Zeenat yar jarida 95

641 41 3
                                    

.🎗🏵🎗                         🌱🌱
            *ZEENAT YAR JARIDA*
  🌱🌱                              🎗🏵🎗
 

'''WRITTEN BY ✍🏼'''
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
                  &
     *NABILANCY LOVE*

*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

     _Sorry muna Mai Baku hakuri na jinmu shuru da kukai, Hakan ya farune sakamakon rashin zama da bamayi always muna busy ne...._ ONE LOVE DEARIES😍💋
  
     _In kunga erros plz karka damu banyi editing ba saboda sauri da nakeyi_

                     *PAGE 95*

Zeenat da asma'u fitowa daga gidan sukai, Asmau ta kalla Zeenat tace amaryanmu, Zeenat tai smiling tafiya suke Basu tsaya ko Ina ba se gidan me gyaran amare

    Suna shiga sukaga mutane cike da gidan, Ko wacce da bukatar da tazo nema, wasu jikasu za'ai da kayan ni'ima wasu dilka etc dai

    Hajiya me gyaran ta kallesu tace" Sannunku da zuwa sukace yauwa, Nan sukai mata bayanin komai yanda sukeso, tace bakomai angama cikin kankanin lokaci Ta fara gyarata, Yamma nayi Asmau tai gida tace gobe Zata dawo

     Bangaren Ango kuwa ba zama se zirga zirga suke Dan su tabbatar abun da suka tsara yayi, Dakin da amarya  Zata zauna kuwa Baku gani ba kamar ba a unguwar yake ba dan wasu tsadaddun Kaya da akasa
 
              Bayan kwana biyu

Ahmad duk ya matsu yaga amaryanshi, 2days da be gantaba har wani Rama yayi, Ga phone dinta be shiga, Zuwa gidan su Asmau yayi yace" Wai Ina saheebanshi? Asmau tace Kai sarkin zalama Kai da ga ganta se gobe ai, Kai da gidanka za'a kaita saima ka Gaji da ganinta shine zakazo wani nemanta

   Dan Sosa keya yayi dan yasan asma'u akwai mayyance yace" lol Sorry bafa wani Abu bane, Ciro kudi yayi ya Bata yace ta kaimata ko zatai wani abun dashi, Hannu tasa ta amsa ta kirga taga 50K tace" ok zan Bata

   Har ya tafi ya juyu yace" please tell her I miss her sosai, Murmushi tayi tace" to Romeo zan fada mata, Shima smiling yayi ya shigq motarshi ya nufa gida

Yana tafiya Asmau takai mata sakon tace kawai kisa a account tunda bama bukatar komai for now zeenat tace yeah ki ajiye a wajenki by Monday Sai kije ki samun

_Washe Gari ran daurin aure_

An daura auren Zeenat da Ahmad Alhamdulillah, kowa yayi murna Yan Uwa da abokan arziki sun Suna musu Soyayya

Yan uwan baban Zeenat kuwa da sukaga yanda tai kyau se gulmace gulmace sukeyi Wai an bar yarinya ta zama yar bariki Dan sunga tayi kyau lol su Kuma Yan kauyena

    Ba wasu frnds gareta Dan haka ba gayya tayi ba Amma Asma'u ta gayyato nata Friends din Dan za'ai wani event a Millennium Hall by 4 PM

Nan abokan Ango suka fara daukan kawayen amarya har hall

      Kabir kuwa shi ya dauka Ahmad da Zeenat se Asma'u kawai a cikin motar,

  Ba Ahmad kadai ba kowa da yaga Zeenat ya yaba da kyan da tayi, Ahmad kuwa da ya zura mata Ido kamar zai cinyeta, kasa hakura yayi a cikin motor ya janyota jikinshi yai mata kiss  Yace" wow you look so beautiful, Kokarin kwace kanta tai Dan tasan Basu kadai bane, lol yace sannan ya saketa Amma Hannunshi rike da nata gam Se wani kallon I wanna be with you take mata

Itadai sedai tace uhm ko ta kauda idonta

****
Sun Isa hall din iya haduwa yayi ga decoration da akai Irin kayan kawayen amarya red and Ash wajen ya hadu sosai

Nan aka fara gudanar da program, Kawayen asmau se gulma suke Wai lalle wannan yarinyar tayi Dace Ji yanda ya kashe mata kudi Kuma da alama Sonta yakeyi sosai, Suma sukai fatan Allah ya kawo Masu Mr Right me sonsu Wanda zai kashe Masu kudi lol

   Nan MC yace" yanason ganin Amarya da Ango a saman stage din hall din, Durkusawa tayi Asmau wlhi banason zuwa, Asmau tace ai baki isaba  wlhi Nan ta rike mata hannu takaita saman, Ango kuwa shi already har yahau

   Nan MC yace" to ga amarya dai ga Ango yanzu zaman amana da hakuri za'ai duk wani Soyayya ya biyo bayan wannan Ahmad wani kashe mata Ido yayi tai sauri ta juyar dakanta, Yana Bata mamaki sosai yanda be boye soyayyarshi ko a inane

   MC ya kara da cewa to yanzu su gwada ma junansu Irin Soyayyan da suke ma junansu, Nan aka sa wani Wakar *Umar M Shariff* _na duk Wanda be murna yayi baya, Amarya kyakkyawace Amarya.._

   Sautin na tafiya ahankali, Ga hall din yadau speakers kota ina sauti na tashi, Nan ya janyo hannunta Wai su rawa tace" a a ya langwabe mata Kai ya rike hannunta Gam suka fara Dan juyu, Nan hall din ya rikeda da ihu Wai Angon beda kunya lol...sunsha rawa itakam Zeenat se nokewa Takeyi Dan me kunyace..

Anyi biki Alhamdulillah Dan komai daidai abinci Kam sedai bakaje ba, AHMAD kuwa duk ya kosa a kawomai amaryanshi

    Family dinshi ma Suna ganin Zeenat sukaji ta kwanta musu arai, Suna Sonta gaskiya

   Angana an dawo gida Nan aka fara Shiryea Shiryen Kai amarya, asma'u ta Miko mata wasu kaya tace ta chanza, Tasa atamfa sun amsa jikinta tsaf, Nan aka kaita manyanta sukai mata fada, Tayi kuka sosai sosai

Mamanta ma tayi kuka Dan dai aure be ba bazataso ta rabu da Yar tilon yarta ba, Nan aka mata fada yanda ya Dace Sannan aka dauketa sai gidan Mijinta Ahmad

    Suna shiga Kawayen Asma'u da Yan Uwa da sukaga gidan Sunyi mamaki, Dan ya tsaru sosai, dangin babanta Kuma basuso haka ba, Masu dai farin ciki nayi Yan bakin ciki nayi

Nan fa Yan mata ganin gidan ya hadu kowa ya fara allaumma arzuquni gida me kyau wa miji me bada kudi, wa tankameman gida...etc Lol


_Duk Masu neman mazan auren both Yan mata da zaurawa ya Allah ka basu_,.... _Allah ya biyawa kowa bukatunsa na alheri..._

*Don't forget to vote and comments please*


Zee & Nab💋

ZEENAT YAR JARIDADonde viven las historias. Descúbrelo ahora