tsatsuba3e

213 6 0
                                    

TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part.E
Kodayarima basmar yazo nan a zancensa sai
mutumin da matarsa suka dubi junansu sukayi
murmushi
sannan mutumin ya dubi basmar yace hakika
wannan abokin
naka zaisha mamaki kuwa domin a yanzu
hakama tuni
siyama ta shiga gasar jarumtakar da za ayi a
fadar mahaifinka
wacce za a fara gabatar da ita gobe kuma ina sa
ran cewa itace zata karbi kambun
wannan gasa
koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya
kyalkyale da
dariya yace haba ai wannan ma almara ce ya za
ayi karamar
yarinya wacce aka ce batafi sa a taba zata shiga
wannan
gasa wacce manyan mutane zasuyi kuma jarumai
na daga sassa daban daban na
duniya har ace talashe gasar
koda jin wannan batu sai ran mahaifin siyama ya
baci
ya murtuke fuskarsa nan take cikin fushi ya
kwalawa siyama kira
itakuwa
sai gata ta fito daga cikin gidan a cikin shigar
yaki
siyama ta kasance kyakkyawar yarinya ta gaban
kwatance duk da cewar yarinya ce yar
shekara shida sai mutum yayi zaton takai
shekaru goma sha saboda ta kasance
doguwar gaske sai mutum ya dubi fuskarta
sannan zai gane cewa yarinyace tana da
cikakkiyar sura da zati irin na
cikakkun mata ababan kwatance
koda yarima hulkas yayi arba da siyama sai yaji
nan take ya kamu da tsananin kaunarta
amma da yaga ta kalleshi tana mai gabza masa
harara
sai zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya bai
bayeshi yaji kamar ya ruga da gudu saboda
kwarjininta
siyama ta karaso gaban iyayanta
ta risina a garesu tana mai amsa kira kawai sai
mahaifin
nata ya daga sandar dake hannunsa da hannun
nasa lafiyayyan yayi nuni a gareta ko da ganin
haka sai siyama
ta zare takobinta ta kwala ihu sannan ta daka
tsalle sama tamkar daga cikin baka aka harbota
ta fada kansa
suka ruguntsume da azababben yaki mai
tsananin ban tsoro ga dukkan mai kallo
nan fa duk su biyun suka wanzu suna masu
kaiwa junansu mugayan hare hare
cikin bakin zafin nama duk sa adda takobin
siyama ta hadu da sandar mahaifinta sai dai kaji
kal
sautin haduwar karafa gami
da tartsatsin wuta na tashi
tunda yarima basmar da hulkas suke ganin
gumurzun mazaje masu tsananin zafin nama da
jarumtaka ba kamar siyama da mahaifinta
siffanta jarumtakar tasu da kwatantata ba zai
yiwu ba
sai dai abinda idanu suka gani
babu wani jarumi daya fadowa yarima hulkas
a rai dayaga jarumtakar siyama da mahaifinta sai
mahaifinsa sarki shardas
hulkas ya numfasa sannan yace a cikin zuciyarsa
babu
wani jarumi da zai iya fafatawa da wadannan
mutumin ko yarsa siyama ya samu galaba a
kansu face mahaifinsa sarki shardas
kash ina ma tare da sarki mukayi wannan tafiya
da yaga wadannan jarumai masu ban al ajabi
da idanunsa yanzu dama she a wannan duniya
akwai irin
wadannan jarumai
sai da siyama da mahaifinta suka shafe sa a
daya da rabi
suna fafatawa amma dayansu bai sami nasarar
koda kwarzanar jikin
dayan ba
duk da cewar suna yakinne a fusace da
dukkan karfinsu da iyakar kwarewarsu tamkar
abokan gaba masu neman hallaka juna
koda sukaga sun kasa cutar da junansu da
makami sai sukaja da baya sukayi
cirko cirko suna haki da kallon junansu tamkar
zakaru kuma suna murmushi
shidai mahaifin siyama murmushin da yake yi
bana komai bane face na farin
ciki
bisa ganin abinda ya koyawa yasa ta kware a a
kansa
ainun harma ta fishi kwarewar a matsayinta na
ya mace
ai dama ance kyan da ya gaji ubansa kuma
barewa batayin gudu ba danta yayi rarrafe
babban abinda ya daurewa su yarima hulkas kai
shine
ganin yadda mahaifin siyama ya iya yin wannan
bkin gumurzu alhalin ya kasance mai hannu daya
kuma gurgun da yake dogara sanda
kwatsam sai siyama da mahaifinta suka ajiye
makamansu
a kasa gefe daya wato shi ya ajiye sandar karfen
dake
hannunsa
itakuma ta ajiye takobinta faruwar hakan keda
wuya sai sukayi alkafira
a kasa suka afkawa juna suka ci gaba da kaiwa
juna naushi da bugu
hannu da kafa sai gashi siyama tana shanye
naushi da bugu kai kace wata katumar namiji
ce ba mace ba
kuma yarinya karama yar shekara bakwai tabbas
horon da siyama ta samu zata iya gumurzu a
tsakiyar
miliyoyin dakarun yaki
ma kuma ta dade tana fafatawa tana mai taka
rawar gani
a wannan fadan hannu ma sai da siyama da
mahaifinta suka shafe kusan sa a biyu
gashi dai sun hadawa junansu jini da majina
kuma sun gaji likis amma saboda tsananin juriya
naci da
dakakkiyar zuciya sunki su daina fadan, Koda
matar mahaifin siyama taga abin ya wuce gona
da iri ta
ruga ta shiga tsakiyansu ta tsaida fadan,
a sannan ne siyama da mahaifin suka zube kasa
suna haki da dariya daga can mahaifin siyama ya
dago kai
ya dubi yarima hulkas yace shin yanzu ka gamsu
kuma ka yarda
cewar yata zata iya shiga wannan gasar
jarumtaka da za ayi a fadar birnin nan?
Koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas yayi
murmushi yace tabbas na gamsu kuma na yarda
dari bisa sari Al amin , zata iya ya kai abul
siyama idan ba zaka damu ba ina son na nemi
wata alfarma guda a wajanka
cikin mamaki mahaifin
Siyama yace yaro ina sauraronka fadi
tambayarka naji
in dai na sani zan baka amsarta, hulkas yayi
gyaran murya yace ina son ka bani
takaitaccen tarihin rayuwarka sannan ina son na
sani shin
wannan lalura da na ganka da ita ta rashin hannu
da kafa daya ta
sameka ne da girmanka ko kuwa a haka aka
haifeka
kai mutumin wace kasa ne kuma ya akayi kazo
nan
birnin domin ga dukkaln alamu kai bakone a
garin nan
bisa lura da yanayin gidanka da na gani wanda
ya banbanta da dukkan gidajen birnin nan
lokacin da yarima hulkas yazo nan a zancensa
sai jikin mahaifin siyama yayi sanyi yayi sauri ya
sunkui da kansa kas don
hawaye ne ya subuto masa
kawai saiyayi shiru baice komai ba, caraf sai
matarsa wato
ummul siyama ta dubi yarima hulkas tace ka
tambayi mijina tambayoyinda idan ya tuno da
amsarsu yake shiga
cikin tsananin bakin ciki mara misaltuwa
lallai a yanzu ba zaka sami amsar wadannan
tambayoyi
ba sai dai wani karon
koda jin haka sai yarima hulkas da barmas sukaji
sun kamu da tausayin mahaifin siyama
nan take hulkas ya tako kafafunsa yazo har
gaban mahaifin siyama ya dafa kafadarsa ta
dama da tafin hannunsa yace ka gafarceni yakai
abul siyama
inda na san cewa tambayoyina a gareka
zasu sosa maka zuciya su tuno maka da wani
abin
damuwa da ba zan gabatar dasu ba a gareka
mun barku lafiya sai gobe a filin fada zamu hadu
idan kunzo filin gasar jarumtaka
Koda gama fadin haka sai su hulkas suka juya
da nufin ya kama hannun barmas su tafi amma
sai yaji abul siyama ya dafa
kafadarsa cikin mamaki hulkas ya juyo suka
fuskanci juna yaga abul siyama yana
yi masa wani irin kallo mai nuna alamar kamar
ya sanshi kuma akwai alamun dumbin magana a
zuciyarsa wacce ya kasa amayar da ita daga
bakinsa
har abul siyama ya budi baki zaice dashi wani
abu sai kuma
ya kasa yace yaro mun gode bisa ziyarar da
kuka kawo mana amma nima ina rokon
alfarma guda daya a wajanku amma bata komai
bace face ina son kada ku sake xuwa nan
wajanmu domin a duk sa adda na kalli fuskarka
ina fama wani mugun rauni dake cikin kahon
zuciyata
abu na biyu kuma ina rokonku da kada ku bayar
da labarina ko na yata ga waninku saboda wani
babban sirri na rayuwarmu har sai bayan an
kammala gasar jarumtakar da akeyi a garin nan
koda gama fadin hakan sai abul siyama ya dafa
kafar matarsa da hannunsa lafiyayyan
ita kuma siyama sai ta tallafa kugunsa suka
taimaka masa
suka juya suka nufi cikin wannan gida nasu na
katako
koda suka isa daf da bakin kofar gida zasu shiga
sai ab
siyama ya juyo ya yiwa hulkas wani irin kallo
idanunsa
cike da kwalla take hulkas yaji tsigar jikinsa gaba
daya ta tashi kuma kaunar abul siyama ta kara
shigarsa
tamkar dama can sun kasance yan uwan juna
nan fa yarima hulkas ya kasa motsawa daga
inda yake kuma yaji kamar yace da yarima
basmar ya barshi ya kwana a nan gidansu
siyama domin ji yayi babu abinda yake so sama
da kasancewa
tare dasu
kawai sai hulkas ya bisu da kallo har suka kule a
cikin gidan
koda ganin haka sai yarima basmar ya rugo ya
kama hannun yarima hulkas ya jashi da gudu
suka bi hanyar
da zata mayar dasu can gidan sarautar
maimakon su wuce kai tsaye izuwa gidan
sarautar
sai yarima basmar ya kaisu
gidan wani dan kasuwa mai suna abul yamzin
wanda kullum sai ya kaiwa sarki hulkasu tulunan
ruwan giyar da
yake sha gami da ruwan inibi
sarki hulbasu ya aminta dari da attajirin
abul yamzin don haka ko caje tulunan
giyar sa da na inibi ba ayi a duk sa adda ya
shige dasu cikin
gidan sarautar
