Chapter 1

1.9K 72 6
                                    


Tsaye take tana kallon mutume daya zo wuce wa a mota yai mata wanka da ruwan saman da ya taru a kasa wajan , duk jikin ta ya jike had da takardun dake hannun ta, Amma shi be ma zan da ita ba ma almajiran dake wajan a zaune yake raba ma sadaka.
Lallai ma ba zai ban hakuri ba ma, ta kawa tayi a hakali ta tsaya a gefan sa ta kalli mutane biyun dake bayan sa da suke kika masa yan dari da yake rabawa sadaka san nan ta jeya tana kallan sa ta bude baki zatayi magana kenan ya miko mata darin daya ke rabawa kudin ta kalla ta kalle shi,

Ni ba shiya kawo ni nan ba ta fada😡

Sai a sanna ya daga yana kallon ta tin daga saman ta zowa kasa shi be ma san wake wajan ba, ajike take sharkaf Maya kawo ki yace da ita yaci gaba da abinda yakeyi
na jinki.

Ji yanda kuka jika min jiki da ruwa da kuka zo wuce wa ko daba aka ya ma haka ai kwa kalle ta ku bata hakuri ban lantana mutan, magana take kama zatayi kuka😢.Amma kuka wats..........

Hannu ya daga mata a laman ta dakata sanna ya jeya ya kalli wanda yake miko ma sa kudin, shi sai yanza ya tina da sun watsa ma wani abu ruwa, almajiran da suka taso ne suka mantan dashi, karban bandir din ya darin dake hannun sa yayi, ya jiyo ya mika mata gashi kiyi wanka ki wanke kayan ki.

Baka ban hakuri ba san nan kana ban abinda ba shi na zo nema ba, kuna ganin talaka ba abinda yake ne ma sai kudi ku walakan ta mutun dan kun ga Allah ya baku muma ai ba hana mu yayi ba haka yake son ganin mu amma sai kuk.........

Abinda ta ji ya doki gefan fiskan ta ne yasa tayin shire hannu ta kai ta rike abin da ke kumatun ta zare na shi hannun yayi ya bar abun,
Kudin dake hannu sa taji a kumatun ta rike kudin tayi tana kallo,kan ta gada tayi magana harya shige mota sun tafi Kasa motsi tayi

Daya daga cikin almajiran taji tana ce tama hakuri zaki yi keda kakar ki tayan ka saka, dani yayi ma haka yana mika min zan karba na tafi abina ai wannan ne hakurin
Amma kin tsaya sai zuba kikayi.

Tsohon dake kusa da ita yake bata hakuri
Sai hakuri yaran masu kudin nan sai a hankali basu da tarbiya gani suke suna dashi za su iya taka kowa kiyi hakuri ki tafi gida kan wani ruwan ya sako. Ita dai shiru kayi tana jin su kuwa da abin da yaka cewa
****

Habib Hasan Majeed yana shiga mota kira ya shiga wayan shi dubawa yayi mama ya gani
Hello mama

Na'am habib ina kaje ne kasan su Omar sun sauka na zan sun kusa shigowa gida

Eh na sani yanzu mukayi waya dashi nima gani nan naji more and more ne yanzu zan dawo

Ok kar ka dade

Toh mama yace

Yana gama wayan motan su na shiga more and more fito wa yayi ya shiga da dan sauri ya duba abinda yake nama ya biya ya fito
Bude motan da zaiyi yaji an watsa masa ruwa tin daga fuskas sa har kafan sa ya jike
Kanya daya yaga waye yaji an jefa masa abu a gefan fuska kai hannu yayi ya rike wajan san nan ya daga

Kayi wanka ka wanke kayan ka tana kai wa nan ta zare hannun ta, tafiya tayi tana murmushi😊

Binta yayi da kallo hari ta hau adaidaita, share fuskan shi yayi da gaske ne ko mafarki yanke, sajen shi ya kuma shafawa ruwa yaji harda kasa kasa, wayan dake hannun sa yayi jifa da ita yana huci ya shiga mota. sule direban sa ne yaji ya dau ko wayan suka shiga motan shi da sani yaran daya ke mishi aikin gida ne kasa magana su kayi, sule ne yayi dan karfin hali yace sorr..........
Hanuya daga masa, san nan ya masa nuni da su tafi.
Yama rasa mai zai yi tunani yake har suka zo gida. Fitowa yayi bangaran sa ya shi ya sake kayan sa san nan yayi wajan taro da akeyi a cikin gidan su.

KhadijaWhere stories live. Discover now