara had'a harda na Naina tana kuka,,yi take ba ko hutawa.. Jin an rukota ta baya yasa tai saurin juyawa.. "Momma"..Naina ce cikin gigin bacci,haka ta ciccibeta ta d'aura a kafada tare da sake sakin kuka mai ciwo, wallahi bazata iya barin Naina ba,d'an ta zama wani bangare na farin ciki a gare ta tun farkon ganin ta,,tun lokacin da bata ma san jininta ba ce. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 2:36 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 56_Dagowa tai tana k'allon Momman,ganin yadda take kuka yasa ta fara kokarin yi,,hannu ta kai tare da goge mata,sai ta dago da sauri,a gado ta d'aura ta,d'uk da haka ta kasa d'aina kukan, bata zata ba taji Nainan tace"papa ne? Da sauri ta k'alleta da mamaki,baki itama take ta6e wa halamar son y'in kukan tana girgiza mata kai,,da sauri ta goge idon ta tare da k'ak'alo murmushin dole.. Jawo ta tai tace"ba papa bane ok? Na daina kinji? Baby ne yake damu na. Sai Nainan ta k'alli cikin Lailan,da mamakin Lailan sai taga tasa hannu a baki,halamar d'ai zancen bai shige ta ba. Tunani take yadda Naina tai wayo,shekara 3? Har ta gano Papan ta ke sata kuka? Kai ta girgiza, ba zata so tun yanzun ta shiga tsakanin Y'a da ubanta ba..Abadan,,sai d'ai tasan in d'ai zasuci gaba da zama da Faruq toh fa Naina zata gane komai a gaba. Da wannan ta samu ta lallasheta koma,tare da cigaba da hada kayan ta. Kofa taje ta datse da key, harda Jam luck,d'an tasan sai ya zo a zuwan huce haushin shi ya ribace ta. Sai ta kira mamy kan tana son gobe a turo mata kud'i daga account d'in ta,yawan kud'in yasa momy mamaki,d'an wannan ne karan farko da tace a ta6a kud'in, koh dan ta kusa haihuwa? Sai ta bari a hakan ne ma. Washegari sukuku ya tashi ya wuce masallaci, sukam warai ta tashi,ganin tunda Naina ta tashi take k'allonta, sai ta hau abinda take ganin Nainan zata ware. Wanka sukai,suka shirya abinsu,gari da d'an sanyi ta sa ma Naina k'aton rigar sanyi pink da fari,da wando pencil, sai ta d'aura mata hula mai gashi shi pink. Sam ta ma hakura da tafiya yau,sai d'ai ma shirin ganin likita,d'an yace in har Monday bata haihu ba taje,d'an EDDn ta tuni ya d'aura 2days. Kusan takwas da wani abu ya shigo,jiya da k'yar ya samu yai bacci,so yake ya bata hakuri,sannan ta guji fada mishi magana son rai. Dariya suke kamar ba ita bace jiya,da mamakin shi sai ya ganta yau d'aure da riga da zani harda d'aurin dank'wali, tai masifar k'yau. Dama ta ita take kin d'aura wa? Sai yai murmushi tare da k'ada kai. Y'ar shi har kullum kara ganin k'yaunta yake. Wajen su ya iyo,sai d'ai mey? Chak ya tsaya tare da k'allon abinda Lailan take. Wai Naina ke ambatan babyn su,wai zaizo yaushe? Sai Lailan ta rike k'ugu cikin wasa tana cije le6e "wassh,gashi nan zuwa kin shiry.. ''Laila.. Cikin tsawa ya katse ta,tsananin bacin rai zaka ga a fuskar shi, kai ita sai ta rantse akan bata ta6a ganin shi a wannan yanayin ba,,matuka ta tsorata daga ita har Nainan,ba shiri ta mike tana ja da baya ganin yana tunkaro su. Da gudu Naina tai gurinta ta fara kuka,d'aukar ta tai itama tuni ta fara hawaye,tabbas tasan mai hali baya fasa halin shi. Sai d'ai yaja ya tsaya,amma bai fasa sababi ba. "Ya'u na gama yarda bakida hankali...da sauri ta dago da tsabar mamakin jin kalaman shi,"oh,ta haka kika bullo kuma? Ai da bai kamata ki kawo wannan lokacin ba,da tunda ya mutu sai ki hadiyi zuciya irin na Lailan gaskiya lokacin da Maj'nun ta ya mutu ki bishi.. d'an wallahi baki isa ki mutar min da d'ana ba,sai d'ai ki bishi ke kad'ai kamar yadda kika ce. Ido ta rintse tana kuka mai sauti Naina na yi, da hannu ya bugi bango, wato a gidan shi bazai fada ba sai a hau mishi kukan 6aci? Sai ya barsu nan ya d'au mukullinshi yai waje. K'warai ya haukace.. D'an ita kam bata ga abinda tai ba,sai d'ai karan nan ta rantse da Allah bazata kara second 60 a gidanshi ba. Sauke Naina tai,tare da d'akko hijab,d'an abin ba na g'yale bane. Jakarta da ta zuba kayan su ta jayo sukai waje. Taimakon ta d'aya? Baba mai gadi baya nan,komawa tai,ta d'akko d'uk wani kud'in da yake bata in zai tafiya da bata ci,ta zari mukullin gate,dan sauri har ta manta wayar ta. Kofar ta rufe,taji dirin keke Napep a bayan su,da sauri ta juya tare da tsayar shi,ba kowa layin kamar kullum,na aiki sun tafi aiki. Gidan Maman Nana ta shiga,time d'in zata raka Abban Nana ya fita,sai suka koma,tsiya take mata kan ta ganta kuwa a zani? Kai tai k'yau, murmushi tai,tare da mika mata mukulli,sai lokacin ta kula da fuskar ta,"Mom Naina Lafiya kuwa? K'allo ta tai,"mey kika ga? Kinga ni asibiti zamu,ga mukli nan in Abban Naina yazo zai kar6a. Galala take k'allon ta,"Abban Naina kuma? Mey zanyi da mukulli bayan tare zaku? Ganin zata gano ta yasa ta tashi tare da fad'in.."ni kar kisa layi ya cika na rasa awo da wuri..dariya take,tace"Ku da k'anku masu abin? Sai tai murmushi tare da biyo ta,"wai ni kam anya ba wani abu Mom Naina? Tsayawa tai a bak'in gate d'in,"ki koma ba komai,kin san d'ai ba k'yau leke koh? Harara tai mata,tare da juyawa,"toh uztaza,sai kun dawo. Da sauri ta shiga napep d'in, ganin bata gano kom ba,sai d'ai bata jima da barin layin ba Maman Nanan ta fito da sauri, sakamakon tambayar ta shin lafiya yaga Mom Nainan da kaya a Napep? By Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 2:37 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 57_Fitar shi da awa d'aya ya dawo,lokacin har tara ta wuce, a bakin gate ya tarar da maigadi,tambayar shi yake ya yaganshi a zaune bai shiga ba? "Ai ku nake jira ne..da mamaki yace"a rufe ne?.."Abban Naina ina k'wana..Maman Nana ce ta katse su lokacin ta kara fito wa, ya amsa,da mamakin shi sai yaga ta miko mishi mukulli, sai ya mikawa Baba maigadi har zata wuce ya tsayar ta,"Manan Nana tace miki zata wani waje ne? Tai d'an jim,kan tace"asibiti tace min zata kawai,,kai ya k'ada,"na gode. Har ya shiga gida tana tsaye,bata so aji mutuwar sarki a bakinta ba,amma in d'ai mutumin ya kai Maman Naina bango ta tabbatar tafiyar ta tai,toh amma ganin Naina yasa ta fara ko k'wanto,ga ta kira wayanta tana ringing ba'a d'auka. A parlour ya zube a kujera,wace iriyar K'ADDARA CE wannan wai? Kowacce mata sai ta mishi irin wannan karyar nakudar a gida? Ya rasa Naina akan hakan,itama Lailan so take ya rasa ta ko mey?..daga magana kuma cibi ya zama k'ari? Kai ya jijjiga,"kiyi hakuri Laila,daga yau zan barki kiyi son ranki,kila ni an K'ADDAR to min rasa mata yayin ciwan nakudar su ta karya. Dagowa yai,tare da zaro wayan shi ya hau bugu,sai d'ai da mamakin shi tana kusa da dashi a kujera. Tashi yai,ya d'an watsa ruwa, sai yai sauri ya shirya yai asibitin. A Office ya samu Dr Auwal d'in, hannu ya bashi yana mishi ya gida,"ina madam d'in ga file nata ya gaji da jiran ta? Da mamaki ya k'alleshi,"kana nufin wai bata karaso ba? Baki sake Dr ke k'allon shi,"gaskiya da tuni ta shigo in tazo..da sauri ya mike tare da dafe kai,"Toh ina Laila ta yi? Bai ma san maganar ta fito ba sai da yaji yace"ba tare kuke ba hala? Kai ya k'ada mishi,sai d'ai tuni hankalinshi yai gaba. Gidan ya koma,dan a tunanin shi ta koma, kawai sai ya makale a kofar su Maman Nana,so yake ya tambaya ko d'ai tana gidan? Sai d'ai mey? Maman Nanan yaga ta fito a gidan zata koma gidan nata, tsaye tai tare da kawar da kai,dan wallahi ko ita haushi yake bata bare Laila. "D'an Allah in tana ciki Maman Nana kice ta fito muje, likita na jiran mu,cos zai tafiya 10am.. Kukan data fara ne ya katse zancen shi,"Laila ta tafi Abban Naina,,sai d'ai ban so abin naku ya kai haka ba Sam.. Laila abin ka tausaya mata ne,d'uk da kaima abun a tausaya maka ne..a d'ukkan al'amarin ta da Mas'ood yake tafiya,saboda ya mata sabon so,lallashi,jin kai,d'uk da haka tai sacrificn nata damuwar ta kawar da taka..a d'an takaice take bashi labarin wace La'ilaMaj'nu?... In banda zufa da k'allon Maman Nana ba abinda yake. "D'ukkan ku kun kasa kar6ar K'ADDARAR da ta saukar muku, amma wallahi Laila ta amsa tai har Istigfari a gabana, kan zata k'yauta ta maka iyakar iyawar ta. Ido ta goge,tare da k'allon shi,"ka kara godewa Allah,kai Allah ya azurta ka da Y'a ta tsatson Naina,,wanda in kaga kana jin dad'i, ita kwa Laila bata da ko d'an yatsa, d'uk da tsawan shekara uku tana nema Allah bai nufa ba, bayan hoto ba abinda ya rage gare ta na Mas'ood.. Na zata zaka wanke maza agun Laila,,na zata zaka nunawa Laila lalle akwai masu kula da ita sama da Mas'ood a duniya, har ta manta komai. Kai sake Abban Naina, d'uk da Abban Nana yace kar na sanar ka ya zama dole ka sani. "Tun kan Laila tama nisa ka dawo da ita, Abban Nana yace ya bi sawun Napep d'in sunyi Bank,nai imani daga nan tasha zatai,dan bazata tsaya a nan ba. By Feenat Ja'afar. [3/22, 11:49 PM] Feenat Ja'afarí ½í¸: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 58_Jiki a sullube ya shiga gidan,d'uk tunanin shi ya kare. D'akin Lailan yayi,komai a g'yare kamar bata debe kaya ba, a gadon ya zauna, tare da dafe hannun shi duka a kan gadon,, a hankali ya k'alli bangaren da ya ji hannun shi na taba wani abu. A hankali ya janyo shi,frame ne nasu Laila da Maj'nun ta data manta a kasan pillow. Sanye suke da suite,ita na mata da wandon shi baka,rigar ta dame ta sosai,sai g'yale data nannada pashmina iya kafada, shi nashi fari ne,da yar ciki ja,dariya suke tana k'allon shi,shi kuma yana k'allon mai camera,a U.K suka dauk'a.. da ka gansu,tabbas za kasan masoyan juna ne. Mas'ood d'in yake k'allo, kamar ka kirashi yazo,a zabure ya mike kamar an tsikare shi,, mota ya shiga, tukun yanzu ina zashi? In Bank ne yanzu ai ta bar wajen,toh wani Banki ma zai nufa ba suna? Kawai sai yai tasha. Kiran Dr Auwal ya gani,kamar kar ya d'auka, sanarshi yake ya fasa tafiya,zasu iya samun shi bayan azahar..."Aboki ina cikin matsala,bari zan kira ka.."kana ina yanzun? "Tasha..kit ya kashe tare da sa mota cikin tashar. Dube ya fara,d'uk bai tabbatar nan d'in tazo ba,mota-mota yake bi, tare da tambayar mace mai ciki da Y'a a hannu. Kamar ance ta juya,taganshi,da sauri ta duk'ar da kai tana salati,Naina ta janyo, a hankali take neman sauka,dama ta kosa motar ta cika amma taki,driver take wa magana cikin masifa,"ka cire min kaya na tunda ba tafiya zaku yi ba.. Hakuri ya fara bata, kan tai hakuri ta kusa cika. Baya ta k'alla, ya kusa cimmata,tuni ta bud'e wa mai mota wuta kan sai ya ciro mata jakarta. Juyin da zatai taga ko ya kusa kamo sun suka had'a ido,, da sauri ta kama hannun Naina cikin sauri zata arce ya cim mata. Ihu ta fasa tare da nuno shi hannu tana neman su taimake ta,"Wayyo Allah..."jama'a ku taimake ni,wallahi d'an yankan kai ne... Tuni mutane sukai chaa kuwa,,chak ya tsaya tare da ware hannun shi halamar yayi surrender, amma ga Nainan shi,gurin shi mutane suka fara yi,yayin da ta kara makalo Naina a bayanta da ta fara kuka. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:41 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 59_Bata zata ba taga ya zube mata g'wiwa biyu hannu dage,ya wani marairaice ma ta,,"Laila 4give me..please,, da sauri tace"karya ne,ni ba sunana Laila ba,ku rabani dash... Ciki tai saurin rike wa tare da cije lebe..kowa na fad'in abinda ya dace ai ma Faruq,yayin da mai motar ya fara duba list d'in littafin shi, ba wanda ya kula da yana y'in Lailan,da azama ya tashi zai kamota ganin tana neman durkushe wa.. Hannu ta daga mishi, "kar ka kusanto ni,, zan sa suma d'ukan tsiya wallahi..."washh,,sai kuma ta rike ciki,tare da kara jawo Naina. Nainan ya k'alla, yadda fir taki ko kulashi,saima kara manne wa Momman take,sai ya furzar da iska,"Laila kar ki illata kanki,bakida lafiya.. Ido jawur ta dago,"ai mutuwa itace farin cikin ka gare ni, ko ba haka kace ba? G'wara ka kashe ni sai ka huta, nima na huta. Ido ya lumshe,, yanzu dame zai cece kanshi da sharrin Laila? Dr Auwal ne ya shigo da motar shi,chan nesa dasu ya parker,ganin cincirindon jama'a yasa ya tsaya jin ba'asi daga d'an nesa k'adan dasu. Da sauri dabara ta fado ma Faruq d'in,sai ya matsa k'adan,,"Tunda hakane toh nima ki bani y'ata.. Hannu ya mika mata. Baki ta cije,d'an wani baya rufa katara, jin ciwan ya lafa mata yasa ta mike sosai,, "ai ba yau ka sanar ni ba tawa bace,, nice marar zuciya,, y'arka bazata hanani tafiya ba ai... "Subhanallah.. Laila, Faruq...kowa ya zuba wa mai maganar ido. Dr Auwal ke k'allon su baki sake, zai magana ta kara cewa,"Wallahi bakin su d'aya, ni ba sunana Laila ba.. Mai dubo list yai saurin katseta,"jama'a ya kamata mu watse, ina tunanin ciwan nakuda ke damunta,d'an nima Laila Abdull Basir taban a sunan ta. Murmushi Faruq yai, sai Dr ya katse su,"amma hakan bai kamace Ku ba Laila,atasha? Toh mey ya miki haka? Da harara tace"ai bani zaka tambaya ba.. D'an ban sanku b... Ciki ta kara rikewa,, sai d'ai wannan karan ido duka ta rintse tare da rike baya,da ido yai wa Faruq d'in kan ya kamata,dan yasan labor take. Amma d'an k'arfin hali saida ta mike,sam kwa ba zuciyar, Naina na makale a hannun ta. Jama'a d'uk an watse,sai y'an tsirari da suka tsaya ganin k'wak'waf. Ganin yana kokarin kamata bakin bai mutu ba,Allah ya isa take mishi in ya ta6a,ko kulata bai ba Dr ya d'au Naina,d'uk idonta ta kumbura d'an kuka. A labor aka tura ta,sai d'ai ta saduda, yanzu tana kula Dr,kodan ya taimake ta,fir Faruq yaki fita a d'akin, gani yake kamar yana fita itama zata mutu ne kamar Naina. Yadda take nishi tana zufa gaba d'aya sai ta sashi hawaye,,ya bala'in tausaya mata, sai ya matso d'an mata sannu, da jaraba ta bar laborn ta fara zazzaga mishi masifa, wanda tuni yai waje yana bata hakuri. A hannun wata nurse yaga Naina tai baccin dole. Shi hankalin shi ya ma kasa bashi ya nemi wani a gida. Ko minti 10 bai da fitowa ba ta haihu, da taimakon Karin da tasa dole a mata. Babyn tai saurin k'allo ganin yadda an d'aki bayanshi ya fara kuka.. Uwa kenan. Fitowar Dr ne yasa ya matso gare shi da sauri, "ya Laila? Hope bata mutu ba? Kai ya k'ada yana dariya.."tana ciki,dak'yar muka k'wak'ulo d'anka,ana g'yara ta, so nake ka shigo pls, zaka tausaya matuka in kaga babyn ku da Laila. Ana mata d'inki ya shigo, da sauri ta K'awar da kai tare da rintse ido, kai ya k'auda, lalle ya gaida mata, d'inki ake ma jikin mutum ga azabar haihuwa. Sannu yake mata,har aka gama d'inkin, babyn aka nad'o a koran mayani, suka bawa Dr,yana dariya yai wajen su Lailan, tare da mika wa Faruq, sai ya k'alli Lailan kamar mai neman Umarnin d'aukan babyn. Kamar su guda da baban shi,wato kamar Nainan su sak. D'akin hutu aka kai ta, sai sannan ya tuna ya sanar da su Hajiya. Shiga sukai shida Dr,sai yai wajen ta da babyn,da sauri ta k'au da kai,sai ya marairai cewa likita, d'an tunda ta haihu ko masifar taki mishi bare ya ji dadi. K'ar6ar babyn Dr Auwal d'in yayi,sai cikin wasa yace"madam baki karbi babyn naki ba fa, gashi sai hannu yake sha halamar yunwa. A hankali ta juyo,hawaye na bin idonta,,"Mai d'an zaka ba wa Dr,ba nawa bane, ni na gama nawa aikin, tunda na haife shi,, ka bashi, zai shayar shi kamar yadda yake fadamin. Turkashi! Ba Faruq ba, har Dr zuba mata ido sukai,sai dai da mamakin su suka ga tama juya musu baya. Hmm! Wannan shine 'IDAN MAYE YA MANTA... BY Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 2:44 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 60_Wani durkushen ya sake, karan nan yai bala'in y'in kalar tausayi a gaban Laila, shi fa Dr har yau bai san komai ba,don kalau suke zuwa ganin shi. Amma ayau ya ji abubuwa da dama a bakin Laila. "Kimin horon komai, amma banda wannan, laifi nawa ne Laila, amma Mas'ood karami babyn kine halak malak, ("am begging you...please) da sauri ta juyo tana hawaye,, "Mas'ood d'ina ka sa? Da sauri ya k'ada kai harda murmushin dad'i, baki ta ta6e, kan ta koma ta k'wanta. "Wani Mas'ood d'in d'ai chan,ni ba nawa ba kam. Hannu Dr Auwal ya nuno mishi,halamar yai shiru,,"No ba damuwa madam,bari mu barki ki huta, yanzu zamu dawo. Shiru tai musu,tana ji suka k'wantar shi a bayanta suka fita. "Yanzu friend ya ka ke gani zata so d'an kuwa? Murmushi yai,lokacin da yake bud'e musu office d'in shi suka zauna. "Mey yasa kace haka? Labarin abun baya da take ya ba shi, dariya sosai yayi,sannan ya k'allo shi,"wani sa'in wallahi Faruk(u r impossible) "ta ya wannan zai sa ka gane bata son cikin ta? "No, bama wannan ba, wallahi a d'uk duniya babu wanda ya kai uwa son yaron ta Aboki,, "dazun fa ana mata k'warfar jini,amma d'uk da gashi acikin wahala take,amma ina d'ukan d'an ta dan baiyi kuka ba da sauri ta k'allo shi,,cos a wannan time d'in nai imani ji take kamar ita na duka,, "kai! Kasan kuwa wace uwa da d'anta kuwa Faruq? Kai ya girgiza yana murmushi. ''Bana tantama yanzu haka tana rungume da d'anta. Murmushi yai, yana fatan Allah ya sa haka. "Toh amma ni abinda zai ban mamaki shine yadda Laila ke zaro wasu maganganu, hala kai mata laifi ne? Ajiyar zuciya ya sau,kan ya k'allo shi, "laifi babba ma aboki,, d'uk da wani ina hujjar kare kai,amma nasan naima Laila laifi. Ataikaice ya bashi matsalar, k'warai ya jin-jina mishi,, "bazan boye ma ba Faruq,ranar dana fara ganin Laila a gidan ka, matsayin matar ka nai matukar mamaki, cos ban zata zata iya aure bayan rasuwar Maj'nun ta ba,, Mas'ood irin mai sangartar da matan nan ne Faruq, wajen aikin mu d'aya, amma ina sanar maka ba wanda bai san su waye LailaMaj'nu ba, cos sun shimfida tsaftacacciyar soyayya wanda koya yake burin k'wafar irin ta,, masoya ne na karshe,en mutuwar shi ta jijjiga Laila, kiris ya rage tai Losing Memory Allah ya cece Faruq, amma sai naga tana zaune a gidan ka lafiya,, dole ta tsoraci sauran maza, cos bakai mata koda k'watank'wacin Mas'ood ba.. Fada yake ta mishi, da sanar shi Lalle Laila macen zama ce. "Ka barta zuwa ta huce, sai ka nuna ma ta kai nadama matuka, sannan kai kokarin k'watanta koda zama Mas'ood ne a gunta. Ita kam suna fita ta sau ajiyar zuciya,, a hankali ta juya ga babyn nata,,hannu a baki, Nainan ta sakk kawai babyn ya dawo mata,,hannu takai kan summar shi ta shafa tana murmushi,,a zuciyarta ta fara magana ita kad'ai..."my Mas'ood.. (I so much love you.) "Ashe bazan iya barin ka ko awa d'aya ba,, ashe haka uwa ke ji a son d'anta? Su Aunty Salma ne suka zo da sauran y'an uwa, kowa sai yaba baby yake mashaAllah, gogan kam baki har k'unne, ganin ta rukunkume Naina,yasan son su daga Allah ne ita Naina. Duk da murmushi take a jama'a, amma fa ko k'allo shi bai ishe ta ba. Asali ma yi tai kamar ba ai ruwan aa gun ba, sai suka zata y'an uwan ko kunya take. Kayan baby suka jido a gida,d'uk zasu iya ma tafiya, amma an bari sai safe, yaro yasha kayan sanyi aka d'aura ma Naina, sai dariya take mishi tana ma momman ta yaren ita kad'ai ke gane wa. Da kuka aka tafi da ita da zasu tafi da daddare, sai aka bar Inna Bilki agun ta. Tun daren ta fara tunanin ta wace hanya zata fara? Ga nan inna Bilki ta tare ko'ina. Har asuba,kan dabara ta fad'o mata,band'aki ta shiga,tai wanka,ta gasa ruwan d'umi sosai,kan ta fito,kaya ta sa,ta k'alli jakar ta, jiya ya cire mata wasu kayan dayawa ya mayar gida,ya kawo mata kuma wayarta,na baby ne da kala uku,zuge jakar tayi, ta hada tea mai kauri tasha kan ta kimtsa babyn shima da hula da socks,goya abunta tai,tai imani tana bud'e kofa inna zata tashi, sallah ta tada innan, da k'allo ta bita, "kuka ya ke kika runduma shi baya? Kai ta k'ada,"A'a inna zan d'an zaga ne kadan, nayi allura ne yanzun, toh ba'a son ka zauna. Baki innan ta ta6e, "ai ko kam ak'wai iya yi, toh ki kunce d'an kije ke K'adai, dan gari da sanyi sosai,, ya Allah! Wannan so take ta bata mata bujet, da sauri tace"ai inna da kayan sanyi,ga goyo, ga hijab, kad'ai shiga kiyi alwala kan na dawo. Tace"bama wannan ba,nifa Umaru yace kar na barki ki d'ara ko kofa jiya.. Fuska ta tamke,,"ni wai da aiki na Inna? Sai kuma ta dawo sanyi,"ba jimawa zanyi ba,yi hakuri Inna ta.. Kai ta k'ada, tana kokarin tashi tace"ku kuka sani d'ai. Tana ganin ta shiga bayi ta janyo jaka a kasan gado,ta zura hijab ta wuce,, adu'a take Allah yasa kar ta samu kowa a gate, securityn d'akin mata d'uk sun sheme baki suna bacci har ta fice ta kofar baya. Ana sallah a masallacin asibitin, tana ganin lokacin da d'ayan securityn gate d'in yai masallaci, d'ayan ya d'au buta halamar kama ruwa zai yi,, da sand'a ta zare sakata, tana mai gode Allah da ya fitar ta ba mishkila. "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 61_Tai tafiyar K'afa sosai, dan ma jan trolleyn take, d'uk tsoro na Laila ranar ji tai babu, Allah ta taimaketa ta samu abun hawa sai tasha. K'warai da sa'a ta fito, dan motar farko ta samu saura mutum biyu,dan tsabar sauri sai ta sai kujerar,burinta ta sauka garin Kano. Ko da inna ta fito taga bata nan kawai sai ta k'ada kai,sallarta ta tada,tana fad'in"in kin k'waso mishi mura ke da uban d'an ai. Sai d'ai gar gari yai shaa,ba Laila ba dalilin ta,bata kawo komai a ka ba,sai ma ta kishingida ramuwar baccin da baby ya hana ta. Misalin k'arfe bak'wai yazo asibitin, da flask d'in tea,direct d'akin nasu yai mai mutum d'aya. Jin bud'e kofa yasa ina cewa"sai yanzu zaki dawo? Ni fa Laila banson fitina... "Inna ina ta je Lailan? Da sauri ta bud'e ido ta watssake, "au Faruku? Bata dawo ba har yanzu ashe? Bai ko kula ta ba ya ajiye flaks d'in tea ya leka gado,wayam ba jaka. "(I knew it).."amma inna sai da nace kar ki barta ta fita ko'ina,gashi nan ta gudu yanzu,, tashi inna tai tana"kai bana son iskancin banza,allura tai ta fita zagawa d'an tana d'aukar ta.. "Wane guduwa sai kace a shirin film... Ina ai shi bai ma gama sauraran ta ba yai waje,, waya ya d'auka ya kira Dr Auwal,ba amsa, tuni ya juya