PART 1-END.

1.1K 57 3
                                    


😭😭🔪🔪   *K'AZAFIN KISAN KAI.......*
        _{ąlmơʂɬ ɬrųɛ lıʄɛ ʂɬơrყ}..._

                🔪⚔⚔🔪
                       😭
            



*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ*
        *ცყ*
_HAWWA M.U.{ʂmąʂɧɛr}..._



_ცıʂmılląɧır-rąɧmąŋır-rąɧɛɛm..._

*WANNAN LABARIN BA K'IRK'IRARRE BANE,DA GASKE YA FARU........KADA KU CANJAMIN LABARI BA TARE DA IZININABA,DUK WANDA YAYI HAKAN NA BARSHI DA ALLAH............AKIYAYE...*

*KADA WANI/WATA SU CE ZASUYIWA WANNAN LABARIN KWASKWARIMA,DAN ALLAH,HAKA LABARIN YAZO..........*



      



*ıŋ ɖɛɖıƈąɬıơŋ ɬơ ʄąɬɛɛmą ıცrąɧım (mųŋɛɛrąɧ),rɛąllყ ɧɛąrɬ ų cwɛɛɬყ,Ɩıყą ῳwųყą mųŋą mųɠųŋ mąk'ąlk'ąlɛ... 🤞🏻😍*


*℘ąɠɛ 1↔🔚*



*Y*arane k'anana suna tafe suna tsalle,alamun dake d'auke akan fuskokinsu na nuni da irin murnar da suke ciki,kasancewar tasowar su daga makarantar boko ta gwamnati kenan,uniform en jikinsu blue ne da farin hijab,sai y'an jakunkunansu dake goye a bayansu.............
Misalin k'arfe 5:30pm,da murnarsu suka shigo gidan dake babu laifi,duk da kasancewarsa na k'asa,amma mutanen gidan akwaisu da yalwar tsafta........
Ko Ina a share k'al,haka yaran suka shigo,duka² babbar bazata wuce shekaru (11) ba,sai k'aramar da bana tunanin za ta haura shekaru (8)........

Da sallama suka shigo,ummah dake tafkeken tsakar gidan ta amsa,tana murmushi,had'e da cewa "an dawo?"..........
"Eh ummah", suka bata amsa,lokacin da take cewa "suʝe su ajiye kayan tukun,su zo su d'auko abincin ʂų"...........
'Daki suka shiga,lokacin ne umman ta sake fad'in "kuyi maza fa ku cire kayan,kuzo Ku ci abinci",ko amsawa basuyi,suna hanzarin suyi su fita.........
Basu ko cire kayan makarantar da ummah tace suyi su cire ba,suka fito suna sand'a...........
Ganin ummah bata tsakar gidan,suka ranta a na kare,sai k'ofar gida,cikin wata rumfa da ake makarantar allo..........

Da yake ranar ta kasance ta alhamis,gaba d'aya yara suna nan,daga masu zuwa makarantar safe har masu zuwa ta yamma........
Kasancewar rumfar babbace,kuma a line en an kawo farar k'asa da ake paint da ita a wani gida,yaran kowa ya d'auka suna wasa da ita..........
Kowa ya baje basirarsa,yana zane akan allunan da akayi a cikin rumfar,kasancewar har makarantar islamiyya akeyi aciki da daddare..........

Kiran sallar Maghreb yasa kowane yaro ake turowa nemansa daga gida,wani yarone ya fito daga gidan dake jikin rumfar ta b'angaren gabas,da bazai ,wuce shekaru (4) ba,sanye da kayan sanyi,da yake lokacin na sanyine muku²..........
*"UMMI* Ku zo inji ummah tana kiranku",juyawa tayi tana neman k'anwarta ganin bata gantaba,a can d'an nesa da rumfar ta hangota,hakan yasa ta fara kwala mata kira *"HAFSAT!!!* kizo muje  inji ummah",  ta mai²ta mata..........
Kama hannunsa tayi suka nufi cikin gidan..........

"Ummah gamu", Ummi ta fad'a,tana zuwa kusa da umman,kama kunnenta tayi ta ruk'e tana fad'in "me nace muku da kuka dawo?, dafe kunnenta tayi tana fad'in "dan Allah ummah kiyi hak'uri,wallahi da zafi", "nasan da zafi ai shi yasa nayi miki haka wata k'ila gobe baza ki sakeba", ta fad'a tana dad'a murd'a kunnen.............
"Wato saboda kunnen k'ashi,dana ce Ku cire kayanku kuci abinci,shi ne kika jata kukayi waje,ko cire kayanma baku yiba,saboda gaku sarakan wasa shi ne kuka fita ko kayan baku cireba bare asa ran zaku zauna cin abincin,daga dawowarku har kunyi wuf kun faki idona kųnyi waje,saboda k'aunar yawo ko?..............
"Dan Allah kiyi hak'uri",
Ta fad'a,
"Maza ku wuce kubani guri,lokacin da ta saki kunnen.........
Da gudu sukayi d'akin,suka hau cire kayan jikinsu........

K'AZAFIN KISAN KAI.! (1--END)✔Where stories live. Discover now