Tsatuba part3a

473 11 2
                                    

TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part A.
.
Koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya mike
tsaye
ya fice daga cikin turakar ita kuma ta bishi da kallo
kawai cikin alamun tsananin damuwa da tashin
hankali
kamar yadda sarki shardas ya bukata haka al
amarin
ya kasance,
wato daga wannan rana suka ci gaba da renon
juna biyun nata tare, ya zamana
cewa fiye da rabin rana sarki shardas na bata
lokacinsa tare da shadila,
yana bata kulawa ko yaya yaga wani abu na
damunta
take zai tura a kirawo likitoci su dubata
sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba
aje ba
kwana a tashi sai cikin shadila ya tsufa
ya zamana cewa bata iya yin komai da kanta sai
dai ayi mata
A ranar da cikin ya cika wata tara da kwana tara
ne
nakuda ta zo mata, tana fara nakudar sai kawai
akaga yanayi ya sauya ba tare da wanzuwar
hadari ba ko tasowar iska sai akaji an fara tsawa
da
walkiya ; al amarin da ya razana jama'a kenan aka
kama guje guje
A wannan lokaci da rana ne tsaka ana ta gabatar
da hidimomin yau da kullum, nan fa kasuwa ta
watse
jama'a suka rinka rugawa izuwa cikin gidajensu
suna
rufe kofa wasu kuma suka ruga izuwa fada domin
a sanar da sarki abindake faruwa don ana zaton
ko
allolin da ake bautawa ne a kasar suka yi fishi
zasu
hallakar da mutanen kasar
Koda jama a suka iso fada sai suka iske boka
marwas a tsaye a tsakiyar fadar shi kadai fuskarsa
a murtuke yana muzurai
koda ganin haka sai jama a suka zube kasa a
gabansa
aka yi tsit kamar mutuwa ta gifta, wani tsoho mai
shekaru da yawa ya dago kai ya dubi boka
marwas yace ya kai dirkar birnin
Romaniya wannan kuma wace irin masiface tazo
mana?
Ta yaya tsawa mai ban tsoro gami da walkiya
suke faruwa
a sararin samaniya alhalin babu ko alamar hadari?
Koda jin wannan tambaya sai boka barwas ya
bushe
da dariya
Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan
boka barwas ya turbune fsuka yace matar sarkice
zata haihu yu
zata haifi wani yaro dan baiwa wanda sunansa zai
shahara
a ko ina cikin wannan duniya
daga yau za a sami yalwar arziki a wannan birni
namu mai
albarka
za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali irin
wanda ba a taba samu ba har izuwa ranar da
wannan
yaro zaiyi wata tafiya
manufa ya fita daga cikin wannan gari namu
koda jin wannan batu sai mutane suka rasa abinda
zasuyi
tsakanin murna da bakinciki domin ta leko ne ta
koma,
babban abinda ya dugunzuma hankalin mutane
a cikin bayanin boka barwas sunji cewar da zarar
wannan
yaro da za a haifa ya bar birnin duk farin ciki zai
yaye don haka sai wasu suka
fara tunanin to ai gwara rashin aihuwar yaron da
dai
a shiga farinciki da farko a karshe kuma a shiga
tasku
Nan fa mutane suka kama kace nace kowa na
fadin albarkacin bakinsa
Ana cikin wannan haline aka yi wata irin tsawa
mafi
karfin gaske wacce ta firgita komai da kowa har
gidajen birnin gaba daya saida yayi rawa, kasa
tayi girgiza bishiyoyi suka kama cin wuta
dabbobi suka kama guje guje suna shigewa
maboya, mutane kuwa suka rude
suka dimauce kamar zasu haukace, A dai dai
wannan lokaci ne kukan jaririn
Shadila ya cika birnin gaba daya har da amsa
kuwwa
izuwa cikin dazuzzuka
Faruwar hakan keda wuya sai aka kece da ruwan
sama
kamar da bakin kwarya wata irin iska mai dadin
sanyi ta rinka kadawa kamar ana cikin tsakiyar
damina alhalin ana ranine kuma a lokacin zafi ya
addabi mutane
faruwar wannan sabon yanayi keda wuya sai
murna ta kama kowa gami da mamaki nan fa
jama a suka ci gaba da cincirindo a kofar gidan
sarautar birnin kowa burinsa shine yayi arba
da wannan sabon jariri da aka haifa ko ya sami
tabarrakinsa domin tuni kowa ya gama yarda cewa
wannan jariri dan baiwa ne tunda gashi ni'ima ta
sauka a birnin a irin lokacin
da ba ataba samunta ba
shi dai wannan ruwan sama da ya sauka ba ruwa
bane daga Allah, ruwane daga shaidanu domin
kawai su juyar da hankalin mutanen dake wannan
