***
Ba mai shago ba harta Napep ɗinda ta hau ta koma gida saida suka kaura dashi. Baida canji yace taje ta samo nan ta zage ubansa kuma tace taci banza karfin sa ya kwace mai, sai tayi tafiyar ta, Allah ya isa ya bita dashi yana gunguni. Lantana ta gani a bakin kofa tana gogewa. Babu abinda ya dameta tasa takalmi tayi wucewarta duk ta ɓata. Daki ta je tayi zaman dirshan bakin kofa. Anan ta buɗe sabon babin kuka.Yi takeyi tana shesheƙa. Har muryanta yana son dishewa 'na bani na lalace' ta rinka maimaitawa. Tana yi tana tafa hannunta tareda dafa kanta. Tashin hankali take gani, gatada ciki kuma Isi ya gudu. Tabbas abinda ya faru da Haske zai faru da ita. Yanzu tayi dana sanin da batayi saurin cewa a kore Haske ba kila itama da an yafe mata. Ammi ce taga shiganta kuma tabbas abu na damunta.
Ammi mace mai san yaranta sosai bata san taga bacin ransu. Musamman ma Fijr duk tafi shiga ranta. Fijr na kama da kakansu na Misra sosai dan duk family din dakyar a samu wanda ya ɗareta ta fannin kyan fuska. Kawai dai tanada uban girma ne kamar mutanen farko. Gashi muryanta a sama yake kamar an kunna injin markaɗe, ba'a iya sirri da ita yanzu zata tona tanayi tana kallon wanda ake maganar sa. Gashi bata kama jikinta tayita saɓar saɓar jiki yana rawa. Sannan ko bra mai kyau masu karfi bata sawa tunda tanada dukiyar Fulani mai yawa. Haka zakaga kirjinta kamar an rungumo agwagi.
Tura kofa Ammi tayi sai taji kamar da mutum bakin kofan, nan ta sake yi wanda saida Fijr ta motsa. Ita kuma saita juya domin taga waye kafin ta watsa ashar. Ammi ta gani saita miƙe tsaye domin ta shiga. Gaban Ammi yayi mummunan faɗuwa saboda bazata tuna randa taga hawayen Fijr ba. Sai dai ta saka ka kuka amma wane mutum. Wannan shi ne abin mamaki wai ciyawa da cin doki.
"Fijr dear ! Meya faru halan? Wani ya mutu ne?" ta watso mata. Karkata baki Fijr tayi ba tace komai ba. Yadda ta tona ma Ammi asiri akan Haske tana tsoron karta tona mata yanzu. Gwara tayi gum da bakinta. "Lafiya lau Ammi kaina ke ciwo"
"Ke kam wani irin ciwo ne wannan harda kuka?"
"nidai nace ki kyale ni kaina ke ciwo" ta faɗa
"Allah ya kiyaye, bari Lantana ta kawo maki abinci da panadol"
"Uhmm hmmm"
Ranar gabadaya Ammi batada walwala, yadda taga Fijr cikin damuwa duk taji babu dadi. Tabbas Fijr tana cikin matsala amma ai ita ce mum dinta. Zata iya mata komai a duniya.Kashegari Fijr kafin 8 tabar gida. Maternity clinic taje inda ta saba zuwa. Nan ta rinka roƙan Doctor da Allah da Annabi ya cire mata cikin ko nawa ne zata bashi. Shi kam yace bazai iya ba tunda dai yasan zata iya mutuwa kuma bai so tayi hannunsa. Daga nan ya tambaya cikin wata nawa ne? Narai narai tayi saboda bata sani ba.
Ta riga ta saba daukar ciki alamu taji kawai kuma kwanan nan. Anan ya gwadata sai aka ga watan cikin biyar. Dayake tanada jiki baya nunawa kamar tumbi yake. Tabbas bataga baƙonta na wata ba amma kuma tunda taga suna amfani da kwaroran roba wanda bokan bature ya kera bata kawo wani tunani ba. Dama chan basa amfani dashi sai yanzu.
Anan ta ci kwalarsa tana jijiga shi tana cewa 'Karya ne! Karya ne! Karya ne dan bakwal uba!' sai kuma ta sake shi tareda zubewa ƙasa tana kuka, saida ta kusan lankwasa masa kujera tana bori. security ya kira domin su taya shi rakata waje kuma karsu kara bari ta shiga mashi asibiti. Haka ta fita tanata zage zage kamar sabon hauka.
Ammi Hadiza bata gida sanda ta koma, Lantana daga nesa ta hangeta ta boye saboda ta lura kanta yana touching. Daki taje tayita kuka, a ranar tayi kukan da bata taɓa irinsa ba. Gashi sai ke war Isi takeyi. Hotonsa tasa a gaba tana kallo tana shafawa tareda sumbatan screen din Wayan. "Come to me my darling, I promise to behave" tace. Sanda Ammi ta dawo Lantana ta sheda mata Fijr na gidan, a wannan yanayin ta riske ta.
"Wallahi sai kin gaya min meke damun ki" tace a haslace. Kuka Fijr ta cigaba dashi, tasan ta kusan girban abinda ta shuka. Daddy ma yafi bata tausayi zata bata mashi suna a gari. "Ammi ki yafe min... Dan Allah" tace cikin kuka. Dama Ammi tanata neman fada, da sauri ta rungume Fijr tana shafa mata kai tareda buga mata baya cikin kulawa.
YOU ARE READING
Hasken Lantarki (Completed)
RomanceDan mutum yana maka wasa da dariya kuma ya nuna akwai aminci tsakanin ku ba lallai bane yana kaunar ka. Makashinka yana tare da kai, da dan gari ake cin gari... Ku biyo ni