2.ASHANA
LAGOS
1981QURAISHA ASHANA, shi ne sunanta.
Ita ce oloshin da a zamaninta aka dinga rufe gidan karuwai saboda masifa da bala'inta. Ta zo bariki tun tana yar shekara Sha Shida lokacin iyayenta sun rasu, 'yan uwanta kuma za su aura mata wani Wada da ake raɗe-raɗin yana da cutar kutarta.Sun ɗaura, ta kuma zauna da shi har tsawon shekara ɗaya. A daren da ta cika shekarar ta haifi ɗanta Namiji, da gama mata wanka ko ɗuminta yaron bai ji ba ta direshi gefen yar tsohuwar da ke kula da su tana barci, ita kuma ta haɗa ya na ta-ya na ta za ta gudu. Sai dai cinkaro da ta yi da mijinta daga zaure ya sa ta tsayawa suna kallon-kallon, kan ya buɗe bakinsa jin ba'asi ta caka masa basilla a kirjinsa, inda nan take ya zube gurin. Ita kuma Zakara ya ba ta sa'a ta cale ita da Aminiyarta Zenabu da ta ɗora ma ta wannan shawarar ta kashe mijinta, sai su gudu gidan Auntynta da ke zaune legos.
*Sun isa, sun kuma samu tarba mai kyau, in da ta ciyarsu na tsawon kwana bakwai. A ranar na takwas ta ce kowa sai ya je ya nema, kamar yadda ita ma take nema danta kula da marayun yaranta. Zenabu ta ba su shawarar su dinga sai da maganin gargajiya, haka suke gammo su tafi, ganin ba wata riba ya sa suka watsar suka koma yiwa mai tuwo-tuwo wanke-wanke a kasuwa, nan ma hantara ta yi yawa suka watsar sukai dawowarsu gida suka zaune.
Auntyn da ta tambayesu dalili suka gaya ma ta, Zenabu ta ƙara da cewar su dai ta sa su ana ta harkar suna taya ta. Murmushi ta yi tana kallonsu, su ba su san me take yi ba, kawai gani suke tana shiga tana fita, sana'arta ba ta tayi ba ce, ba kuma ta hutu ba ce, sai dai kowa jikinsa ya nema masa. Da ta faɗa musu ba ɓata lokaci suka yarda.
Su fa kuɗi suka zo nema ba hutu ba, a ƙauyensu da suka baro a shekara sau ɗaya suke ganin shinkafa da Masara, sai fa gero da dawa. Kai ko raken nan mai ɗan zaƙi babu, balle su Acca da Alkama masu ƙara lafiya.
A ranar ta kai su babban gidan da take harkar, a take kuma aka ba su ɗakuna a gidan da cewar dole sai an musu karatu kan harkar, da sharaɗin duk abin da suka samu raba dai-dai ake yi da uwargijiyarsu da ake kira Anty Kankana, kuma ba za ka bar gidan ba sai ka yi shekara goma, sannan za a baka 'yancin kai. Ba ɓata lokaci suka yarda da duka sharaɗin, inda Quraisha ta koma Ashana, Zenabu kuma ta koma Bitas, rayuwa ta fara kyawu.
A shekara biyar da Ashana ta yi cikin gidan nan ya yi tumbatsar da babu wani gidan karuwai da zai doke shi. Sai da ta kai ta kawo har Anty Kankana na shayinta saboda ita ce macen farko da ta karya duka dokokin gidanta, saboda Zenabu ta samu wanda take so za su yi aure, sun hana.
Haka Saboda ita ɗan takarar gwamnan garin na wancan lokacin ya bige gidan da suke ya sa a gina musu wani na zamani mai daƙuna Hamsin, domin kawai Ashana ta yarda ta aure shi. Ita kuma da ta ji labarin bokansa ne ya ce idan har ya aure ta sai ya yi shekara Ashirin yana gwamna a garin ba tare da an sake wata siyasar ba, sai taƙi, a cewarta ba sonta yake ba, ita wanda zai dinga kwanciya tana taka bayansa da tsinin takalmi take so, ba ma za ta yi auren ba sai ta shekara Arba'in domin ka da ta haihu.
A shekara ta goma da zuwansu legos Aunty kankana ta kai takarda, nan take aka ɗora Ashana a matsayin shugabar gidan. Nan ta bawa kowa dama ya ci karensa babu babbaka, ita kawai a biya ta kuɗin hayar ɗakunanta, haka ta saka dokar daina karɓar yara 'yan ƙasa da shekara ashirin.
