8

125 1 0
                                    

FATIMA TA GARBA

Wattpad@neerat_lurv

*Daga Alqalamin✍*

*NEERATLURV😍*

        Tare Da

*ABDULAZIZU AAJ*

  
*Page 36_40*

        **

An jima ana shagalin biki, sai can Garba ya dago kansa ya hada ido da wata santaleliyar yarinya, wacce tun lokacin da ya hada ido da ita bai kauce ba, sai Mudassir ya dago da wurin da Ggarba yake kallo sai ya tabbatar akwai yarinyar da ya gani awurin, lokaci daya Muddassir yaji farin ciki a ransa. Ita kuwa yarinyar da taga Garba ya kuramata ido kuma yaki kaucewa abin ya sakata jin kunya ta nufi hanyar fita, shi kuma ya bita da kallo, da yaga alamar fita zata yi sai kuma ya tashi ya bita waje, shima kuma Mudassir ya bisa a baya batare da yace masa komai ba, suna fita Garba yayi sauri ya ci gaban yarinyar yana zuwa yace “Fatima ya akayi kika zo nan?” yarinyar kallonsa kawai tayi tareda yin tsaki ta kauce masa ta nufi tafiya, sai ya riko gyalenta, tana juyowa ta maresa sai Mudassir yayi yunkurin marinta, da hanzari Garba ya rike hannunsa tare da cewa “karka mareta, domin batada laifi, ni ne nakeda laifi nida na riko gyalenta” sai yarinyar ta kalli Mudassir wanda tun dazu huci kawai yake da alamar yaji zafin hana marinta da Garba yayi masa, sai tace “ai da ka barsa ya mare ni din, da wallahi yayi nadama a rayuwarsa mtsww” ta karasa maganar da tsaki ta tafi.
Bayan ta tafi Mudassir ya dubi Garba wanda yayi tsaye yana kallon tafiyar yarinyar, sai Mudassir yace “Innalillahi wa’inna ilaihir raju’un” Garba ya dawo da kallonsa ga Mudassir yace “me kake yiwa wannan taslima sai kace wanda ya hadu da Shaidan ko wani bala’I” Mudassir yayi tsaki yace “to miye marabin wannan jarabar taka da bala’I” “Miye bala’I kuma atattare dani?” Garba ne yayiwa Mudassir wannan tambaya cikin yanayin mamaki, sai Mudassir yace “Kana nufin wannan yarinyar siffar Fatima ka ganta?” Garba yace “wallahi kuwa, wannan dalilin yasa na biyota, ashe ba ita bace” Mudassir ya sake jan tsaki a karo na biyu sannan yace “lallai dole sai an hada da addu’a cikin wannan lamari naka, saboda idan ba’ayi hankali ba, sai an wayi gari kowacce mace matsayin Fatima kake kallonta, idan kuwa hakan ta faru bazaka daina shan mari awurin ‘yan mata ba” sai Garba yayi murmushi yace “Hmm, nidai bana tunanin wannan al’amari daya sameni bala’I ne wanda za’a yiwa addu’a, saboda ban taba tsammanin soyayyar Fatima zata iya zamomin bala’I ba. Shin gobe dai zamu koma gida ko?” Mudassir yace “kai kuwa daga gama biki yau din nan sai muce mu koma gida gobe” Garba yace “to gaskiya nagaji idan har gobe baka shirya mun koma gida ba, sai dai na shiga motar kasuwa nakoma gida, so kake duhu ya dusashe min idanuwa sakamakon rashin ganin Fatima, so kake kullum zuciyata ta rinka azabtuwa na rashin kusantar abar sonta” Mudassir yace “ko daya bana nufin haka, zamu je gobe din insha Allahu” sai Garba ya danyi fara’a tare da cewa “ko kaifa” sai shima Mudassir ya dan yi murmushi, sannan suka koma wurin Diner aka cigaba da biki suna kallo.
Washe gari bayan kammala bikin aure cikin koshin lafiya, an kai amarya dakinta, su Mudassir suka shirya kayansu suka yi bankwana da mutanen gida suka shiga mota suka hau hanya. Suna tafiya Garba sai murmushi yake yi shi kadai, bakomai bane sanadi face, zai dawo gida yaga abar kaunarsa. Shi kuwa Mudassir tukin kawai yake amma ransa abace yake saboda rashin samun cikar burinsa wanda ya kudurta aransa na ganin Garba ya samu wacce ta maye gurbin Fatima, abin yana kara bata masa rai musamman idan ya tuna mahaifiyar Garba da kuma yadda suka yi da ita.