akalar motar shi, sai tasha. Sai d'ai duben duniya ba Laila,ba dalilin ta. D'an sunan karya ta bada,ya kira wayarta a kashe..gashi bai san motar wani gari ake hawa d'an tafiya Cotonou ba. Gidan Hajiya ya nu fa, Naina na bayan ta, har yanzu kukan akaita Momman ta take, tana ganin Papan nata ta fara mika mishi hannu. "Kazo a d'ai- d'ai,na gama,ga Naina ta ishe mu da kukan Momma.. "Hajiya wallahi ta gudu, kuma naje har tasha ban same ta ba.. "Waye ya gudu? Da sauri ya juya,ganin Abba yasa ya tashi, "Abba Laila ce, Salati Hajiya ta hau, kan Abba yace"a wane dalilin zata gudu? Bana son shirme. "Wallahi Abba da gaske na ke,ba jakar, ba d'an,,dan Allah a bata hakuri,Hajiya zan sauya.. "Da me zaka sauya Faruq? Sai kuma yai shiru, harda hawayen shi. Gaba d'aya suna parlourn sun tasa shi gaba akan sai ya fad'i mai yai wa Lailan? Inna tace "Kai bayani Umaru.. Toh ta ina ma zai fara? Yasan d'uk Inna da Aunty Salma suka ja mishi komai. Da sauri ya dago yana k'allon Abba,"Bayanin mey zan miki? Wallahi Abba da sa hannun Aunty Salma da Inna a batan nan,sun san komai,musamman Aunty Salma. Salati Inna ta fara,Aunty Salma na k'allon shi baki sake,,Inna tace "au,sharri zaka min Umaru? Zaman gidan ku nai bare nasan komai? By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:47 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 62_"Eh man,ya za ai in ba da had'in bakin ki ba ta d'au d'a ta d'au jaka ta fita? "Sannan Abba Aunty Salma kusan kullum sai taje gidan da muke, su shiga d'aki tana kitsa ma Laila ya zata gudu, ai ranar na ji komai. Aunty Salman Abban ya k'alla,"ki min zancen da zan fahimta,ba wai na gane d'aya daga zancen Faruq bane Salma. Faruq d'in ta k'alla, kan ta k'ada kai, "tunda kaso tona asirin ka da k'anka nima k'wa bazan rufa maka ba,, d'uk halin da Lailan take ciki ta sanar wa su Abba,"tai d'uk iya kok'arin taga ta saita shi Abba ya ki, bakin cikin yau daban, na gobe daban, kuma dama auran nan fa ni na shawo kan Laila ta yarda in zaku tuna, da sharad'in in har wa'adinta ya cika bai g'yaru ba dole asa ya sake ta. "Gashi nan, yanzu yai ma kanshi.. "Wani aure ne akai shi akan sharad'i Salma? Wane wa'adi kike magana? Cewar Hajiya,, sai kuma ta hau inda-inda. "Abba Laila basu zo garin nan da sanin aure za'a mata ba fa, sama ta ka ta tsinta a bakin ku,, a lokacin ai d'aki ta nufa ba tare da ta yarda ba,, k'warai ni na tausayawa Laila, don a ido na tai borin rashin mijinta, ganin zata dawo da abin yasa nace ta aminta ko dan biyayya gare ku da d'iyar Naina,sanan tai jahadin saita Faruq kodan yana a matsayin d'an uwanta daga,a lokacin tai mun tuni da alkawarin da ta d'aukarwa Mijinta, d'uk a zato na in anyi auran zata manta komai ta rike auren ko dan Naina da rabon da ta samu. Abba bai san Aunty salma bata girma ba sai yau d'in nan. K'allon mamaki kawai yake mata. "Amma d'ai Salma bansan baki da wayo ba sai y'au. "Ace da ke za ai wannan d'anyen aikin? Aure abin wasa ne Salma da har zaki sa mishi wa'adi? Fada sosai Aunty Salma tasha,d'uk da ita har ga Allah ba ta so hukuncin Lailan ba. Kan Faruq ya dawo, tass ya wanke shi daga ciki har ba'i,ya kuma sanar shi alhakin nemo Laila na wuyan shi. Shi ko kadan fad'an bai wani dame shi ba sama da ina Laila tayi? Zuwa dare Abba ya kira Cotonou, ko chan ta nufa, d'an yasan bata da wajen zuwa sai chan,sai d'ai network ba k'yau, sai aka bari sai gobe a tambaya. Suma a chan Cotonoun shirin zuwa Nigerian suke,basu san Wa'inar da ake toya wa ba sai kuma jiya suka tsinci haihuwar Lailan. Laila bata sha wahala wajen isa gidan momy ba,sama ta ka,ta tsinci sallamar Lailan ita da Zunnu da suka had'u a gate. Da sauri tai wajen momyn tana hawaye,,"Momy,, momyn tace"ikon Allah, Laila da magriban nan ki ke tafe? Kai ta k'ada, ta zaunar ta kusa da ita. "Toh meye na kukan? Jin mutsu-mutsun D'a yasa ta fara leka bayan Lailan, sai ta kunto shi,baki sake momyn take k'allonta. "Haihuwa ki kai Laila? Daga ina kike yanzun? Kawai sai ta fashe mata da kuka,, "Jiya na haihu momy..."Jiya? Kai ta k'ada mata,kan ta share hawayenta, "ni dai Momy kar ki fadawa kowa ina nan, wallahi ko na bar gidan. Da kai tai wa zunnu ya kai kayan d'aki, kan ta karbi Mas'ood,, hannu na baki halamar y'unwa. Ita d'ai Momy sai k'allon mamaki take mata,da tambaya fal bakinta. Sai da ta sa mata ruwan d'umi tai wanka ta bata tea da abinci kan ta zauna tambayar ba'asin daga ina take? "Daga Yola nake Momy,, ba wanda yasan nan na zo, ki rufan asiri,wallahi ban son auren mutumin nan sam Momy,,d'an Allah kar ki fada musu ina nan, duka na tsani yolan ma,bana son ta Allah Momy.. Ganin kukan da take ya sa momyn cewa ba zata fada ba,tai shiru, sai d'ai a ranta tana tunanin mey akai wa Laila haka? Dan ko shekaran jiya sunyi waya,kuma kullum lafiya take cewa suke, sai d'ai kuka da ya zama dole in sunyi waya sai ta mata. By Feenat Ja'afar. [3/27, 2:01 PM] Feenat Ja'afarâí ¼í¿½í ¾í´: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 63_ "Momy sunan shi Mas'ood,tak'waran Mas'ood,, sai kuma ga hawaye, kai momyn ta k'ada,"wa ya sa mishi sunan Laila? Kai ta K'awar,"Faruq ne, sai itama momyn ta k'au da kai tare da goge hawayenta, momyn ta k'allo,"Allah ya sa yai halin mai sunan shi Momy,, kai momyn ta sake k'ada mata tana k'allon yaron,"Amin Laila,,sai d'ai ko ma mey baban yaron ya miki bai kamata ki taho ba,ga d'anyen jego, yanzu baki san a wanne hali yake ciki da sauran y'an uwan ki ba Laila.. Baki ta ta6e,, "nasan zai farin ciki in ya bud'e ido ya ga bana nan Momy,, "Naina kawai nake ji wallahi, amma ni bana ta kowa, d'an aure kam,na gama shi a duniya.. Hararar da Momy ta s'au mata ne yasa tai shiru tana goge k'walla,, "zan so ki ji abinda aka min Mom, wallahi ina da hujjar fad'in hakan.. Kai ta girgiza mata, "Laila ka'r ki fad'an komai,dan kema nasan da lefin ki fa.. Da sauri ta dago tana girgiza kai, ci gaba momyn tai,"kullum fad'a na dake kenan, ki cire Mas'ood a ranki, ki d'auke shi a gaban ki, shine zai sa kiji dad'in zaman auren ki. "wallahi Momy ina k'watantawa.. "Faruq ya wuce inda kike tsammanin shi Momy,"kullum fad'a, hancini,t'sawa, Momy ko kad'an bai bani uziri,,irin halin Faruq ta hau zaiyanewa Momyn, tabbas ta jinjina mata, sai d'ai tai mishi uziri irin na Lailan,tunda d'uk matsalar su d'aya. Har ta k'wanta bacci tana tunanin halin da y'arta take ciki,wato ''Naina''. Su Hajiya ganin bazasu iya da Nainan ba yasa suka bashi abar shi,, a zaune ya ke a parlourn, dak'yar ya samu Nainan tai bacci,shima dan ya lallabata kan yanzu Momman zata dawo. Yau a cikin kunci yake, wanda rabon shi da shiga cikin shi kusan wata tara,, bai san Laila ta kawo mishi farin ciki gidan shi ba sai yau da bata nan.. Bai san Laila duk'anta ce farin cikin shi da Walwalar Naina ba sai yanzu da suka rasa ta. Bai san har wani tsawo ya d'auka ba rabon shi da zaman y'in tunani ba tun bayan auran su da Laila ba sai yau,a yau yana matukar K'ewar mutane biyu, a yau ya gano sune farin cikin shi musamman Laila, wacce da ganinta yake gani kamar Nainan shi ce,gashi yau yayi biyu babu,ba w'an? Ba k'anin. Dagowa yai tare da k'allon Naina,in banda saukar da ajiyar zuciya ba abinda take. Sai ya samu kanshi da kara jin haushin kanshi na raba soyayyar Laila da y'arta Naina. Bai san gobe in ta tashi da wani budiri zata tashi ba? Rokon shi Allah yasa Laila na garin nan,toh a gidan wa? Gashi Babban tashin hankalin shi yadda Abba ya cire hannun shi a batun dawowar Laila ko an ganta,,ya tabbatar mishi da sai yadda Lailan tace,zama dashi? Ko rabuwa? Toh da mey ake so ya ji? Ina ake son ya sa kanshi? Ina zaiga Laila? Shin zata yafe mishi su dawo zaman su? Shin zata yarda da cewar itace Farin cikin gidan shi? Shin zata yarda yayi nadama ya kuma sauya halinshi? Tabbas ya gano ya kamu d son Laila.. Amma ta ya ya zai nuna mata hakan? Shin zata yarda dashi ma kuwa? Bai nufa ba ya ji saukar hawaye. Toh fa,Laila ki agazo ma Faruq. By Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 2:48 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 64_Ranar sai k'wanan parlour sukai,sai d'ai kiran sallah ya tsinkaya cikin baccin shi,a hankali ya k'wantar da Naina kan kujera,ya shiga yai alwala yai masallaci, fatan shi Allah sa kar Naina ta tashi. Bai jima da fita ba ta fara motsi,tashi tai tana k'allon parlourn, sai ta sauka a kan kujerar tai kitchen, a zaton ta Momman na chan,, ganin bata nan yasa tai kofar d'akin su,"Momma".. Kira take tana bugun kofar halamar ta bud'e mata. D'uk a tunanin ta Momman na gidan. A haka ya cimmata tana kiran Lailan,har ta fara kuka jin bata bud'e mata ba. Da sauri ya karasa yana kiranta, sai ta juyo tana k'allon shi,, rikici ta fara mishi,sai kawai ya bud'e ma ta d'akin ta shiga,tunda ta fuskanci Momman bata nan ta hau mishi bori,,lallashin duniya taki shiru. Ya kira layin Lailan har ya gaji a kashe, kawai sai ya bada Cotonou ta nufa. Gidan su Hajiyan yai k'arfe 10,kan ko sun ji Lailan ta isa chan Cotonoun,sai dai da Abba ya kira tambayar Lailan sai abin ya basu mamaki, tambaya suke tun yaushe bata gida? Abba ya sanar shi jiya, mamy ya k'alla, wacce d'uk ta kosa taji mey ke faruwa,"kinji Laila bata Yola,tun jiya sun zata nan ta nufo, ban tunanin yarinyar nan bata hakura ta saduda tai zaman auran ta ba. Tunani Mamy take, sai ta k'allo Abban Lailan, "indai ba nan ta nufa ba Abban Laila toh Kano ta nufa. Kai ya k'ada, sai yanzu ya tuna chan,kan yace"Allah ya k'yauta, kira mana mu tabbatar. Momyn ta kira,lokacin tana shirya Mas'ood ta mishi wanka yai bacci, ganin Mamy yasa tai jim, tabbas tasan Laila zata tambaya, d'akin ta bari ganin Laila na bandaki. Bayan sun gaisa Mamyn tai shiru. Sai momyn tace"Laila koh? Ga ta anan, naso Kira, amma ta sanar ni inna fada zata gudu,toh bansan kuma ina zata nufa ba,sai dai dole dama kusan tana nan ko dan yan Yola. Kai Mamyn ta k'ada,sai tai mata godiya, tare da sanar ta suma suna hanya Washegari ne ranar zuwan su dama Nigeria,jirgi suka biyo, direct gidan su Faruq suka sauka,d'uk suna parlourn, har yayun Faruq d'in, jimami suke har sun gaji da neman Laila, kowa dai Faruq yake bawa Laifi,yayinda shi kuma yai musu shiru, shi ta inda zaiga Laila ya ke, kodan yadda a k'wana biyu har Naina ta fad'a dan kukan neman ta. