Page 29

1.9K 79 0
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S P.M.L*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
  *ZULAYHEART RANO*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

                        2⃣9⃣

Har awa daya ya shude Alhaji bai farka ba, hankalin Daddy da Alhaji ya tashi addu'a kawai suke iya yi domin samun lafiyar Alhaji, karfe ɗaya da mintina Mummy ta isa cikin kuka mai ban tausayi domin a duniya Mummy taba matukar son Alhaji, haushin kukan da take ya turnike Daddy kamar zai gaura mata mari don takaici "kin ga Asma'u idan ba zaki yi shiru ba tashi ki bar asibitin nan ki bar mutum ya ji da abu daya." A zafafe ya gama maganar. "Ka yi hakuri Alhaji amma dole na yi kuka ka dubi yadda yaron nan ya koma idan ya mutu me zamu cewa Allah?" "Tambaya ta kike ne? Ya bude baki zai ci gaba Yayansa ya matso kallo ɗaya ya yi masa kawai ya yi shiru da maganar tare da barin wajen. Lallashinta Alhaji Babba ya yi ta yi har ta yi shiru toilet ta nufa ta dauro alwala ta soma gabatar da salla tana rokarwa Alhaji sauki wajen Allah bata gushe ba har sai da ta ji zuciyarta ta yi sanyi.

Bai farka ba sai hudu Dr ne ya kuma duba shi, sosai ya yi mamakin ganin har lokacin bugun zuciyarsa bai daidaita, tabbas Alhaji yana cikin yanayin da babu abin da yake buk'ata sai addu'a, jiki a sanyaye Mummy ta fara tambayarsa jikin Alhajin "Hajiya ku daina damuwa ku yi addu'a sai dai yana da kyau ku nemo masa abin da yake so shi kadai ne zai iya sanyawa ya samu rangwame daga azabar da yake ciki, bugun zuciyarsa ne har yanzu bai koma daidai ba." "Za a yi kokari insha Allahu Dr a ci gaba da kulawa da shi." Bayan wucewar Dr Mummy ta shiga sabuwar damuwa, tasan babu abin da Alhaji yake so sai Zainab to ita a ina zata samo masa Zainab to idan har taga Zainab ta ina zata soma mata magana domin ta san babu yadda za a yi zainab ta saurareta "to kuma idan ta yi aure fa?" Wata zuciyar ta jeho wa Mummy wannan tambayar wanda ya yi sanadin tsayawar numfashin ta na dakika, sabbin hawaye tare da tunani kala kala ne suka dirar mata har ta rasa daya da zata yi.

Kamar yadda Dr ya fadawa Mummy haka ya faɗawa Daddy, to shi Daddy ya shiga damuwa sai dai ba irin ta Hajiya ba, saboda duk wani hali da Alhaji ya shiga shi ya jawa kansa da tun farko bai rabu da Zainab ba babu shi babu shiga irin wannan halin duk dai komai na Allah ne, babban matsalar yana kunyar yi wa mahaifinta maganar saboda ko shi aka yi wa haka ba zai yadda ba, to kuma idan ya yi wa mahaifinta maganar ya ce masa ta yi aure da matsala sai dai Alhaji ya mutu "hasbinallahu wa ni'imal wakil" haka ya maimaita a bayyane.

Kaiwa da komowa kawai yake ya rasa abin da ya ke masa daɗi.

****
Rayuwa ta yi wa Zainab daɗi tana cin mai dadi ta sha mai daɗi ta yi shi mai kyau ita da danta, ta je inda take so wani irin kyau ta yi na musamman shi yasa samari da zawarawa suka fara yi mata caaa, duk da ita sam basa gabanta don ta ce ta gama aure tun da ta rasa Ik masoyin gaskiyaa, hankali kwance take komai kullum Umma cikin yi mata nasiha take akan ta yi aure shi ne rufin asiri sai dai ta yi murmushi ta ce

"Umma aure lokaci ne idan lokacin ya yi zan yi, kuma ni Umma bana jin zan kuma yin wani aure na rasa Ya IK Mai sona da gaskiya, bana jin zan kuma samun kamar sa duk maza halin Alhaji garesu."

"Ke dai kike yi masu kallon haka amma kowa da halin sa ki yi duk abin da zaki yi da kyakkyawar niyya sai Allah ya taimake ki."

"To Umma zan yi amma ki ci gaba da yi min addu'a." Haka take fadi don ta rufe maganar.

Yau sunday bata da school haka ma Fawzan don haka wanka suka sha cikin shiga mai kyau da ɗaukar hankali, riga da wando yan kanti ne a jikin Fawzan, rigar fara ce kal wacce aka yi rubutu da manyan haruffa *BOSS* sai wandon blue sosai kayan suka amshi jikinsa turare mai sanyin kamshi ta feshe shi da shi sosai yaron ya yi kyau, sannan ita ma ta shirya kanta cikin doguwar riga baka mai yarfin golden a jiki wacce ta yi matukar dacewa da jikinta farin hijjab ta sanya iyakar sa wuya, simple kwalliya ce a fuskarta amma ba karamin kyau ta yi ba key ta dauka suka nufi falo wajen Umma dake zaune.

