01-03

498 17 0
                                    

♠♠♠♠♠♠©°•
LAIFIN SU WAYE
♠♠♠♠♠♠®°•
*It's based on true life story*

Story & written by :faridat Husain mshelia (momy khairy).

*edited by:malam shafee'u dan gatan rasulullah (SAW)!*

*GODIYA*

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangijin sammai da qassai daya ßani ikon rubuta taqaitaccen labarin nan domin Neman kawo gyara acikin wannan al'umma tamu dangane da Abunda Yake yawan Aukuwa Yau da kullum Na 6arna Acikinta Kuma dama Manzon Allah (SAW) Yace Wanda Yaga Wani Abin 'kyama daga Gareku To Yacanza shi Da hannunsa idan bai sami iko ba to da Harshensa...... (Sahih)

Tsira, yarda, aminci, martaba, Daraja, Wasila, fadhila, su qara tabbata ga masoyin mu mai ceton mu Muhammadur-Rasulullah (SAW), da iyalan gidansa tsarkãkã da sahabbansa yardaddun Allah Da Manyan ßayin Allah Salihai Da masu bibiyarsu Har Yazuwa Ranar sakamako.

ßismillāhir-Rahmãnir-Rahīm.

01

"Mtwss!! Bariki baraka ? wallahi bariki batayi ba"

ta share hawayen dake ambaliya a fuskarta Wanda tsananin rudani da Tashin hankalin Da take ciki yasa ta gagara tsaida su, gefen zaninta ta kwanto Wanda yayi yaga-yaga kamar an fiddashi daga bakin kura dan tsabar dauda da jemewa da yayi ta share majinar dake hancinta, wacce aka Kira da baraka ta yamutsa fuskarta! 😙 cike da kyankyani ta kawar da fuskarta ga barin kallon talatu qawarta.

"Bariki mai take haifar ma 'ya mace baraka da har kike sha'awar yinta?*! "Baraka Wanne Irin zane ne wanda Ni talatu ban daura ba a jikina ?! "Wadanne irin kudade ne Wadanda asusun banki na basu gani ba ? Saboda Yawan kudin Dake cikin Bankin nawa ma ko kasuwanci Bãnãyi Tunani Bazasu 'Kare ba!

LAIFINSU WAYE?Where stories live. Discover now