nahiya su dada dulmiyar dasu a cikin hanyar
bata mabaiyaniya tunda sunyi imani da shaidanun
a matsayin ababan bautarsu,
bayan kofar fada ta cika makin
da mutane
ana ta turereniya, gashi ruwan sama na dukan
mutane sanyin iskar dake kadawa har ya fara
addabar
jama'a
amma saboda naci sunki su tarwatse sai
tsulum akaga sarki shardas ya fito daga cikin gidan
sarautar dauke da jaririn da shadila akan tafin
hannayensa
jaririn tsirara yake ko al aurarsa ba arufe ba
ga sabon yankan cibi a jikinsa ruwan saman nata
dukan jaririn amma ko a jikinsa sai dariya yake
kyakyatawa
yana ta wutsil wuts irin ta jarirai masu koshin lafiya
koda sarki shardas ya iso gaban dandazon jama'a
sai ya daga jaririn sama yayi kuwwar murna
take jama a suka amsa masa kuwar muryoyinsu
suka cika birnin gaba daya sai da aka yi haka har
sau
uku
sannan sarki shardas ya mikawa boka barwas
jaririn ya karba,
ya fuskanci jama a yace yaku jama ar wannan
birni
na
Romaniya kuyi sani cewa yau allolinmu sun dubi
kukana sun bani da alhalin na shafe shekara
da shekaru ina neman haihuwar ban samu ba ina
mai tabbatar muku da cewar wannan da
dana samu rahama nega kasarmu gaba daya don
haka ina son kowa ya kaunaceshi kamar yadda
zai kaunaci dan cikinsa,Koda sarki shardas yazo
nan
a zancensa sai jama'a suka amsa masa da cewar
sunyi Alkawari zasu so wannan da tamkar dan
cikinsu.
Cikin matukar murna sarki shardas ya juya ya dubi
boka barwas ya mika masa hannu domin ya karbi
jaririn
kawai sai yaga fuskar boka barwas a murtuke
babu annuri nan dai ya karbi jaririn ya sallami
jama'a kowa ya watse aka tafi
ana ta murna ana ta kade kade da bushe bushe
bayan jama a sun watse sai sarki shardas da boka
barwas
suka juya suka nufi cikin gidan sarautar suna
masu jera kafada
tsawon dan lokaci suna tafiya dayansu baice
uffan ba
sai sarki shardas ya dubi boka barwas yace
yakai abin dogaro na yakai shamakin dake
tsakanina da allolinmu ina son ka gaya mini
dukkan
dalilin da yasa ka murtuke fuskarka a lokacin da
na umarci jama a dasu so wannan jariri na shadila
koda jin haka sai boka barwas yayi doguwar
ajiyar zuciya sannan ya dubi sarki shardas cikin
alamun takaici da damuwa yace ya shugabana ai
wannan abu da kayi shine babban kuskurenka na
farko
a kan wannan yaro da aka haifa, shin ka manta ne
cewa a duniya kaf baka da wani makiyi wanda
yafi wannan yaro? Shin ka manta ne cewa a halin
yanzu
yana matayin danka ne na cikinka, tabbas yadda
suke son
ka kuma zasu so ya gaji karagarka anan gaba, a
lokacin
da ni dakai zamu yi shiri mu tafi neman hular
lamsara
shine zai hau karagarka ta mulki kuma idan muka
je muka
samo hular lamsara muka dawo saukeshi daga
kan
karagarka ba abu bane mai sauki duk da cewar
zamu
iya hallakashi farat daya a wannan lokaci
saboda zamu fuskanci fishin jama a domin a
sannan suna kaunarsa fiye da kai
kuma suna matukar jin dadin mulkinsa, dolene
sai daimu hallakashi a sirrance ta yadda babu
wanda
zai gane cewar dasa hannunmu, ni abinda nake
so
dakai kawai shine duk yadda za ayi kada ka
kuskura
wannan yaro ya san cewa ba kai bane uban sa ba
har izuwa
tsawon shekaru bakwai da zaka rabu dashi
akwai ragowar kurakurai guda biyu wadanda bana
son kayi kuskuren aikatasu, a nan gaba domin
idan
ka aikatasu tofa koda ka mallaki hular lamsara
saimun
sha bakar wahala kafin mu sami nasarar hallaka
wannan yaro
Auwzab nake Typing, kuskuren kuwa shine kada
ka
kuskura ka bari son wannan yaro ya shiga ranka
domin hakan zata iya faruwa
don yaron zai taso da tsananin farin jini da shiga
rai
Akwai wani magani da zan baka ka rinka sha
bayan kowane kwana talatin, indai kana shan
wannan akan lokaci babu yadda za ayi son
wannan yaro ya shiga ranka
shi kuwa kuskuren da zaka yi na uku ba yanzu
zan sanar dakai ba sai idan lokacin da ya dace ka
sani yayi
Koda jin wannan batu sai jikin sarki shardas yayi
sanyi yana mamaki da tunani har suka kule a
cikin gidan sarautar bai kara cewa uffan ba