A wannan shekarar ta ta ƙaddarar ta fara tambali da rayuwarta ta hanyar sa ma ta soyayyar wani talakan mutumi tiƙis da ko me goge ma sa takalmi ya fi shi cin abinci sau uku a yini.
A daren wata lahadi ne suka fita dan fasa gidan wani babban Attajiri saboda ya taɓa 'yar lelenta Soupy. Soupy ita kaɗai ce yarinyar da Ashana ta yarda ta shigo gidansu a shekararta ta Sha Bakwai, ba don kome ba sai dan labarinta da ta ji na kwarewarta a satar tabarmar masallaci da kaji da tumakin garinsu ne ya sa mutanen garin suka ma ta atile har wajen garin.
In da bata ya da zango ko'ina ba sai gidan Ashana, bayan interview ne ta samu babban matsayi na zama yar lelen Ashana. Baiwar sata gareta irin wacce ko gaisawa za ku yi yanzu za ka ji ba sarkar wuyanka. Tamkar dai wacce ke da siddabarun rufa ido.
Wannan kuma ita ce fitarta ta farko, anan tama Alhajin da aka haɗata da shi satar Agogo, shi kuma ya zaneta da dorina mai baki biyu. Sharaɗin ɗaukan karuwa gidan Ashana kuwa babu duka, duk kuwa cin kashin da karuwar za ta maka.
Wannan dalili ya sa ranta ya ɓaci an taɓa yar lelenta, shi ya sa ta fito dan suyi operation a gidan Alhaji. Duk kuwa fitar da za ka ga anyi da Ashana, ba ƙaramar fita ba ce.
*A wani ƙofar shago mai ɗan duhuwa motarsu ta tsaya. Nan ta ce su ƙarasa gidan ita za ta jirasu saboda kanta da taji yana sara ma ta. Take suka amsa inda suka sassaka manyan hijabansu da niƙab suka fi ce, bayan ta gargaɗesu da karsu taɓa kowa banda Alhajin.
Ɗora kanta tayi saman sitiyarin motar jin kan na ma ta wani nauyi. Ta shafe minti ashirin a haka kafin kuma taji wani ƙamshin turare irin ɗan saudi na dukan hancinta kasancewar yana da ƙarfi. Dagowa ta yi a hankali jin kamshin na ƙara karuwa, sai dai ga mamakinta babu kowa. Ƙofar da ke gabanta kuwa ba ta tunanin akwai mahaluƙin da zai rayu cikinta saboda yanayin kwararraɓewar shagon. Sai dai jin sautin buɗe ƙofar ya sata ware ido don son ganin mai buɗewa.
Ƙirjinta ne ya buga, ya ƙara bugawa sau ɗari da tamanin ganin mutumin da ya fito. A cikin hasken farin watan ta gama hango tsantsar kyawu da nutsuwarsa na Fulani, a kuma lokacin Allah ya da sa na sa ikon kanta, kallonsa take shi ma kallonta yake yana mamakin abin da mace ke yi a wannan talatainin daren.
Kauda kansa ya yi yana mai bi ta gabanta dan zuwa masallacin da yake limanci.
Ba ta san tana binsa a baya ba sai da hannun Soupy ya jawo ta zuwa baya, ganin kawai tafiya take ba tare da sanin in da za ta ba. Da ƙara Soupy ke janta da su tafi an kira 'yan sanda, sai dai ina har aka kama su a ɗura su cikin motar yan sandan ba ta dawo hankalinta ba. Ba abin da take ambato sai; "wallahi ina sonsa, idan ban same shi ba mutuwa zanyi." Kafin akai police station ta cika carbi uku da waɗannan kalmomin!*Idan har na yi ne domin nishaɗinku, to kunfini sanin abin da za ku min Ni ma na ji daɗi.*
*Ba sai ina ta riƙonku kan ku dinga nunami naku kyautayin ta hanyar latsa wannan maɓallin mai alamar tauraro*
*Ku yi domin Allah, Ni ma zan kai ƙarshe da yardarsa*
YOU ARE READING
ASABE REZA
Romance'Kwallina!' Zuciyarta ta buga da wannan kalmar, jan jikinta ta fara yi tana son isa inda ta jefar da kwallin, ji take shi kaɗai ne Zai iya taimakonta, shi kaɗai ne zai iya hana HAMOUD aikata duk wani abu da yake hari. Dafe kwalbar kwallin ta yi tan...