Tsakanin yarima basmar da attajirin abul yamzin
akwai
kyakkyawar alaka da fahimtar juna don haka sun
san sirrin
junansu sosai
da zuwan yarima basmar da hulkas gidan attajiri
sai aka sanyasu a cikin manyan tuluna guda biyu
wadanda babu komai a cikinsu aka hada da
wadanda ke dauke da ruwan giya guda goma
dana ruwan inibi goma aka
zuba su a cikin dana ruwan inibi
aka zuba su a cikin wannan amalanke aka tura
aka tafi dasu gidan sarki
a can gidan sarki kuwa hankalin gimbiya shadila
dana luzuraina ya tashi ainun
domin ganin cewa tunda su yarima suka fita
basu dawo ba har bayan tsawon sa a uku
nan da nan aka baza dakaru zuwa kowani sako
na gidan ana nemansu koda aka duba ko ina ba a
gansu ba sai hankalin
su shadila ya sake tashi
suna shirin su tura aje a sanar da sarki hulbasu
kenan saiga yarima hulkas da basmar sun shigo
cikin
turakar
koda ganinsu sai shadila ta ruga izuwa yarima
hulkas cikin
matukar farin ciki ta rungumeshi daga nan
ta jashi zuwa cikin dakin barcinta da aka bata ta
kulle kofa
ta dubeshi cikin fishi
da matukar damuw atace ina kukaje kuka buya
haka har kukayi matukar tayar mana da hankali
koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas ya
sunki
da kansa kas ya tuna cewa shifa
a rayuwarsa bai taba yin karya ba
dan haka take ya yanke hukuncin ya sanar da ita
gaskiyar duk abinda ya faru tun daga
lokacin da sukaje bangaren da ake aikin kashin
gidan
kawo sa adda aka kaisu bakin kogi sukayi wanka
sannan suka wuce gidansu siyama
hatta kamannin siyama dana mahaifinta dana
babarta sai da ya zaiyana mata har dama irin
tsananin jarumtakar baban
Siyama a matsayinsa na musaki mai
hannu daya da kafa daya sai da ya shaida mata
koda shadila taji siffifin baban siyama da yadda
yake yakinsa sai nan take zuciyarta ta
kama bugawa da karfi, ba komaine ya haddasa
hakan ba face tunowa da tsohon
masoyinta hailur wato mahaifin hulkas na
gaskiya domin
shine kadai yake da siffa da sura irin wacce
hulkas ya shaida mata yanzu kuma shine
kadai mutumin da ta san cewa yana irin salon
yakin da aka fada
cikin firgici da razana shadila ta mike tsaye
zumbur
ta kama kafadun hulkas ta girgiza dakarfi tace a
ina kaga
wannan jarumi mahaifin siyama
ya za ayi ka kaini inda yake
na ganshi
cikin alamun matukar mamaki yarima hulkas ya
dubi
shadila yace yake ummina shin kinsan wannan
mtum ne ko kuwa kun taba jin labarinsa ne a
jana wani baniba?
Koda jin haka sai shadila ta tuno da gargadin da
shardas yayi mata akan cewar
idan ta kuskura ta shaidawa hulkas cewar bashi
bane mahaifin sa na gaskiya sai ya kasheta ya
lalata dukkan rayuwarta nan take shadila ta
wayance ta
bagazar da maganar ta nunawa hulkas cewar
kawai
jarumtakar baban siyama ce ta burgeta
nan dai ta lallaba hulkas yaje ya kwanta saboda
ya
mance da komai ita kuma saita juya masa baya
a lokacin
da hawaye ya zubo mata tace a ranta
duk yadda za ayi sai nayi naje na ga mahaifin
siyama
domin na gani da idanuna ko tsohon mijina ne
ya zama nakasashshe
kai ba zata yiwu bama ya za ayi ace hailur yana
na a raye
a duniyar nan amma har ya
manta dani yayi wani auren harma ya haifi ya
alhalin yana tsananin kaunata fiye da komai a
rayuwarsa......
.
SHIN SU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI
NASARAR SAMO
SAURAN ABOKAN TAFIYARSU..??
.
SHIN SHADILA ZATA SAMI DAMAR ZUWA INDA
MAHAIFIN SIYAMA YAKE??
.
SHIN ZARGIN DA TAKEYI CEWAR TSOHON
MIJINTA NE MAHAIFIN SIYAMA GASKIYA
NE???
.
TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA
HULKAS WAYE ZAI FARA MALLAKAR HULAR
LAMSARA
.
Mu hadu A Littafin Tsatsuba Na hudu (4) Don jin
Cigaban
wannan labari

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 08, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Tsatsuba part 3Where stories live. Discover now