Saedae dole xamu tashe tsaye akan yarinyar dan sae anyi da gsk da wannan tunanin tashige dakinta tanata kissifa abubuwa kalala akan fatee,itako gwanar tana ganin goggo ta fita dakin ta aje kwanon abincin tabi lpyar gado sae bacci,ana kiran magrib hajiya ta tashi fatee daga baccin asarar data keyi tace taje tayo alwala tae sallah,sae alokacin ta tuna ashe ko azhar batayi ballantana kuma la'asar ga magrib idan batayi wasa bama yanxu taji ankira ishaa tace tab gsky sunyi yawa hajiya ta kalleta tace mene sukayi yawa tae saurin cewa aa wani homework ne aka bamu shine nake tunawa,hajiya ta gyada kae tace Kim mayi azhar kuwa,da saurinta tace ehh nayi mna tun a skul la'asar ce banyiba,toh maxa aje ayi amma kar ayi barna da ruwa kinji jumah hajiya ta fada,toh tace mata ta dauki buta tayi waje har xata debi ruwan alwalar sae kuma ta fasa ko tunanin metayi allahu wa'alamu sae cewa tayi naga sallahn ae badole bace akaena shekarata shidda fa kawae ta kalli dakin hajiya tace shima abideen ae ba kullum yake sallah ba tunda mu yarane,har xata shiga dakin goggo sae kuma tafasa komi ta tuna ohoo,a hankali ta sulale sadaf sadaf tafice daga gidan aeko tana fita taga aunty saddiqa da saurayinta suna zance tako xuba ma saurayin ido yana magana tana kallon bakinsa gashi ko ina wuni batace kawae ta xuba masa idanu tun aunty saddiqa nadan hararrata harta fara yimata dakuwa data ga ita oganniyar batasan me takeyi ba sae ko ta daka mata tsawa tace ke barnan mara kunya ko gaesuwa baki iyaba amma kin kafe mutum da mula mulan ido kamar na mayu saekace xaki cinyeshi.....aa saddiqa dakata saurayin ya tsayar da ita kinsan yara yanda suke fa kiringa hakuri dan Allah,ita wacce akema fadan ko ajikinta kuma bata daena kallonsuba,saeda saurayin yace yan mata ashiga gida ko dare yayi,wannan karon kallonshi tayi daga sama har kasa sannan tajuya tashige gida tana magana ciki ciki nima bansan metake cewa,maimakon tashige dakin hajiya ko goggo sae aka nufi wurin goggon cikin gida duk cikin goggoninta tafi tsoronta saboda ita batason raeni gata yar akidar addini ce atakaice dae malamace har da'awa tana xuwa kae itama tana cikin yan agaji tana xuwa tayi sallama tashiga tadan rabe a bakin kofa tace goggo an wuni lpy,lafiya lou jikar da namiji wahal da kaka(kirarin da takeyi masu knn idan tana cikin farinki)fatee najin kirarin nan tasan yau goggo nacikin farin ciki tsulum ta mike ta dane kan kujera tace yau goggo ina kikaje bayan kinje islamiyyarmu(munafuka kamar taje makarantar)ae bansamu naje ba bakuwa nayi goggo tafada cike da jin dadi,fatee akayi saurin cewa wacce taxo(da hakanan banxa bata isa tayi wannan tambayoyin ba)goggo tace kafin Allah yayi ma maigidana rassuwa mun rike wata yarinya hasina tun yaye har muka aurar da ita maji ta haihu shiru kannenta biyu anyi musu aure sun haehu amma bnda ita y shekara tara knn sae yau Allah yasa ta haehu ashe suna ta boye cikin sunyi mna baxata wlh tasamu yan tagwayenta mata,fatee tayi xugudi tana kallon goggo sae cen tace amma dae tayi kuka,goggo tace kukan me,tace har biyu yara ae sunyi yawa Allah danice ita boye daya xanyi ince daya na haefa wlh,goggo tayi dariyar takaici tace knn tayima Allah butulci kike so ae yara basa yawa fatee idan Allah yaba saeka gode masa,hmmm tace batayi magana ba sae cen kuma ta tashi tace saeda safe goggo tace Allah yakaemu,tunda taga aunty saddiqa da saurayin ta takeson ta fesa ma aunty zakiyya labari(saboda zakiyya ta iya tsokana)amma bata gantaba duk da cewa daki daya suke kwana amma tasan lkcin daxata shigo ita kam tayi bacci gashi tana tsoron shiga dakin goggo dan tasan fadane sae tasha shi labewa tayi wajen window ta dakin goggo tana lekawa ta inda ya bule saboda lokacin sanyi ne ta rufe window din ita kanta sanyi takeji amma dayake tanason kae gulma taki tafiya tana cikin lekenta taji anriko mata riga har xata kurma ihu sae taga ashe aunty zakiyya ce hmmmm tayi ajiyar xuciya aunty zakiyya tace yar karama dake kin iya leke dan ubanki me kike lekawa,fatee tace nifa ke nake nema wlh,zakiyya tace toh gani meya faru danke wani lokacin ganinki da matsala,hannun zakiyya taja sukayi dakin hajiya suna shiga taga hajiya nayima zainab kalaba tace tab ke zeezee kika xauna hajiya na daure miki gashi ko,zeezee da dan tsamin bakinta tace ehh anyi din,hajiya tace daedae knn maeriga baki tafara budewa,cuno baki tayi tajuya wurin aunty zakiyya tace kinga wanda aunty saddiqa take kulawa kuwa,aunty zakiyya ta baje baki tace waye ya yake yanada kyau,fatee tace tabdijan wlh bashi da kyau fuskar shi kamar zaeyi kashi gashi baki kuma baya brush inata kallon bakinsa ba kyan gani ga.........bata karasa maganar ba sukayi ido biyu da aunty saddiqada tadan xare ido tana kallonta,itako aunty saddiqa tanemi wuri ta xauna tace baki karasa ba ae,zakiyya tace karasa fdamin mna ina ruwanki da ita,budar bakin fatee sae cewa tayi gashi da dadin murya harya fi aunty saddiqa
YOU ARE READING
HASKE!!!
RomanceLabarine akan wata yarinya maisuna fateema,takasance mae shegen surutu fitsara ga uwa uba rashin kunya,lavarin ya kunshi bayyana niyar kauna...kubiyoni kusha lbr