Page 21

2K 98 0
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

                        2⃣1⃣

"Na baki saki daya Asma'u..." Daddy na gama fadar haka ya bar falon cikin kunar rai. Mummy kam sabon kuka ta fashe da shi na zallar nadamar abin da ta aikata, jiki a saɓule ta shiga bedroom ɗinta, ruwa kawai ta watsa duk da zuciyarta na mata zafi, bata jima ba ta fito da akwatin kayanta a falo ta same su cirko-cirko, bata iya cewa komai ba ta fita Fatima da Ammar kuka suka fashe da shi. Shi kam Alhaji idonsa ne ya yi jawur, domin mutuwar auren iyaye ba karamin abu ba ne.
   Suna kallo Mummy ta sa kai ta bar gidan, ciki suka koma suna ci gaba da kukan, shi kam daddy ko a jikinsa sai ma harkokin sa da ya ke yi. Bayan wucewar Daddy Alhaji bangaren shi ya koma, shima wanka ya yi sannan ya shiga tattarawa Daddy duk wani abu nashi, ATM card sai motar da ya saya kwanaki kawai suka rage a hannunsa. Falon Daddy ya shiga ya aje masa komai cikin ladabi, ko kallon sa bai ba har ya aje ya fita.
  Cikin awanni duk wanda yaga Alhaji zai yi tunanin ciwo ya yi domin yadda ya yi wata iriyar rama,  nan ko babu ciwo sai dimbin damuwa, motarsa ya ɗauka ya bata wuta sam ya rasa ina zai bi, haka ya gama zaga gari daga karshe ya ɗauki hanyar Kano don baya jin zai iya zama a garin Abuja. Karfe shida ya isa Rano a family hause ya sauka, ya samu kyakkyawan tarba daga Alhaji Babba, sai da ya ci abinci ya huta kafin ya nufi gidan Aunty Ameena. Kallo ɗaya ya yi wa Aunty Ameena ya tabbatar bata cikin nutsuwa, hakan ya nuna masa ta ji abin da ya faru tsakanin Mummy da Daddy kenan, bayan sun gaisa ne suka shiga tattauna matsalar, inda Aunty Ameena ta cewa Alhaji ya zauna a gidan Mummy har Allah yasa yaga Zainab kuma gobe zata raka shi gidan mahaifin Zainab ɗin kila ko ta je can. "Hmm! Wallahi Aunty abin da ke damuna da ciki kuma tana nakuda Mummy ta koreta, kila ko ta haihu ko a wane hali take domin Daddy ya ce wai Zainab bata a gidan mahaifinta."
   "Ka yi addu'a shi ne mafita, amma tabbas ban so ka biyewa Mummy ba, duk da dai Mummy mahaifiyarka ce amma gashi yanzu an aikata dana sani ba a cikawa Daddy burinsa ba." "Na yi nadama Ni kaina yanzu Babban BURINA shi ne in ga Zainab ta dawo gidana da yaronmu." "Addu'a zamu dage kawai sai komai ya dai-daita." Sun daɗe suna hira daga bisani suka yi sallama ya koma gida Alhaji Babba. Washegari da safe misalin karfe goma bayan ya yi break ya yi wanka suka nufi gidan Malam Ali, cikin mutunci ya karɓe su suka  gaisar da shi, fuska sake ya amsa duk da bai wani gane su ba, sai da Aunty Ameena ta yi masa bayani, aiko take ya bata rai domin sosai ya ji takaicin korar da akawa Zainab a halin nakuda, badan Allah yasa Khalil ya ganta ba sai dai ta mutu. Don haka sai ya daure fuska tamau kamar bai san wani abu dariya ba ya ce "ina jinku sai aka yi yaya?" "Ehmm Ummh dama Baba..." Saurin katse shi Malam Ali ya yi ya ce "karka ce min komai Abdallah domin ka salwantar min da 'ya, kuma akan me zaka zo neman ta baya ka saketa?" "Don Allah Baba.." "tashi ku bani waje bana son Jin komai." Baba ya k'arasa maganar da ɓacin rai mai tsanani.
    Ganin babu wani fuska yasa suka tashi jiki a saɓule, yana aje Aunty Ameena ya kama hanyar Kano, domin yasan gidan da Mummy ta sauka don shi ya saya gidan da kansa. Kwanan sa daya ya koma Abuja da tunanin tarbar da Daddy zai masa. Ko alama Daddy ba nuna masa komai ba ya zuba masa ido kawai, haka kwanaki ke tafiya, har aka share sati biyu amma babu labarin ganin Zainab Alhaji kuwa ba ya da aiki sai na zirga zirga bashi Kano ba shi Abuja.

