TAKWAS

712 57 4
                                    

LAIFI 8.

Zama na da Auwal Zaki a matsayin miji da mata wani irin zama ne kamar irin mafarkin da mutum zai tashi daga barci ya fara tunawa. Zama ne da a kayi cikin rudani da rashin mafita. Zaman aure ne wanda mutane da yawa basu taba jin ko labarin irin sa ba. Bayan an kare biki an kai ni gidansa dake unguwar Arkila a sokoto, nesa kadan da gidan mahaifinsa, bai wuce tafiyar mintuna biyar zuwa bakwai a tsakani. Auwal yayi duk kokarin da zai yi na sake da shi, Auwal yana da hakuri matuka, yayi hakuri dani kuma yayi min uzuri sau babu adadi, ga kuma uban mijina wato baba Alh zaki da yake so na kamar 'yar cikinsa.

Bature yace "you can't have it all" mahaifiyar auwal Hajiya Murja sam bata so na, idan zan yi mata adalci kuma bata da LAIFI, saboda ta samu labari cewa ban so auren jininta ba, dole a kayi min.

Farkon zaman Auwal baya kusanta kanshi dani, yayi kokari ya bani lokaci na wasu kwanaki, amma kullum ne sai ya tambayeni, "akwai abinda ki je bukata?" Bayan wasu kwanaki ya fara kokarin kusantad da kansa zuwa gareni amma abu ya faskara. Ya fara da kokarin rike hannuna, ko ya shafa kaina ko gefen fuskata. A bangarena, duk lokacin da yayi haka ban sanin lokacin da nike kawo hannuna in kare wajen, kamar zai soka min allura.
Ko zama kusa dani idan yayi jikina zai dinga rawa, sai in dinga samun kaina cikin wani irin yanayi na rashin nutsuwa.

Wani dare yayi min nasiha kamar yadda ya saba, ya hada da magiya, da kyar na daure na tattaro duk karfin halin da nike da shi akan tsoron da ban san daga ina yake zuwa ya mamaye ruhina ba, nayi kokarin mika wuya. Shi kuma da ya fahimci hakan sai ya rungume ni.
Ai ko yana fara shafa jiki na sai na rikice mai na fara kokarin kwatar kai na. Duk kokarinsa na ganin ya lallabani, tare da lallashi bai sa naji zan iya bari ya kwatanta abinda yake so ba. Idan ya rungumeni ko sumbata a fuska sai ina ji kamar kashe ni zai yi ko ya hallaka ni. A firgice na tunkude shi daga jikina na tsallakeshi zuwa makewayi.

To haka muke zaune, zaman hakuri. Abinci da komi zan ba shi amma bani so mu hada jiki. Daga ya rungumeni sai in fara jin hankali na ya tashi. Jikina ya fara rawa, idan ya ki saki na sai in fara kuka da kokawar kwatar kaina, har cizon Auwal ni keyi idan yaso gwada karfi a kaina.

Haka muka zauna bani kaunar Auwal ya zo kusa da jikina, wasu lokutan yayi nasiha wasu lokutan ya shareni ya kwanta a falo ni ina daki. Ban san yaya a kayi ya gano bani son kwanciya tare dashi ba a gado daya, idan muka kasance daki daya, sai in kasance cikin fargaba bacci ya dade bai dauke ni ba.

Cikin wannan yanayi har lokaci yayi na fara zuwa makarantar polytechnic ta Umaru Ali Shinkafi dake Sokoto. Anan muka fara samun matsala da Auwal. Yana jin haushin yadda nike sanya sutura zuwa makaranta. Ko yayi magana in saka hijabi bani iya sa yalwatacce, saboda ban saba ba.

Watanni kadan da auren ya dauke ni wata lahadi tun da safe muka kama hanya zuwa kano, da yake washe gari litinin hutun easter ne. Muna isa bayan mun gaisa, Auwal ya ajiye kunya gefe daya, ya zayyanewa mama yanayin zamanmu yadda zata fahimta, a lokacin daddy baya nan yayi tafiya zuwa abuja. Cikn bayanin sa yana ta maimaita cewa, mama kiyayyar da karima ke yi min, ko shiga dakinta nayi ta dinga firgita kenan, balle ace na matso kusa gareta, ya dora da maganar yanayin sa sutura. A gaban idanunsa tayi min fadan saka suturar da mijina ya keso. Sannan ta roka ya wuce masauki, ya bari in kwana wajenta kafin gobe lokacin da zamu wuce.

Mama ta zauna ta dinga tambaya ta akan harkokin auratayya, tayi ta faman bayani da bani shawara akan zaman aure. Har littafin "everywoman" ta dauko ta bani. Ta dinga ba kanta laifi, tace a zatona karatun boko da na addini ya isa ki gane cewa akwai wata alaka ta kusantaka jiki da jiki tsakanin mace da namiji bayan aure. Ashe nayi sakaci karima, tabbas ya kamata ace na sanad dake yadda abubuwa suke.
Ta kara da fadin "don Allah karima ki debe kiyayyar Auwal a ranki. Ina laifinshi yana sonki idan kika ba shi hadin kai za ki ji dadin zama dashi." Washe gari da safe kusan karfe goma na safe ya dawo muka kama hanya bayan munyi sallama dasu mama.

LAIFIWhere stories live. Discover now