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 2:48 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 65_Da sallama su Mamyn suka shigo, ganin yadda sukai a parlourn yasa suka tuna ashe basu fada musu anga Lailan ba. Kai Faruq ya saukar, har bai son su had'a ido da iyayen Laila, dan a ganin shi suma shi zasu d'aura wa alhakin batan y'arsu. Bayan an gaisa shima ya gaishe su kai duk'e, duk sai ya basu tausayi,, ganin hakan yasa basuyi wata-wata ba suka sanar su inda Laila take,,basu wani nemi ba'asin tafiyar lailan ba suka tafi masaukin su. Shikam Faruq gida ya nufa,tare da sanar da Dr anga Lailan. Badan yamma tayi ba,da ayau zashi Kano,Naina yake tambaya wacce har ta saduda da neman Momman wai zata momman? Kai ta daga,sai kuma ta hau mishi kuka. Asubanci yai,ko a bacci Naina bata gama watstsa kewa ba ya sauya mata kaya tare da jidar wasu harda nashi, dan kafarshi kafar Laila, ko yai ta zama har randa ta huce ta dawo gare su. Sai kusan La'asar ya isa Kano,sai d'ai shaf ya manta unguwar, da taimakon Dr Auwal yaje unguwar har gidan da tambaya, sai biyar suka iso. Ga Naina na mishi kukan gajiya,in banda youghout ba abinda taci. A parlour suke an ma Mas'ood wankan yamma Momy na mishi gashi,pampers Lailan taje ta masanyo wa momy da karama, momyn bata nufa ba ta tsinkayi muryar Naina na cewa"Momma".. Dagowa tai,a zaton ta ko a TV ne,Nainan ce tsaye tana k'allon ta, tunda Faruq yace Lailan na nan ta gudu ta riga su,sai d'ai ganin ba Momman yasa ta fara 6are baki ta fara kuka. Daga d'aki taji kamar kukan Nainan ta,sai ta rintse ido,a tunanin ta sata da tai a rai ne yasa take jin kamar hakan, sai ta fito parlourn. Sai d'ai mey? Jin Momy na kiran "zo baby, hala batan kai tayi? Da sauri ta k'alli kofar parlourn inda Naina ke kok'arin komawa gun papan ta. Da sauri tace"Naina".. Jin muryar Momman yasa ta juyo da sauri tare da barin kukan. Suna ar'bawa da gudu sukai wajen juna,kam ta rike ta tana sumbatar fuskar Nainan ta ko'ina tana hawaye,baki sake Momy take k'allon su,, Badai Nainan Lailan bace?.. Tsaye yake yana k'allon ikon Allah, ko shi da ya reni Naina bai jin tana sonshi kamar na Momman ta,, ganan Lailan yadda yake agunta,ko y'ar cikinta iyakar son da zata mata kenan ya sani. Cikin shag'wa6a Nainan kema Lailan mitar ta gudu ta barta,, murmushi tai tare da ce mata"sorry baby,sorry". Naina kuka ya kare. Muryar zunnu dake cewa Faruq ya shiga ne yasa ta k'alli kofar, ya zuba musu ido, tana ganin shi ta had'e rai tare da yin gun Momy sa6e da Naina. Parlourn ya karaso shida zunnu, sai momyn ta tashi tare da k'wantar da Mas'ood a net tana mishi sannu da zuwa. Mamakin kamar y'an gidan da Mas'ood yake,musamman Zunnu. Cikin girmamawa ya gaida Momyn,fuska sake itama ta amsa,tana kula da yadda Lailan ta had'e rai tam. Sai ta d'au Pampers ta d'akko Mas'ood ta sa mishi,,ta d'aura shi a showel pink ta nad'e shi ta mikawa Baban shi,,mikewa Lailan tai kamar ta fasa ihu tai d'aki da Naina. "Waya sanar shi toh tana nan? Tasan ba mahalukin da ta fadawa tazo Kano har Maman Nana, wayanta a kashe bare tace an d'au numbern shi,, "su mamy fa? Kai ta k'ada, sai dai su, kenan Momy ta sanar su? Kawai sai ta hau kuka Naina na k'allon ta, a haka Momy ta cimmata. Fad'a ta hau mata,"bazamu shirya dake ba sam Laila,ko bakiga darajar yana mijinki ba ai k'ya ga darajar yana w'anki kuma d'an uwan ki, sam ba so haka ba, sarai kinsan dan ke yazo,amma ba gaisuwa bare k'allon arziki.. Dole momyn tai shiru,dan kuka take kamar ta hadiyi zuciya, fad'i take"shima baiga darajar tana y'ar uwarshi ba ya rufe ido sai ita? Aure ne ta gama shi dashi,toh dan mey zata gaida shi? Baki sake momyn take k'allon ta, bata san Laila nada hawa dokin naki ba sai yau. Duk da tasan tana tausayin ta amma dole ta nuna mata k'inta. D'akin ta bari tana sanar ta taje maza ta gaisa shi in tana son su shirya,, ganin ran momyn ya 6aci yasa ta gaida shi badan taso ba ta dawo d'aki. Fir taki fito wa parlourn, sai Momy kad'ai ke hidima dashi, Naina na makale kamar mai son shiga ciki. Har dare suna d'akin momyn,sai d'ai in Mas'ood yai kuka a kawo shi,da ta bashi abincin shi zasu koma parlour. Da akazo k'wanciya fir Momy tace sai d'ai ta tafi d'akin Mas'ood, dan nan ya musu kadan. "Amma Momy naga nan muke k'wana tare fa? Kai ta K'awar momyn,"eh,amma yau ai mun karu, kinsan gadon nan bazai ishe mu ba ga Naina, kuma nidai ba son kasa nake ba...galala take k'allon momyn,"toh ni zan k'wana a kasan,Ku hau gadon,, da harara tace''wai yaushe kika koyi musu Laila? Hawaye ta fara,dan sarai tasan mey momyn take nufi. "Toh ki bar min d'aki maza,zan k'wana da Nainan. Haka tana ji tana gani tai d'akin Mas'ood, d'uk da a zatan ta Faruq d'in baya gidan. Tura kofar tai,tana karewa d'akin k'allo, a bandaki taji kamar rufe famfo,da mamaki take k'allon shi da ya fito a bandakin, shima haka, dan sam bai kawo ita ba ce da yaji an bud'e kofa. Murmushi ya sakar mata, baki ta ta6e tare da kok'arin juyawa, da sauri ya kira ta. "Dan Allah kan ki tafi ki saurare ni.. Juyo wa tai fuskar nan had'e, kawai sai ya zube mata a kasa g'wiwa biyu,ya wani marai rai ce tare fara bada hakuri. Kai ta k'auda,"Ka d'auka baka ma min laifi ba,balle ka nemi yafiya,, ka d'auka bakai rayuwar aure da ni ba,dan komai ya kare,wallahi... Hannu yai saurin mika mata,halamar karta rantse, sai d'ai tuni ta rantse, sai ya rintse ido,"laifi na bai kai na wannan hukuncin naki ba Laila,, bai kai haka ba,ki duba Allah ki zo mu koma, kodan yaran mu da d'angantakar mu...Bai nufa ba yaji ta sau dariya,wacce a gunta tafi kuka ciwo,, "yanzu ne ka tuna da ak'wai d'angantaka a tsakanin mu? Lalle ya kamata ka farka Faruq.."dan ka ji na rantse bazan koma maka ba,,idan dan yaranka ne zaka iya d'aukar su,ko ka manta ba nawa bane naka ne, zan iya rayuwa ai ko babu su. Juya wa tai ta doko mishi kofar, d'akin momyn ta nufa, sai dai ganin yadda taki k'allon idon ta yasa tai mata shiru, tanaji tana ga ta k'wanta kusa da Naina, kai ta k'ada, tasan Laila ta d'au zafi da yawa... karshe sai d'akin Abban su Mas'ood ta k'wana. By Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 2:57 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 66_Tashi yai,tare da k'ada kai,jakar shi ya ja,sai ya ciro kayan shi ya bud'e sif d'in yana jera wa,ga wasu daga cikin suites d'in Mas'ood a jakar su a rataye,, sai kayan Naina ya ware gefe,k'warai yaso ya kama hotel,amma Momy ta ki,system d'in shi ya jona a chargy, kan ya nemi gefen gado ya zauna,drawern gefen gadon ya ja zai sa wallet d'in shi,,wani diary ne yaja hankalin shi aciki,, kamar kar ya d'auka,dan ya gane na Mas'ood ne, Paging farko ne yaja hankalin shi da kara bud'ewa, "Laila/
Maj'nu'' yaga an rubuta. K'wanciya yai tare da fara k'undarin Diaryn. Farkon haduwar su,firar su,fassarar ta ga Maj'nun,har zuwa fara soyayyar su,,"wato anan aka samu "Laila Maj'nu? a hankali ya dago kamar mai tunani,"interpretè" Kalmar ya furta,kan ya cigaba, na dariya yai, na girgiza kai yayi, na bata rai yayi,, sai d'ai da yazo gun k'wanciyar shi a asibiti har k'walla ya zubar, dan wani waje da yaja hankalin shi da Mas'ood d'in ya rubuta "Da zanyi tsawan rai Laila,da na zan maishe ki k'warai abin k'watance ga sauran mata.."Dama ace zanyi tsawan ran da zanga yaran mu Laila,da sunyi alfari da samu na a matsayin uba Laila.."Da..da..da.. Har zuwa karshen aya. Ya Salam, ashe ba karamin Baiwa Allah ya mishi ba shi? Ashe ana irin soyayyar nan a zahiri ba a film ba? Lalle yau ya kara yadda da Allah bai barin wani da wanin ya ji dad'i ba..da yana bari,da ya bar wa Laila Maj'nun ta.. Ya sani da wuya a samu mai matukar hakuri,kula,taw
akkali,rarrashi,iya So agun Matarshi kamar Maj'nun, ga d'ai laifi tayi,amma shi ke lallashi. K'warai yai jin-jina ga soyayyar Laila da Maj'nun ta.. Ina ma zaya iya fin Mas'ood a wannan fagen..Ina ma Laila zata dawo Lailanta ta da.. Ina ma shima zai samu ko da rabin soyayyar da Maj'nu ya zaiyana Lailan shi na mishi.. Ina ma,ina ma.. Kan ya farga har dare ya ja sosai wajen karanta Diaryn da tunanin duniya.. Yana matukar kishi ya ji Laila na ambartar Maj'nun nan,amma a yau, yana matukar tausayawa yar guntuwar soyayyar nan da aka gina ta tamkar an shekara dubu.. Abu d'aya yasa a ranshi,d'uk randa Laila ta bashi dama shi kuma zai maishe mata g'urbin Mas'ood, zai d'aura daga inda Mas'ood ya tsaya,, zai nuna mata tabbas Faruq ne a duniyar nan ba Mas'ood ba. A haka bacci ya tafi dashi. Washegari da safe sun dawo a masallaci shida zunnu ya shiga d'aki ya k'waso kayan Naina ya bawa Abbakar ya kai ma Laila,wanka yai kan ya samo su zunnu parlour,,yau tsabar shaukin ganin Lailan yake,hakan yasa yana ta k'allon kofar d'akin. Sai d'ai har aka ci abinci ba Laila,sai d'ai Naina da ta fito tasha wankan ta. Momy ta kula dashi, sai da su zunnu suka tashi kan ta k'allo shi,, gaba d'aya ya kasa sakin jiki dasu,d'uk da yadda suke ganin kamar Mas'ood d'in su,barin su zunnu. "Faruq" k'allo Momyn yai kan ya amsa ta da girmamawa,"kai hakuri da abinda Laila tai, k'warai banji dad'i ba, na kuma mata fad'an hakan,sai d'ai ka cigaba da binta a hankali har zuwa ta huce,,ka kara hakuri, inshaAllah komai zai wuce soon.. Kai ya k'ada, sai dai a zaton shi ko momyn bata san komai bane,"InshaAllah mom, amma ki tayani bata hakuri,nasan ni mai laifi ne agunta. Sai momyn ta tausaya mishi,, baki tai ta bashi, sannan tace ya same ta d'aki. A kunya ce yai d'akin momyn,ido momyn ta rufe,jinshi take kamar Mas'ood d'in ta,musamman da ya kirata da"Mom''. Suna kan gado ta d'aura ma Naina Mas'ood a hannu tana mata surutu suna ta dariyar su,halamar ba abinda ya dame su. Sai ya jingina yana k'allon su da murmushi,dama a gidan su suke ace kuma su d'auwama cikin nishad'in, riga da zani ne jikin Lailan tasha d'auri, yakan yi mamakin yaushe ta koyi d'aurin zani dana dank'wali, dan ya santa tun a karamar ta bata iya ba,har auran su bai ma taba ganin ta da zani ba,sai ranar da sukai rikici. Kai ta dago,jin kamshin turaren shi, suna had'a ido ta d'auke nata,karasowa yai tare da zama yana taya su murmushin. Fad'an Momy na safe ne yasa ta gaishe shi, fuskar ta kawai yake k'allo, sai d'ai fir taki bari su had'a ido,kawai sai ya biyewa Naina dake nuna mishi baby. A hankali ya dago ya k'alleta, ta juya d'ayan bangaren ita kad'ai,, hakurin d'ai ya hau bata kamar kullum da sigar lallashi da lumana,, sai d'ai karan nan da yaren su na fillo,,d'uk yasan ba ji take ba amma zuciya takan iya sanyi da rarrashi na kowacce siga. Fitilar gefen gad'on kawai ta sawa ido tana sauraren shi,,har ya kammala. Ba tare da ta k'alleshi ba ta fara bashi amsa,sai d'ai ko sama da kasa zasu had'e bai san mey take cewa ba,ainashi ma shi bai taba jin yaren ba. Ido kawai ya sa mata har ta kammala. Ajiyar zuciya ya sauke, d'an yasan bai isa tambayar fassasra ba. Yana a Kano har Abban su Mas'ood ya dawo, a lokacin saura k'wana biyu suna,shirye-shirye sai d'ai yai da Momy,in dan ita ne bazatai taron suna ba tace, tun safe tana kula da momyn taki zama,ga wani shiri da ake kamar masu tarbar baki,tana kula da su zunnu suna dibar wasu kaya suna y'in boys quarters dashi,ita dai nata ido, dan ba mai kulata yau bare ta ji ba'asi,gani take ma d'uk yanzu a gidan sun zama y'an partin Faruq. Da kamar magariba sukaji hayaniyar jama'a a cikin gidan. Kofar parlourn suka zubawa ido,sai d'ai ganin masu shigo wa da sauri ta mike ta zuba da gudu gunsu. Aunty Salma,Mamy,Matan yayun Faruq biyu,Inna Bilki sai K'anwar mamy, da wata ta rufe fuska da