****

Zuwa yanzu watan Fawzan goma kenan, kuma tuni ya soma gudunsa duk wanda ya  gansa sai ya burgeshi, irin yaran nan  ne masu shiga zuciyar mutum farat ɗaya,  wani lokacin Zainab har mamakin farin jinin Fawzan take, shi yasa ko da yaushe cikin tofe shi da addu'ar neman tsari take. Shirye-shiryen biki ya kankama don Kwanaki bikin saura goma sha huɗu kacal!  Duk wani shiri sun kammala sai jiran ranar kawai.

Zainab ce ke kai kawo tsakanin kicin da falo, a kokarinta ta kammala aikin da take yi domin abinci take shiryawa IK, saboda yau zai iso garin amma sam Fawzan ya hanata sukuni, ruwan hannunta ta aje sannan ta ɗauki Fawzan dake mata kananun kuka ta nufi bedroom din Umma "a'a lafiya kuwa kukan me yake yi?" Umma ta yi tambayar tana zama don a kwance take.
      "Nima ban san kukan da yake bafa Umma, Allah kwanan nan Fawzan wata rigima ya tsira." Kallonta Umma ta yi tare da girgiza kai ta ce "amma kin bashi ya sha kuwa?" "Umma ɗazun fa ya sha rigima ce." "Kara bashi yanzu ma." Umma ta dire maganar tana tsare Zainab da ido. Cirowa ta yi ta mika masa amma sai ya ki amsa sai ma sabon kukan da ya saki, rarrashin duniya Umma ta yi amma ya ki shiru, don haka sai ta fara taɓa sassan jikinsa don ta ji ko wani wajen ke masa ciwo aiko tana kai hannun kunnensa ya kara sakin wani kukan, magani ta dauko ta sanya masa sannan ta shiga jijjiga shi har ya yi shiru bacci ya kwashe shi.
    Zainab kam bata shigo ba sai da ta kammala komai ta shirya a bangaren sa, sannan ta koma falon Umma "Wai har ya yi bacci ne?" "Eh tun da na sanya masa maganin ciwon kunne, kunnen ke masa ciwo." "To Allah ya sauwake bari na yi wanka tunda na gama komai, abinci na dining Umma." Daga haka ta wuce. "Allah ya yi albarka."  Umma ta yi maganar tana nufa dining din.
       Bayan ta fito wankan sallah ta soma gabatarwa sannan ta shirya ciki wata jallabiya baka mai ratsin pink sosai rigar ta karbi jikinta, wayarta dake kan dressing mirror ce ta soma fitar da wani sauti mai daɗi, murmushi ta saki kafin ta kai hannu tare da ɗaukar wayar ta kara a kunne tana faɗin "Assalamu Alaikum." Daga ɗaya bangaren IK ya amsa cikin jin dadi "My Zee barka da yammaci, na shigo gida ban ga my boy ba?" "Yana bacci baya jin dadi ne fa Ya IK." "Ina jiranki a falon Umma." Haka kawai ya iya faɗa ya datse wayar.
      Murmushi ta kuma yi sannan ta tashi, har ta kama hanya sai taga motsin Fawzan dawowa ta yi ta ɗauke shi sannan suka nufi falon, a zaune ta samu IK da Umma suna hira sannu da gida tawa Umma. Bayan Umma ta amsa ta fara gaida IK, amsawa ya yi bayan ya amshi Fawzan. "Oh! My boy ashe baka jin dadi sorry." "Kunnensa ke ciwo sai kananun kuka yake wa uwar amma kaga yanzu da na diga masa maganin ya ji sauki." Umma ce ke maganar.
