Kosan Dankali + nama
KAYAN HADI
DankaliNamaKwaiAttaruhuAlbasaMaggiGishiriMan gyaďaFulawa ko garin busashen buredi
*YADDA AKE HADA WA*
Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya sai ki zuba maggi da gishiri ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki jajjaga tare da albasa da attaruhu idan yayi laushi sai ki kwashe a kwano ko roba,sannan ki dawo kan dankalin turawa ki tafasa yayi laushi sai ki murmushe shi ko kuma ki jajjaga a turmi sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika jajjaga sai ki ďauko kwai ďanye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busashen buredi a ciki ki sa gishiri da maggi ki juya sosai, ki ďauki farantin suya ki zuba man gyada ki ďora a kan wuta ki dinga ďiba kina zuba wa a cikin man gyada mai zafi idan ya soyu zaki ga yayi brown sai ki kwashe kiyi wa Oga yayi breakfast dashi.KOSAN DANKALI
*KAYAN BUKATA*
Dankalin turawa NamaFulawaKwai Albasa AttaruguGishiri MaggiMan gyada
*YADDA AKE YI*
Ki jajjaga albasa da attaruhu ki kwashe a kwano ko roba sai ki ďauki dankali ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attaruhu da albasa ki tafasa nama shi ma ki daka a turmi duk ki hada da sauran kayan hadin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan kwai ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man gyada mai zafi ki soya , akwai daďi matuka...KOSAN DOYA
KAYAN HADI
DoyaKwaiNamaFulawa Albasa AttaruguGishiri Maggi
*YADDA ZA'A HADA*
Ki fere doya ki dafa ta sai ki daka sama sama ko kuma ki murmushe sannan ki samu albasa da attarugu ki jajjaga ki hada da doyarki da kika daka ki sa maggi da gishiri, ki tafasa nama ki jajjaga a turmi ki kwashe ki zuba a ciki ki juya sosai sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan kwai sai ki jefa a fulawa ki saka a cikin man gyada mai zafi ki soya shi, idan yayi brown sai ki kwashe daga cikin man gyadan,,wannan girke kam ba za'a bawa yaro mai 'kiwiya ba
VOUS LISEZ
KOSAN DANKALI2
حركة (أكشن)Kosan Dankali + nama KAYAN HADI DankaliNamaKwaiAttaruhuAlbasaMaggiGishiriMan gyaďaFulawa ko garin busashen buredi *YADDA AKE HADA WA* Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya sai ki zuba maggi da gishiri ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki ja...