33 An Daura

2.6K 436 92
                                    

Tun karfe takwas na safe jama'ar Kubaisu suka taso domin daurin auren Yerima Bukar da Gimbiya Hafsa.

Masarautar Bilbah kuwa ta cika taf da al'umma sai hidima ake yi. Masu bangaren abinci ana yi, bangaren gyaran gida ma ana yi. Kafin karfe goma an gama komai sai jiran isowar mutan Kubaisu a daura aure karfe sha biyu na rana.

A bangaren amarya kuma ta sha ado cikin farin material da ya ji duwatsu, irin handmade din nan mai tsada. Sai aka yafa mata farin mayafi shi ma mai duwatsu. Banda kamshi babu abin da take badadawa. Irin fara'ar nan ma da aka san amare da ita babu a bangaren Hafsa. Ta sha mur a ganin ta dariyarta za ta kara jawo raini tsakaninta da na kasa da ita. Ana cikn haka suka ji kararrawa alamun Sarkin Kubaisu da tawagarshi sun iso. Hannu Hafsa ta sa ta dafe zuciyarta tana murmushi, alamun ta ji dadin isowarsu.

Minti talatin da isowarsu aka isar da sadakin Hafsa ga maimartaba Sarki Sani, jajayen rakuma guda biyu da doki daya, sai dunkulen zinari manya guda biyu. A take aka daura auren Gimbiya Hafsa da Yerima Bukar. Babu inda shelar daurin auren nan ba ta isa ba a cikin gidan.

A tare Kursiyya da Hafsa suka mike jin sunan wanda aka ambata a matsayin ango. Ba wuri daya suke ba amma tamkar tare suke aikata komai. Tare zukatansu ke kitsa musu abubuwan da suka kasa gasgata su.

Wani irin nauyi Hafsa ta ji a kasan ruhinta. A take idanuwanta suka fara barazanar kawo ruwa. Ta kokarta nayar da su cikin gaggawa gudun kar kaskantattun mutanenta su fahimci wani abu. Kafin ta koma ta zauna ta ji takun Zabbau da karfin gaske ta iso gabanta. "Ranki shi dade, Fulani Kursiyya na son ganin ki da gaggawa..." Tun ba ta karisa rufe bakinta ba Hafsa ta fara ajje takunta. In da a ce ba zureren takalmi ba ne a kafarta da gudu za ta fice saboda tsananin zakuwa da ta yi ta gana da mahaifiyarta. Tana son jin duminta a daidai wannan lokacin. Tana son gamayyar kirazansu, ta yi musayar numfashi da Fulani Kursiyya ko za ta samu sassaucin zafin da take ji a kasan zuciyarta. Tun ba ta karisa ficewa daga dakin ba takalmin ya turgude ta ta fadi kasa. Runtse idanuwanta ta yi, tana jin kunya na gama lullube ta. Wai yau ita ce ta yi irin wannan faduwar a gaban idon mutanen da ta raina. Ba ta iya tashi ba sai Zabbau da ta tagaza mata ta mike.

"Ki taka a hankali shalelen Bilbah." Zabbau ta fada tana rike da ita har suka isa dakin Kursiyya. Duk masu rusunawa suna kwasar gaisuwa babu wanda Hafsa ta kalla.

Suna isa cikin dakin ta saki hawayen da ke ta kunno kai tun sadda ta ji sunan wanda aka daura mata aure da shi. Da sauri ta fada jikin Kursiyya tare da fasa kuka mai karfi. "Umma ki ce min mafarki ne nake yi ba gaske ba. Don Allah kar ki furta ba da Yerima Abu Sufyan aka daura min aure ba. Wallahi shi nake so. Da shi kadai zan iya rayuwar aure. Ban san wanda suke magana ba. Ban san da wanda aka daura min aure ba."

Bubbuga bayanta kawai Kursiyya ke yi. Ita kanta mamakin wannan abu take yi. Ta yaya ma za a yi wannan danyen aiki?  Don me za a ci amanar 'yarta?  Ta kuta da karfi. "Zabbau! Maza-maza ki je ki ga Khalili. Ki ce da shi ya sanar wa Waziri ina son ganin maimartaba da gaggawa."

"An gama ranki shi dade." Zabbau ta fada hade da kokarin fita. Har ta isa bakin kofa kuma ta juyo ta kalli Kursiyya. "Fulani shi kanshi Khalili ganinshi zai yi wuya. Masarautar nan ta yi cikar da ban taba ganin irinshi ba. Hanyar da za ta sada ni da farfajiyar daurin auren kanta wahala ce, bare in ce zan nemi wani. Ko za ki yi hakurin zuwa a dan jima kafin nan taron mutanen ya rag...?"

Tsawar da Kursiyya ta daka mata ne ya sa ta gaggauta yin shiru. "Ji wata banzar magana da kike kawo min Zabbau!  Kina ji ana fadin da an yi sallar azahar za a tafi da amarya kuma kina cewa in bari sai an rage?  Ya kike son in yi ne?  Ki kalli yadda Hafsa ke kuka mana. Idan har ban ga maimartaba yanzu ba akwai matsala. Har za a tafi da amaryar ma ban samu mun magantu ba."

GIMBIYA SA'ADIYYA (Aljana Ko Fatalwa?)Where stories live. Discover now