[12/17/2017, 3:08 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 67_Harara Mamy da Inna da Aunty Salma suka sau mata a tare, saita ja ta tsaya,tuni hawaye ya tarar mata,inna Bilki tace"Y'ar tselar nan,k'auce ki bamu gu mu y'ar Kot'ar nan, wai sai ta sa musu kuka, Aunty Salma ce ta ruko ta,"ke wasa ake miki fa, k'alli nan.. Maman Nana ce ke mata murmushi, da sauri ta karasa ta rukumkume ta cikin murna,da fara'a momyn ta kar6e su. Sai yanzu ta gane abincin t'ar6ar y'an Adamawan ake. D'aki suka kule da Maman Nana, ta d'an hararo ta,"ni ai munyi fad'a Mom Naina, sai ta juya baya,, k'unne Lailan ta kama,halamar tai hakuri. "Ya akai Abban Nana ya barki zuwa har Kano? Murmushi tai kan tace"Da taimakon Abban Naina nazo, kuma muna da y'an uwa sosai a Kano, tare muka zo ai, shi yana chan masaukin shi. Tace"wallahi naji dad'in ganin ki, d'an k'wana biyu nai Missing naku, ta wani marairaice.. Hararar wasa ta sau mata, sai ga nan Momy da Mas'ood yana kuka, K'allon shi Maryam take,kamar an tsaga kara da Naina,, lamarin ita kam sai hamdala wani.. Bata shi tai bayan ya gama sha,, "kai Laila kun iya haihuwa wallahi, ji gashi kamar mace.. Dariya ta hau mata, kai sai abar Maman Nana. Zancen serious ta dawo mata. "Gaskiya kin sha damu Mom Naina,sannan kin sha da Abban Naina bawan Allah,d'uk kika tashi hankalin jama'a barin Abban Naina, haba Laila,ashe d'uk hakurin da nake baki ba k'ya d'auka? Ashe kice har yanzun bamu zama d'aya ba da ke kenan? Ba komai.. Ta girgiza kai. Hannun ta Lailan ta kama ta wani marai rai ce mata. "A gani na Maman Nana ke zaki fara mara min baya kan na bar Faruq,ba kaunata yake ba,ba kuma tausayi na yake ba, d'ukkan abin da zai sa nai zaman hakurin dashi baya a tare dashi,,mud'in ba so nake bak'in cikin shi ya kashe ni ba. "Wallahi nai hakuri iyakar iyawa ta, na san kuma baiyi nadama ba, kawai d'an dai na koma mishi ne kodan rainon y'arshi da bukatar kanshi in yaso mugunta.. "Baza ku gane bane, kawai d'ai daga nesa zai fi mana nida shi.. Kai Maman Nanan ta k'ada, "tabbas baza mu gane ba Laila,dan har yanzun na fahimta kina a dokin nakin ki ne.."kin kasa k'allon zahirin rayuwa sai bad'inin ta Laila, rayuwa cike take da jarabawa da dama, in kinji na wani,wallahi sai kinyi Hamdala a wacce kike ciki.. "Bazai ta6a kasancewa mutum kullum ace yana a farin ciki ba Laila,dole ak'wai bak'in ciki.. "Dole in wani ya sa6a miki wani ya faranta miki, abu d'aya muke kin ganewa Laila a rayuwar mu shi yasa muke ganin ba d'ai-d'ai ba,wato"Yarda da K'ADDARA.. "Ki yarda har cikin zuciyar ki cewa K'ADDARA CE had'in ki da Faruq, d'uk wani abu da ya shigo ciki yana a jarabawar Ku ne Laila,, kiyi kok'arin kiga kin cinye jarabawar nan, ta yuwo kice kila ina bayan Faruq ne,wallahi ba ko d'aya, zance ne na gaskiya da gaskiya nake miki Laila, shine zaman tare,bance kuma kar ki k'arbi y'ancin ki agun Faruq ba,,amma ki karba ta inda baki saba Allah da Manzon sa ba Laila. Har suka k'wanta tana tausar zuciyar ta,wanda daga halama ta tausu, amma ko ita tana son ta d'an gara Abban Naina,ko da k'watank'wacin yadda ya mata, tanan zasu gane ya g'yara hali ko A'a. Sai d'ai har Washegari daga Lailan har Faruq d'in ba wanda a y'an Adamawa yace ci k'anku. D'uk da shi Faruq bai so haka ba, Inna ce ma kad'ai ke d'an mata in tsiyarta ta motsa,wai mijinta ya kusa d'aure ta kan da had'in bak'in ta ta gudu. Suna an taru kamar a garin suke,y'an uwa su Mas'ood d'in sun bala'in musu kara,musamman da sukaji sunan Mas'ood aka maida. Maijego irin albarka kamar ba ita ba,kaya kuwa har baki ta saka tana k'allo da mamaki, ga nan nasu Momy,ga na dangi dana Abban ta ga na Faruq,shikam nashi har dariya ya bata,tamkar lefe ya biya haka ya ka'r kud'i. Abin sai sambarka, Naina ma ta fito kamar ka d'auke ta. Bayan suna da k'wana biyu su Aunty salma sukai shirin tafiya,, sai d'ai da mamakin Faruq ta ji sun ce kafar su kafarta ba. Momy taji dad'in zaman Inna,d'an ita kad'ai ta fuskanta take iya taka burki, ta kuma san mud'in ta zauna wani abun zai g'yaru, hakan yasa tace tai hakuri ta zauna suyi arba'in,ba musu Inna ta zauna. Bayan kowa ya watse su zunnu da Faruq suka dawo ciki, dama ba samun shiga yake ba tun zuwan y'an Adamawan. Har zuwa yanzu ba abinda ya dad'u bayan gaisuwa tsakanin su, haka zaizo ya karaci firar shi kad'ai da Inna bata ko tankawa, sai d'ai ma ta basu gu. Da safe sun dawo a jogging shida su Zunnu ya ji hayaniyar iya da Momy a kitchen da Naina. Sai kawai ya zire d'akin su Lailan, tana kan gado tana shayar da Mas'ood ya shigo, riga da skirt ne na pink da yellown attamfa, ta saki gashin nan yai baya,halamar bata jima da fitowa a wanka ba so take ya bushe, wani irin abu ya ji yana tsirga mishi,babu tantama Kauna ce. Suna had'a ido tai kasa da kai,sam ba taji shigarshi ba. A bak'in gadon ya zauna. Kai duk'e tace "ina k'wana? Shiru ta ji, d'uk kuma sai ta takura,dan bai taba ritsata tana a haka ba, ko kuka Mas'ood yake sai ya fita take shayar shi. Ganin hannun shi kan sumar Mas'ood d'in da sauri ta g'yara rigar ta tare da cire Mas'ood d'in. Da k'allo ya bita, kan ya k'ada kai. "Laila".. Sai kuma yai shiru, na bar aiki mai tarin yawa a kan ku, nai asarar "contract" da dama da aka d'aura ni akai d'uk a dalilin ku.. "Laila ki fad'an cikin ki da abinda ke zuciyar ki game dani, kice kin yafe ko ba dan hali na ba. Zamowa yai kasa,tuni har ta fara hawaye, "gani gaban ki Laila ki min d'ukkan hukunci amma d'ai d'ai laifi na Laila.."ki ce komai,amma banda rabani da k'anki,please.. Baki ta bud'e zatai magana sukaji Inna tace"mey hakan kai kuma? "Sai kace wani yaro? Durkushe gaban mace kana neman kuka? Dan harara ya sakar mata, kila ma Lailan cewa zatai ta yafe ,dan sosai ya kaskantar da kai, amma tazo ta bata komai. Sai d'ai shi mai duk'ar da kaine, dan yasan sarai sai Inna ta hana shi shiga d'akin ma. "No Inna, ki bari kila in na sa mata kuka sai taji dad'in hucewa. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 3:12 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 68_Baki Innan ta ta6e, kan ta shigo da k'wanon abinci a hannunta,"Ku fa kuka jiyo,ka bamu gu zamu karya. Da gunguni ya tashi,kamar kaka haka suka d'au Inna ba Uwa ba,har ya fita tana mita, kan ta dawo kan Lailan. "Ban son kukan ni fa munafurci,,in ba d'ai dan iyayen ku sun hana a tanka muku ba da wallahi tuni ni an shata ta kare a waje na.. Ita d'ai kala ba tace mata ba,har tai ta gama ta dawo kuma lallashi. Washegari ya d'au hanyar Adamawa, dan sosai ana neman shi, sai d'ai kusan kullum sai ya kira wayan Inna yace ta bata,dan in ba ita tace ba bana ta waiwayar kiran shi, shima daga um,sai um-um. Satin shi d'aya da k'wana biyu ya kara dawo wa,sai d'ai har ya tafi ba abinda ya sauya zani. Sai ya zamto wani sati na kara yi ya kara zuwa, a haka har sukai wata da k'wana uku,in ka gansu ita da babyn g'wanin ban sha'awa, kamar ba abinda ke damunta. Sallamar shi ne yasa suka dago k'allon kofar suda su Inna, Momy har ta gaji da tausayin bawan Allahn Faruq, dan Kano da Yola tafiyar ba nan bace, sannan ace kusan d'uk sati kana hanya, kuma tabbas yadda ta kula har yau basu d'ai-d'ai ta ba. Tunda ya dawo ta koma rayuwar d'aki, Washegari Y'an gidan har Inna da Naina aka fita shan iska tun bayan la'asar, dawowar shi kenan ya ji gidan tsit, sai d'ai da halamar motsinta a d'aki. Ruwa ya watsa, sai ya samu kanshi da zuwa yau d'an suyi ta ta kare,d'uk da lalla6a ta yake amma ya fara kaiwa bango, ko wanin ta ya kashe mata yaci ace ta yafe. Sif d'in d'akin ya bud'e, sai ya samu kanshi da ciro kayan Mas'ood, farar suite ne da y'ar ciki ja, kawai sai ya zira su,sai ya ajiye necktie d'in bai d'aura ba,ya d'an bar maballin sama bai sa ba, kanshi ya k'alla a mudubi, kayan sun amshe shi sai kashe real Mas'ood d'in. Sumar shi ya taje, tare da jawo takalmi ja aciki ya zira,kamar dan shi zirif ya shige. D'akin Lailan ya nufa, tana tsugunne shirya Mas'ood, jin bud'e kofa yasa ta dago, ganin shi a kayan yasa ta gama dagowa duka,Ya Salam! Tamkar Mas'ood d'inta yau ya juye mata, murmushi yake tare da karasowa da murnar samun nasara, kai tai kasa ta koma abinda take, sai ya zauna kusa da Mas'ood d'in tare da mika mata pampers d'in da yaga ta ajiye kusan shi, a d'an kai kaice ta k'alleshi da harara kadan kan ta Matsa ta ciro wata pampers d'in. Sai ya k'ada kai,kamar kullum ya fara sanarta sirrin zuciyar shi da yaren fillo,d'uk da yasan tana bukatar fassara, a haka har ta gama shirya Mas'ood,, sai d'ai takan dan jinkirta ta jishi,sai ta cigaba, g'yara wa Mas'ood k'wanciya tayi, kan ta juyo gare shi, hawaye yaga a idon ta, ido kawai ya zuba mata,sai ta dan goge kan ta fara magana cikin sanyin murya,"(you know what?).. K'allon ta kawai yake, sai ta girgiza kai tare murmushi, amsa ta fara bashi da yaren da in d'ai zai mata fulanci zata amsa mishi dashi, bak'inta kawai yake k'allo, yadda yake fidda lafazin cikin nutsuwa, sai d'ai d'uk da baya ji yasan sirrin zuciyar ta take sanar shi, bai katseta ba sai da takai Aya,kan yace ta fassara. