Babi Na Uku

82 5 2
                                    

            Rubutawa
Badeeyerh Beauty Queen
          Da
Fauziyya Lawal Ammany

      Labari
Queen Mermue

          

Haka rayuwar Zahra ta kasance a koda yaushe tana online, bata da lokacin yin cikakkiyar ibada. Ko makaranta bata da lokacin zuwa saboda tsananin burin data dora kan karatun litattafan online.

Saukinta daya tana mutuwar son Aminullah, duk kuwa da baya da hali sosai tana sonshi a haka.

Aminullah malamin makarantar firamari ne wanda albashinsa bai gaza duba talatin ba, gashi shike kula da mahaifiyarsa da kanwarsa mai suna Khadeeja, cikin rufin asiri suke rayuwa da dogara rayuwar su kacokan kan albashin sa. Khadeeja na aji shidda yanzu zata yi jarabawa gashi baya samun kudi kan kari sai dai maleji. Yana kaunar Zahra yana burin ta zamo uwar yayansa duk kuwa da sanin dogon buri irin na Zahra da ya yi, domin wani lokaci idan yazo hira takan karanta mai irin rayuwar da take fatan samu daga cikin abun da ta ke karantawa a cikin littafai. Kullum yana kokari wurin nuna mata ba gaskiya bane amma bata fahimta, shiyasa ya dage da addua tare da fatan wata rana ta fahimta.

Yau Zahra bata da kudin siyan data gashi Aminu bai turo mata kati ba, don haka ta shiga dak'in Gwoggo da nufin tambayar ta rancen kudi. Karaf idonta su kayi tozali da naira dari ajiye kan kujerar dak'in. Gwoggo kuma bata nan, don haka kawai ta dauka ta fita. Kati ta siyo ta sanya a wayarta tun a hanya ta bude data domin ta kosa ta ganta online. Idanuwanta na kan wayar taji ana mata wani gigitaccen horm da mota. Rikicewa ta yi har wayar hanunta ta fadi kasa, a fusace ta juyo sai lokacin ta lura kan titi take.

Mai motar ya fito yana murmushi ya tsugunna ya dauko mata wayar tare da mika mata yana fadin "Yi hakuri mai kyau kin tsaya kan hanya ne."

Harara ta zabga mishi tana murguda dan karamin bakinta" Sai akace ka dinga min horm kamar wata kurma ?"
"Tuba nake mai kyau."

Mika hannu ta yi da nufin ya bata wayarta. Kallonta ya yi ya kalli wayar yaga ta dan fashe kadan, ya sanya hannu cikin aljihu ya ciro wayar shi sabuwa iPhone. Ido Zahra ta zuba mishi ganin yana cire sim dinshi daga cikin wayar, bata kara tsinkewa ba sai da taga ya bude ta ta wayar tecno y6 ya cire sim dinta ya sanya cikin iPhone din. Ya dube ta yace"Ayi hakuri Mai kyau nayi laifi, amma ga wannan kiyi amfani da ita."Ya mika mata dukka wayoyin biyu.

Kallon hannun shi ta yi da yake miko mata wayoyin tace"Mai zanyi da wayar ka, nace ma ina son aro ne?"
"Kyauta na baki mai kyau ba aro ba." ya fadi cikin sanyi domin yaga kamar ta yi fushi.

Da sauri kuwa ta amsa tana juya wayar a hannunta "Kyauta fa kace bawan Allah?"
"Eh Mai kyau."
"To na gode Allah ya saka."
"Ameen Mai kyau, amma baki fadamin sunan ki ba."
"Zahra sunana."Ta fadi hankalinta na kan wayar.

Murmushi ya yi "Ashe banyi kuskure ba da nace Mai kyau, gaki da kyau ga sunan ki ya dace dake Zahra."
"Na gode sai anjima."cewar Zahra tana kokarin barin wurin domin kuwa murna ta cika ta yau itace rike da iPhone.

"Sunana Ahmad ina fatan zan samu number ki?"
"Eh sosai ma."ta karanta mai ya sanya sannan sukai sallama.

Da gudu Zahra ta karasa gida tana kiran Nana. Nana dake zaune gefen Gwoggo suna neman kudin cefane ta mike da sauri tana fadin " lafiya anty Zahra da wannan kiran?"
"Kalli kiga."ta mika mata wayar.

Amsa ta yi tana kallon wayar cikin mamaki "Anty Zahra waya baki wannan wayar?"
"Yanzu wani ya bani kyauta wallahi."
"Ke Zahra uban me kika mai da zai baki wannan katuwar wayar?"cewar Gwoggo.

Turo baki Zahra ta yi "Nifa yarda min waya ya yi ta fashe shine ya ban tashi kuma wallahi ba rokon sa nayi ba."
"Idan ma rokon sa kika yi wallahi ba ruwana, domin wannan zamanin abun tsoro ne gara ki kula."
"To Gwoggo, wannan kuma zan ba Nana." cewar Zahra tana mika ma Nana tecno din.

Amsa ta yi tana juyawa a hannunta domin ita dai ba farin ciki ta yi da wayar ba, bata fatan ta yi irin rayuwar da Zahra ke yi a waya. Tana kuma yi ma Zahra addua domin tasan yanzu ita da cikakkiyar ibada sai Allah, dama ya ya lafiyar kura.

Zahra ta kalli Gwoggo ta ce"Ga kudin ki dana dauka."
Harara Gwoggo ta sakar mata tare da kai mata duka tana fadin"Ja'ira wannan matsiyacin aikin wayar sai ya sakaki sata." Da gudu Zahra ta shige dak'i tana dariya.

    Da dare Aminu yazo, cikin doki ta shiga nuna mai wayar. Hankalinshi yai mutukar tashi yace " Zahra meyasa kika amsa, kinsan da manufar daya baki wayar?"
"Karka damu Al'ameen kai kadai nake so duk kuwa da ya fika kyau kai ne a raina."

Yaji dadin kalamanta ya kuma gasgata domin Zahra mai kyau ce, duk namijin daya same ta ya yi dace kuma tana da suffar matan manya, amma gashi shi da ba kowa ba ya samu soyayyarta, yana alfahari da hakan. Don haka duk da ranshi baya so ya bar maganar wayar.

"Zahra inasan na aiko da kayan auren ki kwanan nan insha Allah."cewar Aminu.

Rufe fuska ta yi tana dariya ta ce " Allah ya kaimu lafiya Al'ameen nawa."

Cike da jin dadi da tsantsar kaunar juna suka cigaba da hira har sukai sallama ya tafi da alkawarin sati mai zuwa zai turo gidan su.

2018

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 08, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BAHAGON TUNANIWhere stories live. Discover now