Babi na biyu

84 5 5
                                    

        BAHAGON TUNANI

        RUBUTAWA
Badeeyerh Beauty Queen
        Da
Fauziyya L. Ammany

Labari
QUEEN MERMUE


                           2

Nana ce ta shiga dakin dauke da abincin su, zama ta yi tana fadin,"aunty zahra taso muci abincin." "to." kawai ta ce ma ta taci gaba da chatin din ta.

Ganin an dauki lokaci ba ta taso ba ya sa Nana kara yi ma ta magana,"Anty don Allah kizo muci abincin nan, so nake nayi karatu ina da gwaji gobe, gashi ba wani karatu nai sosai ba."

Kafin ta rufe bakinta Zahra ta taso ma ta da masifa,"na hana ki cin abinci ne da zaki ishe ni da magana?, bana son iskanci fa kici naki mana idan na gama nazo naci, kawai kin wani zo kin ishe ni da surutu."

"Allah ya baki hakuri Anty." Abincin ta faraci ita kuma ta cigaba da chatin dinta ba tare da ta kara magana ba. Bayan Nana ta gama cin abincin ne ta aje mata na ta sannan  tace,"Anty ga naki nan,naci nawa."

Kala bata ce da ita ba, kai ga dukkan alamu ma ko jinta ba ta yi ba catin dinta kawai take. Nana kam tashi ta yi ta dauko Littafinta ta fara karatu.

"Assalamu Alaikum". 
"Amin wa'alaikussalam" gwogga ce ta ansa tana fitowa daga daki.

"Wai ana sallama da Anty Zahra".
"Wake sallama da ita?"
"Yaya Aminu ne na gidan malam Salimu".
Tsaki gwogga tayi sannan tace"Na zata wani mutumin arziki ne,ce mashi gata nan zuwa tunda ta makale mashi ai ita ta jiyo."
Yaron ya ce "to" sannan ya fita.

"Yaya Aminu na gaya ma gwogganta tace gata nan fitowa,Yaya wai miyasa tace kai ba mutumin arziki bane bayan kuma kana da kirki tunda idan kana da kudi kana saya mana minti da biskit,kuma ina ji su mama na fadin kana da kirki sosai."Murmushi  Aminu ya yi sannan yace dashi"Baka gane abin da take nufi bane shiyasa, amma yanzu karbi nan kaje kasha minti kaji". Ansa yai yana murna yace "Nagode Yaya sai da safe."
"To sai da safe Jamilu a gaida su mama."

"Zahra! Zahra! Zahra!.
Wai baki jina ina kiranki?" "Ganinan Gwogga." tsaki ta yi sannan ta fara gunguni ta na maganganu  kasa-kasa gudun kada Gwoggo ta jita ta fito.

"Wancan mara amfanin ne yazo wajanki,kinbi kin nace masa ko ubanmi zaki tsinta gare shi,(mi na sama yacci balle yaba na kasa.)"

Shagwaɓe fuska ta yi "to Gwaggo nidai ina son shi a haka ai yana da dan damar shi tunda ban samun wanda ya fishi ai gara in lallaɓa da shi."

Gyalenta da ke saman igiya ta ja,ta yi soron gidan nasu.

"Sannun ka da zuwa".
"Assalamu Alaikum"Aminun ya faɗa.
"Wai na manta ne yi hakuri" Zahra ta fadi tana murmushi.
"Assalamu Alaikum."
"Amin wa'alaikussalam,Malama Fadimatul Zahra'u".Aminu ya amsa yana kallonta.

"Na fa gaya maka bana son sunan nan ka kirani da Zahra ta mana". Ta fadi tana shagwabe fuska domin tana kaunar Aminu.

"Tuba nake Zahra farar mace alkyabbar mata".

Murmushi ta yi tana satar kallon shi, tana jin duk duniya babu mai rabata da Aminullah. Nan suka sha hirar su ta masoya, daga bisani ya yi mata sallama ya tafi cike da kewar juna suka rabu.

              ********
WASHEGARI

"Anti Zahra lokacin makaranta ya yi fa,kiyi sauri ki shirya kada a fara taron latti".

"Banason takura Nana akan mi zaki rika damuna inace har yanzu da sauran lokaci?"

"Amma Anty zahra har yushe ki ka bar wannan karatun litattafan da baya amfanin ki da komi kika ta shi ki ka shirya?" Nana ta tambaya tana gyara hijabinta.

"Kinfa raina ni Nana,wai ni sa'ar ki ce?, ki shirya warki ki tafi idan na shirya zan biyama zainab mu wuce tare".

"Allah ya kyauta muku,yasa ku gane gaskiya,idan Gwoggo ta dawo ki ce mata na wuce."Nana ta fadi tare da barin dak'in.

Tsaki Zahra ta yi hade da gyara kwanciyarta, domin tana mutukar jin dadin karatun da take yi.

Shigowar Gwoggo gidan ya sanya ta tashi ta fara shirin islamiya.

Gwoggo ta ce"Zahra baku zuce zuwa makarantar ba, ina Nana take?"

"Cewa nayi ta wuce kada abar gidan haka nan shiyasa na tsaya jiran dawowar ki"

"Tafi can kin dai tsaya latsar wayarta ki,ina ce gidan Ladi kuke kai min makullin,shiyasa sai da na fara shiga gidan ta ce baku kawo ba, Allah ya shirye ki kiyi maza don nasan yanzu an fara taron latti."

Da fitar ta gidan su Zainab ta wuce kamar kullum kwance ta iskota tana sana'arta ta,fahintar bata ji shigowar ta bane yasa ta fisge littafin da ta ke karantawa,zabura ta yi sannan cikin mamaki tace "Zahra yaushe kika shigo?"

"Yanzun nan mana ai naga alamun ba kiji shigowata ba ne da gani wannan littafin ya yi ba karya".

"Wallahi ko kamar kinsani jarumin cikin nan yana wasa da nera son ranshi,kai Allah ya kai damo ga harawa ko beci ba yai birgima,yau an yi posting?".

"Eh anyi sabo kai wallahi Prince Aryan na kasheni sosai  dinnan fa".

Dariya Zainab ta kwashe da ita sannan ta ce "kedai bari, bani na karanta".

Ta mika mata wayar kasancewar ita Zainab bata da babbar waya, yasa idan Zahra ta karanta sai ta bata wayar ita kuma Zainab ta ba Zahra Littafi, a haka suke gudanar da rayuwar su.

Yauma bata bar gidan ba sai shidda sannan ta yi ma Zainab sallama ta kama hanyar islamiyar su.

Kamar kullum Nana na isowa kusa da ita ta hau fadan ta barta tana jiranta,ita kuma ta fara bata hakuri suka wuce gida.

2018

BAHAGON TUNANIWhere stories live. Discover now