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 3:18 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 69_Zama kawai tai tana share hawayen ta, sai ya s'akko tare da tsugunawa ya dafa cinyarta,, "Laila,, hannu ta daga mishi,"nasan da ka tsane ni, baka kaunar ganina a farin ciki, komai a gidan ka da d'ari-d'ari nake yi Ya Faruq,ban san mey na tsare maka ba a rayuwa, tun yarinta dama ba dani ka ke ba nasani,buh na jure, na zauna,amma d'uk ranar da zanyi nishadi a gidan ka sai ka nakushe ta,,why? Hala ni na kashe maka Naina da zaka min irin wannan rikon? D'uk abinda zan maka baka gani, randa na kirkin ya shigo sai d'ai ka fake da cewar da Naina ka ke, ka sani koda da ina tsananin son Mas'ood bai sa kashe kaina ba, amma kullum burin ka na mutu na bishi, saboda ka tsane ni baka muradin ganina, sai yanzu dana baka waje zaka lallabo na koma? Hawayen ne yaki ya tsaya, kai kawai ya duk'ar, sai da yaji tai shiru kan ya dago kai yana k'allonta,, sai ya sa hannu ya taro hawayen. K'awar da kanta tai,"nasan ni mai laifi ne a wajen ki Laila, nasan na sa6a miki ta hanya da dama, nasan ba irin rainon Mas'ood na g'wada miki ba,amma ya kamata ki ban uziri,ki yafe tunda na gane kure na Laila, ki yarda dayawa a bisa gaskiya ta nake miki abu, ba wai dan sanin zai bata miki ba. Hannunta ya kamo duk'a biyun ya matse, sai ya cigaba,"da farko ganin ki nai tunanin Naina tace ta dawo min ko gizo ne, d'uk da nai kok'arin daina yawan tunanin ta,buh zuwanki rayuwata ya dawo min da kewar Naina sosai, sannan ki kanyi wani abu dake shige da nata. "Kawo samun cikin ki Laila, nasan baki san meye musababbin mutuwar Naina ba, nasan da kin sani zaki bani uzirin wasu abubuwan.. "Tunda cikin Naina ya tsufa ta fara wasan nakuda,musamman in ba taso nai mata nisa, abin har ya shige mana jiki,da ta fara Shikenan zan fasa fita. "Ana haka har ranar na gaskiyar yazo,, zan fita naga ta fara yatsina kamar kullum, sai na zata na wasa ne as usual, da hannuna na d'au remote na k'unna TV,ina mata sai na dawo,d'uk da tana kira na,amma sam ban kawo she's serious ba Laila.. D'ukkan abin da ya biyo baya ya bata labari,har zuwa ga rainon ya'rshi zuwa auran su. "Tun daga ranar na tsani inga ana k'allon TV,dan harda ita wajen sanadin rasa Naina, "na tsani nakudar karya Laila, dan har yau ban daina zargin sakacina ne yasa na rasa Naina ba,d'ukkan abin da ya biyo baya nasan kin sani, ki kan k'watanta abinda na tsana ne Laila,shi yasa kike ga nake burkice miki,, amma bacin haka,wallahi ban tsane ki ba sam,, ki yafe ni, kin dawo da farin ciki rayuwa ta da na y'ata, kar ki nakushe shi Laila, nai miki alkawarin zama sassanya a gare ki. Tabbas da halama ta gamsu da zancen shi, sai d'ai abu d'aya da bata yarda ba shine baison ta barshi dan yana mata k'allon Naina. Sai ta k'ada kai, "wannan bai zama hujjar da zai sa kana muzguna min ba sam,, "wannan bazai sa na yarda cewar inna koma maka zaka k'alle ni a matsayin Laila ba Naina ba,, "nasan Naina ce zabin ka, ka fada da bak'in ka cewar kana min k'allon Naina ne, D'uk da baka sona"(buh atleast,keep me alive in ur memory, i wasn't a dream Faruq),Laila ce ni,amma na gane komai in kanayi kana d'aukar kamar a mafarki.."Laila nake,ba Naina ba,,kasa a ranka,Laila ce. Kai ya k'ada, "bazan miki karya ba,a da ina k'allon Naina ne ake Laila,duk da bansan ya fito fili ba har kin gane, amma yanzu na farka, tun ba yau ba,"Laila yanzun kina a d'ukkan jiki na,ki yarda ina sonki,ba Mas'ood bane nima,kisa a ranki zanfi Mas'ood iya rikon ki, zan so ki bilhakk'i, (and,inshaAllah,I will love you till d end of eternity).. Ya sake marai raicewa tare da kara matso yatsunta,"believe me,,Allah Laila,kice kin yarda,pls"interpretèèè" Maimakon amsa kawai sai ta sa mishi kuka,baki sake yake k'allonta, dan bazai iya fassara kukan dad'i take ko A'a ba. Kawai sai ya mike yai d'aki. Bai jima da shiga ba ya ji hayaniyar su Inna. A parlour su Inna suka zube,zunnu ya k'wanatar da Naina da tai bacci, kofar taji an bud'e, sai ta kara goge idon ta, da k'allo momyn ta bita, sai ta zauna kusan ta sannan ta dafa ta. "Laila" bazan gaji da sanar ki hakuri ba,musamman akan D'a namiji,nasan kukan nan na meye, ya fa kamata ki gane,"Faruq bazai taba zama Mas'ood ba,haka Mas'ood bazai zama Faruq ba,ki cire a ranki cewar zaki ta samun farin ciki a zaman aure kamar kullum, kowa da halin shi,kowa da kuma ra'ayin shi, dole sai kin d'aina hango rayuwar ku ke da Mas'ood zaki iya zaman aure, dole ki sani zo mu zauna tamkar zo mu sa6a ne Laila,d'an Adam ajizi ne,ko yat'sun mu ba su zama d'aya ba,rayuwar sangarta Mas'ood ya miki Laila,irin rayuwar da ba k'wa6a acikin ta, ya sangarta ki irin yadda zai wuya ki samu a gidan wasu mazan,ta yuwu kuma ya miki haka ne saboda shi ba mai nisan k'wana bane. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 3:22 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 70_Nasihar da ta mata bata jin ko da rasuwar Mas'ood ta mata. In banda hawaye dake bin fuskarta ba komai. "Ki bawa Faruq dama ta biyu kiga yadda zai kaya, sannan ki sa a ranki zakiyi zaman aure ne na fisabilillahi, kodan yadda kullum yake sintirin zuwa gare ku,ni nasan yana sonki Laila... Da sauri ta dago tana k'allon momyn tana hawaye, kai ta k'ada ma ta"sai kin nutsu zaki gane, "ki cire son ki Laila,kisa son Allah,,ki d'auka rayuwar da kikai ke da Mas'ood ta shafe har abada,ki duba zahirin ki kibar bad'ini Laila, ki kama yaranki ku zauna waje d'aya, ina mai tabbatar miki zaki fi samun k'wanciyar hankali,ki koyawa zuciyar ki son Faruq ki bar Mas'ood, adu'a ita kad'ai zaki mishi ki nunan Lalle kina son Mas'ood Laila. "Kimin alkawarin nan. Kai ta k'ada mata, sai kuma ta hau lallashi. Shikam yana shiga kayan ya cire,ya mayar su inda suke,sai ya hau had'a kayan shi a jaka. Sai dai ya sa wani abu a ranshi kan bazai tilasta ma Laila komawa a gareshi ba. Washegari takwas ya fito,ya gaida su Momy kan yai d'akin su Inna. Suna zaune suna tad'in duniya,kamar wani abu bai damunta, sai yai murmushi, Ashe shi kad'ai yake kid'anshi? Inna ya gaisar,ya sanarta kuma shi zai wuce, yau kam y'an mutuncin na kanta,Allah kiyaye hanya ta mishi harda bashi waje sukai parlour ita da Mas'ood da Nainan. A gefen gadon ya zauna,ta d'an saci k'allon shi kan ta gaishe shi,karan nan ya amsa harda ya suka tashi? Shikam kamar kullum ya ajiye girman kai yana lallashi a gare ta, "Zai wahala na dawo Kano satin nan,cos a dalilin ki kad'ai nasan hanyar kano. Sai kuma yai shiru, "Laila" kai ta dago tana k'allon shi, "nasan har yanzun kina jin haushi na, hakan kila shi ya hanaki yarda da maganganu na,, "ina son ki, sannan nima ki sa a ranki bazan zama Maj'nun ki ba,sai d'ai randa kika yarda da batu na kika dawo aure na toh zan k'watanta iya iyawa ta Laila,, ga nan kayan Naina na karo mata, ni zan wuce. Kai tai kasa dashi, kan ta k'ada mishi, a haka ya fita ba tare da tace kala ba. Inna ce ta shigo d'auke da Mas'ood dake kuka, zama tai bayan ta bata shi, "D'uk da iyayen ku sunce musa ido aga gudun ruwan ku toh ni bazan iya ba, dole yau kam na sanar ki gaskiya, fad'a itama ta hau mata k'an zaman rayuwa dole sai da hakuri,tunda har Faruq zai iya fad'an laifin da ya aikata a gare ta sannan ya nemi ta yafe dole tai hakuri ta koma,kodan yaransu,, "indai har ke d'in mai jin maganar manya ce toh kiji maganar iyayen ki kiyi zaman auren nan, sannan ki sani a satin nan zan wuce Adamawa.. Sai kuma ta hau fad'a da fillonci, kawai sai Lailan ta hau ma ta dariya.. "Au dariya ma na baki? Kai ta girgiza, "yi hakuri innar mu,, baki innan ta ta6e, "ni fa tuni dama na gane borin munafurci kike wa Yayan nan naki, tunda ban kara ji anyi batun saki ba. Dariyar tace ta karu,, "woo kinga na koma ne? Da za'a min gori.. sai k'wa innan ta kule, k'wafa tai,kan tace "maza garin jan aji ki rasa shi gaba d'aya, k'ya huta ai, tunda kina k'allo wannan zuwan dak'yar yasha.. Da sauri ta g'imtse dariyar tana k'allon Innan, "mey ya same shi inna? Da mamaki take k'allonta,"au bai fad'a miki ba? Kai ta girgiza tana k'allonta. Baki innan ta ta6e,"ina zakiji tunda yana zuwa zaki shige d'aka kamar matar kulle, nan mukai ta jaje mu da Momyn taku, kan tayar motar shi ne ta kunce,Allah kad'ai ya auna arziki,, Ya Ilahi! D'uk sai ta rasa abinda ke mata dad'i.. Ya ta iya da abinda ya gagari wuta,, Wai inji kishiyar konanniya. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 3:30 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 71_Ya zatai da abinda yafi k'arfin ta, tabbas bata so komawa ga Faruq ba abadan, sai d'ai karan nan anci k'arfin ta, daga faruq d'in har y'an team nashi. Mas'ood ta k'alla, ana haka sai ga Naina ta shigo kukan Papan ta ya gudu ya barta, tabbas tasan tsakanin D'a da mahaifin shi sai Allah, bazata so tai amfani da damarta wajen wargaza gidan nan ba. Kai ta daga tai d'an guntun murmushi, "Allah,gani gare ka... A gajiye ya dawo ya zu6e a parlour kamar kullum,sam ya d'aina zaman gidan sai bayan magriba yake dawo wa,d'an gizon muryar y'an gidan yake ji da ganin su, yasan sai ya hadawa kanshi tension, shi yasa sai bayan magriba koh isha'i yake dawowa,, in d'ai yana lissafi d'ai-d'ai toh yau ne sukai arba'in, gidan ya k'alla, Ashe da gaske ne gida in ba mace sunan shi "k'ango? Rayuwa yake mai wahala da tafi da, dan in da yana ma kanshi komai,toh zuwan Laila yasa ya 6aci, haka yake jagula komai ya kai cikin shi, dan ko gida yaje Hajiya ce mishi take ba tai dashi ba. Sarai yasan da biyu ake mishi, kai ya k'ada kan ya zaro wayan shi, kamar kullum ya kira Inna,kuma sai ya kashe, wayan Lailan ya kira, Naina na game lokacin, sai ta ba momman,ita kuma sai ta d'auka tare da ce mata "papa ne'' da murnar ta suka fara waya,dawowar su kenan su ma, "ba ma Momman ki, kawai sai ta kara ma Mas'ood tana mishi yace"ello papa,. Murmushi kawai yake, sai da suka gama ya kashe, tunani yake kan har yanzu Laila na kan bakanta, dan sarai ya ji lokacin da ta kira shi. Text ya hau mata. "Rashin daga kira na Laila shike nuna kara nesan ta na..Kowa yanzu ya d'aina yi dani, ko abinci ba mai ban,cos na fahimci fushin ki shine nasu kila... bazan gaji da mika kokan bara na ba gare ku, (I really need you here.. And I love you..) Ajiyar zuciya yai kan ya furta"(I wish you were here with me) sai yai sending, d'uk shi bazai ma ce ga abinda ya rubuta ba. Shidai burin shi ya isa ga Lailan shi ko ma a ya ya ne. Wayan ta k'ar6a lokacin da Naina ke ce mata"Umm.. K'ar6a tai,dan taji shigar text, bud'ewa tai, Sai d'ai da mamakinta taji ta kishingida karatun text d'in, dagowa tai da murmushi a fuskar ta tana k'allon Naina dake ma Mas'ood wasa,, sai ta kara lafewa a pillown tana k'allon su,tunanin bazatar da zatai ma Faruq take, k'allon text d'in ta sake yi, sai ta matsa kusa dasu suka cigaba da wasan su har ita. Inna ce ta shigo,"y'ar nan wai ina zan kai wannan tsaraba da aka jibgo mana haka? "Au, har kin idda shiryan tawa jakar ma? Dagowa tai tare da daga mata kai, "Toh Allah miki albarka da yaran ku,ni ai kin min komai Laila,k'warai in Abban ki ya ji da Mamyn ki zasuyi murna, kai tai kasa dashi tana murmushi, tun jiya take samun albarka gurin Inna Bilki da Momy,,"Amin Inna, ke d'ai Allah kiyaye. Washegari ya shiga busyn wani contract da aka bashi tun safe, a gajiye yake likis,ga yunwa data adda6e shi,malt da madara kawai ya samu yasha tun rana da biscuit, tuki yake yana t'saki, ga magriba ga gajiya, dole kuma tunda ya d'aina cin abinci yanzu ko indomie zai d'aura ko dan Berry. A waje ya bar motar, sai ya k'wank'wasa Baba ya bud'e mishi, fara'ar Baban yau tai yawa,da mamakin shi sai yaga yau bai tayashi ko da da takardun hannunshi ba kamar in yasan iyalin shi na ciki,, wuce wa yai,sai yai wajen Berry, tana k'wance lak'was, tana ganin shi ta fara tsallen murna, shi da yazo bata hakuri ya barta da yunwa sai yaga abinci har ta rage,a zaton shi ko Baba ne ya zuba mata a wanda aka kawo mishi a gida. Parlourn ya nufa,tuni wani kamshi ya bugi hancin shi,kawai sai ya rintse ido tare da jan numfashi ya shak'i kamshin, a hankan ya zaune ya kujera yana d'an jin kacha'u-kacha'u a kusa dashi da wakar Naina, ido ya bud'e ya sauke su kan Nainan da hankalin ta yai kan k'ada ma Mas'ood abin wasa tana mishi wakar"I love you baby" irin wanda Laila ke mata in tana son tai dariya. Tasha gown ja da ratsin fari da stones a jiki,gashin nan