1

145 5 0
                                    

FATIMA TA GARBA

Wattpad@neerat_lurv

*Daga Alqalamin✍*

*NEERATLURV😍*

      *Tare Da*

*ABDUL AZIZU AAJ*

      *Happy new year we are here wishing all brothers and sisters a maveleous and wonderful new year may Allah SWT fulfilled all our wishes*

  *Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 01-5*

  ************

    Yana shigowa farfajiyar falon gidan. Ya tarar da Hajiya wato Mamar Garba a tsakiyar falon tana zaune tayi tagumi, ya shigo a hankali tare da yin sallama, ta dago kanta cikin fara’a ta amsa masa, amma da ganinta kasan akwai damuwa atattare da ita, cikin ladabi Mudassir ya durkusa ya gaisheta ta amsa, sannan ya dan dudduba falon bai ga abokinsa Garba ba, sai yace da Hajiya “Hajiya ina Garba yake?” sai ta dan tabe baki tare da yin ajiyar zuciya tace “wallahi kai dai Mudassir har yanzu ban samu Garba ya fito ba, kullum acikin daki yake, abinci ma idan na kaimasa baya ci” cikin damuwa Mudassir yace “yanzu shi Garba har yanzu bai cire wannan abin a zuciyarsa ba, so yake tunani ya janyo masa matsala” ba tare da ya jira Hajiya tace wani abu ba, ya tashi tsaye tare da cewa “Hajiya bara na shiga daga ciki nagani, kinga sallar Juma’a ce nazo muje” sai Hajiya tace “hakan ma yafi, yaje yayi sallar ko zai samu walwala” Mudassir bai ce komai ba, ya nufi dakin Garba.
Yana shiga dakin Garba, yayi sallama amma ba’a amsa masa ba, a kwance saman gado ya hango Garba, a hankali ya doshi wurin Garba tare da kallon dakinsa wanda ya zagaye da hotunan Fatima. Dakin Garba babu wani hoto ko wani abu a bangon dakin face zanen Art na hoton Fatima da kuma rubutun sunanta, abin yayi matukar baiwa Mudassir mamaki saboda baisan abokinsa Garba ya iya zane ba kuma yasan Garba ya daina fita waje ballai har ya bayar ayimasa zanen, “to idan ma ya fita ta yaya zai basuwa ayi masa zanen Fatima bayan bayada hotonta ballai a duba azana masa” wannan maganar ita Mudassir yayi alokacin da yake tsaye yana nazari akan zanen Fatima da ya gani a dakin abokinsa.
Bayan ya karasa wurin Garba cikin mamaki ya rinka kiran sunan Garba yana cewa “Garba! Garba!! Garba!!! Tashi muje masallaci lokacin Juma’a ya karaso” amma sam Garba ko motsawa bai yi ba. Mudassir yayita kiran sunan Garba amma bai waigo shi ba, can sai Mudassir ya bugi kafafunsa tare da cewa “Garba nasan fa kana jina kyaleni ne kayi kawai, amma ba bacci kake ba” a lokacin Garba ya jiyo cikin sanyin jiki tare da duban Mudassir, sannan yace “hakane ina jinka, sai dai Allah ne bai bani ikon amsa maka ba, amma kayi hakuri” Mudassir yace “ya za’ayi ka amsamin, tunda kana can kana tunani marar amfani, kaga babu lokacin wasu magangannu, kawai ka tashi ka shirya muje zuwa masallaci” sai Garba yace “kaje zan iskoka” “Ban yarda ba, ka tashi kaje kayi wanka ka shirya ina nan ina jiranka” cikin rashin karfin jiki Garba ya tashi yaje yayi wanka  ya shirya, sannan yazo wurin Mudassir suka tafi masallaci.
WAYE GARBA?
Garba Saurayi ne mai kimanin Shekaru Talatin (30), wanda ya taso cikin gata da jin dadi, yayi shekarunsa a baya cikin jin dadi da kwanciyar hankali babu abinda yake damunsa. Garba bashi kadai mahaifansa suka Haifa ba, yanada kanne biyu kuma duk Maza, amma mahaifiyarsa tafi sonsa sakamakon shi ne babba, Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa. Acikin kwanakin nan da suka gabata, Garba yayi karo da wata diya mai ban sha’awa wacce ta sace zuciyarsa, sanadin wannan yarinya Garba ya samu sauyin rayuwa, ya shiga wani hali wanda bai saba ba. Dukkanin hankalinsa da tunaninsa gami da nutsuwarsa sunyi bankwana da gangar jikinsa, ya dawo tamkar zuciyarsa bata taba sanin wani abu da ake kira farin ciki ba. Mudassir shi ne babban abokin Garba wanda Garba bayada kamarsa shima bayada kamar Garba. Abubuwa da dama sun faru sanadin haduwar Garba da Fatima wadanda suka  yi sanadin tarwatsewar farin cikin su. Muje labari ….
Bayan sun dawo daga masallaci Garba bai tsaya a falo ba ya zarce cikin daki, kafin ya shiga mahaifiyarsa ta dakatar dashi tace “Garba yanzun ma daki zaka koma? Bazaka tsaya kayi hira da abokinka ba, kuci abinci?” sai Garba ya dubi Mudassir, sannan ya dan yatsune fuska yace “Hajiya bana jin karfin jikina, abinci kuma ko wanda kika kai dazu ban samu damar ci ba” bai jira me Hajiya zata sake fada ba, ya zarce cikin daki jikinsa a sanyaye.
Mudassir kallonsa kaawai yayi ya kada kai sannan ya samu wuri ya zauna. Bayan Mudassir ya zauna shida Hajiya, sai Haajiya ta dubi Mudassir tace “Mudassir yanzu miye mafita, kafi kowa sanin irin halin da Garba yake ciki, kuma idan ba’a nemi mafita ba, a sannu-sannu zamu iya rasa shi wata rana, wanda niko bazan so hakan ba” Mudassir ya dan yi ajiyar zuciya yace “Hajiya wallahi wannan tunanin shi nake yi kullum, saboda nasan wannan matsalar zata iya janyo rugujewar dukkanin farin cikin gidan nan, kuma nayi iya bakin kokarina amma abin yafi karfina, sai dai mu cigaba da addu’a, sannan zan cigaba da nema masa maganin matsalar har lokacin da Allah yasa aka samu” sai kuma ya tashi tsaye ya cigaba da Magana yana cewa “yanzu daga nan bazan tsaya ko ina ba, sai gidansu Fatima, zan jure komai zata yimin koda Allah zaisa ta tausaya ta taimake mu” “Allah ya bada sa’a” Hajiya ce tace haka, Mudassir ya amsa da “Amin” sannan ya fita....

_how was d first chapter I hope you guys has enjoyed it we need more of your vote and comment sweerys._

  Don't forget to votes, comment's, and share...

Neeratlurv.blogspot.com

FATIMA TA GARBAWhere stories live. Discover now