     "Umma duk da haka za mu je asbiti a duba shi dubi yadda ya saki fa." IK ya dire maganar yana duban Fawzan ɗin. "A dawo lafiya gobe nake son ka kai Zainab Rano tunda maganar auren yana gabatowa." "Tom in sha Allah Umma, bari na watsa ruwa ga Usman da sauran abokaina suna zuwa Allah yasa da abinci mai yawa." "A fito lafiya amma abinci ina tunanin har sai kun rage."  Mik'ewa ya yi da Fawzan a hannu ya ce "Zee ki shirya kafin na fito, ga key ki kwaso kaya a mota tsarabar ku ne kowa a bashi na shi." Amsa ta yi cikin ladabi kusan a tare suka fita.
      Bata wani jima ba ta dawo, da taimakon mai aiki suka shiga da kayan cikin falon, aje kayan ta yi tana faɗin "wash Umma wallahi na gaji ga kayan nan bacci nake ji." "Bacci da yamman nan? Ki bari dai har daren ya yi. "Ai bazan kwanta ba, tunda fita zamu yi." Suna hiran su IK suka shigo "shirya shi mu je na ji jikinsa da dumi." To ta amsa tana nufa bedroom. "No! Akwai wasu jessy a cikin kayan ki sanya masa." Jessy ta ɗauko mai kyau har da rubutun sunan sa a jiki da manyan haruffa *FAWZAN* aka rubuta da ratsin Golding shi kuma jessy ɗin blue ne, sosai kayan suka masa kyau Ball IK masa karama mai kyau sannan sukawa Umma sallama suka tafi cikin kyakkyawan motar IK kyar karama mai tsanani kyau da burgewa.
    Asbiti suka fara zuwa basu daɗe ba aka gama duba Fawzan ɗin, magunguna kawai aka rubuta masu a hanyar su ta komawa gida Fawzan yasa rigima sai an je an saya masa ice-cream "bar kuka ka ji My boy mu je a saya maka." "Kai Ya IK akwai ice-cream fa a gida." "No! Bana gida yake so ba don haka mu je a saya masa babban BURINA in ganku cikin farin ciki." Hmmmm kawai ta ce daidai lokacin da ya faka motar gaban wani makeken super market. Ciki suka shiga ya ice-cream ɗin Fawzan aka soma siya Sannan ya juyo da hankali kan Zainab "Zee ki zaɓi abin da kike so." "A'a babu abin da nake so." Zainab ta bashi amsa. "Ki zaɓa na ce bana son musu." Da dan ɓacin rai ya yi maganar, ganin haka sai ta fara zaɓa sam basu lura babu Fawzan ba, sai da ta gama ɗaukar kayan har suka biya.
   Babu inda basu duba ba babu shi ai da sauri cikin kidima Zainab ta fita harabar wajen. Turus ta yi ganin Fawzan rungume a jikinsa, har abada ba zata taɓa manta fuskar nan ba balle kuma ga photo copy ɗinsa a wajenta, take abinda suka mata ya dawo mata sabo a zafafe ta isa wajen tare da kamo hannun Fawzan ɗin cikin daure fuska, a masife ta ce "Kai Malam mahaukacin ina ne daga ganin Yaro ka wani rungume shi?" Kallon bakinta ya tsaya yi cikin mamaki, kamar ya taɓa jin muryar sai dai wannan tafi sanyi da daɗi, kafin ya yi wani yunkurin sai gani ya yi ta nufi Wajen motar ta  daidai da fitowar IK da kayan da suka saya don yaga lokacin da Zainab ta ɗauko Fawzan ɗin. Da sauri Fawzan ya kwace daga rikon da Zainab ta yi masa. Bata san lokacin da ya iso wajen ba sai jin amon muryar sa ta ji yana fadin "Zain..."

      *RANO* ✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now