yasha g'yara da fararan bands da ribbons, harda siririyar sarka silver da d'ankunne, takalmin ta ja da socks fari. An shimfid'e mata Mas'ood a cikin karamin abin kwanciyar shi pink, shima yasha gayunshi da jar riga da farin Jeans na yara,sai takalmin ja da fari yana ta dan wuts'ul-wuts'ul yana k'allon abin wasan. Kai ya dafe, tare da rintse ido da furta"Allah!Allah" a baiyane,, kad'ai fa ya zare akan kewar iyalinshi,azaton shi "imagining yake, sai dai jin ance ''papa" da sauri ya bud'e idon shi, Naina ke k'allon shi tana dariya, sai kuma wai ta hau k'wala wa Mommanta kira Wai ga nan Papa. Da sauri ya tashi yazo gun nasu dan tabbatar da ba gizo suke mishi ba kamar kullum. Dariya Nainan ta fara, tare da tashi ta ruko hannunshi wai ya zauna,ai shi ina,da dan gudun shi yai d'akin Lailan, komai a g'yare ga nan jakunkunan su da kamshin Lailan, bathroom ya bud'e, bata ciki, da sauri ya fito yai kitchen inda yake jiwo kamshi, chak! Ya tsaya ganinta tsaye a bak'in kitchen da "service spoon" a hannu tana mishi murmushi, sai yanzu ya kula da kan dining da flaks. K'allo ta ya kara yi cikin wani irin farin ciki d'auke da murmushin murna,ya ma kasa karasawa bare yai magana, bakin nan ne d'ai kamar gonar auduga. Sanye take cikin Orange da blue d'in Swiss, ta kashe d'aurin nan an sau gashi baya, sai ta kama karshen ta sa ribbons,, tasha fashion masu k'yau na d'ankunne da sarka da bangles masu k'yau, in ka ganta, lalle zaka san ta dawo a'inashin Lailan ta g'wanar ado da K'walliya,ga wata y'ar kiba datai dan ma tana shan ruwan d'umin Inna,karshe ta kure sun kure mishi k'yawu yau,wanda bak'in nan a sake gun k'allon sh musamman Lailan da murmushin. Hannu tasa tana tushe bak'inta jin dariya nason tana son ku6uce mata ganin a yadda taso haka abin ya kasance. By Feenat Ja'afar. ®NWA.
[12/17/2017, 3:36 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 72_"Laila..hara
ra ta d'an mishi tare da kawar da kai ta nuno shi da serves spoon d'in,kan tace"ta tafi koyar Sallama. Murmushi yai,kan ya sosa keya,"sorry,kawai sai ya karasa ya ruko hannunta, d'uk ya wani susuce mata,Lallen yake k'allo yana k'allon fuskarta da murmushi, kawai sai dariyar ta subuce mata,sai Naina ma ta hau taya ta, bai wata-wata ba ya ruk'unk'umota shima yana darawa,, sai kuma ta dawo kuka, da sauri ya dago tare da k'allon fuskar tata, "Oh Allah! Marairaice fuska yai tare da fad'in"Laila(I said I am sorry, But if you could forgive me this time, I promise you this will never,ever happen again.) Hawayen yake goge mata da hannun shi,sai ya cigaba, dan a ganin shi ko har yanzun bata yafe ba. "Laila Dagowa tai tana k'allon shi,ido cikin ido suke k'allon juna,cikin hankali ya cigaba da tona mata sirrin zuciyar shi. "( I know it may be difficult to believe right now, but I really do love you Laila.) Ban san da haka ba sai da naga ina gaf da rasa ki.. Sai kuma ya hau tsuma zuciyar ta cikin harshen Larabci,chan ya koma fillanci, ido kawai ta sa mishi tana k'allon yadda yake fidda lafuzzan daga bak'inshi, dad'i ke ratsata ta ko'ina, shaf sun ma manta da yaran.. "Yanzun kin yarda ina za masifar son ki Laila? Da yaren nasu ya fad'a, sai kuma ya tuno bata ji, da sauri yace"sorry,, Murmushi tai kan ta kara lafewa jikin shi,, da mamakin shi ya ji ta fara bashi amsa itama cikin fillancin.. Da mamaki ya dago ta, sai kuma kunya ta kamata,,ido d'aya ya kan'ne, "so,dama kina ji kenan? Kai ta langwa6e gefe ta marairaice fuska,"yare na fa,koh ka manta? Murmushi yai tare da kada kai, sai ya lakuce mata hanci. "Allah yasa ban taba fad'in wata maganar ba.. Murmushi tai, tare da k'allon Naina wacce ta saki baki da ido da hanci tana k'allon su, da halama tana mamakin abin,da sauri zata ja baya ya kara ruko hannun ta, Naina ta nuna mishi da ido, sai ya mak'e kafada, "batta ta gani,kila ta gane itama difference. "Ya akai kuka taho? Kai ta k'ada,"it's a long story, yanzu muje ka shirya,en nasan kana jin yunwa, after dinner,zakaji kom. Fir yake cikata,sai Mas'ood ta d'akko da Naina suka bisu d'akin, ji yake kamar in ya matsa zasu gudu ne,, kiran sallah akai na isha'i, wai suyi tare a gidan,dak'yar ta lalla6a shi ya tafi masallaci ita kuma ta kintsa mishi komai suka fito. Sallamar shi da Abba taji,lokacin tana goye da Naina, kai jama'a, wai bacci zatai a dole, ai dole ma Naina nan ta tafi gidan Hajiya Hutu,dan gani yake yadda take ji da ita ko kanta batai wa haka. Kunto ta tai da dabara, dan ta fara bacci, sai ta ajiye ta kan kujera, ta ware d'aurin dank'walinta zuwa kafada tana ma Abban sannu da zuwa, murmushi Abban yai, yana "Laila rigima.. Kasa tai da kai tana d'an dariya, sai Faruq d'in ya tashi ya d'akko mishi Mas'ood, adu'a ya mishi,kan ya rike shi tsam suna gaisawa, yau ne zuwan Abban su Faruq d'in gidan na farko tun auran shi da Lailan. "Sosai nai farin cikin jin kun dawo a gun Inna Bilki,, hakan yasa nace ba sai an k'wana ba zan zo gare ku. Duk sunyi kasa da kai suna sauraran shi. "Da farko d'ai munce a barku karan nan kuyi son ranku nida Abban ku na Cotonou, dan ni a gani na hakan shi zai fi muku, dan kun san d'ai-d'ai, sai d'ai jin irin abubuwan da kai Faruq ka tona yasa nai alkawarin d'uk ranar da Allah yasa kuka dawo zaman ku zan sanar ku wani abu. "D'uk wani bawa da ku ke ganin shi shimfide a doron kasa baya rasa kalubalai na rayuwa,, ban so naja zancen ba, Allah ya jikan ita Naina da Mas'ood d'in, Baki suka had'a wajen cewa "Amin".. Ya cigaba, "tun rasuwar Naina na zuba ido nake ganin iya gudun ruwan ka kai Faruq, yadda fir ka ki amsar K'ADDARAR da ta saukar maka ta rashin Naina da kai, mun d'au lokaci wajen ganin borin ka,kamin na tsinci labarin itama Lailan. "Rasa abin so yana da matukar ciwo, anji kunyi rashi babba a rayuwa,wanda har kuka butulce wa Allah wajen kin yarda da cewar K'ADDARA CE. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 3:48 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 73_Kai suka dago,ita kam Laila harda hawayen ta,, kai shima ya daga musu,, "K'warai kunyi butulci,dan baku dauki hakuri da d'angana kamar yadda ma'iki (SAW) yace ba yayin da ka rasa wani naka, kai hakuri,sai Allah ya baka lada mai tarin yawa ya kuma musanya maka da mafi alkairin abinda ka rasa,,shi yasa Allah ya bar ku kuyi son naku,kunga kun fad'i a jarabawar farko. Na biyu,Allah yai had'in auran ku,a d'ukkan yadda kai Faruq d'in ka fad'a, da yadda ita Lailan ta tsara da Salma sam babu wani ladabi da kuka bawa aure, aure ya wuce wasa balle har ya zama k'aiyadadde a gare ku, rayuwar auran da kukai dak'yar ne in kun samu lada hamsin aciki. Da sauri suka kara dagowa. Sai yai murmushi, "ni fa nai hadin auran nan, ince kai ko d'aurin auran kin zuwa kai, akazo zama shima babu niya, kai a dole wai ka gama aure sai a Aljanna koh?,ita kuma wai da alkawarin matacce a kanta,saboda haka bazata ci amana ba,koh ba haka akai ba? Salma ta fad'an komai.. Sosai yai musu nasiha, kan suyi zama na amana, sannan ko ba wannan suna d'aukar duk wata K'ADDARAR da ta sakko musu wala khairan? Ko Sharran. "WAMAN K'ADDARALAHU HA'KKA KADARIHI. "Ni zan wuce,Allah ya albarkaci rayuwar ku, Faruq ne kawai ya amsa,dan ita kam taji wa'azin,har ba tasan kukan ta ya tsananta ba, har bak'in parlour ta rako shi tana mishi godiya da ya gaida Hajiya. A kasan carpet ta zauna tana k'allon yaran da suke bacci, lalle ne a baya sunyi kuskure da har suka manta K'ADDARAR su, Allah kam ya fisu son Mas'ood da Laila, amma babban abinda suka manta shine yarda da cewa K'ADDARA CE a cikin K'ADDARAR rayuwar su,Allah ya nufa bada Mas'ood zatai rayuwa, haka shima bada Naina zai karasa rayuwar shi ba. Hawaye ta goge,tana mai kara istigfari a ranta. Tsaye yake yana k'allonta hannu a hard'e, lalle yaso yai fachali da musayar da Allah ya mishi, yai imani yanzu Allah kad'ai yasan karatun Kurma,,inshaAllah wannan karan zai kokarin yaga sunci jarabawar nan a karo na biyu. Karasa wa yai shima ya rankafo a kansu, a hankali ta dago tana k'allon shi, sam Faruq baida aibu,sam bata nufa yana da irin wannan saukin kan ba, in za'a bi ta k'yau, toh dole ya dara Mas'ood, yana kok'arin ibada,har yakan k'wank'wasa mata kofa,yana sauke d'ukkan wani hakkinta akan shi,tunda bai rageta da komai ba. Hawayen ya goge mata yana girgiza mata kai,"nasihar Abba ta shige ni Laila,kuma nai matukar da nasani wanda a yanzu kam it's too late, sai dai Allah ya yafe mana, mu d'auka kawai munyi rashin manyan masoya agare mu,muyi zama na fahimta da son juna,kinji Laila? Kanta ta d'aura a gefen kafadar shi tare da daga kai. Agun cin abinci ta zuba mishi yana ci tana k'allon shi da murmushi, hakan yasa yaci ba kad'an ba. Irin k'allon shi gare ta yasa ta fara kunyar shi,d'aki ta nufa tai wanka tare da sanya sauk'ak'un kayan bacci,ta tufke kanta da kitso d'aya, zani ta d'auro ta fito parlourn. Da k'allo ya bita cikin wani yanayi,sai ta K'awar da kai gefe tana murmushi, kai ya k'ada mata shima yana murmushin. Mas'ood ya d'auka sukai d'aki yana kafadarshi, sai ta k'ada kai, wato dole ta bishi d'akin shi. Sai itama ta d'au Nainan ta a kafada,ta koma ta d'akko mata rigar baccin ta. D'ukawa tai a hankali tana sauya ma Nainan kaya, sai yai tsaye yana k'allonsu shima yana sauya nashi, in sun had'a ido sai d'ai su sakar ma juna murmushi, wanda nata kam ita na kunyar shi ne. Sarai yasan ta gama amma ta hau g'yara mata gashi, sai yai murmushi ya tako kusa da Nainan ya k'wanto yana leken fuskata,,'' yau kuma kunya ce ta motsa ta y'an fillon hala? Daga d'uken tai murmushi, bata nufa ba taji ya ruko hannunta d'uk biyu ya zago da ita ta d'ayan gefen,a hankali ta k'wanta tana d'an sunne kai da murmushi,, hannu d'aya ya kai fuskarshi yana k'allo,"kina son Naina da yawa,kila shi yasa har yanzu ni banni gu ba? Kai ta k'ada,sai shima ya k'ada nashi, a hankali tai rub da ciki tana k'allon hannunshi dake a nata. "Kaunata da Naina daga Allah ne nasan, tun farkon ganinta a wani super market, ina son yara,amma ganin Naina a wannan ranar naji kaunar har cikin raina,tamkar nasan jini nace,d'uk da nai mamakin yadda nima ta zuban ido tana k'allo na, sai d'ai time d'in kana sanya kaya a boot, sannan ko da tana nuna maka ni banga ka dago ba,so ban gane ka ba. Sake haduwa na da ita a gidan Hajiya yasa na gano ashe ma tawa ce, dan abuna yai Naina babba shi yai Laila. "Hope ka tuno ranar? K'allonta kawai yake da mamaki,sosai ya tuno lokacin,"sosai, a time d'in nan kawo komai ba,d'an Naina ko wacce mace Momma ce a gunta,ashe ita Momman gaske take nufi. "Ban so dawo gare ka ba tabbas,amma ganin yadda k'anin ba zata yasa tun a zuwan ka Kano na biyu na yanke shawarar hakura na koma gidan ka ko dan Naina. Sai d'ai nai kok'arin naga shin da gaske kayi nadama? K'warai nai mamakin s'aukin k'anka a gare ni,d'uk da haka ban nuna maka na s'akko ba,kullum ka kanyi magana da wai yaren da a ganin ka bana ji, "Naina ina sonki,Naina ki yafen,Naina ka za,Naina ka za,ki yarda bazan kuma ba.. Sai ta sa dariya "Hhhh, sosai fa nake dariya in ka fita, sai kawai nima na zabi nace na yafe ta yaren da baka ji, sai d'ai matuka na firgita jin na kusa rasa masoyi a karo na biyu, jin wai tayar ka ya fita, tun daga ranar na hau shirin dawo wa gare ka,cos nasan na samu masoyi a k'aro na biyu a rayuwata,nasan kuma ko na dawo bazaka so maimaita baya ba I know, sai d'ai ban san yaushe ka fara sona ba. K'allonta yake ba ko kiftawa,hannunta ya rintse kan a hankali ya tashi itama ya tashe ta. A gaban mirror ya tsayar ta,ita d'ai nata ido,jaka yaje ya zuge, sai ga nan ribbon nata data taba barin shi tun a zamanin rikicin su, gashin ta ya ware yana k'allonta ta mudubin, sai ya d'aura mata ribbon d'in tare da k'wanto wa a kafadarta yana murmushi. Ta mudubin ya k'alleta, "kin tuna ranar chan da kika manta shi nan? Murmushi tai kan ta sad'da kai tana k'ada mishi halamun ta tuna, dan bata manta ba datazo g'yaran gado tana ta neman shi bata ganshi ba,dan shi ne babba sosai a ribbons nata wada take jin dad'in tufke kai dashi. