21-26

109 3 0
                                    

♣♣♣♣♣♣
LAIFINSU WAYE❓
♣♣♣♣♣♣
~*ιт'ѕ вαѕed on тrυe
lιғe ѕтory*~

ѕтory&ωrιттen вy:
ғαredαт нυѕαιn
мѕнelια(мoмy ĸнαιry).

edιтed вy:ѕαyyed
ѕнαғee'υ dαn gαтαn
αnnαвι(ѕ α ω).

вιѕмιllαнιr-rαнмαnιr
rαнeeм.

*Dedicated 2 my
yayancy sayeed
shafee'u dan gatan
Annabi (s a w)*

kyautar shafi gareka
umar dalha (zama na
amana 2) kayi yanda
kakeso dashi , alkhairin
Allah da albarkar shi su
tabbata a gareka da
ahalinka nagode da
karamcinka gareni

21
_____

sun 'Dan jima suna
tsaye a k
Qofar gidan su jibson
suna hon amma shiru
dan maigadin ya zaga
bayan gida,

isowar shi gurin keda
wuya yaji Wani
mahaukacin hon wanda
jibson yayi cikin jin
haushi nan take baba
maigadi ya rude da
hanzari ya wangale
musu qofar gidan ya
tura hancin Motar cikin
gidan,

Kuuuuy yaja burki tare
da dirowa ya kwala ma
baba mai gadin kira
wanda tuni yasha a
jinin jikin shi,

Maseefa jibson ya fara
yi mashi sai kace Dan
daya Haifa tare dayi
mishi kyakykyawan
Warning akan duk
wanda yazo gidannan
kar ya sake ya barshi ya
shigo koda maigidan ne
kuwa,

Cikin takunta na qasaita
da izza taqaraso gurin
nasu ta janye jibson

"haba bee (baby)
wannan ba girman ka
bane"

"A tausaya mishi mana
kodan furfuran .....Ko
kafin ta gama rufe baki
ramsy ta amshe,

Lallai zee yau kece mAi
tausaya ma tsoho?

Ta dalla mata muguwar
harara tare dayin kwafa,

Naga ko parley
(babanta) bakya
girmama wa balle
wannan da baki sanshi
ba,

"wai toh ina ruwan kine
ramsy?

ganin zasu saida hali a
tsakanIn junansu yasa
jibson surar zee-baby
tamkar wata yar tsana
yayi hanyar dakin shi da
ita,

a baya suka biyo su
suka zube cikin
tangamemen falon mai
cike da ababen more
rayuwa nan da nan
suka rikita gurin da
kida,

kamar kullum yau ma
saida sukayi tatul
sannan kowa ya dauki
baby'n shi suka shige
daki domin cigaba da
aikata alfashar da suka
saba .
Vasa ko tunanin suna
iya mutuwa acikin
wannan halin.

Zina dai Alfah-sha CE
kuma tana Daga cikin
Kaba'ira, Allah Yana
cewa

ﻭﻻ ﺗﻘﺮﺑﻮﺍ ﺍﻟﺰﻧﺎ ﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻓﺎﺣﺸﺔ
ﻭﺳﺎء ﺍﻟﺴﺒﻴﻼ

"Kuma kada Ku kusanci
zina Lallaine ita ta
kasance Alfah-sha,
kuma mummunar
Hanya ce!

(Al-isrã'i:32)

★ASIBITI★

bayan shafe tsawon
awanni likitocin da suka
rufu akan shureim
(wanda su zee-vaby
suka jiwa Mummunan
Rauni a fadansu Na
makaranta)suka yanka,
da wuya akayi nasarar
dinke Gurin,

Cikin jimami da
girmamawa mahaifin
shureim ya miqama mr.
aleeyu hannu sukayi
musafahã! dan ya
kasance dan sarkin
daya gabata (yayan
shine akan karaga
yanzu)dan labari ya iso
mishi da dumi-dumin
shi na yanda ya zamto
silar ceton ran dan shi
wanda ya fiso duk da ya
kasance kangararre
lamba 1,

Cike da girmamawa da
jajantawa mr. Aleeyu ke
kallon shi wani bangare
kuma yayi mamakin
yanda akayi dan shi ke
cikin wannan
makarantar kasancewar
shi babban alqali a
kasar nan gashi kuma
daya daga cikin jinin
sarauta Na wannan
gari,
yana cikin wannan
tunanin yaji justice
sadeeq ya katseshi da
cewa,

LAIFINSU WAYE?Where stories live. Discover now