31 - 41

3.9K 135 0
                                    

[6/16, 10:29 AM] Aishat Muhammad: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

31...

Suna cikin mota Yusuf ke driving wayarshi tai kara dan karamin tsaki yaja sanan ya ijiye, Yusuf dake tuki ne ya kalli Screen din yana ganin number yagane, kallonshi yay baice komiba ya cigaba da tuki har suka kai gida inda kaninshi da Goggo da Umma ke tambayar lafiyan shi.

Around 8 nasafe ya shigo hospital din yana sanye da dark blue yadi da akamai half jumper sai uban kamshi yake, tura kofar yayi da sallama Anty Hindu ce ta amsa, kwance ya ganta idanunta biyu tayi filo da kafar Anty Hindu tana danna waya batare datako dago kai ta kallai ba, Anty Hindu cike da fara'a tace "barka da zuwa Khaleel, ya karfin jikin naka" murmushi yay yace "Alhamdulillah ina kwana Hajiya ya masu jiki" Anty Hindu tace "gatanan taji sauki Dr ma muke jira yanzu za'a sallamemu" daka mata duka Anty Hindu tayi abaya tace "baki iya gaisuwa bane" shafa wajen tayi sabida yanda dukan yamata zafi sanan tadan juyo ta kallai da sauri ta dauke kai, turo baki tayi tace "gud morning" kasa dauke ido yayi akanta tana sanye cikin bakin doguwar riga mai stones fuskar ta yay fayau, maganar Anty Hindu ce tadawo dashi duniya tace "bari naje office din Dr nagaji da jiranshi" daga Islam daga cinyarta tayi ta sauko daga gadon tafita daga dakin tana murmushi. Ahankali ya karaso gaban gadon yay folding hannu a kirji yana kallon fuskarta dena danna wayar datake yi tayi tadan dago kai ta kallai kafin ta kawad dakai da sauri, fari tai da ido tace "kadena kallona, zaka shanyemin jini kawani tsaya akaina kaman soja" murmushi yayi sanan yadan zauna abakin gadon ya kalleta ahankali yace "yea am one" da sauri ta kallai gyada mata kai yayi yana murmushi kawad dakai tayi da sauri ta cigaba da danna wayarta tana tabe baki, ahankali yace "Ummi" ajiyewayar tayi ta kalleshi sabida yanda yakira sunan har zuciyar ta saida taji kawad dakai tayi tace "Abba na kadai ke kirana da sunan nan dan haka kadena" sosai takejin haushin shi sabida shi har yanzu Fahad yaki daukar wayarta. Ahankali yace "ya jikin?" kin magana tayi hakan yasa yace "are you angry sabida yaki daukar wayar ki?" da sauri ta kalleshi mutum kaman maye hararan shi tayi tace "injiwa Fahad baya iya fushi dani" murmushi yamata dawata irin murya yace "amma ai nafishi sonki" yakarashe maganan yana langabar dakai dauke kai tace "kaga karabu dani I don't want to talk to you" da sauri yace "are you sure?" dago kai tayi ta kalleshi suka hada ido, kusan 30sec sukayi suna kallon juna ita tafara kawad dakai, ahankali ta juyamai baya tana facing bango batare datace komiba, dan ajiyar zuciya ya sauke ya mike tsaye yace "am going take care" yafara tafiya, ko taku biyu baiyi ba yaji tace "thanks for saving my life yesterday" shiru tadanyi ahankali kaman bata so yaji mezata ce tace "am grateful" dan juyowa yayi ya kalleta har lokacin bata juyoba fuskarta na facing bango, komawa yay jikin gadon ya tsugunna yadan daura kanshi akan katifar ahankali yace "look at me Ummi" yanda yay maganar yasa taji gabaki daya jikinta ya mutu, murya chan kasa yace "turn" kaman magic ahankali ta mirgino tareda daura kanta akan filo da idanunta dasukai kaman tanajin bacci ta kallai, dudda kanshi nata bakin gado bai hanashi jin dan karan numfashin ta dake fita ahankali ba, dawata irin murya dake ratsa gabobi yace "I love you" dan lumshe ido tayi kafin ta bude su kadan ta daura akanshi, ahankali ya kwantar da fuskarshi anan bakin gadon yana kallon fuskarta, hanunshi ya mika ahankali ya daura akan filon da kanta yake ya ijiye ahankali yace "will u marry me? " Ahankali tadan matso da fuskar ta wajen hanunshi tana kallon fuskarshi da idanunta dasuka kankance kaman zatai bacci batare datace mai komiba, hancin ta ta daura akan yatsar shi tana shakan sassanyar kamshin da hanunshi yake tana kallonshi, shima ita yake kallo da kwalla dayaji ya cikamai ido, kara matso da fuskar tayi ahankali ta saka fuskarta akan tafin hanun nashi tana kallonshi.
[6/17, 4:09 PM] Aishat Muhammad: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

