BABI NA UKU (REZA)

4.3K 658 31
                                    

3.

Tafin hannu tasa tana dukan goshinta kamar mai son tuna abu, da sauri kuma ta fara dube-dube, can gefen gado ta hangota ta yi ɗai-ɗain da ba za ta ƙara amfanuwa ba.

"Damn it!" Ta faɗa tana duban Soupy. "Latsomin Sumoli maza a wayarki ta zo nan inda nake, jirani na watsa wanka."

Bin ta ta yi kawai da ido tana mamakin canjawarta lokaci guda tamkar wata mai Rauhanai.

Mintina arba'in ta kwashe tana wankan sai gata ta fito, tundaga tafin ƙafarta za ka gane ta canja, ta cire zobunan da ke ƙafar haka sarkar, ta cire duk wani tarkace na fuskarta.

Ba Soupy da ke tsaye tamkar an dasa ta ba, hatta Sumoli da shigowarta ke nan sai da ta ƙame tsaye tana ma ta kallon mamaki.

Ba annurin da take yi ba ne ya ba su mamakin, a'a, shin ina sirrikan da ta ce suna jikin duk wani ƙarfe da ta huda jikinta ta maƙala? Shin ina asarar da take ikirarin za ta yi duk lokacin da ta ciren?

"Come on, let's go!... Ta faɗa tana duban Sumoli da ke ta zare ido. Ganin ta gaza magana ya sa ta ci gaba.

"Let's go and show Fakriyya that I am still the very best..."

"Maa..."

"Wait! This is an order, Sumoli."

Ta faɗa a kausashe tana ci gaba da ɓalle botiran baƙar Abayar da ta saka. Ta yane kanta da gyalen Abayar bayan ta karyoshi yadda zai rufe fuskarta kamar Niƙab, sai ta yi wani irin kyau mai sanyin kallo, ta fito a Asabenta Sak! Ba Reza ba.

Ganin ta yi gaba ya sa Soupy saurin shan gabanta, "Haba mana Reza ki bi a hankali, yau fa ta tare? Me za ki je yi gidan Amarya a wannan daren in ba wani sabon ɓacin ran kike son ƙarawa kanki ba

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Ganin ta yi gaba ya sa Soupy saurin shan gabanta, "Haba mana Reza ki bi a hankali, yau fa ta tare? Me za ki je yi gidan Amarya a wannan daren in ba wani sabon ɓacin ran kike son ƙarawa kanki ba."

"Amarya? Hahaha." Ta fasa wata irin dariya.

Sai kuma ta yi shiru idanuwanta na ƙara cikowa.

"Wannan Amaryar ba za ta amsa sunanta ba muddin ina numfashi Soupy. Sai na hanata duk wani jin daɗi na rayuwar nan, sai na nuna ma ta Ni ce dai Asabe da akai naƙudarta tsakiyar gidan karuwai ba wai haye na yi ba! Bariki jini na ne da aka ciyarni da shi aka shayar Ni!"

Sai kuma ta ƙarasa daidai saitin da Sumoli ke tsaye.

"Ki tabbata na tararki a motar kafin in gama saka takalmi."

Ta fice tana mai maida kwallar da ke shirin zubo mata.

*** ***

A hankali motar ta tsaya nesa da tangamemen gidan da ke fuskantar su. Daga cikin motar take ƙarewa gidan kallo wani abu na sake zauna mata a kirji, zuciyarta na ƙara curewa, tunawa take yi da ranar da ya fara kawota gidan ya kira shi da matsayin mafarkinsu.

"My everything wai gaske kike ba za mu fita ba? Ya faɗa yana mai kewaye hannunsa saman barimar girarta"

A hankali ta ture hannun da sigar wasa tana harararshi.

ASABE REZAWhere stories live. Discover now