Kwalar rigarsa takama ita a lalle fada xasuyi,ya kama hannunta ya murde yace dani xakiyi fada yakara kyalkyale da wata dariyar yace dan kawae kinyi karya a makaranta an ganoki shine xaki huce akaena,
Yakara cewa mushiga gidan ma xakiga abinda xanyi miki ya saketa yashige ciki abinshi,tafi karfin minti ashirin a wurin kafin tashiga cikin gidan fuskarnan a daure tashiga dakin hajiya tahaye kan gado ta kwanta ,abideen yana xaune baece kala ba,har sukaje islamiyya suka dawo babu wanda yake ma kowa magana sae shi lokaci lokaci yana kallonta yana dariya,
Saeda yabari duk antaru a dakin hajiya ana hira kawae sae yace Kunsan wani abu,aunty saddiqa tace munafuki wata gulmar kasamo kenan,yace ae ba gulma bane asirin watane ya tonu yau a school,dasauri fatee ta kalleshi yace mene ko kin tsargu ne,
Aunty xakiyya tace meya faru fadamana,yace fatee ce dae fatee ce dae ........duk ya fada musu irin karyar dayasa taringa yima yan ajinsu shikuma ashe bayayi ma nasu yan ajin sannan yabasu labarin ihun da wakar da akayi mata a ajinsu tun kafin yadire labarin su aunty ummah suka fara dariya aunty xakiyya harda fadowa akan gado tarike ciki haka hajiya itama taringa dariya,
Wani abu yaxo ya tokare wuyan fatee dakyar take hadiyar miyau kawae basu ankara ba sukaji ta tsandara ihu sae kuka taringa birgima akasa tana kuka,amma hakan baesa su sundae na mata dariyan ba abideen kam mugu har jan rigarta yake yana mata cakulkuli,
Jin dariya tayi yawa shiyasa goggo tashigo tace lafiya hajiya meya faru na farinciki haka,hajiya tace shigo kiji abinda yarki tayi itama aka bata labari goggo tayi dariya tace fatee keda ko tashar jirgi kafarki bata taba takawa ba amma harkina karyan kunada jirgin,
Fatee cikin kuka tace abideen ne yace infada fa,aunty xakiyya tace tohh ae gashinan yasaki shikuma baeyi ba,aunty ummah tace ashe wayon naki na banxa ne,kina nan kina fama da sauro da xafi amma kinacen kina ce musu wae a london kike,
Goggo tace ni jamila wae toh su basuga uniform dinki bane yarnan,hajiya tace bar yarinta haka suka dinga mata dariya ana hira hardae tayi bacci,
Koda taje ranar talata ba wanda ya tsokaneta,itama ummu'ayman dakanta tadawo suka fara wasa gashi zeenat itama taxama kawarta,ita bata taba jin dadin school din tasu ba irin yanxu,gaskiya karya batada kyau,
Ana tashi abideen ya biyo yace taxo taraka su wani waje,tace ban xuwa,yace fatee bakisan abinda xamuyi ba acen kixo muje,tace inane,yace kedae kizo,tace nifa gaskiya yunwa nakeji,
Wani abokin abideen nafi'u yace muje xan siya miki awara,ba musu ta wuce ita da jameel ne agaba suna dan labari tace masa wae ya naganku dayawa ina xa'aje,
Yace gidansu sulaeman, cak ta tsaya ta kwalalo idanu tace wallahi nafasa ba inda xani nafasa,jameel ya kira abideen yace kaji wae tafasa xuwa dan nace gidansu sulaeman xamu,
Abideen yajata gefe komae yafada mata ohoo,suka dawo abideen yace mujeko ta gyada kae,akan hanya kafin su karasa taga mae awara nafi'u yasiya mata ta goma,
Saeda sukaje kofar gidan sannan jameel shima ya tsaya yace ga gidan nan,abideen boss yace tohh tafi gida abinka,yaja kafafunsa yayi gida,su kuma kowa yafara tsintar duwatsu akasa,sunkae su bakwae,
Suka fara jefa duwatsu cikin gidan su sulaeman,hajiya sahura na yanka alayyahu taji duwatsu tako ina acikin gidan,tae ihu irin nasu na yarbawa ko gyale bata tsaya yafawa ba tayo waje,
Da fatee tafara arba taga ta daga dutsenta sama xata cilla a gidan tace keeeee da iyakacinta karfinta,sulaeman daya fito shima yace fatee ce,ta juyo tae musu gwalo tace abideen sun fito,
Aeko suka hadu suka fara mata ihu suna cewa yarbawa masu kwalekwale da duwawu suke tukin tuwo,dama yaran anguwan duk haushinta sukeji suma suka hadu aka dinga mata ihu tarasa yanda xatayi dan kanta tajuya takoma cikin gida,
Dattijan anguwan ne suka kora su kowa ya watse fatee tace kae abideen yau tayi dadi sosae amma nasan dolene xataxo gida fa kuma idan goggo da goggon cikin gida sukaji kasan mun bani,
Yace dalla kinsan indae xata xo saeta wuce ta kofar gidansu nafi'u kohh tace ehhh yace tohm shi kuma xae tara mata yara su hanata wucewa kinga shikenan munshaa suka tafa hannu suna dariya,
Tundaga ranar sulaeman yake tsoran fatee dan ko a aji idan ta fadi abu baya musu bama yashiga harkarta,gashi ita kuma tasamu banxa zeenat takawo abinci Bashir yakawo ga ummu'ayman ma takawo nata duk suci,
YOU ARE READING
HASKE!!!
RomanceLabarine akan wata yarinya maisuna fateema,takasance mae shegen surutu fitsara ga uwa uba rashin kunya,lavarin ya kunshi bayyana niyar kauna...kubiyoni kusha lbr