7

24 1 0
                                    

FATIMA TA GARBA

Wattpad@neerat_lurv

*Daga Alqalamin✍*

*NEERATLURV😍*

       Tare da

*ABDULAZIZU AAJ*

*Page 31_35*

         *

Babu wani abu da yake tsayar dasu saman hanya face Sallah sai kuma abinci idan sun tsaya saye, sannan suna hirarsu cikin mota tareda sauraren waka ko wa’azi koma kira’a kowanne dai sakawa suke. Sunyi tafiya mai nisa har tsawon bayan sallar isha’I basu kai Adamawa ba, sai can wuraren karfe goma sha biyu na dare suka kai garin Yola wato jihar Adamawa, suna zuwa basu tsaya ko ina ba, sai gidan Yayan Mudassir wanda ake kira Alhaji Jamilu, bayan sun isa bakin kofa suka yi Horn mai gadi yazo ya bude musu da yake Alhaji Jamilu ya riga yayiwa Maigadi bayanin zuwansu, ya gayamasa komai dare idan suka zo ya bude musu kofa, suna shiga ciki suka tarar da Alhaji Jamilu tsaye yana jiran zuwansu, suka fito cikin mota Maigadi ya dauko kayansu ya saka cikin gida.
Alhaji Jamilu yayi murnar zuwansu Mudassir sosai, ya kuma nuna musu farin cikinsa, sannan yaje da kansa ya dauko musu abinci da soft drinks wadanda matarsa Hajiya Sabi’a ta kammala ta ajiye tun kafin tayi bacci, suka zauna suka ci suka sha sannan suka tashi ya kaisu masaukin su, shi kuma yaje nashi dakin.
Bayan sun shigo dakin Mudassir yaje yayi wanka ya fito shima Garba yaje yayi wanka ya fito, sannan suka kwanta basu tsaya yin wata hira ba saboda gajiyar hanya. Washe gari iyalan Alhaji Jamilu sun hallara a dinning table, ‘yar aiki ta kawo breakfast sannan aka je aka tasuwa su Mudassir daga bacci suka je suka yi brush tare da yin arwala suka yi sallah suka zo suma a dinning table. Matar Alhaji Jamliu harma da ‘yarsa wato Amarya wacce suka zo bikin aurenta mai suna Yasira da kuma kanenta Uzaifa sunyi farin cikin ganinsu Garba sosai, suma kuma su Mudassir sun nuna musu farin cikin ganinsu tare da karramawar da suka yi musu.
Bayan an kammala breakfast aka zauna aka sha hira sosai cikin farin ciki da walwala ana dariya ana raha. Bayan dogon lokaci Garba ya tashi ya shige daki yabar Mudassir da Matar Alhaji Jamilu da ‘ya’yansa, Muddassir kallonsa kawai yayi baice masa komai ba. Sai kuma Hajiya ta tashi itama zuwa yin wani uzurinta. Bayan ta tafi sai Mudassir ya matso kusa da Amaryar wato ‘yar yayansa, ya dubeta yace “Yasira inason kiyimin wata alfarma kuwa” cikin yanayin mamakin ganin Kawunta yace yana nemanta alfarma ta ajiye wayarta da take danna tace “Kawu alfarma kuma, ai fadi abinda kawai kakeso nayima basai kace alfarma ba” sai yayi guntun murmushi yace “Yasira so nake dan Allah a ranar bikin ki zan so muje wurin domin magance wata matsala, so nake wannan abokin nawa da kika ga nazo tare dashi yana cikin wata matsala wacce nazo dashi dan samun maganinta, kuma bana son barin garin nan batare da mun samu maganinta ba, yanzu haka shigar nan da kika ga yayi tunani ne yake can yana yi” sai Yasira tace “Kawu wace irin matsala kuma ni wace gudunmuwa zan bayar wurin yaye masa ita?” sai yabata labarin soyayyar Garba, sannan kuma yace “gudunmuwar da nakeso kiyi anan itace, inaso ki gayyato kawayenki na nesa dana kusa, musamman kyawawa koda Allah zai sa yaga wacce yake so acikinsu, idan ya samu to anan nake so kimin taimako wato kiyi kokari wurin ganin ya samu karbuwa awurin yarinyar”.
Sai Yasira ta gyara zama tare da nisawa sannan tace “indai wannan ne insha Allahu Kawu bakada matsala, zanyi kokari wurin ganin kun samu cikar burinku, sannan indai matane kyawawa to kun zo inda suke, sai dai ina tsoron kar aje zuciyarsa tayi nisa wurin son wannan yarinya, sannan idanuwansa sun makance baya ganin kyawon kowacce irin mace inba wannan yarinya ba, idan haka ta kasance to za’a asha wahala wurin magance matsalar nan” sai Mudassir ya kada kai yana tunani, sannan yace “wannan kuma hakane, amma dai mu jaraba mu gani ko Allah zaisa adace” “Amin Kawu” Yasira ta amsa da haka, sai Mudassir yace “kinga ya shiga daki bara nabi bayansa” bai jira abinda zata fada ba ya tashi ya tafi.
Kadaici, damuwa, kukan zuciya, muradin ganin abarso, kwadayin jin sautin abar kauna, takaici da bakin ciki su suke damun Garba kullum acikin zuciya harma da idaniya, Mudassir fama yake dashi wurin rarrashinsa kamar wani karamin yaro, saboda kullum Garba tamkar yayiwa Mudassir kuka akan sai an koma gida kuma gashi ko bikin ba’ayi ba, da Garba ya gaji da hankurin rashin ganin Fatima sai yasa aka nemo masa kayan zane yazo cikin dakin ya zana hoton Fatima, wannan zanen da yayi shiyasa aka samu saukin damuwar da yake nunawa akan sai an koma gida.
Ranar biki an tashi cikin farin ciki da annashuwa kowa hakoransa a washe daga iyayen Amarya har abokan arziki da dangi, Mudassir yana farin cikin yau watakil abokinsa zai ga wacce yake so, shi kuma Garba yana farin cikin yau za’a yi bikin gobe su koma gida.
An je an daura auren Yasira da Angonta, sannan aka je akayi abubuwa da dama na al’adar garin wanda ake yiwa Ango idan yayi aure. Mudassir ya shiga cikin mutane tamkar dan gari shi kuwa Garba duk inda aka tsaya zaune yake yi tare da yin tagumi da ganinsa kasan akwai damuwa atattare dashi. Da Yamma suka je wurin Diner wacce ta hada Manyan ‘Yan Mata da Manyan Samari. Tabbas Adamawa ta cancanci kirarin da ake yimata na Land of Beauty, hakika akwai kyawawan ‘yan matan Fulani acan harma dana hausawa, suna shiga suka tarar kowa sai farin ciki yake, Mudassir ya dubi wurin sannan ya dubi Garba batare da yace masa komai ba suka je suka samu wuri suka zauna suna kallon mutane. Abinda ya baiwa Mudassir mamaki da suka zauna marmakon Garba yabar kansa asama yana kallon mutane amma sai ya sunkuyar da kansa a kasan kujera tamkar wanda aka aikowa da sakon mummunan al’amari. Wannan dalilin yasa Mudassir ya debe tsammanin samun nasara.

Neeratlurv.blogspot.com

#Votes
#Comments
#Shares

FATIMA TA GARBAWhere stories live. Discover now