32 & 33

Kaman mai rada yace "I love you so much, zuciya ta bazata iya jure rashin kiba, nasan baki sanni ba but please give me a chance, ina sonki sosai" dan hawaye taji ya gangaro mata, girgiza mata kai yayi ahankali yace "will u marry me please" dan lumshe ido tayi tareda dagamai kai maganar Anty Hindu dataji tawaje ya mai do da ita hankalin ta da sauri ta tashi ta zauna ta kawad dakai kirjinta na bugawa sosai tashi tsaye yayi shima yana kallon fuskarta, bude kofa Anty Hindu tayi ta shigo ita da Dr, dubata Dr yayi sanan yace "Hajiya babu wata matsala, nan da yan kwana biyu yan ciwukan nan zasu warke zaku iya tafiya" Anty Hindu tace "to nagode Dr, bari nakira Bala yazo ya dauke mu" da sauri Khaleel yace "basaikin kirashi ba nina kaiku Hajiya" yay maganar yana kallon fuskar Islam da har yanzu taki kallonshi, "to shikenan, ke tashi mutafi" ahankali ta mike tsaye tadau Hijabin ta tasaka shiya fara fita sai ita da Anty Hindu dasuka fito suna biye dashi abaya kofar baya ya bude musu suka shiga sanan yarufe sanan yakoma gaba yabude motar ya shiga ya kunna yafara driving har suka fita daga hospital din, ta mirror gaban mota yaketa kallonta amma taki dago kai saima wasa da yatsun ta da taketayi, har cikin compound ya shiga dasu suka fiffito da sauri tai cikin gida dan bataso su sake hada ido, Anty Hindu ce tamai godiya cike da fara'a da addu'a sanan ya kunna mota yafita daga gidan.
Afalo taga Farida ta zauna taci uban tagumi tsakanin jiya da yau duk tai zuru zuru tana ganin ta ta taso da gudu ta rungumeta tsam tsam sakinta tayi ta kalli fuskarta tace "sannu Islam ya jikin?" dariya ma tabama Islam hakan yasa tai dan dariya tace "ke dalla am fine ciwo fa kawai naji, Ina Mum?" jiki a sake tace "tana daki" tace "bari naje na gaishe ta" sama tayi saida ta gaida Mum tamata ya jiki sanan ta wuce dakinsu bayi ta shiga tai wanka da ruwa mai dumi sanan ta fito, light kaya tasa tazo ta kwanta akan gado dan bacci takeso tayi ta lumshe ido, fuskar Khaleel tagani yana mata murmushi da sauri ta bude ido tajuya dayan gefen tasake lumshe ido tuna sanda ta daura fuskar ta akan hanunshi tayi, bude ido tayi da sauri ta tashi ta zauna tareda jan uban tsaki dan mugun haushin kanta takeji tayaya ma tai hakan wat was wrong with her, waya ta dauka tasake dailing number Fahad bai dauka ba, message ne ya shigo wayar ta bude bakuwar number ce hakan yasa ta bude "I love you so much. Khaleel" wirgi tai da Wayan akan gado tareda yin tsaki "mutum sai shegen naci anaci"

JARABTA Where stories live. Discover now