Da ranar suna ta zagayo sai aka yi gagarumin
taro aka gaiyaci sarakaim attajirai, bokaye, jarumai
da sauran manyan mutane na nahiyar gaba daya
boka barwas ne ya radawa jaririn suna
yarima HULKAS, nan fa aka shiga shagalin suna
sai da aka kwana ashirin da daya kullum ana
gabatar
da walima a gidan sarki abinci da abinsha kuwa
saida
akayi ta almubazzaranci tamkar a bola ake tsunto
su
hatta talakawan gari ma sai da suka rinka shirya
walima tsawon wadannan kwanaki sarki shardas
a cikin tsananin farin ciki yake kai kace yarima
Hulkas dansa ne na cikinsa wato jininsa ne hm
daga wannan rana wani abin mamaki ya fara
wanzuwa a cikin birnin
romani ya zamana cewa fatake suna ta tururuwa
a cikin birnin suna tahowa daga manyan kasashe
na duniya suna kafa tushen kasuwancinsu
a birnin
Nan fa kasuwanci ya sami gagarumar bukasar da
bai taba yi ba a nahiyar
gaba daya nan da nan talauci da fatara suka yaye,
arziki ya yawaita a hannun talakawa, kayayyaki
iri iri akayi ta shigowa da su birnin da hajoji kala
kala, kai irin kasuwancin da baya juyuwa ma a
nahiyar
fiye da shekaru daruruwa da suka wuce sai da
akazo dashi ana yinsu tamkar dama can an saba
dasu
al amarin shadila kuwa itama ta tsinci kanta a cikin
sabuwar rayuwa ta farinciki tamkar bata taba tsintar
kanta a cikin wata damuwa a baya amma da zarar
ta tuno da mahaifin hulkas na gaskiya wato Hailur
saita kefe kanta
a cikin daki tay ta kukanta ta more bata yarda
sarki yasan halin da take ciki
duk da cewar sarki shardas ya fara shan wannan
magani wanda boka barwas ya bashi don kada
soyayyar Hulkas ta shiga ransa saida yaji yana
kaunar Hulkas din tamkar Dansane bana wani ba
a ranar da ya sha maganin ne kadai yake jin ya
tsaneshi domin a ranar ne yake tunawa da cewa
nan gaba fa wannan yaro ne zai kasheshi muddin
bai rigashi mallakar Hular Lamsara ba
a wannan rana daga safiya zuwa dare sarki
shardas
baya kusantar shadila don kada ma yayi arba
da Jarumi Hulkas hmm
Domin zai iya hallakashi nan take saboda
zuciyarsa
tana tafarfasa ne kamar zata kone bisa jin tsananin
kiyayyar hulkas a cikin zuciyarsa kuma jikinsa
na
tsuma da kyarma yana jin kamar idan bai kashe
jariri Hulkas ba shi zai mutu ne a ranar, A kwana
a tashi sarki Shardas yana kiyayewa gami da jure
duk irin abinda zuciyarsa
ke raya masa akan wannan yaro Hulkas har dai
aka sami
tsawon shekara Uku
A sannan ne ya tsinci kansa a cikin tsananin so
da kaunar yarima Hulkas harma yana ji kamar
ba zai iya yin rayuwa ba idan babu shi
wani iko na Allah Kuma sai shima yaro Hulkas ya
shaku da sarki Shardas ya zamana cewa yama
shaku dashi fiye da yadda ya shaku da uwarsa
Shadila har takai cewa ko abinci baya yarda yaci
sai tare da sarki shardas in ba haka ba kuwa sai
dai ya kwana da yunwa
shima sarki shardas din baya iya cin abincin shi
kadai idan ba tare da hulkas ba kai hatta telan
da yake yiwa sarki shardas dinki iri daya dana
Hulkas yake dinka musu kullum
sai dai kaga sunyi anko sunzo fada tare sun zauna
akan karagar mulki duk da rana babu abinda
yake rabasu kullum ..
sai bayan hulkas yayi barci akan kirjin sarki
shardas
sannan shadila ke daukeshi tayi masa shimfida
a kusa
da gadon sarki domin ko cikin dare idan ya farka
baiga
sarkiba sai dai ya fashe da kuka kuma babu mai
iya rarrashinsa yayi shiru face sarki din
ita kanta shadila lokacin da taga shakuwar sarki
da yarima hulkas ta wuce saninta ta wuce duk
tunanin mai tunani sai hankalinta ya dugunzuma
ainun
taji zuciyarta ta fara yi mata gargadi kada ta
kuskura ta sanar da yarima
hulkas asalin abin dake tsakaninsu a nan gaba
idan
hulkas ya girma
A duk sa adda ta tuno da alkawarin da ta dauka
na rufe wannan sirri dakuma
gargadin da sarki shardas yayi mata da
matakin da yace zai dauka idan ta tona sirrin sai
hankalinta ya dugunzuma tayi ta kukan bakin
ciki........
Uhm Allah sarki Shadila Komai Lokacine
A nan ne Kuma Ni nake cewa Sai mun Hadu a
part Na gaba

Tsatsuba part 3Where stories live. Discover now