139

801 60 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online WRITERS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH DAUKAKAKI YASA KI GAMA DA DUNIYA LAFIYA.*

*REALLY LOVE U ANTY NA*

*THANKS FOR UR LOVE ND SUPPORTING*

*PAGE*
*139*

*Maman Ihsan. Nagode da kulawar ki. Nagpde Allah bar zumunci.

Shi ya bude mata mota ta shiga. Sai da suka hau titi sannan ta kalle shi, ta ce,
"Hamma"

Kallon ta yayi, ya amsa da
"Na'am Baby."

"Hamma dan Allah baka da lafiya ne?"
Murmushi yayi, ya ce,

"Lafiya ta lou."
"Hamma dan Allah ka fadan gaskiya. Hankalina bazai kwanta ba in har baka fadan ba."

"Kar ki damu. Wata yar matsala ce kadan."
"Hamma matsala kadan fa kace, abinda duk naga ka fita a haiyyacin ka."

"Bari anjima zan fada miki."
"Toh!"

"A ina za'ayi ne."
"A cikin Shoprite ne."

Tayi shiru bata kara magana ba. Sai shi da yake bata labari.

Har suka karasa ya fito ya bude mata mazaunin ta.

Fitowa tayi, suka jera. Gaskiya ba karamin dacewa sukai da juna ba.

Sunyi kyau kowa ya gansu zai tsammanin ango da amarya ne.

Suna shiga Khadija tazo ta kamo Najwa. Murmushi Najwa ta saki suna gaisawa.

Khaleel ne ya karaso gun shima suka gaisa.
"Dady da Mummy kufa ake jira kawai."

Khaleel ya fada musu, Dariya Najib yake ya ce,
"Muje toh."

Lil N na hango Najwa ya taho a guje yana cewa,
"Mummy na. Mummy nah."

Kayan hannun ta, ta mikewa Khadiya ta rumgumoshi.

"Mummy na ina yini?"
Ta amsa da
"Lafiya."

"Happy Birthday boy na."
"Tnx u Mummy nah."

Hannun ta ya kamo suka karasa cikin wajen.

Tare suka yanka cake ya saka wa Dadyn sa da Najib. Sannan yasawa Najwa da Mamin sa.

Sun sha hotuna inda yara sukai rawa. An ci ansha an bawa yara gift din kayan wasa.

Shima ya samu kyaututtuka. Sai magariba suka tafi gida gaba dayan su.

A can ma wani partyn ne su biyar sukayi shi.

Duk inda Najwa tayi Najib yana haska ta da waya yana mata vedio.

Banda hotunan da ya sukayi da wanda ya dinga daukar ta.

A nan ne ya bawa Lil N mukkulin wani katon store daya bude masa.

Khaleel da Khadija sunyi murna sai godiya suke haka ma Najwa.

Daga nan store din sukaje. Katon store ne wanda aka zuba masa kaya komai akwai a cikin sa.

Daga nan gida sukai. Su Najib ma suka yi hanyar gida.

Tin a hanya, take tambayar sa ya fada mata abinda yace zai fada mata.

Haka ya ce sai sunje gida wai duk dan ta manta ne fa.

Ai kuwa suna zuwa gida ta ce,
"Hamma baka fada min ba."

Kallon ta yayi, ya ce,
"Kawai auren ki nake son yi, kuma time din da akasa yayi yawa gaskiya zan fadawa Dady wani satin ayi komai a gama."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now