💎💎Dalili Na💎💎
Ummu Subay'a
بسم الله الرحمن الرحم
0⃣1⃣
"Sweetheart, Sweetheart, Sweetheart"
Da gudu take bin bayansa tana kiransa
Shiko ko a jikin sa sai sauri yake don kada ta cimmasa
Yaxo daidai xai bude kofar motarsa yaji karar bude kofa
Kallo daya yayiwa motar yasha jinin jikinsa
Itama tana kallon motar tayi saurin goge hawayen fuskarta ta fara yake
Dawowa wajenta yayi ya rumgumeta yaxo daidai kunnenta yace
"Ashe kinada wayo"
Yake ta mishi tace
" kamar yadda kake dashi "
Janta yayi bakin motar wadda ya shigon suka tarboshi
Janye jikinta tayi daga gareshi ta fada jikin bakon
"Oyoyo Bobbona"
Jan hancinta yayi yace
"Bakya girmane Zahra wannan ai sai Husnah"
Tsayawa yayi yana jinjina irin soyayya dake tsakanin Zahra da Bobbonta daga bisani yace
"Ai kai ka shagwa6ata Mahbub"
Tura baki Zahra tayi kamar yarinya tace
"Bobbo baka gansaba wai Mahbub kai tsaye, bayan na hanashi"
Dukan wasa yakai mata, Bobbonta ya janyeta yabi iska suka saka daria kamar bbu komai a tsakaninsu
A dinning space Zahra ta shiga hidimar xuba musu abinci
Mahbub ya dubi Mas'ud yace
"Man ina ka shigane tun 10 akace kabar office"
Satan kallon Zahra Mas'ud yayi yaga itama dubansa take, yayi gyarar murya yace
"Nakai motata service ne"
"Da kuma ka gama shine ka xarce gida ka barni da aiki"
Daria Zahra tayi tace
"Bobbona shiyasa nace maka kayi aure, idan kayi aure kaga kaima kanada excuse sai kayi tafiyarka"
Yake Mahbub yayi yace
"Lil lokaci ne insha Allah kamar yau"
A tare Zahra da Mas'ud suka amsa da "yasha'ullah"
"Ina my daughter ne"
Mahbub yayi tambayar don kawar da maganar aure
Mas'ud dake kokarin kai spoon din jallof na couscous yace
"Taje holiday gidan Mami"
Daidai kunnen Mas'ud, Mahbub yaxo yace
"Nasan kai ka kaita don ka takurawa My Lil da shegen bukatarka"
Limshe idonsa Mas'ud yayi an tabo inda ke masa kaikayi, amma ya cije yace
"Kai fah Bobbonmu ne inajin kunyarka"
Cikin tsigar tsokana
Zahra data xuba musu ido ta shagwabe tace
"Haba Bobbona gulma fah bbu kyau"
Murmushi ya mata yace
"Ba gulma bane My Lil maganarmu ce"
Gyada kai tayi ta cigaba da cin abincinta tana tufka da warwara