101-105

687 57 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*




DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

PAGE *101-105*.

Suna gama shirin su bayan sunyi sallar magariba suka, sauka kasa. Mami zaune akan sallaya tana jan carbi, suka karasa gefen ta.

*Najwa* ta ce,
"Mami sannu da gida ya aiki?"

Mami ta dubi *Najwa* cikin fuska me nuna so da kulawa tace,
"Lafiya *Najwa* ya karatun?"

"Alhamdulilah!"
"Allah taimaka."

"Ameen Mami."

*Najwa* ce ta kalli Basma ta ce,
"Basma Fara kawon haddar ki."

"To Adda!"
Basma ta fada tana gyaran muryar ta, karatun ta fara cikin kwarewa da fitar da ko wacce harafi da hakkin sa. Suratul Nisa'i take kawo mata hadda.

Sai da ta kawo mata shafi uku sannan ta tsaya.

Mami ta dubi Basma ta ce,
"Masha Allah Basma, kamar bake kika karanta ba. Allah kara basira"

"Ameen Mamai!"
Suka hada baki suka fada

" *Najwa* a ko da yaushe zaki ga nafi miki magana akan fikihu, ba kome yasa nake miki ba sai dan inganta rayuwar ki, dan sai da tsarki da ibada rayuwa rake yiyuwa. Kuma haka nan ibada bata yiyuwa sai da tsarki da ilimin fikihu."

*Najwa* tayi kasa da kai, ta ce,
"Haka ne Mami. Shi daman fikihu ai ilimin rayuwa ne. Duk abubuwan mu na yau da kullum na ibada yana  cikin sa. Allah abamu sani akan sa da kuma amfani dashi."

"Ameen! Shin daga ina ake kawar da Najasa?"
Mami ta tambayi *Najwa*

"Ana kawar da Najasa daga waje 3,
1. Daga jiki, Allah madaukakin sarki yana cewa, "in kun kasance masu janaba kuyu tsarka."

2. Daga Jikin Tufafi. Allah Mabuwayi da daukaka yace, "Tufafin ka, ka tsarkake shi."
Akwai hadisin da aka rawaito daga Subarata Allah kara masa yadda, ya ce, "Wani mutum ya tambayi. Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi, ya ce,
"Shin ze iya sallah da tufafin da yajewa iyalin sa?"
Anbabi (SAW) Yace, "Eh! se dai yaga, wani abu na najasa shine ze wanke."
Ibn Maja ne ya rawaito.

3. Daga wajen da za'ayi Sallah. Allah mabuwayi da daukaka, Yana cewa,
"Munyi alkawari zuwa ga Annabi. ibrahim, da Annabi Isma'il, dasu tsarkake dakin Allah, dan masu dawafi, da masu ittikafi, da masu ruku'i da sujada.

Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi yaga wani balaraben kauye, yana fitsari a massalaci, sai ya ce da sahabai su kyale shi! Har se da ya gama fitsarin sannan ya ce, a kawo masa ruwa. Sai ya kwara."

*Najwa* ta kalli Mami ta ce,
"Mami daga waje ukun nan ake kawar da Najasa."

Mami ta jinjina kai, dai dai lokacin sukajiyo horn din motar Dady.

Da gudu Basma ta fice, tana cewa,
"Dady oyoyo! Dady Oyoyo!"

Yana ganin ta ya Bude hannu ya daga ta sama.

Dariya take, tana farin cikin dawowar Mahaifin nata.

*Najwa* ce, ta karaso wajen ta ce,
"Dady barka da dawowa."

"Yauwqh Maman ya gida!"
"Lafiya Alhamdulilah. Ya aiki."

Dady yace,
"Alhamdulilah!"

Ta karbi jakar hannun sa tayi wajen Hamma Salim.

Ta ce,
"Hammana kun dawo lafiya?"

Murmua
shi Hamma Salim yayi mata, ya ce,
"Lafiya lou kanwata."

Fuska ta dan hade, ta ce,
"Hamma gashi har ka kusa tafiya, amman ko zama bama yi."

Dariya yayi, ya ce,
"Yau kuma darun ne ya tashi. ai nazata yanzu kin girma."

