part 2 page 12

676 46 5
                                    

*Y'AR ZINA CE*
    _(KADDARAR IYAYENA)_

*NA*

*MUNEERA*

_Wattpad👉🏻Fatimamuneera001_

*PART 2*

_PAGE 12_

'''After one month'''

Zuwa wanan lokacin meenat tafara sakin jiki da yazeed  bawai tafara sonshi bane dukda ba gari daya sukeba but every weekend yana kano saboda meenat.

Ton tana wulakanta Aliyu tanaqin daukar wayarshi, idan sun hadu a waje ta shareshi koda yai mata magana, sauda dama yasha binta school danko gadinta yafarayi dawuri yake shirin zuwa office saiya packer mota yazauna a ciki dazaran yaga driver meenat yafito saiya bisu a baya har school.

Amma duk abinda yakeyi a banza danko meenat bata sauraran'shi, yanda yake turo mata text messages na soyayya dakuma ban hakuri akan ta dinga daukar wayarshi hakan yasa meenat tausaya mishi harta fara daukan wayan amma abunda yabata mamaki shine tana daukan wayan Aliyu ya saka kuka yana fadin haba meenat abinda kike kina ganin yadace kinsan yanda kike azabtar da zuciyata kowa?
Meyasa kike wulakantani bayan bani nasa ma zuciyata kaunar kiba, Allah ne ya jarabceni dan Allah kiye hakuri ki sasautamin ki amsa soyayyata bazaki tabayin dana sani ba dan'Allah meenat

Tausayin Aliyu ne yacika zuciyarta gaba daya sai taji tana matukar tausaya mishi wai itace namiji kema kuka yau...Allah sarki

Cikin sanyi murya meenat tace dan'Allah kadaina min kuka fadamin me kakeso amma banda maganan soyayya dan meenat bata soyayya bazata iya mallaka wa kowa zuciyarta ba.

Dogon ajiyar zuciyar yasauke kamar zaice wani abu saikuma yace to shikenan amma dan'Allah na rugeki kidinga daukar wayata sanan duk sanda nazu nimanki kifito kitaimakamin meenat ne kaina bansan irin kaunar da nake miki ba

Tsintar kanta tayi dajin tausayinshi cikin sanyin murya tace to shikenan

Kamar yanda Aliyu ya roga meenat akan ta amince mishi yadinga zuwa gurinta haka kowa akayi ta amince mishi yana zuwa amma a kwanakin da yayi yana zuwa babu abinda ta lura dashi bayan tsan'tsan kaunarta a zuciyarshi tabbas a yanzu ta yarda Aliyu na sonta so mai karfi wanda ita kanta abun nabata tsoro.

Kamar kullum motar gidanso ta danno kai waje dan kaita makaranta dasauri Aliyu yafito daka motar shi sanan yakarasa gurin motan

Knocking window yayi hade da kallon meenat yana smiling, itama kallonshi takeyi saboda yayi mata kyau

Aliyu dai baqi ne amma kyakyawan ne wanda samun irinshi a cikin baqaqe zaiyi wuya, murmushi dauke a fuskar meenat tabude motar tafito

Atare suka furta kinyi kyau... Kayi kyau...

Murmushi tayi sanan tace nikam babu wani kyau da nayi amma ka ganka kowa barin maka hoto, nanta shiga kashe mishi hoto sanan sukayi wasu tare.

Agogon hannunta ta kalla kana tace yakamata natafi karnayi late
Hannu ya daga mata game daciwa
Ok byee
I luv you
Murmushi tai batare da tace komai ba

Kwance Aliyu yake a bed sai juye'juye yake yana tunanin yanda zai bulloma lamarin meenat, shi kanshi besan wani irin so yake mata ba tabbas bashi dawani buri daya wuce yaga ya mallaki meenat amma ya zaiyi? Wani tunani yayi wanda yasa yasauri ya mige tsaye yana fadin yauwa ina ganin zansamu mafita ta haka, cikin hanzari yafita daka dakin.

Babban parlor yanufa inda ya iske iyayan nashi su uku suna zaune hira(Maman Aliyu tana da kishiya itace uwargida amma zaune suke lafiya ba tashin hankali akwai fahimta mai karfi a tsakaninso)

Y'ER ZINA CE (kaddarar iyayena)Where stories live. Discover now