Page 12

206 25 0
                                    

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
  
             
           12                
Muna isa gd wata mace kyakyawa ta fito, tace sannu da dawowa Abban Auta ya hanya, cikin sakin fuska ya amsa lfylau Alhamdulilah, tace ina kasamo kyakywan saurayi haka, dad yace mushiga ciki tukun, Allah sarki Dad gwanin taimako. Ko da suka shiga cikin gd abinci ta kawo musu nan Ammar ya faraci daman da dan yunwa ajikinsa, har saida dad ya tausaya masa sosai,
bayan ya sun ci abinci ne dad yace suje falo koda sukaje nan ya tambayi Ammar mai yasa yake kuka da ya tambayesa, san nan ina iyayensa, nan idon Ammar yaciko da kwalla, dad ya rararshesa, Ammar ya basu lbr iyayensa dad saida yayi kwalla ya tausaya masa, kafin yace ya kwantar da hankalinsa zai rikesa, bisa “AMANA” nan Ammar yayi godiya dad ya kaishi dakin da ke waje gefen na masu gadi ya ce ya zauna anan.
        Dad ya saya ma Ammar kaya bana wasa ba haka ya cigaba da rayuwa acikin gidansu Auta gashi sun shaku da Auta sosai, a iya zamansa a gd yanda yasamu lbr a gun dad wata rana suna zaune ya soma bashi lbrsa dake sun saba sosai2 dad ya ja shi ajiki,..
Ammar sai da ya kurbi surki mai zaki yaji suga kafin ya ci gaba da cewa barin baku lbr Auta a takaice
Wacece Auta Zee
Asalin Alhaji Al-hasan Kano haifefan dan garin kano ne, zama ne ya kawo su kaduna dake yayi karfi anan yake kasuwancin sa, tun da ya dawo kaduna bayan rasuwan iyayensa , sai ya dibo yan uwansa ya sasu akan dukiyarsa, mahaifiyarsh ita kadai ta haifa yayinda yake da yayu yan uba wato Sani da Isiyaka uwar su daya yayinda Sani shine babba sai Baba isiya ka,
     Baba Sani yana da Yaya 4 Sadiya itace baba sai kabir san nan Anas sai Autarsu Sa’dat sun kasance abin so gun iayensu da kulawa Baban Auta shi ya dauki nauyin karatun Sady ya hada su da Auta gashi jininsu yazo daya baka rabasu ko ina taresuke,.
Baba isiya kuma matarshi daya da yara 2 Fauziya ana kiranta da pinky sai kan warta faima sina kiranta da faty, haka rayuwa tayita tafiya.
    Dad ya kasance mai yawan taimako da son talakawa sabanin yan uwasa da ko kyauta yayi sun rinka mita kenan basa son ganin wani ya rabe shi baran in yana taimaka masa,
tun randa suka san dad ya kawo gdn suka fara hada rai in ko mun gamu zagi da hantara ba wanda ban sha duk in kauda kaina sabida dad ya rikeni da “AMANA” hakan nazamo mai aika a gd kuma wani lokaci mina tare da auta da Bilisu kawarta yar makwabtasu wato yar inspector Abubakar bilki kasancean sunan Maman Babanta ne shiyasa suka boye sunan ana kiranta da futha wato fatuhatul-khair, ba karamin shiri Futha da Zee Auta sukeyiba, haka Ammar yana ji da ita.
Hajiya Aysha itace Maman Auta ita kadai Dad ya aura tun aurens da yan watanin Allah yabata cikin cikin ikon Allah cikin baizo da wani laulayiba, nan tayita kula cikin koda wata haihuwanta yazo nan ranan nakuda ta kamata basu jima da zuwa asibiti ba ta haifo yan biyunta kyawawa mace da na miji murna gun dad ba’a magana nan suka dawo gd, tun kafin suna na mijin ya rasu ya rage sai mace, mum tayi kuka daga karshe ta hakura ranan suna yar taci sunan zainab zainab wata ta 4 ta kamu da rashin lby, asai bana tashiba basuyi dogon jinya ba Allah ya karbi abusa, tun bayan rasuwansu hajiya bata sake ko bariba sai bayan shekara 5 ta samu cikin Auta nan suka dau son duniya suka daura akan cikin nan bayan wata tara ta santalo yarta kyakyawa nan taci sunan Zainab, haka sukayita rai non xee harta girma.
Tun da na dawo gd Alhaji ya mai dani makaranta nan nacigaba da karatuna ina dawo inyita wasa da Zee da futha, ko muyita karatu haka rayuwa tayita tafiya
        Su baba sani basuda birin da yawuce suga na bar gun dad don ba zan manta ba akwai randa suka min sharrin sata ranan nayi kuka kamar raina zai fota.

  
Rash Kardam

AMANA TA CEWhere stories live. Discover now