Y'ER ZINA CE (kaddarar iyayena)

1.6K 86 5
                                    

*Y'ER ZINA CE*
         _(kaddarar iyayena)_

*muneera*

wattpad👉🏻fatimamuneera001

Pg~2

Tunda sakina ta fita kaka ta mike ta fara kokarin dora musu abincin da zasu da dare shuru-Shuru taji sakina bata dawo ba tana wanan tunanin ne taji sallama sakina a jiyar zuciya ta sauke kafin kakar ta fara yiwa sakina kallon tsaf kamar tana nazarin wani abu, kakalo murmushi sakina tayi tace kaka yadai, kuma zuba mata ido tayi tana kara nazarin ta.
   Sakina ya akai kika jima haka, seda ta danyi shiru sanan tace da baje baya nan seda na jira ya dawo kakata kije ki zauna nizan cigaba da girkin komawa tayi ta zauna kamar yarda sakina tace Kafin wani dan lokaci tuni Sakina ta gama girkin tana saumewa ta shige bayan gida domin yin wanka da dauro alwala ta fito a lokacin iskar La'asar har tasa kaka yin bacci har sakina ta iddar da sallah
Kaka na kwnce dan haka seta lalaba tare da daukar abincin sir hashim tai gidan a bude gidan yake dan haka kawai seta sa kai dakin nasa ta shiga kwnce ta ganshi da waya a hannu yana wayar yana lumshe ido da Alama dai yana jin dadin wayar katse wayar yayi yana fadin malama sakina sannu da zuwa Amsa masa tayi kafin ta ajiye kwnon tana cewa mlm hashim inason insan waye kai pls kallon ta yayi da murmushi sanan ya fara magana kamar haka
    "sunana dai hashim da daya tilo a wurin iyayen shi asalin mu daga mamana har babana yan kano wato haifafun kano ni kadai Allah basu daga kaina kuma basu kara samun haihuwa ba dan haka banida kanwa koo kani na taso cikin kadaici da sha'awar dama inada yan uwa musaaman ina shiga dangi naga kowa da dan uwanshi babana ma'aikacin gomnati ne mamana kuma likitace toh kinji takaitacen tarinhi na" ya fada yana sauke numfashi sanan yace ke kumafa 'Dan murmusawa tayi kafin tace malam
    " ni sunan sakina  Muhammad iyayena y'an asalin nan madubi ne babana fatauci yake sunyi auren soyaya kafin mamana ta samu cikina wurin haihuwata Allah ya mata rasuwa lokacin da babana labarin mutuwar mahaifiyata yaje masa shima zuciyar ta buga ya rasu  yanzu ina wurin kakata ne a zaune  a wurinta na taso komi ita take min harda ma bokon nan ita tasani duk da cewa yawancin mutanen kauyen nan basa barin yaransu suyi karatu Amma ni kakata ta sani saboda tana da burin taga nazama likita"
     "sakina" hashim ya kira sunan ta "a shirye nake na aure ki kuma a shirye nake na kalubalanci ko wace matsala akanki  murmushi tayi ta dan sukuyar da kanta tana mai jin dadin cewa yanzu kamar hashim dan gayu dan birni irinshi ze auri y'ar kauye irinta anya ba yodurar ta ze ba. Kamar yasan metake tunani yace ki cire tantama sakina bazan yodare ki ba auren ki nake son yi mu rayu tare mu kuma mutu tare tun lokacin da na ganki sakina naji ina son ki so bana wasa ba ki yarda dani bazan cutar dake ba" numfasawa tayi tana kallon kwyar idon shi tsantsar gaskiya ya hango ta cikin idon shi duk da har yanzu tana tantama zuciyarta bata gasgata abinda ya fada ba din "Sakina  inaso zanje wurin kakarki mugaisa" dago kai tayi suka hada ido sanan tace toh a sanyaye jiki ba kwri dan se yanzu ta gasgata kalaman sa da taji ya ambaci zeje wurin kakar dan girgida kai kawai tayi sanan  Tamasa sallama ta koma gida
    "sakina kaka ta fada cikin tsawa nagaji da fice-ficen nan naki kinji koo bana son shashanci da rashin kamun kai ki nutsu na fada miki" zunbura baki tayi "ai dama nasan basona kike ba ke kullum se kinyiwa mutum fada gaskiya ni kaka bana so ta fada" tana buga 'kafaa "Sakina ai mutumin da ake masa fada dan gata ne ba kadan ba wallahi saboda a wanan zamanin wasu ma suna nan suna neman masuyi musu fadan amma basuda shi ke kuwa da ake miki har kike wanan iya shegen ki sani sakina baki da uwa bakida uba se ni nima kuma so kike na fadi na mutu ki huta shikenan ai zunbura baki tayi tana shigewa daki domin ita a ganinta kaka ta fiye masifa


_______________________

Shiryayen bikin hashim momy ketayi gidan duk ya taru da jama'a dan befi saura sati 3 a daura aure ba yana dawowa kenan zasu fara shagalin bikin yan uwa na nesa duk sun fara zuwa yayinda zakadidyar amaryar tashi domin kuwa auren zuminci zaa musu yar kanwarta ce sedai fuskarta ba walwala sanadiyar tunda hashim yaje garin can baya daga kiranta sosai a ranta kawai taji anya ba garin zata bishi ba(🙄nida ke gefe nace kyje ki ganowa kanki bakin ciki😂domin yana can yana holewarshi da sakina yar fulani) 

    Ana sallama da sakina yaron ya fada kaka seda taji gaban ta ya fadi tace wai injiwa ,yaron yace inji wanan dan gayun da yazo.... Kaka tace kace ya shigo ciki..........

Fatiman ku ce👌🏻

Y'ER ZINA CE (kaddarar iyayena)Where stories live. Discover now