"Daukan mataki na daga cikin abubuwa mafi wuya da mutum zai aiwatar, musamman idan zabi ne tsakanin inda mutum ya kamata ya kasance da kuma inda mutum yakeso ya kasance" Eshat
6:00 am,12th February, 2020. Abuja International Airport.
Airport ya cika makil da jamaa musamman fararen fata masu komawa 'kasarsu saboda cutar Covid-19 data 'bullo daga China. Cikin darurukan jamaan dake shiga da fita dole kwarjininsa ya sanya ka kara masa kallo na biyu. Yanayin takunsa cikin natsuwa da 'kasaita, Matashi mai kimanin shekaru talatin da biyu, sanye cikin Maroonblazer da bakin T-shirt ta ciki, sai wando ruwan kasa.Dogone mai ginannen jiki tareda faffadan kirji fuskarsa gemune da gashin baki (beard) da yai masa kawanya wanda tsayinsa bai wuce inci biyu ba. Fari ne tas tamkar wani balaraben madina ga dogon fuska hade da dogon hanci. Kyakyawane ajin farko a sahun maza da suka amsa sunansu. Wasu 'yan mata biyu da ke tura trolley nasu suka tsaya sakeke suna kallonsa har yazo ya wuce ta gefensu shi bai ma san sunayi ba. 'Dayar saida ta rike yar uwarta ganin tana neman sulewa. Muhammad Dikko Bakori kenan effect da yake dashi gun 'yanmata. Hankalinsa sam baya a jikinsa yanaga badakalar da ya sanya kansa a ciki. Tafiya yake yana girgiza kansa harya iso inda jerin wasu private jets suke, daya daga cikinsu an rubuta 'Bakori airways' wanda mallakinsune na Bakori enterprises. Jabir daya kasance aboki kuma manager a gareshi yana tsaye bakin jirgin shida cabin crews biyu, mace da namiji suna mashi welcome hannu kawai ya daga masu wannan ya nuna masu baya son hayaniya.
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Ciki ya shige kawai, Bismillah yai a hankali ya zauna kan kujerar dake kusa da window. Sai a lokacin yaji hankalinsa ya dawo jikinsa, reality sets in. Jikinsa har rawa yake tamkar yana cikin sanyi. Fuskarsa dauke da mamaki alamun ya kasa tabbatar da abunda ya faru. A kullum Baba Alhaji wato kakansa yakance kowane decision zai dauka kada yai wanda zaiyi dana sani, ya dau matakin da yasan yafi masa kwanciyar hankali saboda saurin daukan mataki na kawo dana sani mara amfani. Sai yasa tun yana karaminsa baya abu at the spur of the moment, komai zaiyi sai ya auna yaga daidai ya karanto mai zai iya zuwa ya dawo. Amma sai gashi lokaci 'daya ya jawo wa kansa bala'i da jaza'i data kasance 'wannan yarinyar'. Yau shi Dikko ina tunaninsa da kaifin basirarsa da ake cewa yana dashi? Ina ma hannun agogo zai juya ya canza matakin da ya dauka? Saidai ina! bakin alkalami ya bushe. Nan yaji wani nauyi ya bugi zuciyarsa wata irin tsana da kyama yamamaye daya tuno da fuskarta. Wani irin numfashi yake cikin kunar rai. "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" ya furta a hankali.
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Jabir daya shigo ya sameshi a haka ya zauna a kujerar dake kallon na Dikko yace "Haba Dikko, kasa wa ranka salama mana, kana daukan abu da zafi fa. Sheelah kuma contact naka sunce New Castle suka tafi jiya ai kaga akwai hope na samunta. A hankali Dikko ya dago kansa yana kallon Jabir na kusan sa'a talatin kana cikin dacin rai yana magana a hankali sai na kusa dashi zai ji me yake cewa "She should keep praying bamu had'uba don na tabbatar maka she will regret ever knowing me because I hate her with a passion and am going to make her life a living hell". Shi kansa Jabir saida yaji wasu chills in his bones because of the intensity of how Dikko yai magana. Bai taba ganin sa a haka ba zai iya cewa hawayene kwance kasar idonsa Shikenan Sheelah taki ta kare!!!!