Mudassir ya baiwa motar wuta sam baya sassautawa, da yake wannan lokacin ko hira basu samu yi da juna ba, sun yi tafiya mai nisa batare da yada zango ba, Sallah kadai kesa su tsaya kuma da sun yi ta, to sai kuma hawan hanya. Wuraren karfe goma na dare suka shigo garin Jega, suna shigowa gate din garin Jega, alokacin Garba yayiwa Mudassir Magana yace “amma dai kasan ba gida zaka wuce direct ba, sai kaje gidansu Fatima ko?” Mudassir bai ce komai ba ya nufi unguwar su Fatima.
Bayan sun kawo unguwarsu Fatima sai suka tarar mota zata shiga cikin gidan, da hanzari Garba ya dubi Mudassir yace “Kai wallahi mun zo a sa’a inaga waccen motar Fatima ce, bara naje nagani” sai ya nufi fita yaga Mudassir baida niyar fitowa sai ya sake cewa “kai bazaka je bane?” alokacin Mudassir yayi Magana yace “jeki dai kai” sai kuwa Garba ya tafi. Da gudu ya karasa wurin yana zuwa ya kwankwansa gilas din mota, cikin sa’a kuwa ya tarar da Fatima ce tare da kanwarta, sauke gilas Fatima tayi taga Garba ne, batare da tace komai ba ta mayarda gilas din motar ta shige cikin gida, yabi motar da kallo yana fara’a. Bayan maigadi ya mayar da kofar gidan ya rufe sai Garba ya dawo cikin motar Mudassir ya zauna. Yana fara’a yace “kaga kuwa mun zo a sa’a wallahi Fatima ce kuwa” sai Mudassir yace “kadai zo a sa’a, ina fatan dai ka biya bukatarka?” sai Garba yace “eh, yanzu kaga zan kwanta cikin farin ciki” batare da Mudassir yace uffan ba, ya kunna mota suka nufi gidansu Garba, suna zuwa yayi parking din mota a bakin kofar gidan, sannan suka fito tare suka shiga cikin gidan.
Suna shiga suka tarar da ba kowa tsakiyar gidan suna can suna bacci, Garba da Mudassir suka yi sallama ya fito ya shiga motarsa ya tafi gidansu.
Washe gari mahaifiyar Garba ta tashi taga Garba ta kuma yi farin ciki sosai, a bangaren Mudassir ma haka. Mudassir ya sanarda Mahaifiyar Garba duk abubuwan da suka faru, ta kuma nuna jimaminta na rashin samun nasarar abinda suka kudurta a ransu.
BAYAN SATI BIYU
Garba na tsaye a bakin kofar gidansu Fatima yana jiran fitowarta, tana fitowa bayan tazo wurinsa batare da tayi masa sallama ba, shi kuwa sai yayi mata amma taki amsawa, bayan nan kuma ya gaisheta tareda tambayarta mutanen gida amma duka taki amsa masa, sai ya gyara tsayi yace “Fatima bakomai yasa nazo wurinki ba, face inason ki taimakamin ki amsamin wasu tambayoyi da zan miki a yanzu” cingam take ci, saida ta buso shi tayi Dan Kwai ta fasheshi sannan tace “ina jinka” sai yaci gaba da cewa “Fatima me yasa kika tsaneni a rayuwarki, me yasa baki tausayina, miye dalilinki na rashin sona? Ko akwai wata matsala da nakeda ita wacce ban cancanci ki soni ba? Ko bana cikin jerin irin mazan da kikeson ki aura? Ko kuma akwai wani laifi da nayi miki?” Fatima kallonsa tayi sama da kasa sannan tace “ko daya babu abinda kayimin kuma banida wani dalilin rashin sonka kawai bana sonka ne, idan ma kai kanada dalilin sona, to ni banida dalilin rashin sonka. Idan kuma har zaka taimakeni dan Allah inason ka fita daga cikin rayuwata” sai Garba yace “naji duk zancenki, to inason kiyimin wata alfarma daya wacce daga gareta bazaki sake ganina ba a rayuwarki, ko a hanya wacce nasan zan iya haduwa dake bazan bi hanyar ba” cikin yanayin farin ciki Fatima tace “wace irin alfarma ce, fadamin ko menene insha Allahu zan ma” sai ya cigaba da cewa “zan so ki rakani asibiti domin tantance wani abu, muddin kikamin haka to zan barki har abada”.
Cikin tsananin mamaki Fatima ta dakatar da cin cingam dinta tace “asibiti kuma? Tantance wani abu? To me zai kaimu asbiti kuma me za’a tantance?” Garba yace “duk wadannan amsaoshi zaki samesu acan, nidai kiyimin wannan alfarma” tayi shiru na dan wani lokaci sannan daga bisani tace “to shikenan zan je, amma bazan je cikin motarka ba, tawa zan shiga zan bika a baya” sai yace “to shikenan baida matsala” sai ta shiga cikin gida ta janyo motarta ta fito, shima ya shiga tashi suka doshi asibiti.

Neeratlurv.blogspot.com

#Votes
#Comments
#Shares

FATIMA TA GARBAWhere stories live. Discover now