31-35

42 2 0
                                    

31

Da haka muka fice daga gidan muka afka cikin hadaddadiyar motar shi zuwa gidan shi dake cikin garin kaduna garin gwamna.

gida ne nagani na fada Wanda ya mallaki dukkannin wani Abu na more rayuwa wanka muka gabatar tare da duraa ma cikin mu abincin daya aika aka saya mana a gurin cin abinci,

Sai da mukayi qat! sannan muka afka cikin dulmiyayyar hanyar da bata bullewa (alfasha)

nan da nan shaidan ya dinga yi mana famfo har dukkannin mu muka samu biyan buqata.

soyayyar zee ta shiga zuciyar Alhaji yusuf farat 1 Dan tunda yake mu'amala da mata bai taba jin gamsuwa kamar yanda yaji daga gareta ba duk da ya kasance manemin mata Dan shi kanshi bai San yawan adadin matan daya nema ba a rayuwar shi Dan haka zuciyar shi ya rada mishi zai auri zee-baby wacce mutanen tafa keyi mata laqabi da Talatu.

Nan ya sanar mata amma ta nunar mishi da ita Sam aure bashi ne agaban taba Dan yanda duniya keyi mata dadi a hakan bai wani damu ba suka cigaba da zama tamkar mata da miji.

(wa'iyazu billahi, Wannan Zama Ne Na keta Haddin Allah Kuma zama Ne Na fito-Na-fito da shari'ar Allah, Allah Ya hana Amma Sun tubure sai sunyi, Allah Yaganar da Duk mai Aikata irin Wannan Ameen)

Alhaji yusuf shine mutum na farko daya fara siyama zee-baby motar hawa 'yar uban su, ya kuma nemo direva ya koya mata tuqi,

account ya bude mata tare da zuba mata kudi aciki Wanda zatayi duk buqatun rayuwarta ,duk da bai rageta da komai ba hatta man shafawa da sabulun wanka shiyake siya mata

sutura a gurina kuwa hadda na banza Dan duk fitar da zamuyi saiya siyomin kayayyaki kama daga English wears, Atamfa, less, ghalila har arebian gown Ds

nan danan jikina ya mulmule Dan nagartattun abincin daya ke bani Dan duk dare Sai naci kaza da madara ko hollandia Dan yana buaqatar yaji ni'ima a tattare dani kuma alhamdulillahi ya samu.

nan na bude wani Sabon babin rayuwa na holewa Dan bani da matsalar kwabo magajiya ma mukan ziyarceta time to time muyi mata alhairi a wata kuma sun tsadance maqudan kudin da zai dinga bata Dan mallaka mishi zee da tayi.

haka ma bangaren mahaifina muna waya tare da saqon kudi danake tura mishi Dan da taimakon dayayi min yasa nayi wannan kamun.

damuwata daya a wannan lokacin duk da tarin daular danake ciki yanda Alhajina yake maseefar kishina koda wasa baiso mu'amala ta hadani dako macace balle Namiji Dan adah duk yammaci saiya daukeni a mota mun zaga gari tare da zuwa guraren shaqatawa kala-kala amma ganin yanda maza suke kawomin hari yanzu ya hana wannan nan nashiga damuwa in yaga nadameshi da maganan hakan saiya yimin gaggarumar kyauta Wanda zaisa in mance da hakan Dan alokacin ya mallakamin gidan da muke zaune Wanda ya qunshi dakunan bacci 4 da qaton falo biyu, kicin, store da garden mayalwaci.
  kamar kullum yauma ina zaune akan cinyarshi yana kallon labarai raba hankalin shi gida biyu yayi hankalin shi nagareni kuma yana ga TV qarshe dai ya janyoni jikin shi sosai tare da miqar dani zuwa cikin dakin baccin mu bayan ya kashe TV, kukan kissa na fara yi mishi jin cewar da yayi zaiyi tafiya katseena domin duba iyalan shi nan take hankalin shi ya tashi Dan aduniya in kanason ganin tashin hankalin ALHAJI yusuf to yaga zee na kuka, nan yashiga aikin rarrashinta dakyar yasamu tayi shiru a qarshe yace tunda bataso ya hakura da tafiyan amma dayar zuciyar shin na tunasar dashi nauyin iyalin shi, nuna ta amince tayi yaje amma karya Dade Dan tana da buqatar shi a kowani lokaci nan suka dinga yima juna musayar kalamai tare da zantukan tada sha'awa har suka samu biyan buqata.

dakyar suka rabu washegarin ranar ya Lula motar shi akan kwalta domin ziyartar garin shi na haihuwa wato katsina ta dikko dakin kara, kunya gareku badai tsoro ba.

ficewar shi keda wuya zee ta cancara kwalliya cikin wata doguwar Riga yadin irin mai rawa a jikin nan ya lafe ya fito da dukkannin wata sura na jikinta musamman kirjinta Wanda akayi adon roba ya tattaro na shanayenta a ciki babu Wanda zai kalleta sau 1 bai qara ba.
    nan ta cancara kwalliya mai daukan hankali dan qara gogewar datayi a bariki taja motarta na nufi wani gurin shaqatawa Dan tasamu abokin da zan huta gajiya dashi ,

LAIFINSU WAYE?Where stories live. Discover now