Shimfida

16.3K 888 327
                                    

SHIMFIDA


A hankali take saukowa daga matattakalar jirgin cikin kasaita, hannunta riqe da hannun wani kyakkyawan yaro da baxai wuce shekara hudu xuwa biyar ba, d'aya hannunta kuma tana rataye da wata yar madaidaciyar jaka mai matuqar kyau.

Sanye take cikin doguwar riga pink, mai tarin duwatsu (stones) a gaban rigar, kanta nannade yake da gyalen rigar, sai fuskarta dake sanye da niqab, duk da haka kyawun idanunta kadai xai bayyana ita din kyakkyawar gaske ce.

Ga tsayi ga diri, ta ko ina bata da makusa, kallo d'aya xaka mata kasan hutu da wayewa  suna aiki a tattare da ita.

A sanyaye ta cigaba da saukowa xuciyarta tamkar xata hudo qirjinta ta fito saboda tsananin bugawa da take, me hakan ke nufi har yanxu tana son Dr. Aiman Merah ne kome?

No... ta girgiza kanta da sauri cikin son basar da xancen xuciyarta, tana son ta qaryata xuciyarta ta hanyar kauda tunanin sa ta kowane fannin, sautin muryar Sultan taji wanda ya maido hankalinta xuwa gare sa,

'Mami na bar Ball dita acikin jirgi, ki jirani anan xanje na dauko, kafin tayi wani yunquri tuni ya fisge hannunsa daga nata yayi cikin jirgin da gudu.

Hankalinta ya tashi sosai musamman da ta tuna Aiman Merah yana d'aya daga cikin mutanen da suka shigo jirgin tare dashi.

Ta tuna sanda suke xaune cikin jirgin, tana rungume da Sultan da yayi barci, Dr merah ya shigo cikin isa da qasaitar sa, kallo d'aya tayi masa ta nemi gusar da hankalinta, Aiman yana nan yanda ta sansa ba abinda ya canxa daga gare sa na halinsa acikin shekaru hudu da tayi batare da shi ba, wannan qasaitar tana nan, wannan ji da kai da taqama duk sunanan sai Ma abinda ya qaru, haka kyawun fuskar sa ba qaramin rudata yayi ba, kallonsa take qasa da sama yana sanye cikin kayan sarauta dana qara fito dashi, tare da wata budurwa da nayi matuqar girgiza tunanin ta.

Wacece wannan? Miye tsakanin ta da Aiman Merah? Me xasu je yi qasar Jordan? Duk bata da amsar wadannan tambayoyi nata ta lumshe idanuwanta yayin da xuciyarta ta cigaba da bugawa, ko dai Aiman ya manta da ita ne, yayi aure yake rayuwa da wata mace ba ita ba?

No.. ta fada a hankali tana furzar da iska daga bakin ta a hankali, dan ma tana sanye da niqab da tuni mutane sun fahimci halin da take ciki, ta sake bude idanunta a Karo na biyu tana kallonsa, wannan Karon ya maida idanunsa da hankalinsa kan wayar sa, ta qanqame sultan a jikinta, yanda taga Aiman merah yau ya qara tabbatar mata da cewa babu ta a xuciyar shi ya manta da shafinta a rayuwar sa, taji tana qara son nisanta  kanta daga gare sa, bata son yaga Sultan ko kadan yanda kamaninsa da komai nasa da yaron ya dauko.

Wannan dalilin ne ya saka hankalin ta tashi sanda sultan ya nufi cikin jirgin, da sauri tabi bayansa dai dai lokacin Aiman ya sauko daga jirgin, yana tafiya cikin isa da qasaita tamkar baya son taka qasa, har yanxu wannan budurwar tana tare dashi.

Kasancewar ita taxo da hanxari shi kuma yana tafe yana latsa wayar hannunsa yasa basu Ankara ba suka yi Karo da juna, jakar ta dake hannunta ta subulce ta fadi haka shima wayoyin sa  ya saka lokaci d'aya.

Da sauri ta russuna qasa domin tattara kayan ba don komai ba, bata son koda wasa yaga kwayar idonta tabbas xai gane ta, idanunta suka sauka akan dalleliyar wayar sa iPad mai kyau da tsada, ta ware idanunta sosai cikin faduwar gaba ganin pic din tane bayyane a wayar tana sanye da alkyabba, baxata manta lokacin da ya dauke ta pic din ba tana da cikin sultan acikin falon mahaifiyar sa, ta tsurawa photo ido tana tuno rayuwar ta da mai wayar, shin yarima ya sauya xuciyar sa  daga qin mace ko me, yana sonta a ynxu kuwa, ita wannan da yake tare da ita mecece alaqarta dashi, da sauri ta dauki jakarta jin muryar sultan na kiran 'Mami.

Har yanxu Aiman na tsaye yana kallonta, baxaka tantance yanayin fuskar sa ba, bacin rai ko sabanin haka,tun lokacin da ya kula ta tsurawa photon wayar sa kallo, miye nata da photon ko kuma me take kallo acikin photon, me yiwuwa ta San ta ne? Dam xuciyar sa na buga,

Affiya ta dago daga tsugunnen da take batare da ta kalle sa ba ta miqawa budurwar dake tare dashi wayoyinsa sannan ta juya da sauri ta bar gurin, daukar sultan tayi jikinta na rawa ta bar gurin kada tayi wata katobarar da xata sanya yarima ya fahimci ko ita wacece.

Tsananin mamakin ta ya hana Aiman motsi, meyasa xata baiwa ilham wayarsa bayan ta san a hannunsa ta fadi, ya tabe bakinsa wannan ba damuwar sa bane can ta matse mata yaga alamar bata cikin nutsuwar ta daga yanda yaga jikinta yana rawa gashi garin sauri ita tabar tata wayar a qasa bata dauka ba, ya waiga a hankali yana kallon airport din babu ta babu alamarta, har xai juya ya tafi sai kuma yaji yana son daukar wayar kada wani ya dauka daban meyiyuwa akwai wani abu mai muhimmanci a wayar qila xasu sake haduwa ya bata wayar.

Meyasa kake son ku sake haduwa, wata xuciyar ta tambayeshi da sauri ya kauda wannan tunanin ta hanyar yiwa ilham alamar da ta bashi wayar dake qasa batare da yayi magana ba.

Ilham ta sunkuya ta dauko ta hada da nashi ta bashi, ya karba ya soma tafiya a hankali yana juya wayar a hannunsa cikin yatsina fuska kamar wanda ya dauki kashi a hannun sa.




MULKI KO SARAUTA 2 zai iya sauka kowane lokaci idan na sami dama, is not free na kudi ne game buqata.

Follow and Vote for more.

Thanks All❤

MULKI KO SARAUTA 2 Where stories live. Discover now