the second encounter

3K 184 4
                                    

Duniya kowa da abunda ya dameshi, na gasgata hakan ganin yadda halayen y'an uwa uku ya sha Banban musamman Ameer wanda kowa ya shaida shi ba k'aramin magulmaci bane.
Domin ganin wasu halayen na wad'annan y'an uwa dole na garzaya na kutsa kai ciki don ganin yadda zasu karb'i bak'on d'an uwansu ( *The crazy Prince*) Suraj.

**** ****** *****

Da sallama ya shiga falon yana mai cije baki cikin nuna alamar ya takura saboda jin haushin wayar sa dake sake ringing a karo na biyu. Abubakar kad'ai ne ya amsa Sallamar yayinda Saeed da Ameer suka k'ura wa takalman kaf'an shi ido baki sake, ganin yadda suke kallon shi yasa ya dubi k'afafun nashi.

"Is that what I think it is?" Saeed ya tambaya cikin d'aga murya yayinda Ameer ya k'undume dariyar da taso kufce masa yace
"Of course it is a cow's dung!" Cikin d'aga murya yayi maganar kafin ya fece da dariya.
"Kashin shanu fa! A ina ka samo wannan kai da yau shigowar ka gari am sure ko fita baka yi ba!

Dariya Suraj yayi ya sake duban takalman karo na biyu yace

"Oh wannan wai? D'azu na taimaka wa wata shine ban sani ba na taka".

Duk'a wa yayi ya cire takalman kafin kyafta ido wata mai aiki ta d'ebe su daga wajen for cleaning , sannan ya k'arisa cikin falon ya nemi waje ya zauna suka gama gaisawa da Abubakar Saeed da Ameer kuwa hanci suka toshe tsabar neman magana hakan yasa Suraj ya k'ura musu ido, amma sai ya kai zuciya nesa ya mik'a ma Saeed hannu su gaisa. Kamar wanda aka mintsina Saeed ya mik'e tsaye ya nufi upstairs Ameer kuwa ya tuntsire da dariya ya mik'e tun kafin ma Suraj ya mik'a masa hannu su gaisa.

Haba Bro! Ka gama taimakon wata K'azama har hakan yayi sanadiyyar da ka tako poop sannan zaka mik'a masa hannu ku gaisa? Ko ni nan bazan yarda ba, tukunna ma kasan yadda tun shigowar ka kake k'arin daud'a it will be better in zaka fara freshening up kafin mu gaisa" Ameer yana isowa nan a maganar shi ya kwashi wayoyin sa ya fice yana y'ar fito.

Tuni bugun zuciyar Suraj ya sauya, idanuwan sa suka kad'a ya mik'e da zummar barin wajen zai koma side nasu though bazai ji dad'in zama chan ba saboda Oummin shi bata nan , dama chan ita kad'ai ne abokin shi wanda ke tolerating d'in shi kuma ta d'auke shi a yadda yake without a complain. Ko da yake uwa ce fa.
Har ya fara takawa ya nufi k'ofa Abubakar ya k'ira shi ganin abunda Saeed suka yi bai ji dad'i ba
"Daman ina son fita saboda yau za'a kawo kaya warehouse I will be glad in ka zo Mun fita tare daga nan zan sa wani daga cikin servants ya nuna maka gari am sure you'll like it". Murmushi Suraj yayi gami da jinjina kai ya juya ya bar falon har kamar zai yi tuntub'e ,ko mota bai jira ba balle takalman shi da aka tafi cleaning, duk saurin da yake driver yana bin bayan shi da motar duk hadimai se kallon shi suke yadda yake cikin b'acin rai, yawancin hadiman sun fi alak'anta fushin Suraj da su Ameer dan babu wanda bai san halin su ba.

Abubakar yana tsaye daga tall French window dake falon yana kallon yadda fushin Suraj ya bayyana k'arara har ya bar harabar gidan ya nufi nasu side d'in.

Duk gaisuwar da masu aikin gidan ke masa bai ko kula d'aya daga cikin su ba ya nufi k'ofa yayinda cikin zafin nama wani security ya bud'e masa k'ofa nan ma ya shige rai a b'ace kai tsaye Upstairs ya nufa yana cire buttons d'in rigar shi ,falo zuwa falo corridor to corridor har ya isa flat nashi , nan yake zama duk lokacin da yazo Belel. Jefa rigar yayi kan gado ya fad'a bayi. Ya dad'e kafin ya fito inda ya riske akwatin sa ajiye da alama yanzu aka shigo da shi, nan take ya janyo ya d'auki kayan da zai sa sannan ya kimtsa kayan a wardrobe. Farar shirt ya saka k'irar lacoste da bak'in Armani jean ya feshe jikin shi da turare Mai ƙamahin gaske da sanyaya zuciya sannan ya saka wani black and white snicker ƙirar Balenciaga a k'afar sa wanda ya dace da kayan jikin shi. Camerar shi ya d'auka da waya ya fice daga d'akin ya nufi downstairs ,ganin babu kowa wajen yasa ya fice waje , ko da driver ya hango shi sai ya tuk'a motar ya nufi inda yake.

"Take a day off bani key ni kad'ai nake son fita I want to be alone all by myself".
Driver na jin haka yace

"but your highness yau shekaru biyar fa rabon ka da garin nan da de ka bari na kai ka kaga gari na yau kad'ai".

Suraj bai saurare shi ba ma yayi shigewar sa mota ya ja kai tsaye ya nufi hanyar main gate wanda zata sada shi da cikin garin Belel......

******. *******

B'angaren Laila kuwa tashin su daga bakin ruwa gari suka nufa sun dade basu isa ba saboda wasannin da sukayi ta yi har lokaci ya k'ure yamma ta soma yi gari ya yi sanyi. inda ake saye da sayarwa suka nufa, wuri ne mai d'aukar hankali, ga cikowar mutane kowa da abunda ya kawo shi, da gudu suka nufi wajen da ake sayar da tsuntsaye iri daban daban a keji sautukan da suke yi gwanin ban sha'awa hakan yasa Laila Lumshe idanuwa, a hankali murmushin sa yake zuwa mata, kyakkyawan fuskar sa ma'abociyar kyau ,ganin bata da niyyar farfad'o wa daga mafarkin da ta shiga yasa Zubaina ta buka mata duka a gadon baya, har saida ta razana hakan yasa suka fara guje guje su buge wancan su hankad'e Wannan cike da nishadi.....

Motar sa yayi parking daidai kasuwar garin wanda ya kasance waje ne mai ban sha'awa cike da koren ciyawa kowa ya kafa y'ar rumfar sa yana Sana'a, maza da mata kowa buzy ,camerar shi ya d'auko ya kutsa kai yana ta d'aukar hotuna yana Murmushi ,wasu kyawawan tsuntsaye ya hango a keji ya yi snapping da camera sannan yaci gaba da d'auke d'auke hotuna bai ankara ba yaji an bankad'e shi har saida suka zube a k'asa daga shi har wanda ta buge shin ,gaba d'aya wajen kallo ya koma kansu wasu da suka san shi suna fad'in
"Wannan ai Yariman mu ne wanda yake ƙasar waje".........

XOXO 💋

Wannan littafin ya zama paid story GA mai son full story ku garzaya link dake ƙasa Domin mallakar naku copy d'in in PDF format nagode DA ƙauna

https://selar.co/Ymkyy

Or chat me up on my what'sapp
At 08160354469

ƳAR MAKIYAYAWhere stories live. Discover now