*💎💎DALILINA*💎💎
NA CANXA YA KOMA*❤❤❤SON* *ZUCIYA❤❤❤*
*NA*
*UMMU SUBAY'A*
*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Kuyi hakuri Fans saboda wasu dalilai yasani canxa sunan littafin daga Dalilina ya koma son Zuciya
0⃣2⃣
A hankali Suwaiba ta bude idanuwanta da suka mata nauyi ssai ta sauke kan Akka data tusata gaba tana kallonta
Cikin hanxari Akka ta karaso kusa da Suwaiba da ta dafe kanta dake sara
"Sannu SuSuna kin tashi, meke miki ciwo?"
Dakyar Suwaiba ta bude baki tace
"Kaina xai fashe Akka, meyasa sameni ne ma"
Tallafa mata Akka tayi ta tashi ta xauna
Akka tace
"Motace ta bugeki Susuna"
Sai a sannan ne Suwaiba ta tuno da Abunda ya faru
Nan Suwaiba ta narkewa Akka sai shagwa6a take xuba mata
"Akka nan na ciwo, Akka can na ciwo"
Sam bata bar Akka ta rintsa mai kyau ba har gari ya waye
Koda Mas'ud yabar gidan Akka bai xame a ko'ina ba sai gidanshi
Bai samu kowa a parlour ba sai TV dake aiki, kashe TV yayi ya wuce dakinsa don ya watsa ruwa
Har ya gama shirinsa na kwanciya baiga Zahra ba, hakan ya sashi mikewa ya nufi dakinta
Murmushi yayi lokacinda yaji kofar a kulle GAM
Tsaki Zahra taja dataji bugun kofar Mas'ud
"Wannan gum din ya dawo, ko barin mutum ya huta baxaiyiba mutum sai kace karfa"
"Zahra don girman Allah ki bude kofar nan ni bbu Abunda xan miki kawai dumin jikinki nakeso naji"
Limshe idonta Zahra tayi tace
"Promise"
"Promise"
Mas'ud ya fada yana maida kwallan daya taru a idanunsa
Ace mutum da matarsa bbu hali ya biya dukkan bukatunsa sai an mishi korafin gajiya
Bude kofar da Zahra tayine ya sanya Mas'ud gimtse tunaninsa yabi bayanta
Haye gadonta yayi tareda bude mata hannunsa bbu musu ta shige ya matseta a kirjinsa
"Yanxu Zahra haka xan kwanta da wutar sha'awa tana huruwa a jikina"
6ata rai Zahra tayi tace
"Amma kasan ina mugun kokari, bukatar kace tafi karfina ka tausayamin mana gashi kuma kasan lalurar danake dauke dashi"
Mas'ud ba kara cewa komai ba har sa'ilinda yaji saukar numfashin Zahra a kirjinsa alamu tayi bacci kan ya lula kogin tunani
"Mahbub baka daukeni amininka ba kenan, tunda har kake kokarin boyemin abunda ke damunka"
Yake Mahbub yayi yace
"Mas'ud bawai ina boye maka damuwata bane, banaso kaima ta rabeka ne"
Riko hannun Mahbub Mas'ud yayi yace