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 3:54 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 74_Juyo da ita yayi suna fuskantar juna, "toh tun a wannan ranar na saddak'ar da (I am in love with you).. "Sai d'ai ina gudun raini ne,wanda a yanzu na gane babu wannan a zaman mu. K'ugunta ya riko,tare da jan numfashi, "(So know,tell me,do u love me?) Kai ta sinne a kafadar shi,sai yai murmushi,"kenan yanzu anayi dani? Kara shige mishi tai tana dan dariya kad'an. Hoto taga ya d'akko yana k'allo yana murmushi, "Ak'wai wata rana da da ita kad'ai nake hasko La'ila,ranar nayi dariya kamar ba gobe a d'aki ni kad'ai. Hoton ya juyo mata dashi yana murmushi, kafawa hoton ido tai kan ta k'alleshi, kai mutumin nan ak'wai ajiya, hoton ta k'ar6a, ita kanta batasan lokacin da dariya ta su6uce mata ba,ta tuna ranar, time d'in sunzo sallah 9ja sallah, zani a hannu dank'walin yayi gefe, k'allon Naina take dake ko'k'arin g'yara mata d'ankwalin tana murmushi, kai yarinta dad'i. Fuskar Nainan ta shafa tana neman kuka, da sauri ya katse ta,"yanzu gaki wai kin iya d'aura zani harda d'aurin dank'wali, murmushi tai tana share hawayen dake neman zubo wa. Sai ya kar6i hoton ya ajiye yana k'allonta. "Adu'a za muna musu ba kuka ba, kai ta daga, "amma fa ka iya ajiya, dan dama ni banni dashi, yanayin yadda suka gudanar da yarintar su take tuna mishi ita da Naina tana murmushi, shikam ido kawai ya zuba mata. Bata aune ba taji yai sama da ita. K'warai yau kam ya bambance mata tsakanin t'saki da t'sakuwa, yau ya fito mata a ainashin Faruq d'inshi, tabbas ta gane kowa da inda ta sashi a babin rayuwarta yanzun,a daren ne ta kara yadda da hasashen Faruq a kanta, tasha kirari dan tamkar maroki ya koma a gabanta,d'uk da itama tayi iya yinta ganin ta fidda kanta dan ya gane ba shi kad'ai ke kid'anshin ba. Fir Washegari ya ki fita ko nan da kofa tun masallacin asuba, kowa ya gansu zai gane suna a cikin farin ciki. Maman Nana ce tai sallama a bak'in kofar parlourn, daga chan d'aki ta amsa tana ko'k'arin fitowa, sai d'ai har ta fito bata ga ta shigo ba, sai tai bak'in kofar, harara ta sakar mata,"au anan kika tsaya? Itama hakan ta mata,"ni na isa shiga gidan amare ba notice, kai ta d'ungure mata, kan ta amshi Nana "kai munyi k'ewar ki Nana,,Maman Nana tace"Oh,wannan matar? Tun jiya da Abban Naina yace wa Baban Nana a sanar ni nake Allah-Allah na shigo,sai d'ai naga umm.. Umm, abin ba'a cewa komai,munafuk kawai,, dariya Lailan ta sa mata,kan tace,"fad'i kar ta ka'r ki mata,, ke fa kika koyan ko kin manta? Hannu ta daga,"wacce ni kaza,wai inji giwa,ai yanzu kinfi k'arfin Maryam,dalibar ki zan dawo,tsaf kin kama wuyan bawan Allah kin rike,ko kofa ya ki ya leka,dariya kawai take bata ma ita. Sosai taji dad'in komawar ta ga Abban Naina,sai ta kara da nasiha kamar kullum, kan ta kara hakuri, gashi yanzu sai labari, tsaraba ta k'waso mata harda su sassaken baure, baki ta rike tana k'allon ta. "Oh ni mairamu, yaushe kika dawo nan,gulma kiri-kiri, dariya tasa,"dan Allah ki barni haka,kar cikina ya kull'e.. "Naga d'uk rainon ki ne,ban son gulma nima. "Toh ina yaran? Tai murmushi,"yanzu suka fita da Dr,da Omar abokinshi har Mas'ood,amma nasan suna hanya,dan Mas'ood acici ne. Nan suka lalace,sai da ya dawo ya same su, sosai yake son K'awancen su da Maman Nana,dan yasan ta taimaka k'warai wajen d'ai d'aitar su. Tabbas zaman lafiya wai yafi zama sarki, hankali k'wance suke bi da juna cikin so da aminci, had'e da girmamawa, d'ai-d'ai da Naina sai da tasan iyayenta sun d'inke kam. Faruq ya dawo mata sabo fil, k'ulle ma babu,yanzu d'uk ranar weekend a gida suke wuni cikin y'an uwa. Ana haka ta bashi shawarar yi ma Baba mai gadi wani d'akin, kenan ya zama biyu,wai ya dawo da iyalin shi kusa. Sosai ya ji dad'in shawarar, cikin wani satin kuwa aka tada aiki. A abinda baifi wata biyu ba suka taro. "Mr Brown" suke k'allo suna nishadi suda yaran su har aka gama,wata hudu kenan da zaman lafiyar su,,maganar makarantar Naina take mishi,kan taci shiga aji,kai ya k'ada mata, "surutun Naina har tsoro yake ban fa,ga Mas'ood shima tun kan yaje ko'ina ya iya son magana, da sannu zasu koyama sauran yara na masu zuwa.. A zabure ta mike had'i da zama da kama k'ugu,"hee Mr,Point of correction,"yaran mu zakace, sai ta hau mishi bori,"kullum akan yaran nan baka ko min kara, dariya Naina ta fara musu, Shima sai ya hau mata,cottion ta d'akko na kujerar ta fara dan dukanshi dashi,sai Naina ma ta d'akko suna mishi taron dangi yana cewa ya tuba, shikam Mas'ood sai dariyar yake k'yalk'yalawa, gani yake kamar wasa suke mishi. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 3:57 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 75_Allura take ma Mas'ood yana k'allonta,kuka ya fara tun k'arfin shi,yau an binciki file, rarrashi take kan ta zauna tana bashi abincin shi,dak'yar ya k'ar6a tana dan hura mishi wajen,shi kuma Faruq na jijjiga shi, har yai bacci, k'allonta yake, wanda tasan tabbas da magana a bak'inshi, sai ta k'wantar da Mas'ood d'in kusa da Naina wace ta dawo a makaranta tana baccin gajiya,, ta juyo kanshi, "ya akai Abban Naina, da magana a bak'in nan. Kai ya k'ada,"sosai kuwa, ya batun aikin ki ne? Naga ba k'ya yi, murmushi tai,kan ta ruko hannunshi tana du6en idonshi,, "ina son zama kusan ku da d'ukkan kulawata ne Ruhh,dz y,buh yana raina,, kai ya k'ada mata,tare da d'aura shima d'ayan hannun akan nata. "No kar kiyi haka,ina son ganin mace na aikin lafiya,musamman ma Nurse,sosai kuna taimaka wa, kar ki damu zan nema miki transfer, ko ta hanyar su Abba ki dawo nan, ganan Inna sai ta dawo d'akin su Naina,ga kuma Iya ta Baba mai gadi,ni kam kinsan yanzu ba mai zama bane,amma soon zan dawo nan duka da aiki,zaki koma aikin ki,in da hali ma sai ki kara karatu. K'allonshi kawai take, har ga Allah bata zata zai ma barta aiki ba,a yadda ta ga yana mai kulafucin su. Ba'a d'au lokaci ba aka dawo da ita kuwa. Inna ya dawo da ita gidan gaba d'aya. Tsaye suke gaban madubi ita da Naina, shiri take yau zata fara fita aiki, yayin da Nainan ta d'au eye pencil zata fara k'yalin nata tsaye a kan gado tana k'allon kanta a mirrion, juyo wa Lailan tai tare da rike k'ugu ta k'anne ido d'aya tare da k'ar6ar pencil d'in tana nuno ta dashi, "I said no make-up" am I clear? Kai ta jijjiga tana ka'rkata shi gefe, "sorry".. Ajiye wa tai,tana kara g'yara mata g'yaran gashin, ta zauna itama ta zaunar ta,socks d'inta take sa mata ita kuma tana g'yara ma Momman nata ribbon, rigar sanyi ta sa mata mai hula, kan itama ta d'aura pink akan uniform d'inta fari, ta d'aura d'ank'wali tasa hijab,,kawai sai Nainan ta hau mata dariyar keta,wai momma da uniform. A gado ta d'aura ta tana mata chakukkuli suna dariya ya shigo, kai ya girgiza, Naina da Mommanta sai Allah.. Tashi sukai tana k'allon shi tare da g'yara kayanta.. Yace"Wow,,kaga Chief Nurse a baki naki daban,kinyi k'yau a uniform, koh Naina? Kai ta daga tana dariya tace"(She looks Mamalicious) dariya suka sa mata Lailan na d'an hararar ta. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 4:01 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 76_D'akin Inna sukai,suna zaune ita da Iya,"Inna zamu fita,a sa min albarka, sai ta mata g'walo. Innan tace"Ahab,ba dan hali ba ai,, Iya tace"amma kayan sun amshe ki sosai,murmushi tai tace ta gode," in Mas'ood ya tashi ga kunun shi na bari a feeder wani a flaks, yana jiran mu kar muyi latti. "Toh Allah d'ai ya tsare mana ku,sai kun dawo. Suna tafe a mota har makarantar su Naina, yau ganin Momman da kuka aka rabu, har suka k'ule yana kula sa yadda take bin y'artata da ido, kai ya k'ada, Laila ak'wai kula,kowa tana kok'arin faranta mishi,karma d'ai Naina, yadda yake murmushi yasa ta k'allo shi,,shafa haba yake yana mata wani irin k'allo, sai ta k'autar da kai tana murmushi. Sanarta yake yau fa kud'inta zai shigo,dazu Abban Mas'ood yake mishi waya, k'allon shi take da halamar tambaya, sai ya ganar ta kan wai kud'in gadon Mas'ood ne da Abba yake ta ajiyar nata sai ta farfad'o, jim tai tana k'allon titi. "Ya akai ne My? Murmushi ta k'ak'alo tare da dan lafe wa a kafadar shi,sai kuma ta tuno a titi suke, dariya ya fara mata. "Nasan ai kin iya mota,right? Ido ta waro mishi,"rufan asiri,ja d'ai muje, stirin ya d'an daka yana mata dariya. "Nima bana baki mota ta ki dagargaza min ba kamar ta Abba.. Da sauri ta k'alleshi, "a ina ka sani? Ido ya k'anne mata,kan yace"Sirri ne. Har ya ajiye ta tana daga mishi hannu har ya kule,numfashi ta sauke, lokacin da take tafiya tana tariyo rayuwar su,kai ta k'ada, lalle ta yarda da had'in ta da Mas'ood da Faruq "K'ADDARA CE" ta Allah, K'ADDARAR ma k'wa ta Alkairi. Godiya ga Allah(S.WT.) da yasa na kawo karshen littafin nan na K'ADDARA CE.. Ina rokon Allah yasa mu kasance masu k'ar6ar K'ADDARAR MU da hannu bibbiyu,Allahu kasa mu tsallake d'ukkan Jarabawar da zaka mana. Sosai na gode ga dumbun masoya littafin nan,,kamar yadda ku ka soshi Allah yasa ya fadakar daku haka. K'yauta ce gare ku masoyana, kamar yadda kuke kauna ta nima haka,I really appreciate your encouragement... I so much Love Da d'ukkan k'warin g'wiwar ku nazo wannan gabar,And I appreciate it! Musamman. Feenat Ja'afar Novel's . Sad'aukar wa gare ki My little sis Maimuna(Muklisa). Ina rokon Allah da ya haskaka Mak'wancin ki, yasa kina a jerin Y'an Matan Aljana. Taku a Kullum.. Nafisa Bashir Tanko. (Feenat Ja'afar),take muku fatan alkairi,tare da fatan Allah ya hadamu a sabon littafin ta,wato... "JUYA"...InshaAllah. Love you all
Like · 5 · Reply · Edit · 31 March 2016