Murmushi tayi, ta ce,
"Ina maka magana kana kawon wata magana ko?"

Murmushi Hamma Salim yayi, ya ce,
"Yi Hakuri yar uwata, kar ki manta fa sauran shekara daya na gama na dawo gaba daya."

"Shikenan!"
Ta fada dai dai lokacin da suka shiga m Falon gidan.

Mami ta mike, tana musu sannu da zuwa.

Daining sukayi dan yau sunyi dare a waje.

Abinci suka ci sannan kowa yayi dakin sa dan yin bacci.

Kamar ko da yaushe sai da ta saka Basma tayo alwala sannan ta zo ta kwanta tana me ambaton sunan Allah.

Sai da taga ta gama ta fara bacci sannan ta mike tayo wanka ta dauro alwala ta zauna karatun alkur'ani.

Ba ita ta kwanta ba sai karfe sha daya. Inda karfe biyu nayi ta mike tayo alwala tayi sallah. Ta jima tana addu'a sanna ta kuma kan gado. Karfe biyar da rabi ta tashi ta tashi kanwar ta sukai raka'atanil fijir sanna suke sallar asuba.

Zikirin Safiya sukai sanan suka fara, Karatun kur'ani, shida da rabi *Najwa* ta hadawa Basma ruwan wanka, ita kuma tayi kasa ta daura musu abin karin su.

Tana gamawa ta jere sannan ta hadawa Basma nata. Sama ta haye, ta karasa shirya Basma sannan ita ma ta shige ban daki dan yin wanka.



Najib ne zaune a dakin sa, yana tunanin nasa da ya saba.

Karar wayar sa ne ya dawo dashi cikin hayyacin sa, yana dubawa yaga Khaleel ne, dauka yayi. Ya ce,

"Dan Uwa ya akayi ne?"

Khaleel ya ce,
"Eh nace ka dai shirya ko?"

Murmushi yayi, ya ce,
"Eh kai nake jira."

"To gani nan zuwa."
wayar ya ajiye ya mike ya shiga bandakin sa, dan yin wanka.

Ya jima a ban dakin sannan ya fito ya shirya cikin wata milk din shadda wacce akai mata aiki da ruwan kasar zare.

Yar ciki da babbar riga sai ruwan kasar takalmi da hular kan sa ruwan madara da adon ruwan kasa.

Yayi kyau sosai kai kace, shine ango sai tashin kamshi yake, farin tabaron sa ya. Dauka ya saka a idon sa.

Take ya kara haskawa ya kuma wani kwarjini.

Masha Allah Najib ba dai kyau ba. Duk inda kyau yake, yakai dan cikaken namiji ne me kamala da kwarji.

Yana shirin zama sai ga shigowar Khallel nan. Kallon sa ya tsayayi, ya ce,
"Abokina ka yi kyau, kar fa kafi ango yin kyau "

Harara sa Najib yayi, ya ce,
"To zage ni."

Dariya Khaleel yayi, ya ce,
"Malam bamu da lokaci kalli fa har mun makara abin karfe takwas yanzu karfe tara. Kuma kasan no african time."

Najib ya ce,
"Bro ai kai ka makarar damu. Dan a shirye ka ganni. Malam shige muje."

Suka fice, Najib na tsokanar sa, kyan ta, Khadija taga kwalliyar sa.

Dakin Mami suka je suka mata sallama sannan suka fice a motar Najib

Summy ana gefe anci kwalliya cikin wani golding din material sai maroon din head da ta saka. Tayi kyau sosai, an zubo da gashi ta gadon baya.

Wajen ya cika da manyan yan mata da samari daga wannan tace tafi wannan sai wacan tace tafi wacan.

Amman Summy na data daga cikin yan matan da sukafi kowa kyau a wajen.

Dan Samari da yawa sai kai mata hari suke amman sam ko kallo basu isheta ta ba,

Amarya da Ango kuwa suna wajen da aka tanadar musu a zaune, sunyi kyau, cikin wani farin material me adon baki! Shi kuma Angon yasa bakar shadda.

Ba karamin kyau suka yi ba.

A hanya ma suna tafiya suna hira abin su, har suka karasa Wajen bikin.

*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now