Page 7

230 25 2
                                    

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
  
                
           7                  
Nan yasaki kuka  mai ban tausayi, jijigata ringayi sai yaga tasaki ba ko alamar motsi atare da ita, da sauri ya dauketa yayi gun rafin da ita yana isowa yaga wani dan tsoho yazo diban ruwa a gora, tsohon nan, ganin halin da Ammar ke ciki yasa yace subhanallah bawan Allah mai yasa meta Ammar kasa magana yayi sai hawaye:'(:'(wani na bin wani, tsohon na ganin halin da Ammar ke ciki ya dibi ruwan goransa tare da bisimillah ya watsamata sau 2 nan take ta saki ajiyar zuciya mai karfi, muryan ta ya dishe, ga jikint ba kwari duk ya mutu, ahankali take magana sai da Ammar ya sunkuyo dai2 bakinta kafin yaji mai takecewa wayyo kafarta, ammar da sauri ya riki kafar sai a lokacin tsohon ya lura da kafan yace yasalam mugani ya rike kafar wan nan ae cizo kunama   ne ya daneta, yace yanzu ku biyo ni in taimaka mata, ammar ya dauketa suka bi tsohon.
A cikin garin kaduna kuwa, su baba sani sun shiga sabon rayuwa mai dadi da dukiyar da suka dade suna mafarkin samunsa, Sadiya sam nataji dadin yanda Abbanta ke zakewa akan dukiyar dan uwansa ba, tunda ba a ga Autaba kuma hakan bai tabbatar da cewa ta mutuba, abin duniya duk ya isheta, haka rayuwa ta kasance musu cikin nishadi har sun manta da wasu wai su Al-hassan da fatima da wata diyarsu Zainab bare Ammar dan kallo.
Ammar ko haka yabi tsoho nan sunyi tafiya mai nisa sosao kafin suka shigo wani karamin kauye wanda gidajen ciki baifi a kirga ba, in kazo gida daya sai kayi tafiya mai nisa kafin ka iske diga daya, ko da suka isa kofar wani diga an masa rufi da da ciyawa sai katangan kara aka dan zagaya gidan naki biyu ne a gidan sai dakunan kaji  da baru  yan kanana da agwagi , suna sallama wata yar tsohuwa ta fito daga dakin danake zaton nan ne gurin kwanan su, tace lale maraba baki mukayi, ganin Ammar rike da joda ga jini ajinsu duka yasa tace lfy kuwa, suwaye wayan nan, tsohon nan yace bakine da sauri ta dauko taburman sakar kaba ta shinfuda musu, ammar ya kwantar da Auta tsoho nan daki ya shiga ya dauko wani yar jakar fata, ya dauko magani da nan ya kama kafar ya matse gun cizon saiga karin ya fito nan ya sake matsewa har sai da Auta tayi kara ta kan kame Ammar sai zufa tayi, saida yacire yashafa mata magani, san nan yasa inna laure ta dafa
Musu ruwan zafi ta kawo masa kadan a kofi ya saka magani yabama Auta da kyar ta iya shan maganin tana runtse ido.

AMANA TA CEWhere stories live. Discover now