"A'a har kun gama shiryawa kenan Fawzan?"

"Eh Umma zamu tafi."

"To Allah ya kiyaye hanya amma a kula bana son shashanci, ya kamata ma zuwa ko gobe ko jibi mu je Rano gano Malam."

"In sha Allah Umma zan kula, to idan na dawo sai mu yi magana." Tana maganar ne tana nufa hanyar fita.

Cikin kwarewa ta ba motar wuta mai gadi ya buɗe masu, gidan su Rufaida ta soma zuwa ta dauketa sannan suka nufi inda za su je domin duk ranar Sunday suna fita su shakata, zoo road suka nufa wani hadaden wajen wasan yara ta shiga da Fawzan yaron yana ganin sun shiga ya soma murna, parking ta yi sannan suka fita karkashin wasu kujeru ta zauna tana amsa kira ita kuma Rufaida ta je wajen masu kula da wajen suka gama tattaunawa sannan ta koma inda Zainab, babu jimawa aka cika masu gaba da kayan ciye-ciye dana shaye-shaye, Rufaida ce ta fara sha ita kuma bata kammala da amsa waya ba, sansanyar muryar da ta ji a bayanta ya sanyata juyawa.

Ido hudu suka yi ta yi saurin janye nata tare da kashe wayar, abin mamaki ta kasa amsa sallamar sai Rufaida ta amsa. "Sannunku da hutawa yammata." "Yawwa." ta amsa tana kauda kai gefe. "Don Allah zan yi samun wajen zama?" "Ga waje nan." Ta dire maganar tana nuna masa dayar kujerar, "na gode." Ya faɗa yana zama. "Please zan iya sanin sunan ki?" Ya yi maganar yana nuna Zainab. "A'a domin Ni matar aure ce, sai dai Yar'uwata sunanta Rufaida." Tana gama faɗin haka ta mik'e tana dariya ciki ciki. Ita kuwa Rufaida harara  ta jefa wa Zainab cikin jin haushin abin da ta yi mata.

Sam ba haka ya so ba domin da niyyar wajen Zainab ya zo amma tunda haka ne zai kula Rufaidar, gyara zama ya yi wajen Rufaida ya soma gabatar mata da kansa "sunana Sameer Usman yaron Alhaji Usman Gaida fatan zan samu karɓuwa?" Murmushi ta saki domin tana jin sunan mahaifinsa sosai, itama gabatar da sunanta ta yi sannan suka shiga hira.

Zainab kuwa can gefe ta tsaya tana kallon yadda Fawzan keta wasansa hankali kwance, tana jin dadin yadda take ganin Fawzan kullum cikin farin ciki bata kaunar ganin damuwarsa, suna wajen har kusan karfe shida sannan suka fita sahada store suka biya kafin suka tafi. Mai gadi na bude get gaban Zainab ya fadi ganin motar da Usman ke ja a gidan, da kyar ta iya parking mota suka shiga ciki turus ta yi ganin Usman zaune a falon, yana ganin ta ya saki murmushi shi kam Fawzan da gudu ya isa wajen sa yana faɗin "uncle." "Fawzan Barka da dawowa me ka siyo min?" "Abu da yawa Momma ta sayo mana."

Murmushin karfin hali Zainab ta yi tana faɗin"sannu da zuwa Usman gobe muke shirin zuwa garin fa." "Ai kam mu kuma sai gamu mun shigo yau." "Mun gode sosai ya su Abba?" "Suna lafiya lau." "To madal... Kafin ta k'arasa sai ganin umma tare da wata mata sun fito daga bedroom har ga Allah bata shaida ko wacece ba, sai dai taga alamun matar bata cikin nutsuwa.

"Sannu da gida Umma." "Yawwa kun dawo?" "Eh Umma." "To sannu ga bak'uwa nan sai dai ina son ki nutsu Zainab." "To Ummata sai dai ban gane ta ba." "Zainab ki yi hakuri." Muryar matar ce ta ratsa mata kunne da sauri ta toshe kunne tana faɗin "no ba Mummy ba ce." "Ni ce Zainab yau gani gabanki ina baki hak'uri ki taimaki ɗana mijinki uban danki." Cikin kuka Mummy ke maganar.

"Ɗan ki wanene ɗan ki? Mummy yau ke ce ke bani hakuri da kanki? No wannan mafarki ne Mummy bazata taba ba zainab makiyyarta hakuri ba please Umma ki ce min mafarki nake yi." "Ba mafarki ba ne Zainab duba da kyau ni ce Hajiya Asma'u a gaban ki."

"Noooo! Please Mummy ki bari don Allah ki barni na yi rayuwa kamar kowa..."

"To yau dai karshen tikatiki tik, ga dau Hajiya Asma'u a gaban Zainab tana rikonta shin Zainab zata yadda ta yafe ko ya? Sai kun biyo alkalamin marubuciyar domin ya warware mana.

*RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now