BAHAGON TUNAN
Rubutawa
Badeeyerh Beauty Queen
Da
Fauziyya L. AmmanyLabari
QUEEN MERMUEUwa abun alfahari,uwa mai share hawaye,uwa mai kaunar farin cikin mu. Yau gashi mun rasa ki muna kaunarki muna fatan rahamar Allah gareki, Ubangiji ya sada ki da aljannarsa madaukakiya. Allah ya bamu hakuri jure rashin ki ya rayamu ya albarkaci rayuwarmu Mama Aisha Allah ya haskaka makwancin ki. Antyna Zetty muna mika gaisuwa gareki Allah ya kara hakuri Ameen.
1
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
"Wayyo! Nana zo ki gani yi sauri don Allah" cikin Ihu ta ke wannan maganar ta na kwance kan tabarma a tsakiyar dak'in su.Wacce aka kira da Nana ce ta shigo dak'in tana fadin " lafiya, meyafaru?"
"Anyi posting cigaban novel din wancan satin wallahi duba ki gani" ta fadi ta na nuna mata wayar hannunta.Tsaki Nana ta yi tare da zama kan tabarmar tana fadin "Haba Anty Zarah yanzu saboda anyi posting shine kike wannan ihun? na dauka ma wani abu ne fa ya same ki kuma..." daga mata hannu wacce ta kira da Anty Zahra ta yi, wanda ya hanata karasa maganar da ta ke yi.
"Ke! Karfa ki raina min hankali, banza kawai dalla fita ki ban waje" cewar Zahra.Tashi Nana ta yi ta na jimamin halin Anty Zahra.
Kyakyawa ce sosai wacce ta amsa sunan mace, gata fara, ta na da doguwar fuska mai dauke da dara-daran idanu ga siririn hancinta wanda ya kayatar da kyakyawar fuskarta, bakinta madaidaici kamar an dasa mata, tana da diri na cikakkiyar mace. Fatima Zahra Adam kenan. Diya mai hakilon cimma burinta na ganin ta mallaki duk wani jin dadin duniya da take gani wurin karance-karance ta.
Lekowa Nana ta yi tana fadin "Anty Zahra talgen tuwon fa yana ta konewa"
"Ina zuwa malama" ta bata amsa ba tare da ta kalle ta ba.Tafi minti talatin tana sake maimaita novel din bayan ta gama karantawa. Da kyar ta ajiye wayar ta mike ta dau dankwalinta ta yi waje. Talgen ya kone sosai ya zama rabin tukunya.
Tace "Amma dai Nana ke banza ce maimakon ki fadamin ya kone shine kika barni ko"
"Haba Anty Zahra na fada miki fa tun dazu"
"Dalla yi min shiru mara kunya kawai" ta fadi tare da daukar garin tuwon da niyar tukawa.Shigowar gwoggo ya sanya ta tsaya ta na yi ma ta sannu da zuwa, ta tsaya ta rike habarta alamun mamaki ta ce "Zahra tuwon dana daura tun sha biyu shine har yanzu karfe uku baki tuka ba?"
"Gwoggo iccen ne baya ci wallahi"
"Ba ruwan icce Zahra, da dai bansan halinki bane, kina nan da wannan tsinanniyar abar wai waya ta ina zata bari kimana abinci?"Sunkuyar da kai ta yi ta na bata fuska tace "Nifa Gwoggo wallahi ko wayar ban taba ba yau, kuma ki tambayi Nana kiji"
Bata ko kara bi ta kanta ba, sai ma amsar garin da ta yi ta tuke tuwanta tana fadin "Duk yanda yakai haka zamuci ai Zahra, amma ki sani watarana wannan wayar saita halaka ki."
"Kai Gwoggo baki kike min?"
"A'a Zahra ba baki bane gaskiya nake fada miki, ki gujema wannan masifar zamanin"Shiru sukayi suna sauraron Gwoggo data cigaba da ganar dasu illar wannan wayar. Har ta gama tuwon tare da dumama miyar kubewa, suka ci sannan sukai shirin islamiya. Sallama sukai mata ta yi musu fatan dawowa lafiya suka fita.
Suna fita Zahra tace "Ke Nana jeki ni zan biya ma Zainab zamu taho tare."
Tabe baki Nana ta yi domin tasan ba islamiyar da zasu zo zama zasuyi dak'in Zainab din suna aikin charting, don haka ba tace mata komai ba ta yi tafiyarta.
*********
Kwance ta samu k'awarta Zainab tana karanta wani novel, jin shigowar Zahra yasa ta ajiye ta mike cike da zumudi tana fadin "Zahra anyi posting kenan?"
"Sosai ma kuwa wallahi na yau ya hadu in fada miki sai kin karanta zakiji yanda ya bada wuta yau"Da sauri Zainab ta amsa wayar tana duba wa, ita kuma Zahra ta dauki littafin da Zainab din ta ajiye ta hau karantawa.
"K'awalli labarin nan na bada wuta wallahi, ina ji dama nice jarumar ciki" cewar Zainab bayan ta karasa karantawa.
"Bari kedai kullum addua nake in samu irin wannan gayen wallahi, nifa naji inasan jarumin nan prince Arya"Hannu Zainab ta mika mata suka tafa suna dariya, tace "Allah Zahra na samu irin daular novel dinnan za a ga wulakanci"
"Kefa banza ce, ai kawai ki dauka mun samu, domin mai kyau sai kyakyawa" dariya Zainab ta yi tace "Hakane tawan Allah ya kawo shi".Nan suka hau karatun wannan novel, sai da taga shidda ta yi sannan ta mike ta yi ma Zainab sallama bayan ta rakota har waje sannan ta yi hanyar islamiya.
Tsayawa ta yi a hanyar da take da tabbacin Nana zata biyo. Tana nan tsaye ta hango ta ta taho, dan haka ta hade fuska lokacin da Nana ta kara so tace "Ke wallahi zan daina jiranki idan an tashi kullum saikin bata min lokaci kafin ki fito"
Dariya Nana ta yi domin har ajinsu Zahra ta leka bata ganta ba, amma yanzu tana mata barazanar iska don haka tace "Yi hakuri antyna na tsaya karban takaddune wurin k'awata"
"wuce mu tafi malama sai iya tsarin zance kamar wata uwar mata".Suka isa gida ana sallar magriba, sukai alwala. Nana ta shimfida musu darduma, tana yin raka'a daya, Zahra ta idar ta shige dak'i. Wayarta ta dauka ta hau yanar gizo.
2018
YOU ARE READING
BAHAGON TUNANI
ActionBaka nemi mu zauna lafiya ba, tunda baka min abun da nake so. Na fadi maka kamin ankon kawata, amma saboda bakin talauci dubu ashirin ta gagareka, ga matan nobel sai dai ace bude doruwa akwai kudi ko kuma ace zan tura ta account dinki, amma kai ko b...