Izinah

220 5 1
                                    

Hawayen dake kwance A saman fuskar ta ta share ta mik'e cike da kasala tana maijin Jiri na neman kwasarta.

kiran wayarta ne ya karad'e d'aukacin  ilahirin d'akin da take ciki, da sauri cike da Razana akan fuskarta ta juya da alamar tsoro akan fuskarta. Jayuwa tayi kusa da wayar takurawa screen din wayar ido. Jikinta na rawa ganin me kiran wayarta ta, tafi minti biyar atsaye har kiran ya katse bata d'auka ba. Adaide lokacin ya kuma shigowa cike da fargaba ta d'auka had'e da cewa "hello" daga can akai magana yayin da ta saka Speaker domin taji da kyau.

  

  

Dariya me maganar ya kwashe da ita.... "Uwargidan Musty"

dafe k'irji tayi donjin muryar wanda take tsammani,take ranta yayi matukar b'aci da kakkausar murya ta maida mai magana.

"Haris na gaya maka ka rabu dani! meya sa kake san sani amatsala ne ehe?? Akanka na canja layi taya akai ka sami wan nan?? ka takurawa Rayuwa ta kaji tsoron Allah!"

Dariya ya kwashe da ita "lalle Shukura harkin manta waye ni? ai to kisani duk inda kike nasani duk wani takun ki kisani akwai wani target danake akanki kuma hak'a na yakusa cimma ruwa,ina baki shawara daki samawa kanki Lafiya ki sallama na rasa inda kika koyo taurin kai yanda nasanki simple baby ceke"

"Enugh! Haris" ta fada cike da fusha "baka da tunani ne? nifa matar Aurece! don haka ka fita harkata domin na maka nisa kasani ina d'auke da igiyoyi uku akaina sunnar ma'aiki nake yi don haka ka rabu dani haba sekace baka san kima da  darajar sa ba! to this is the first nd last da zaka kara kirana if not zan baka Mamaki".

K'it ta kashe wayar ta zauna ta dafe kai dake sara mata, wasu Hawaye ne ke kwaranyo wa akan beauty face nata idanuwan ta sunyi luhu-luhu alamar ta dad'e tana kukan.

**********

Ya Dad'e tsaye akanta yana kallota Wanda ita ta Lula Duniyar tunani D'an gyaran murya yayi ta d'ago firgigit cike da tsoro kar Allah yasa beji wayar da tayi ba. Dan murmushi ta saki ta mik'e "Mustyna welcome" cike da D'an tsoro.

D'an kallonta yayi yace "Shukra na yade? na ganki duk kin birkice" kafad'arsa ta dafa "Mustyna yaushe ka shigo?" kamota yayi suka zauna gefen gado yace "yanzu na shigo na ganki kin Lula duniyar tunani kode tunani na kike ne??"

Murmushi tayi tace "eh mana tun d'azu nake missn d'inka."

Dariya yayi ba wani nan kede na rasa kwana 2 me kika sa aranki, duk kin fad'a haba babyna kome ke da munki ai seki gayamin ni zan share miki Hawaye."

Gabanta Ne ya fad'i nan ta tuno da kahon zukar  da Haris ya kafa mata tun sati uku da suka wuce kullum sayya kirata yana Mata barazana.

Hure Mata ido yayi firgigit ta dawo daga k'aramin tunanin data lula "yace inaga senaje anmin checking naki" dariyar yak'e tayi tace  I know my dear nasan ka damu dani, Murmushi yayi ya lakuce Mata hanci "Ashe kinsan zan iya Amma kike sakaci." Dariya tayi med'an sauti ta mik'e tsaye "Oya muje kayi wanka ka canja kaya kaci abinci."

"Yawwa babyna" nan suka mike atare suka fita daga d'akin.

*********

Can kuwa b'angaren Haris bayan ta katse wayar ya k'urawa wayar ido cike da zogin Zuciya ya cillar da phone d'in kan gadonsa yana cije leb'e tare da shafa sumar sa, murmushi yayi "ni shukra zataiwa haka! lalle dole na nuna mata kuren ta domin ta lalatan tsari na hannunsa ya d'unkule ya D'an daki gefen gadon ya mik'e yana kai-kawo a d'akin  azuciye ya fita harabar gidan su ya d'auki motar sa ya fice.

Drect gidan abokinsa uzaifa ya tafi yana k'ok'arin shiga Shi yana fita ya gano Shi "Aa frnd daga ina?" yace "kai raina abace yake" uzaifa yace "meyafaru?"

 IZINAH CE 2017 (completed)Where stories live. Discover now